2025-12-04@00:39:45 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4852
«Yan sanda sun»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi da tokwaransa na kasar Omman Badr Al-Busaidi sun tattauna a birnin Muscat babban birnin kasar Omman a jiya Lahadi, inda bangarorin biyu suka tabo al-amura da suka shafi halin da ake ciki a yankin musamman HKI da kasashen yankin, da kuma dangane da kara dankon zumunci tsakanin kasashen biyu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kasar Ommam ta taka rawar a zo a gani a kokarin kasar Iran na kyautata dangantaka da kasashe makobta da kuma shiga tsakanin Iran da kasashen yamma dangane da shirin kasar na makamashin Nukliya. Ziyarar da Aragchi ya kai Muscat dai yana daga cikin shirin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran na tuntubar kasashen makobta...
Yayan kungiyar yan ta’adda ta ‘the Islamic State West African Province (ISWAP) ta bada sanarwan kamawa da tsare yan mata 13 a karamar hukumar Askira-Uba na jihar Borno a jiya Lahadi. Jaridar Daily Trust ta Nageriya ta nakalto Abdullahi Askira dan majalisar dokokin jihar Borno mai wakiltan Askira yana tabbatar da labarin ya kuma kara da cewa ISWAP ta kama wadan nan yan mata wadanda suke da shekaru tsakanin 13-19 ne a lokacinda suke aiki a gonakinsu a gundumar Mussa na karamar Hukumar ta Askira. Jaridar ta kara da cewa wannan satar yan mata da yan makaranta ya biyo bayan irinsu da suka yi a makarantar mata ta Maga a karamar hukumar Wasagu na jihar Kebbi da kuma na makarantar...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A shekarar 2014, bayan tashin hankalin da ya biyo bayan sace ɗaliban Chibok da kuma yawaitar hare-hare kan makarantun yankin Arewa maso Gabas, gwamnatin tarayya tare da haɗin gwiwar ƙasashen duniya ta ƙaddamar da wani muhimmin shiri mai suna Safe School Initiative. Manufar wannan shiri ita ce tabbatar da cewa dalibai suna iya zuwa makaranta cikin tsaro ba tare da fargabar hare-hare daga ‘yan ta’adda ko ‘yan bindiga ba. NAJERIYA A YAU: Ba A Yi Ma Nnamdi Kanu Adalci Ba- Emmanuel Kanu DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne akan wannan shiri da...
Shugaban kasan Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin janye jami’an ƴansanda dake gadi ko rakiyar manyan mutane domin mayar da su aikin tsaro. Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar ya fitar Mr Bayo Onanuga, da yammacin wannan Lahadi, ya ce daga yanzu za’a rika tura jami’an ƴansanda ne gudanar da ayyukan ƙasa. Tinubu ya bayar da umarnin ne yayin ganawar da ya yi da shugabannin tsaron ƙasar da suka haɗa da rundunar sojin sama, da na ƙasa da na ruwa da Darakta Janar na ma’aikatar tsaro ta DSS da kuma Sufeto Janar na ƴansanda Kayode Egbetokun. Sanarwar ta ce, daga yanzu duk mutumin da ke son jami’an tsaro su yi gadinsa to ya nemi...
Ana zargin wasu ’yan bindiga da kashe wani fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Muhammad Bakoshi, lokacin da suka kai hari garin Zalau da ke Ƙaramar Hukumar Toro a Jihar Bauchi. Bayan kai hari, sun sace ɗaya daga cikin matansa, Hannatu Muhammad. Tinubu ya dakatar da ’yan sanda daga tsaron manyan mutane a Najeriya An ceto mutum 38 da aka sace a cocin Kwara — Tinubu Wani mazaunin yankin, Shamsuddeen Hashimu Zalawa, ya shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun je gidan mutumin da tsakar dare. Ya ce sun dinga harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin firgici. Ya ƙara da cewa sun nufi gidan Bakoshi kai-tsaye, wanda hakan ya sa wasu ke zargin ko turo su aka yi....
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bai wa ’yan sanda umarnin daina tsaron manyan mutane a faɗin Najeriya. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi. ’Yan sanda sun ƙaryata jita-jitar kai wa coci hari a Gombe ’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda 5 a Bauchi Onanuga, ya ce daga yanzu ’yan sanda za su mayar da hankalinsu ne aikin kare al’umma da yaƙar ’yan ta’adda. An ɗauki wannan mataki ne a wani taron tsaro da aka gudanar a Abuja, wanda manyan shugabannin tsaro suka halarta, ciki har da shugabannin ’yan sanda, sojin sama, sojin ƙasa da hukumar DSS. Sabon tsarin ya nuna cewa duk wani babban mutum da yake buƙatar tsaro dole ne,...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta ce labarin da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta na kai wa cocin ECWA da ke Kashere hari, ba gaskiya ba ne. Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ne, ya bayyana haka, inda ya ce sun bincika tare da gano cewar jita-jita ce. Ya ce DPO na Pindiga da shugaban ofishin ’yan sanda na Kashere, sun tuntuɓi wani dattijo da ya halarci cocin domin yin addu’a a ranar Lahadi. Dattijon ya shaida musu cewa babu wani abu da ya faru, kuma ’yan sanda suna harabar cocin tun safe a domin kula da sha’anin tsaro kamar yadda suka saba. Rundunar ta ce yaɗa irin wannan jita-jitar na iya tayae da hankalin jama’a. Ta kuma ce ta...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta tabbatar da mutuwar wasu jami’anta guda biyar a ƙauyen Sabon Sara da ke Ƙaramar Hukumar Darazo, sakamakon harin da wasu ’yan bindiga suka kai. Kakakin rundunar, CSP Ahmed Wakil ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranae Lahadi. An ceto mutum 38 da aka sace a cocin Kwara — Tinubu Ɗalibai 50 da aka sace a Neja sun kuɓuta — CAN “‘Yan sanda biyar sun rasu, biyu sun jikkata, amma an yi nasarar kashe wasu daga cikin ’yan bindigar a ƙauyen Sabon Sara, Ƙaramar Hukumar Darazo, a jihar Bauchi.” Wakil, ya ƙara da cewa, “Ma’aikatanmu suna jajircewa kuma sun samu nasarar kashe wasu daga cikin ’yan bindigar yayin musayar wuta.” Ya bayyana ’yan...
A Isra’ila Dubban masu zanga-zanga ne suka gudanar da wani babban gangami a Tel Aviv don neman a gudanar da bincike na gaskiya kan harin ba zata na ranar 7 ga Oktoba da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta kai. Masu zanga-zangar adawa da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu sun taru, a dandalin Habima da ke Tel Aviv, suna sake nanata bukatarsu ta kafa kwamitin bincike da aka dora wa alhakin tabbatar da gaskiya da kuma cikakken bincike kan harin na Hamas (Operation Al-Aqsa Storm). Tsohon Firaministan Isra’ila Naftali Bennett, madugun ‘yan adawa Yair Lapid, da MK Benny Gantz, Gadi Eisenkot, da Yair Golan suma sun halarci taron. Masu shirya taron a cikin wata sanarwa sun ce yayin da majalisar ministocin...
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya yi kira ga shugabannin kasashen duniya da suke taro a birnin Johannesburg na kasar Afirka Ta Kudu da su warware matsalar rashin daidaito a cikin harkokin kasuwanci a tsakanin kasashe. Babban magatakardar MDD wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron na G 20 ya yi Ishara da gibin kasuwanci da ake da shi a tsakanin kasashen da su ka ci gaba da masu tasowa wanda ya kamata a san yadda za a magance shi. Antonio Gutrres ya kuma ce: “Wani abu guda daya wanda zan iya bayar da tabbaci a kansa shi ne cewa ofishin babban magatakardar MDD zai yi duk abinda zai iya yi domin yin gyara a cikin rashin daidaito da...
Zabebben magajin garin birnin NewYork na kasar Amurka Zohran Mamdani, a haduwarsa ta farko da shugaban kasar Amurka Donal Trump a birnin Washington ya bayyana cewa HKI tana aikata kissan kiyashi a gaza, sannan mutanen NewYork basa son ganin gwamnatin Amurka tana amfani da kudaden harajin da suke biyu wajen tallafawa gwamnati wacce take aikita kissan kiyashi a duniya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto magajin garin birnin NewYork musulmi na farko na cewa yana son shugaban Trump ya karkata kudaden da yake kashewa kan sojojin Amurka wadanda suke yake-yaken da masa da wani amfani ga mutanen kasar Amurka zuwa magance talaucin da Amurka suke fama da shi a cikin gida musamman masu kwana a waje a...
Mai ba wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya gana da Sakataren Yakin Amurka, Pete Hegseth, a Washington, inda gwamnatin Trump ta nuna damuwarta kan karin hare-haren da ake kai wa mabiya addinin Kirista a Nijeriya. Hegseth ya tabbatar da ganawar a shafinsa na X, yana mai cewa bangarorin biyu sun tattauna kan “mummunan tashin hankalin da Kiristoci ke fuskanta,” tare da bayyana cewa Amurka na aiki da gaggawa da Nijeriya wajen rage hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi. Ganawar ta gudana ne a daidai lokacin da Amurka ke kara nuna damuwa game da tsaro a Arewaci da tsakiyar Nijeriya, inda Boko Haram da ISWAP da kungiyoyin ƴan bindiga ke ci gaba da kai hare-hare a kauyuka, da...
Sojojin Isra’ila sun kashe wasu yara falasdinawa guda biyu a yankin gaza duk da yajejejeniyar dakatar da bude wuta da a sanya hannu akai, da ta fara aiki a farkon watan oktoba kamar yadda hukumar unicef tayi gargadi akai. Tun da aka rattaba hannun kan yarjejeniyar dakatar da bude wuta a ranar 11 ga watan oktoba, akall yara dubu 67 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren isra’ila a yankin Gaza, yayin da wasu da dama kuma suka jikkata, wannan shi ne kididdigar da aka fitar dake nuna cewa kullum isra’ila na kashe yara biyu a kullum Kakakin hukumar kula da kana nan yara na majalisar dinkin duniya yayi gargadi game da matsanancin halin dubban daruruwan yara falasdinawa za su shiga...
Majalisar Dattijai ta nuna damuwa kan tabarbarewar yanayin tsaro a kasar sannan ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta amincewa da daukar akalla matasa 100,000 cikin rundunar sojoji domin karfafa tsarin tsaro na Nijeriya da yake fuskantar kalu bale. ‘Yan majalisar sun kuma yanke shawarar kafa kwamitin musamman domin bincikar yadda aka yi amfani da kudaden da aka ware shekaru da dama don Shirin Makarantu Masu Tsaro (Safe School Programme), a yayin da ake sake nuna damuwa cewa makarantun Nijeriya na ci gaba da kasancewa cikin hadari, inda a baya-bayan nan aka sace ‘yan mata a Jihar Kebbi. Wadannan kudurori sun biyo bayan tayin da Sanata Abdullahi Yahaya (APC, Kebbi North) ya gabatar, wanda ya yi...
Daga Aminu Dalhatu Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Zamfara ta ce ta samu nasarar ceto mutune 25 da aka yi yunkurin sacewa, bayan wani hari da ’yan bindiga suka kai wa kauyen Kuraje da ke yankin Damba a Karamar Hukumar Gusau. Wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya fitar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren Juma’a 21 ga watan Nuwamban 2025, da misalin karfe 10 saura kwara, lokacin da gungun ‘yan bindiga dauke da makamai suka mamaye yankin, suna harbe-harbe tare da tasa keyar mata 10 da yara 15 domin tafiyada su. Sanarwar ta ce bayan samun kiran gaggawa, tawagar sintiri ta ’yan sanda daga sashen Damba da Sashen Ayyuka...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, ta daƙile wani hari da ’yan bindiga suka kai wa al’ummar Kuraje da ke gefen birnin Gusau. Wasu gungun ’yan bindiga, ɗauke da makamai ne, suka kutsa cikin ƙauyen suna harbi, lamarin da ya jefa mazauna Kuraje da maƙotan ƙauyukan cikin tashin hankali. Gwamnatin Tarayya ta musanta jita-jitar rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya Mutane 315 ne suka ɓace bayan hari a makaranta Neja A yayin harin, sun yi awon gaba da mata 10 da yara 15. Kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya ce ’yan sanda sun ɗauki mataki bayan samun kiran gaggawa. Ya ce tawagar haɗin gwiwa daga sashen Damba, Sashen Ayyuka da kuma Rundunar Tsaron Al’umma (CPG) sun isa ƙauyen cikin gaggawa. Sun...
A ranar Alhamis da dare ne janar Thiani wanda ya karare kasar ta Nijar a cikin motoci a wani ran gadi da shi ne irinsa na farko da wani shugaban kasar ya yi, ya sami kyakkyawar tarba a wurin mazauna babban birnin. Kafar wasta labaru ta “Afircanews” ta nakalto wani dan fafutuka mai suna Zakari Bizo yana nuna jin dadinsa da komawar shugaban kasar sannan ya kara da cewa, batun gina kasa da hadin kan al’umma shi ne abinda suke son ganin ya tabbata.” A tsawon lokacin da yake rangadin, shugaban kasar ta Nijar ya yi kira ga al’umma da su zama masu tsayin daka,su kuma sojoji su kasance masu zama cikin fadaka da sa ido. Ana daukar wannan ziyarar...
Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin rufe makarantu arba’in da daya saboda matsalolin tsaro. A wata takardar sanarwa da aka aikewa dukkan Shugabannin makarantu, wadda Daraktan Makarantu Manyan Sakandare na Ma’aikatar Ilimi ya sanya wa hannu, gwamnati ta bayyana cewa sakamakon ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a wasu sassan ƙasar nan da kuma buƙatar kare duk wani yunkurin hari, Ministan Ilimi ya amince a rufe makarantun nan dltaje. Ga jerin makarantu da abin ya shafa: Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Minjibir, Jihar Kano Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Ganduje, Jihar Kano Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Zariya, Jihar Kaduna Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Kafanchan, Jihar Kaduna Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Bakori, da wacce ke Bwari, Abuja. Kwalejin Fasaha...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau. Shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka shafi siyasa, tattalin, arziki, zamantakewa tsaro da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au /////… Madalla, masu sauraro zamu fara shirimmu da labarimmu na farko wanda yake cewa majalisar gwamnoni a hukumar IAEA ta amince da wani kuduri na takurawa JMI a taron da ta yi a ranar Alhamis 22 ga watan Nuwamban da muke ciki. Kuduri wanda kasashen E3 ko Traiko na...
Kakakin majalisar dokokin kasar Iran mohammad Bhakir Qalibaf ya bayyana cewa makiya JMI sun sawya salon yakaar kasar kamar yadda suka saba, a halin yanzu sun fibada karfi kan takurawa tattalin arziki da rikita al-adu da kuma zamantakewa tsakaninmutanen kasar. Kamfanin dillancin labaran IP nakasar Iran ya nakalto Qalibaf yana fadar haka a jiya jumm’a a wani taro na mayakan sa kai a nan birnin Tehran a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa, da wannan dalilin ne gwamnatin kasar ta ke karfafa kira ga mutanen kasar su kiyaye hadin kan da suke da shi, su kara dankon zumunci da ke tsakanin kabilu da bangarorin kasar don hana makiya cimma manufofinsu a wannan yakin da ke yi da kasar. Yayi...
Wani tsohon ma’aikacin hukumar leken asiri ta CIA ta kasar Amurka John Kiriakou ba ce a yakin kwanaki 12 tsakanin HKI da JMI, Isra’ila ta yi barazanar jefawa JMI makaman Nukliya idan har Amurka bata kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin Nukliya na kasar Iran ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya nakalto Mr John Kiriakou yana fadar haka a cikin makon da ya gabata. Ya kuma kara da cewa saboda wannan barazanar ce gwamnatin shugaba Trump ta kaiwa cibiyoyin makamashin Nukliya na kasar Iran wadanda suke Fordo, Natanz da kuma Esfahan. Ya ce shugaban yana ganin hare-haren da ya kaiwa cibiyoyin yafi sauki idan an kwatanta da makaman nukliya wadanda HKI ta yi barazanar zata yi amfani da...
A ranar Alhamis da ta gabata ce karamin kwamiti mai kula da al-amuran nahiyar afirka a majalisar dokokin kasar Amurka ya bude tattaunawa dangane da zargin da shugaban kasar Donal Trump yake yin a cewa ana kashe kiristoci a tarayyar Najeriya fiye da duk wata kasa a duniya. Wanda hakan ya say a yi barazanar daukar matakan soje idan akwai bukatar haka don kawo karshen kissan. Jaridar Premium times ta nakalto Chris Smith dan majalisan da ya jagoranci taron yana fadar cewa zargin Trump gaskiya ne kuma shi a karan kansa ya kai ziyara tarayyar Najeriya har sau uku a baya inda sakamakon ya tabbatar da hakan. Sannan Bishop Wilfred Anagbe daga jihar Benue wanda ya halarci taron ta kafar...
Shugaban kasar Ukrain Volodymyr Zelensky ya fito fili ya bayyana cewa bai amince da sabon shirin shugaban kasar Amurka Donal Trump na kawo karshen yaki a kasarsa. Ya kuma bayyana cewa kasar Ukraine tana cikin mafi munin hali a tarihin kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa shugaban kasar Amurka yana takurawa kasarsa ta amince da al-amura guda 28 da ya gabatar wanda a fadinsa zai kawo karshen yakin shekari kimani 3 wanda kasarsa take fafatawa da kasar Rasha. Labarin ya kara da cewa daga cikin al-amuran da shugaban ya gabatar a wannan shirin kawo karshen yaki a Ukraine sun hada da amincewa da zaben...
Yan wasan kasar Iran sun kammala gasar wasannin sada zumunci na kasashen musulmi wanda aka kammala a birnin Riyad na kasar Saudiya tare da lambobin yabo har 81. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan ya nuna cewa kasar Iran na daga cikin kasashen musulmi wadanda suke da kwarewa a wasannin motsa jiki daban daban. Labarin ya kara da cewa an gudanar da wasannin ne daga ranar 6 ga watan Nuwamba zuwa 21 ga watan. Tare da fara wasu wasannin daga ranar 3 ga watan. Kasar Saudiya wacce ta dauki bakwancin wadan nan wasannin motsa jiki ta sami nasarar tattara yan wasannin motsa jiki na kasashen musulmi a duniya a cikin kwanaki kima 20 da suka...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar Jigawa ta tabbatar da bada cikakken goyon bayanta ga Kwalejin Aikin Noma ta Gwamnatin Tarayya da ke Kirikasamma. Gwamna Umar Namadi ya bayar da wannan tabbaci ne lokacin da ya karɓi tawagar gudanarwar kwalejin ta farko, ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Dr. Muhammad Yusha’u Gwaram, yayin ziyarar girmamawa da suka kai Gidan Gwamnati da ke Dutse. Ya taya shugaban kwalejin da tawagarsa murna, inda ya bayyana nadin nasu a matsayin tarihi kuma mai matuƙar muhimmanci. Malam Umar Namadi ya ƙara da cewa kafa sabuwar cibiyar ilimi aiki ne babba, yana mai bayyana tabbacin cewa mutanen da aka zaba don fara gudanar da kwalejin za su taka rawar gani. “Kafa sabuwar cibiyar ilimi ba abu ba ne...
Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) sun nuna damuwarsu kan sace malamai da ɗaliban makarantar St. Mary’s da ke Ƙaramar Hukumar Agwara, a Jihar Neja. Sun ce wannan lamari babban hatsari ne ga rayuwar yara da makomar ilimi a yankin Arewa baki ɗaya. DSS ta mayar da Nnamdi Kanu gidan yarin Sakkwato Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna Kebbi Shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce wannan hari abin takaici ne wanda ba za a lamunta da shi ba. Ya jaddada cewa makarantu wajibi ne su kasance wuraren karatu da tsaro, ba wuraren tashin hankali ba. Gwamna Yahaya ya ce Arewa ba za ta lamunci koma baya ba wajen rage yawan...
’Yan bindiga sun kai hari makarantar Katolika ta St. Mary da ke cikin yankin Papiri a ƙaramar hukumar Agwara ta Jihar Neja, sannan suka sace ɗalibai da malaman da ba a kai ga tabbatar da adadinsu ba. Har zuwa yanzu dai babu cikakkun bayanai a kan harin, amma majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa an yi awon gaba da ɗalibai da dama yayin harin da aka kai makarantar. ’Yan bindigar da suka sace masu ibada a cocin Kwara sun nemi a ba su N3bn kafin sakin su Sace ɗalibai: Tinubu ya bai wa Ministan Tsaro umarnin tarewa a Kebbi Wata majiya daga ɗaya daga cikin coci-cocin Katolika a jihar ta tabbatar da lamarin, tana mai cewa har yanzu makarantar na...
’Yan bindigar da suka yi garkuwa da masu ibada a cocin Christ Apostolic Church da ke Eruku, a jihar Kwara, sun nemi Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansar kowanne mutum da suka kama. A cewar Faston cocin, Lawrence Bamidele, tsakanin mutane 30 zuwa 35 aka yi garkuwa da su a daren Talata lokacin da aka kai musu mummunan hari suna tsaka da ibada a cocin. Sace ɗalibai: Tinubu ya bai wa Ministan Tsaro umarnin tarewa a Kebbi Muna roƙon Tinubu ya ƙawo ƙarshen taƙaddamar gwamnati da ASUU — Ɗalibai Majiyoyi daga iyalai da shugabannin al’umma sun tabbatar a ranar Alhamis cewa masu garkuwar sun fara kiran ’yan uwan waɗanda aka sace ta hanyar amfani da wayoyinsu. Sakataren cocin, Josiah...
Daga Ali Muhammad Rabi’u ‘Yan bindigar da suka sace masu ibada 38 a Cocin Christ Apostolic Church (CAC), Eruku da ke ƙaramar hukumar Ekiti a Jihar Kwara sun nemi kudin fansa na Naira miliyan 100 kan kowane mutum daya da suka sace. Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa masu garkuwan sun fara kiran iyalan waɗanda aka sace a cocin. Shugaban al’umma kuma Olori Eta na Eruku, Cif Olusegun Olukotun, wanda mutane huɗu daga cikin danginsa suka kasance cikin waɗanda aka sace, ya tabbatar da hakan ga ’yan jarida. Olukotun ya ce yana cikin coci tare da mutane biyar na danginsa lokacin da lamarin ya faru, inda ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin yaran da yake kula da su ya tsere...
Daga Bello Wakili Shugaba Bola Tinubu ya umurci Ministan Tsaro, Alhaji Bello Matawalle, da ya koma Jihar Kebbi biyo bayan sace dalibai ’yan mata 24 a jihar. An umurci Matawalle, wanda tsohon gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a jihar domin sa ido kan ƙoƙarin da ake yi na kubutar da ɗaliban da aka sace. ’Yan bindiga sun sace ɗalibai mata 24 na Makarantar Sakandare ta ’Yan Mata da ke garin Maga, Jihar Kebbi, da misalin ƙarfe 4 na asubar ranar Litinin. Matawalle, wanda ake sa ran zai isa Birnin Kebbi a ranar Juma’a, ya samu ƙwarewa wajen fuskantar matsalar ’yan fashi da garkuwa da mutane a lokacin da yake gwamnan Jihar Zamfara daga shekarar 2019 zuwa 2023. Idan...
Daga Usman Muhammad Zaria Daliban makarantu daga jihohin Arewa maso Yamma da suka hada da Kano, Jigawa da Katsina sun yi kira ga masu ruwa da tsaki da su samar musu da tsaro, ingantaccen kiwon lafiya, da taftataccen ruwan sha. Daliban sun yi wannan kiran ne yayin bikin Ranar Yara ta Duniya da aka gudanar a Kano, wanda Hukumar Kula da Yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ta shirya. Haka zalika ɗaliban sun nemi a mayar da yaran da ba sa zuwa makaranta domin samun ilimi mai inganci. Haka kuma, sun buƙaci a aiwatar da dokokin kare haƙƙin yara tare da ba da dama ga daidaito tsakanin jinsi, musamman a fannin ilimin ’ya’ya mata. Bugu da ƙari, sun koka...
Daga Abdullahi Shettima Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya karɓi Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda suka tattauna kan manyan muhimman abubuwan ci gaban jihar musamman a fannoni na noma, ababen more rayuwa da tsaro. A yayin ganawar, Gwamna Uba Sani ya bayyana godiyarsa ga Shugaban Ƙasa bisa goyon bayan da gwamnatin tarayya ke bai wa Jihar Kaduna, musamman wajen ci gaban harkokin noma da sarrafa amfanin gona. Ya ce kafa Special Agro-Industrial Processing Zone (SAPZ) da African Quality Assurance Centre (AQAC) ya ɗaga martabar jihar a matsayin jagora wajen ci gaban sarkar samar da kayayyakin noma da kuma faɗaɗa damar fitar da su ƙasashen waje. Shugaban Ƙasa ya yaba da wannan...
Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya reshen Jihar Kebbi ta tabbatar da sace dalibai ashirin da biyar daga Makarantar Sakandare ta ’Yan Mata ta Gwamnati da ke Maga a Ƙaramar Hukumar Danko/Wasagu. Lamarin ya faru ne a daren Litinin da misalin ƙarfe 4 na safe a lokacin da ƴan bindiga suka mamaye makarantar, inda suka kashe wani ma’aikaci ɗaya tare da jikkata wani. A cewar wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan, CSP Nafi’u Abubakar Kotarkoshi ya sanya wa hannu, maharan ɗauke da makamai masu ƙarfi sun kutsa makarantar inda suka yi musayar wuta da jami’an tsaro da ke bakin aiki. Duk da ƙoƙarin jami’an, an ruwaito cewa maharan sun haye katangar makarantar suka kuma yi awon gaba...
Shugaban kasar rasha vladmir putin ya bayyana cewa ba zamu ja baya daga ayyukan soji da muke yi a kasar Ukrain ba, bayan rahoton da fadar kremlin ta fitar dake nuna cewa dakarunta sun kutsa cikin kasar ukrain suna kusa da birnin Kupiansk mafi mahumimmanci a kasar A loakcin ziyara da babban kwamanda kasar rasha ya kai a wajen da ke cikin yakin Ukrain putin yace yanzu haka dakarun rasha sun kewaye rundunoni 15 na kasar Ukrain a garin Kupiansk, za su bada dama ga sojojin kasar su mika makamansu kuma su yi saranda Kakakin fadar kremlin Dmitry peskov ya fadi cewa putin ya karbi rahoto game da karbe kula da ikon garin Kuoansk . Wannan bayani yazo ne bayan...
Rahotanni sun bayyana cewa a zaman da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya yayi a baya bayan nan yayi kira a dauki matakin gaggawa don kawo kareshen yaduwa ayyukan ta’addanci a kasashen yammacin Afrika da kuma yankin sahel, yana gargadin cewa yankin na so ya zama cibiyar tsattsauran raayi da rikice- rikice Anasa bangaren babban sakatare janar din majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya bayyan cewa yanayin da yankin sahel da sauran kasahen dake makwabtaka da shi kullum yana kara yin tsananin sosai, kamar kai hare-haren ta’addanci da kuma matsalar da ta shafi mai a kasar mali suna mummunan tasiri a yankin. Haka zalika yayi gargadin cewa kungiyoyin masu iykirarin jihadi masu yankurin kafa daular musulunci a yankin sahara ISGS...
Rahotanni daga birnin Tehran sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi ya fadawa masana tattalin arziki cewa Tehran a shirye take na yi duk wata yarjejeniya idan dai za’a tsage gaskiya, kuma iran ta kara karfafa dakarunta wajen kasancewa cikin shirin ko ta kwana musamman ma bayan yakin kwanaki 12 da aka kallafa mata. Wadannan kalaman sun nuna kyakkyawar niyar iran na tattaunawa sai dai bata yarda da shirin Amurka na tattaunawa kai tsaye ba, bugu da kari dabarun siyasar iran shi ne ta amince da bin hanyoyin diplomasiya amma kuma tana ci gaba da nuna adawrta ga isra’ila Janyewar da Amurka ta yi a yarjejeniyar JCPOA a shekara ta 2018 tasa an shiga zaman dar-dar don...
Kafofin yada labarai na duniya sun mayar da hankali kan taron majalisar shugabannin kasashe mambobin kungiyar Shanghai SCO na 24 da aka gudanar kwanan nan a birnin Moscow na kasar Rasha. Fira ministan kasar Sin Li Qiang ya yi kira ga kungiyar SCO da ta aiwatar da shawarar inganta tsarin shugabanci na duniya da kasar Sin ta gabatar, da karfafa kungiyar SCO a bangaren hadin kai da harkoki da kuma tasirinta. Shekaru 24 da suka wuce bayan kafuwar kungiyar SCO, a karkashin jagorancin ruhin Shanghai, an samu habakar abotan kungiyar, da kara ingancinta, shi ya sa ma ta zama kungiyar yanki mafi girma a duniya, wadda ta kare muradun kasashe mambobin kungiyar, ta kuma inganta zaman lafiya da ci gaban...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esmail Baghaei yayi tir da shigar isara’ila kasar Siriya ba bisa kaida ba, yayi gargadin cewa ci gaba da kai hare-hare da fadada siyasarta ta mamaya babbar barazana ce ga zaman lafiya da tsaron yanki. Haka zalika tahren ta yi gargadin cewa matakin baya bayan nan da isra’ila ta dauka wani bangare ne na nuna tsangwama da kai hare hare da aka dade ana yi ta sama da kasa da kuma mamaye kudancin Syria da zai iya jefa yankin cikin mawuyacin hali. Fira ministan isra’ila banjamin na tanyaho da wasu manyan jami’an gwamnati da suka hada da ministan harkokin wajen da na yaki sun shiga cikin kasar siriya kuma sun zarta iyakar aka yi...
A zana da kotun ta yi a birnin Abuja a yau Alhamis, mai shari’a James Omotosho ya yanke hukuncin cewa mai shigar da kara ya gabatar da kwararan dalilai akan yadda jawaban da Kanu ya rika watsawa su ka ingiza mambobin haramtacciyar kungiyar ” IPOB” su ka kai wa jami’an tsaro hari a yankin kudu maso gabashin kasar. Mai shari’ar ya bayyana Kanu a matsayin wanda ya shirya ayyukan da su ka kai ga yin ta’addanci. A 2009 ne dai Kanu ya fara watsa shirye-shiryen Rediyo Bi’afara daga London, da yake Magana da ‘yan kungiyarsa ta IPOB. Tun da fari dai Alkalin ya bayar da umarnin a fitar da Nnamdi Kanu daga cikin kotun sabdoa abinda ya kira rashin da’a...
Mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya jagoranci manyan jami’an Gwamnatin Nijeriya zuwa Amurka don tattaunawa game da zargin kisan ƙare dangi da ake yi wa Kiristoci. Lamarin ya samo asali ne bayan Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya goyi bayan kafa ƙasashe biyu na Isra’ila da Gaza. A farkon watan nan, Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi barazanar daukar matakin soji a kan Nijeriya, kuma ya bukaci ‘yan majalisar dokokin kasar, ciki har da dan majalisa Riley Moore, su binciki lamarin. Ko da yake Nijeriya ta karyata ikirarin, amma Amurka ta ci gaba da jadadda zargin kisan Kiristoci. A ranar Talata, mawakiyar Amurka, Nicki Minaj a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ta...
An sanar da dan wasan Paris St Germain, Achraf Hakimi a matsayin wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2025, mai tsaron baya da ya lashe kyautar karon farko bayan shekara 52. Dan wasan tawagar Masar Mohamed Salah shi ne na biyu mai taka leda a Liverpool da kuma Victor Osimhen na Super Eagles mai wasa a Galatasaray a mataki na uku. Mai tsaron bayan Morocco ya karbi kyautar sakamakon nasarorin da ya samu a 2025 tare da Paris St Geramin ciki har da lashe Champions League da Ligue 1 da Coupe de France da kuma UEFA Super Cup. Shi ne na farko daga Morocco da ya karbi kyautar tun bayan Mustapha Hadji a 1998, kuma...
Wani magidanci tare da ɗaukacin iyalinsa huɗu sun rasu sakamakon wata gobara da ta tashi a sanadin kunna maganin sauro a layin Baba Impossible da ke Unguwar Kundila, da ke Ƙaramar Hukumar Tarauni a Jihar Kano. Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta tabbatar da tashin wutar da misalin ƙarfe 4:13 na Asubar ranar Laraba. NAJERIYA A YAU: Halin Kunci Da Matan Da Aka Yi Garkuwa Da Su Ke Tsintar Kansu A Ciki Kotu ta sanya ranar fara shari’ar shugabannin ƙungiyar Ansaru Mai magana da yawun hukumar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya ce sun samu kiran wani ma’aikacinsu, HFS Abba Datti, game da gobarar. A cewarsa ba tare da ɓata lokaci ba suka tura jami’ansu daga hedikwatar hukumar zuwa wajen...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mata da dama da aka yi garkuwa da su na shiga wani irin mawuyacin hali yayin da suke hannun wadanda suka sace su, suna fuskantar rayuwar kaskanci, da cin zarafi, da muzgunawa da wasu irin yanayi wanda sai ka tausaya musu. Irin wadannan mata a wasu lokutan basa tsira da rayukansu, a wasu lokutan kuma ko sun tsira, sukan shiga halin ciwon damuwa wanda ke daidaita musu rayuwa, a wasu lokutan ma har sai sun ji kamar su dauki rayuwar su. NAJERIYA A YAU: Matsayar Doka Kan Taron Da Jam’iyyar PDP Ta Gudanar DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace Shirin Najeriya A Yau na...
Tauraron ɗan wasan Barcelona, Lamine Yamal, ya bayyana cewa ya shirya jagorantar ƙungiyar wajen kafa sabon tarihi a filin wasa na Camp Nou, wanda za su koma buga wasa a ƙarshen makon nan yayin karɓar baƙuncin Atletico Bilbao. Tun kusan kwanaki 900 da suka gabata ne aka rufe filin wasa na Camp Nou sakamakon wasu manyan gyare-gyare da ake yi wa filin, lamarin da ya tilasta wa Barcelona komawa wasu filayen waje domin buga wasanninta. An kama miji da mata kan zargin mallakar buhuna 360 na Tabar Wiwi Osimhen ba zai halarci bikin karrama gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana ba Sai dai duk da cewa ba a kammala gyaran filin gaba ɗaya ba, an ba da damar komawa amfani...
Matsayar da Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta dauka kan tattaunawa da Amurka Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ismail Baqa’i ya bayyana cewa: A halin yanzu babu wata tattaunawa da ake yi tsakanin Iran da Amurka. Ya yi nuni da cewa: Babu wata hujja mai ma’ana ta tattaunawa da wani bangare da ke neman ta tsara sharuddansa kan Iran, yana mai cewa wasikar Shugaba Pezeshkian ga Yariman Saudiyya ta kasance ta biyu kawai kuma ba ta da alaƙa da ziyarar da ya kai Amurka. Da yake amsa tambaya a ranar Laraba game da ikirarin Shugaban Amurka na ranar da ta gabata game da tattaunawa da Iran, Baqa’i ya ce, “A halin yanzu babu wata tattaunawa da ake yi tsakanin Iran da...
Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya {IAEA} ya bayyana cewa: Suna tuntubar Tehran kuma masu binciken hukumar sun koma kasar ta Iran Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA), Rafael Grossi, ya tabbatar da komawar masu binciken Hukumarsa ta IAEA zuwa Iran da kuma ci gaba da duba wasu wurare da ba su lalace ba. Ya lura cewa yana ci gaba da tuntuɓar mahukuntan Iran kuma ya yi kira da a ƙara haɗin gwiwa don ci gaba da duba cikakkun bayanai, musamman a wuraren da aka kai hare-haren soji a kwanan nan. A cikin rahotonsa ga kwamitin Gwamnonin a taronsu na yau da kullun, Grossi ya bayyana cewa masu binciken Hukumar IAEA sun koma Iran kuma...
An yanke wa abokan aikin ɗan tsohon shugaban kasar Gabon hukuncin ɗauri a gidan kurkuku Kotun Hukunta Laifuka ta Musamman da ke Gabon ta yanke hukuncin ɗauri a gidan kurkuku daga watanni 26 zuwa shekaru 15 ga tawagar abokan Nouruddine Bongo, ɗan tsohon shugaban ƙasa Ali Bongo, a shari’ar da aka fi sani da “Tawagar Matasa”, wacce ke da alaƙa da zarge-zargen cin hanci da rashawa da kuma satar dukiyar gwamnati. Bayan dogayen zaman shari’o’i da aka kammala a safiyar ranar 18 ga Nuwamba, 2025, kotun ta yanke wa Iyan Ghislain Ngolo, tsohon darektan ofishin Nouruddine Bongo, hukuncin ɗaurin shekaru 15 a gidan yari, tare da dakatar da shekaru biyar, bisa tuhume-tuhumen da suka haɗa da satar dukiyar jama’a, cin...
Rahotanni sun bayyana cewa Iran ta yi suke kudurin Amurka da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya amince da shi na tilasta aikewa da dakarun kasa da kasa zuwa yankin gaza domin tabbatar da zaman lafiya, ta yi gargadin kada ayi amfani da shi wajen take hakkokin alummar falasdinu na kafa kasarsu mai cin gashin kai A wani bayani daya fitar tun a ranar talata ma’aikatar harkokin wajen iran ta ce kudurin da aka amince da shi ya manta da ainihin rawar da majalisar dinkin duniya za ta taka da kuma kudurinta na baya da ya shafi yankin falasdinu. Kuduri mai lamba 2803 an amince da shi ne a ranar litinin da ta gabata inda ya bukaci kafa dakarun...
Amina Hassan, matar Yakubu Makuku, mai gadin makarantar ’yan mata ta GCGSS Maga da ke Ƙaramar Hukumar Danko Wasagu a Jihar Kebbi, wadda aka kai wa hari da safiyar Litinin, ta bayyana yadda aka kashe mijinta. Da take magana da ’yan jarida a wurin da lamarin ya faru, ta ce bayan da maharan suka kutsa cikin makarantar, sai suka shigo cikin gidansu. Mai taɓin hankali ya kashe soja a Legas HOTUNA: Gobara ta laƙume kasuwar Katako a Gombe Matar ta ce ba ta san cewa mutane ne a bakin ƙofar ba sai da suka shigo cikin ɗakinsu. “Da misalin ƙarfe 4:00 na Asuba a ranar Litinin muna kwance ni da mijina sai muka ji ana ƙoƙarin karya ƙofar dakinm. Na...
Majalisar Wakilai ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya sake kawo sabuwar dabarar da za ta kawo karshen kashe-kashe, da sace-sace da sauran ayyukan ‘yan bindiga a Jihar Zamfara da ma kasa baki daya. Wannan ya biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa na kula da muradun jama’a da dan majalisa mai wakiltar mazabar Gusau/Tsafe ta jihar Zamfara, Hon. Kabiru Amadu, ya gabatar a zaman majalisar . A yayin gabatar da kudirin, Amadu ya bayyana cewa, idan aka yi la’akari da kalubalen tsaron da “yaki ci yaki cinyewa” a Jihar Zamfara da ma fadin kasar, za a iya cewa, “gwamnati ba ta yi abin da ya dace ba don kare rayuka da kadarorin ‘yan Nijeriya don ba su damar...
Iran: An Bayyana Taron Gundumomin Dake Gabar Ruwan ” Caspian” Da Cewa Yana Bunaksa Alakar Kasashen Yankin
Fira ministan jamhuriyar Kalmykia mai kwarya-kwaryar cin gashin kai a tarayyar Rasha, Utshir Janibinov ya fada wa manema labaru a wurin taron gwamnonin gundumomin dake gabar ruwan “Caspian” cewa; Taron da aka yi wanda shi ne irinsa na farko yana da tasiri mai kyau wajen bunkasa alaka a tsakanin gundumomin gabar ruwan “Caspian”. Taron na gwamnonin gundumomin da suke a gabar ruwan “Caspian” an yi shi ne dai a garin Rasht a gundumar Gilan dake nan Iran. Mataimakin Fira ministan jamhuriyar Kalmykia ta tarayyar Rasha, ya bayyana jin dadinsa na halartar wannan taron a nan Iran. A Yau Talata ne dai aka bude wannan taron wanda aka bai wa taken: ” Tekun Caspian A Matsayin Wata Gada Ta Bunkasa Alaka...
Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suna ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon, da a yau Talata su ka kai wani hari a garin Bint-Jubail da ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya da kuma jikkatar wani. Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya ambato ma’aikatar kiwon lafiya ta Lebanon tana cewa; Birnin na Bint Jubail ya fuskanci hare-hare ta hanar amfani da jirgin sama maras matuki, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya. Tashar talabijin din ‘almanar’ ta Lebanon ta ambaci cewa, wani jirgin “sra’ila” maras matuki ta jefa bom a kan wata motar haka rami da hakan ya yi sanadiyyar konewarta, wanda shi ma sabon keta yarjejeniya ne. Mahukunta a yankin na “Bint-Jubail” sun fitar da bayanin...
Masu gangamin da adadinsu ya kai 100 sun tsaya a gaban babbar kofar shiga wurin taron kare muhalli na MDD da aka bude a garin Belem dake yankin Amazon na Brazil. Sojojin kasar Brazil sun bai wa masu gangamin kariya, tare da kaucewa yin taho mu gama saboda su sami damar isar da sakonsu akan abinda yake faruwa na sauyin yanayi da shi ne jigon taron. Wata mace da ta fito daga Munduruku daga jahar Par, ta fadawa manema labaru cewa: “Mun zo nan wurin ne tun kwanaki da yawa, kuma muna son a ji muryoyinmu ne. Muna son zama ne domin yin taattaunawa aka abinda ya shafi sauyin yanayi.” Al’ummun karkara, wadanda sauyin yanayi yake shafa kai tsaye, suna...
Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya amince da daftarin kuduri da kasar Amurka ta gabatar mata na kafa sansanin sojojin kasa da kasa a yankin Gaza. An amince da kudurin ne a jiya litinin inda aka amince da shirin na Donald Trump kan Gaza kuma ta bada umarnin kirkiro dakarun kasa da kasa na hadin guiwa da zai hada da mafiyawancin daga kasashen musulmi da zai kunshi kasashen Masar, Indonesia, da kuma kasar Azarbaijan, Kungiyar Hamas ta yi watsi da wannan kuduri da zai kunshi dakarun kasada kasa domin baya wakiltar hakkokin falasdinawa kuma an yi shi ne domin kwabe dammarar dakarun gwagwarmayar neman yancin falasdinu. Haka zalika ta kara da cewa kudurin bai kunshi bukatun siyasa da taimakon...
Ministan harkokin wajen kasar Afrika ta kudu Ronald lamola a jiya a joharnesbourg yayi gargadi game da kwaso falasdinawa da aka yi a baya bayan nan yana nuna irin yunkurin da ake yi na tilasta musu barin yankin gaza, inda ya bayyan shirin a matsayin wani bangare na shirin korar falasdinawa daga gidajensu. Pretoriya ta fitar da sanarwa na kokarin kwashe falasdinawa daga yankin Gaza zuwa kasar Afrika ta kudu, yayi gargadin cewa wannan matakin yana iya zama wani bangare ne na shirin iyakoki don tarwatsa falasdinawa da karyar canza musu wuri don basu taimakon Agaji Minsitan harkokin wajen na afrika ta kudu ya bayyanawa manema labarai cewa batun shirin ajandar iyakoki na dauke falasdinawa daga gaza zuwa yankuna daban...
An ba wa hamata iska a Hedikwatar Jam’iyyar PDP da ke Abuja a tsakanin bangarorin da ke hamayya da juna. Fadan ya barke ne bayan bangarorin sun halarci ofishin domin gudanar da tarukansu daban-daban a safiyar Talata. Idan ba a manta ba, bangaren Ministan Abuja, Nyesom Wike, wadanda uwar jam’iyyar ta dakatar a yayin babban taronta na kasa da ya gudana a karshen mako ya kira taron gaggawa a yau Talata a hedikwatar Jam’iyyar da ke Wadata Plaza a Abuja.
“Cikin hukuncin Allah, sojojin Daularmu sun kama ‘Kwamandan Runduna’… bayan ya gudu daga harin kwantan-ɓauna… Bayan mun yi masa tambayoyi, Mujahidai suka kashe shi.” An kuma wallafa wani hoto a kafafen sada zumunta da ya nuna Janar Uba a ɗaure. Har yanzu rundunar sojin Nijeriya ba ta fitar da wata sanarwa game da wannan lamari ba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ’Yansanda Sun Tura Tawaga Don Ceto Ɗaliban Da Aka Sace A Kebbi November 18, 2025 Manyan Labarai Bai Dace Adalci Ya Zama Na Sayarwa Ba – Tinubu Ga Alƙalai November 17, 2025 Manyan Labarai Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC November 17, 2025
Gwamna Ahmed Idris na Jihar Kebbi ya ba da tabbacin cewa jami’an tsaro za su ƙwato ’yan matan da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Kwalejin ’Yan Mata ta GGCSS Maga da ke Ƙaramar Hukumar Danko Wasu ta jihar cikin ƙoshin lafiya. Gwamnan ya bayar da tabbacin ne a yayin ganawarsa da iyayen ɗaliban kaɗan bayan harin ’yan bindigar a ranar Litinin. Aminiya ta ruwaito cewar da asubahin ranar ’yan bindiga suka kusta cikin harabar makarantar kwana ta ’yan mata ta GGCSS Maga, suka kwashe ɗalibai 25 daga ɗakin kwanansu zuwa cikin jeji. Maharan da suka riƙa harbi a iska kafin su shiga harabar makarantar sun bindige Matakin Shugaban Makarantar, Malam Hassan Yakubu Makuku, wanda ya yi ƙoƙarin...
Alkaluman da suka fito daga kungiyar masu kera motoci ta kasar Sin sun nuna cewa, adadin motocin da kasar Sin ke fitarwa waje ya karu da kashi 15.7 bisa dari a cikin watanni 10 na farkon shekarar 2025 bisa na makamancin lokacin bara. Kasar ta fitar da motoci sama da miliyan 5.6 a tsakanin wannan lokacin, kamar yadda alkaluman suka nuna. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing November 17, 2025 Daga Birnin Sin Firaministan Sin Ya Isa Rasha Domin Halartar Taron SCO November 17, 2025 Daga Birnin Sin Kudaden Kasafin Kudin Sin Sun...
A Damaturu, farashin mudun shinkafa ya ragu daga N5,000 zuwa N2,500, yayin da wake, masara da gero suma suka sauka fiye da rabin tsohon farashinsu. Masana tattalin arziki sun ce yawaitar shigo da hatsi kamar shinkafa da alkama ya taimaka wajen rage tsadar abinci da ake fama da ita a watannin baya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ta Ragu Zuwa Kashi 16.065% November 17, 2025 Labarai ‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga November 17, 2025 Labarai Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi November 17, 2025
An samu wannan raguwar ne sakamakon sauye-sauyen da aka samu a shekarar da muke ciki. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai ‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga November 17, 2025 Labarai Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi November 17, 2025 Labarai MACBAN Ta Nemi Amurka Ta Cire Sunanta Daga Jerin Waɗanda Ta Ƙaƙabawa Takunkumi November 17, 2025
Firaministan kasar Sin Li Qiang ya isa birnin Moscow na kasar Rasha a yau Litinin domin halartar taro karo na 24 na majalisar shugabannin kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO). Bisa gayyatar da firaministan kasar Rasha Mikhail Mishustin ya yi masa, Li zai halarci taron na SCO a ranakun 17 da 18 ga watan Nuwamba. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kudaden Kasafin Kudin Sin Sun Karu Da Kashi 0.8 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana November 17, 2025 Daga Birnin Sin An Sanya Hannu Kan Yarjejeniyoyin Cinikayya Na Biliyoyin Kudi Yayin Baje Kolin CHTF Na Kasar Sin November 17, 2025 Daga Birnin Sin Tsohon Firaministan Japan Ya...
Ya bayyana cewa, zaman bitar ya yi daidai da umarnin Sufeto Janar na ‘Yansanda, IGP Kayode Egbetokun, musamman kan karfafawa jami’an rundunar. Don haka, CP Bakori ya umurci Kwamandojin da su zurfafa wayar da kan jama’a a yankunan karkara da birane domin sanar da su irin rawar da suke takawa wajen wanzar da zaman lafiya da daƙile ayyukan ‘yan ta’adda. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi November 17, 2025 Labarai MACBAN Ta Nemi Amurka Ta Cire Sunanta Daga Jerin Waɗanda Ta Ƙaƙabawa Takunkumi November 17, 2025 Manyan Labarai Bai Dace Adalci Ya Zama Na Sayarwa Ba – Tinubu Ga Alƙalai November 17, 2025
Na’ini: Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Da Kansa Ya Jagoranci Yaki Kwanaki 12 Da Aka Kaddamar Kan Iran
Jagoram juyin juya halin Musulunci da kan sa ya jagoranci yaki da harkokin al’umma a lokacin yakin wuce gona da iri na karshe kan Iran Kakakin Rundunar Tsaron kare Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC), Brigadier Janar Ali Mohammad Na’ini, ya tabbatar da cewa: Maƙiya ‘yan sahayoniyya ba su da yanayin sabon yaƙi, kuma abin da ake gabatarwa a yau shine yaƙin tunani da yaƙin da aka saba gani. A wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Mehr, Brigadier Janar Na’ini ya ba da labarin lokutan shaƙatawa da ba zato ba tsammani na barkewar yaƙin da kuma shahadar wasu manyan kwamandojin soja na ƙasar. Ya kuma lura da yadda aka sake gina sansanin umarni a cikin ɗan gajeren lokaci da kuma...
Wata sanarwa da gwamnati ta fitar a Gaza ta yi gargadin cewa: Akwai wani bala’i da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin jin kai Ofishin Yada Labarai na Gwamnati a Zirin Gaza ya fitar da Sanarwar Manema Labarai Mai Lamba (1021) a yau, Litinin, inda ya yi magana kan sabbin ci gaba da manufofin gwamnati, tare da mai da hankali kan rikicin jin kai da Falasdinawa da aka kora suka fuskanta sakamakon mummunan harin sojojin mamayar Isra’ila. Sanarwar ta nuna cewa gwamnatin mamayar Isra’ila ta haifar da mummunan bala’in gidaje, inda sama da iyalai Falasdinawa 288,000 ke fuskantar mawuyacin hali saboda rashin kayan more rayuwa na yau da kullun. Gwamnatin mamayar Isra’ila ta kara ta’azzara bala’in da gangan...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta kama ƙunshi 66 na ganyen tabar wiwi a wani samame da ta kai a garin Deba, bayan samun wasu sahihin bayanan leƙen asiri. Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare a ranar 16 ga Nuwamba, 2025, lokacin da aka hango wata mota mara lamba, ƙirar Toyota Corolla, da ake zargi tana ɗauke da kayan, a kan hanyar Kuri zuwa Deba. Hauhawar farashi ya ƙara raguwa a Nijeriya — NBS An ɗaura auren Sanata Kawu Sumaila da wata jami’ar soji a Kano Aminiya ta ruwaito cewa, bayan isar jami’an wurin da ake zargin akwai kayan laifin ne, sun lura da wasu...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta kama ƙunshi 66 na ganyen tabar wiwi a wani samame da ta kai a garin Deba, bayan samun wasu sahihin bayanan leƙen asiri. Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare a ranar 16 ga Nuwamba, 2025, lokacin da aka hango wata mota mara lamba, ƙirar Toyota Corolla, da ake zargi tana ɗauke da kayan, a kan hanyar Kuri zuwa Deba. Hauhawar farashi ya ƙara raguwa a Nijeriya — NBS An ɗaura auren Sanata Kawu Sumaila da wata jami’ar soji a Kano Aminiya ta ruwaito cewa, bayan isar jami’an wurin da ake zargin akwai kayan laifin ne, sun lura da wasu...
Ya kuma yi Allah wadai da kisan wani jigo na Jam’iyyar APC, Umar Moriki, da kuma sace-sacen jama’a da aka yi a Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara, inda aka sace iyalai baki daya, ciki har da mata da yara. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai MACBAN Ta Nemi Amurka Ta Cire Sunanta Daga Jerin Waɗanda Ta Ƙaƙabawa Takunkumi November 17, 2025 Manyan Labarai Bai Dace Adalci Ya Zama Na Sayarwa Ba – Tinubu Ga Alƙalai November 17, 2025 Manyan Labarai Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC November 17, 2025
Shugaba Bola Tinubu a ranar Litinin ya gargadi jami’an shari’a a fadin kasar cewa dole ne a tabbatar da adalci ga kowa – Talaka da mai kudi, ba tare da nuna wata wariya ba, ko karɓar cin hanci, “bai dace adalci ya zama na sayarwa ba.” Da yake jawabi a yayin bude taron alkalan Nijeriya na kotunan koli na shekarar 2025 a Abuja, Tinubu ya jaddada cewa jami’an shari’a su ne ainihin masu kula da adalci, don haka, shugaban ya tabbatar da goyon bayansa kan samar da walwala, horo, da inganta Cibiyar Shari’a ta Kasa. ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC November 17, 2025 Manyan...
Ma’aikatar raya al’adu da yawon bude ido ta kasar Sin ta fitar da sanarwa a jiya Lahadi, wadda ke kira ga al’ummunta da su yi taka-tsantsan a kwanakin nan wajen zuwa yawon bude ido kasar Japan. Game da hakan, masani a kwalejin bincike ta Nomura Takahide Kiuchi, ya bayyana a jiyan cewa, raguwar yawan Sinawa masu zuwa yawon bude ido Japan, zai haifar da raguwar GDPn kasar ta Japan da kashi 0.36%, kana hasashen yawan asarar tattalin arziki da hakan zai haifar zai kai JYE tiriliyan 2.2, kwatankwachin kudin Sin yuan biliyan 101.6. Bayanai sun nuna cewa, kasar Sin ce babbar abokiyar ciniki mafi girma ta Japan, kasa ta biyu mafi girma wajen fitar da kayayyaki zuwa kasar, kana babban...
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Taraba, Rt Hon. Kizito Bonzena, tare da ’yan majalisar 15 sun sauya sheka daga jam’iyyarsu ta PDP zuwa APC. A saifyar Litinin ne Rt Hon. Kizito Bonzena ya gabatar da takardarsa ta ficewa daga PDP tare da sauran mambobin zuwa APC. Ya bayyana cewa da sauyin shekar tasu, yanzu APC ce ke da daukacin kujeru 24 da ke Majalisar Dokokin Jihar Taraba. Hakan na zuwa ne jim kadan bayan Gwamnan Jihar Taraba, Kefas ya sanar da shirinsa na komawa APC daga PDP. Masu ibadar Umarah 42 sun mutu a hatsarin mota a hanyar zuwa Makka ’Yan ta’adda sun sace dalibai 25 a dakunan kwanansu a Kebbi Sauran mambobin majalisar da suka sauya sheka sun hada da...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƴan Bindiga Sun Sace Ɗalibai Ƴan Mata, Sun Kashe Mataimakin Shugaban Makaranta A Kebbi November 17, 2025 Manyan Labarai Mutane 42 Sun Mutu A Wani Hatsarin Tankar Dizal Da Motar Masu Umrah A Hanyar Makka November 17, 2025 Manyan Labarai Ba Mu Samu Labarin Kai Wa Laftanar Yerima Hari Ba – Ƴansanda November 17, 2025
Rahotanni da suka fito daga yankin falasdinu sun tabbatar da cewa sojojin Isra’ila sun kai hari a sansanin yan gudun hijira dake gabar yammacin kogin Jodan kuma sun kashe wasu matasa guda biyu,da suka hada da jadalla jihar jumaa dan shekara 15 dake sansanin yan gudun hijira na fara’a a yammacin garin Tubas. Hukumar bada agaji ta yankin falasdinu ta bayyana cewa jami’anta sun kula da wasu mutane biyu da aka jikkata wato wani yaro dan shekara 16 da haihuwa da ya samu rauni a kugunsa, da kuma wani dan shekara 18 da shi ma ya ji rauni a lokacin da suke dauki ba dadi da sojojin Isra’aila a sansanin na fara’a, sai dai an hana ma’aikatansu zuwa daukar mutum...
Tawagar wasannin Wushu na kasar Iran ta nuna rawar gani sosai a gasar hadin kan kasashen musulmi da ake yi a kasar saudiya inda ta samu lambobin yabo guda 4 wato Azurfa 1 tagulla 1 da kuma zinariya 2 a ranar karshe na gasa a wannan bangaren. A bangaren mata kuma Sara shafi’I wacce ta fara fitowa a gasar kasa da kasa ta doke abokiyar hamayyarta daga kasashen kargyzstan da Turikiya ta kai ga wasan karshe , daga nan kuma ta yi galaba a kan abokiyar hammayarta ta kasar masar da ya kai ga bugun daga kai sai mai tsaron gida a zagayen farko don samu lambar zinariya Haka zalika a bangaren mata masu nauyin kilograme 60 Sohaila Mansurian ta...
Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta kasar iran Mohammad Eslami ya bayyana cewa harin da Amurka da isra’ila suka kai kan tashohin nukiliyar ta a tsakiyar watan yuli ya nuna cewa Amurka da kawayenta ciki har da isra’ila suna harin naurorin kimiyya na jamhuriyar musulunci ta iran ne. Shugaban ya fadi hakan ne a wata hira da yayi da gidan talbajin din Al-Masirah na kasar Yamen inda ya jaddada” cewa ba’a taba kai irin wannan harin ba kan nauraron kimiyyar kasar a cikin tarihi, don haka yanayi kai harin yana nuna cewa Amurka da kawayenta sun shiga wani sabon mataki mai hadari, na karuwar tashin hankali kan yakin da suke yi da kimiyyar kasar iran. A ranar 13 ga watan juni...
Hamas Da Sauran Bangarorin Falasdinawa Sun yi Watsi Da Shirin Aikewa Da Dakarun Kasashen Waje A Yankin Gaza
Rahotanni sun bayyana cewa bangarorin falasdinawa sun yi watsi da kudurin da aka kaddamar ga kwamitin sulhu na majalsar dinkin duniya na shirin aikewa da sojojin ketare zuwa yankin Gaza sun yi kira ga kasar Aljeriya da sauran mambobin da ba na dindin ba a kwamitin sulhu da su kalubalance shi. Daftarin kudurin an tsara za’a kada kuri’a akan shi a yau litinin na yiyuwar akewa da dakarun kasashen waje 20,000 domin kulawa da iyakokin Gaza, da kuma bada huro ga yan sandan falasdinu . A Sanarwar hadin guiwar dukkan bangarorin falasdinawan sun yi tir da wannan shiri, inda suka bayyana shi a matsayin wani sabon salo na kara mamaye yankin dama alummarsa, domin bada halacci ga zaman dakarun kasashen...
’Yan ta’adda sun harbe Mataimakin Firinsifal har lahira, sa’annan suka yi garkuwa da dalibai 25 a Makarantar ’Yan Mata ta Gwamnati (GGCSS) da ke yankin Maga a Karamar Hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi. Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun bindige Malam Hassan Yakubu Makuku ne a yayin da yake kokarin kare daliban, a lokacin farmakin da aka kai makarantar da misalin karfe 5.20 na Asubahin ranar Litinin. Wani shaida ya ce, “Harin ya dimauta al’ummar garin Maga, yanzu muna cikin zullumi da alhini.” Ya kara da cewa, ’yan ta’addan sun harbe Malam Hassan ne a yayin da yake kokarin hana su tafiya da daliban.”
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja November 16, 2025 Manyan Labarai Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su November 16, 2025 Manyan Labarai Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara November 16, 2025
’Yan sanda sun yi nasarar kama wasu ’yan bindiga biyar tare da ƙwace tarin makamai a hannunsu a yankin Zuru–Tadurga da ke Jihar Kebbi. Rundunar ’yan sanda ta musamman da ta kama su, ta bayyana cewa, ’yan bindiga suna cikin waɗanda suka kai hare-hare a kan al’ummomin Zuru a kwanakin baya. Ta ƙara da cewa dukkansu ’yan asalin kauyen Birnin Tudu ne da ke cikin ƙananan hukumomin Bukkuyum da Gummi a Jihar Zamfara. Kakakin ’yan sanda a jihar, CSP Nafiu Abubakar, ya ce makaman da aka ƙwato daga hannun ’yan bindigar sun haɗa bindigogi AK-47 guda 7 a wata ƙaramar gida guda 1 da harbi-ruga guda uku. ’Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace 64 a Zamfara Da amincewar...
’Yan bindiga sun kashe mutum 3 tare da yin garkuwa da wasu 64 a ranar Asabar a Karamar Hukumar Tsafe ya Jihar Zamfara. Cikin waɗanda ’yan ta’addan suka kashe har da wani jigon jam’iyyar APC, Hon. Umaru Moriki wanda aka bindige a kan hanyar Gusau zuwa Tsafe, waɗanda aka yi garkuwa da su kuma har da mata da ƙananan yara a kauyen Fegin Baza. Harin ta faru ne washegarin da Ministan Tsaro, Bello Matawalle ya ziyarci jihar, inda ya sanar cewa Hedikwata Tsaro ta girke ƙarin jami’an tsaro a jihar. A yayin ziyarar ministan ya bayyana cewa zai gana da jami’an tsaro inda zai ba su umarni kar su raha wa ’yan ta’adda. NAJERIYA A YAU: Matsayar Doka Kan Taron...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Matsayar doka ta zama babbar abun tattaunawa a Najeriya yayin da jam’iyyar PDP ta gudanar da taron ta na kasa duk da mabanbantan hukunce hukunce daga kotuna biyu. Umarnin kotu guda yana goyon bayan taron, ɗayan kuwa ya haramta shi gaba ɗaya. Wadannan hukunce hukunce ba baiwa jam’iyyar damar yi ko haramta musu taron kadai suka yi ba, harda baiwa hukumar zabe ta kasa umurnin saka ido ko haramta musu wannan dama yayin taron. Duk da wadannan hukunce hukunce, jam’iyyar ta gudanar da taron inda ta zabi shugabannin da zasu cigaba da jan ragamar al’amuranta da kuma daukar wasu kwararan matakai. NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Manoman Najeriya Noman Rani...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su November 16, 2025 Manyan Labarai Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara November 16, 2025 Manyan Labarai Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle November 16, 2025
Babban lauya kuma mai kare haƙƙin ɗan Adam, Femi Falana (SAN), ya bai wa ƴan Nijeriya shawara da su kai Gwamnatin Tarayya ƙara don neman a mayar musu da kuɗin fansar da suka biya yayin da aka yi garkuwa da ƴan uwansu. Ya ce gwamnatin ta kasa sauke babban nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mata na kare rayuka da dukiyoyin ƴan ƙasa. Falana ya yi wannan jawabi ne a lokacin buɗe sabuwar shekarar Shari’a ta Tsangayar Shari’a ta Jami’ar Yakubu Gowon da ke Abuja. Ya ce yawaitar garkuwa da mutane a sassan ƙasar nan ya nuna gazawar gwamnati wajen tabbatar da kariya kamar yadda kundin tsarin mulki da Yarjejeniyar Afrika kan Haƙƙin Dan Adam suka tanada. Ya kuma...
Babban jirgin ruwan yaki mai dakon sojojin kasa da sauran kayan yaki da ake amfani da su a kan-tudu samfurin 076 irinsa na farko a kasar Sin mai suna Sichuan, ya koma tashar jiragen ruwa da ke birnin Shanghai da misalin karfe 5 na yamma a yau Lahadi, bayan kammala gwajinsa na farko a teku. Gwajin jirgin na kwanaki uku ya kunshi gwada ayyukan na’urar da ke sarrafa tafiyar jirgin da na’urorin lantarkinsa da sauran kayayyakin aiki, inda aka samu sakamakon da ake sa ran samu. Kasancewarsa sabon jirgin ruwan yaki na zamani na rundunar sojojin ruwa ta ‘yantar da jama’ar kasar Sin, jirgin ya kunshi sabbin fasahohin majaujawar mayen karfe mai aiki da lantarki, da fasahohin rike jiragen sama...
Kungiyar kasa da kasa mai kula da ‘yan hijira ( IOM) tana yin kira ga shugabannin kasashen duniya da su bayar da kariya da kare hakkokin wadanda suke rayuwa a yankunan da suke fama da matsalar sauyin yanayi. A taron da ake yi a yanzu haka a garin Belem na kasar Brazil kungiyoyi masu zama kansu dake fafutuka da rajin kare muhalli suna gabatar da shawarwari akan yadda za fuskacin matsalolin da duniya take fuskanta. Kiran kungiyar ya ambato mutanen da sauyin yanayi ya tilasta musu yin hijira, ‘yan asalin kasa a cikin karkara da ‘yan gargajiya. Ibtila’oin dabi’a irin su ambaliyar ruwa, zafi mai tsanani, fari da mahaukaciyar guguwa, suna tilastawa miliyoyin mutane barin gidajensu a kowace shekara. Da...
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya buƙaci al’umma su ƙara kula da tsaro tare da yin aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin tsaro, yayin da ’yan bindiga suka fara kai hare-hare a ƙauyukan da ke iyaka da Jihar Katsina. Sarkin, ya yi wannan kira ne yayin ziyarar jaje da ya kai wa al’ummar Faruruwa da ke Ƙaramar Hukumar Shanono a Jihar Kano. Gwamnatin Gombe ta bai wa alƙalai da Khadi-Khadi kyautar sabbin motoci 16 Ba da yawuna PDP ta kori Wike ba — Muftwang A baya-bayan nan ’yan bindiga sun kai hari yankunan, inda suka sace shanu tare da yin garkuwa da mutane. Sarki Sanusi, ya ce yawan hare-haren da ake fuskanta a yankin ya nuna cewa ana...
Yanzu haka ana gudanar da taron bangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayin duniya ta Majalisar Dinkin Duniya, karo na 30, wato “COP 30” a takaice, a birnin Belem na kasar Brazil, inda a ranar Juma’a 14 ga wata aka kira wani taro a gefe mai taken “Dabarun Kasar Sin Na Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya”, don bayar da fasahohin Sin a fannin daidaita al’amura a kokarin sabawa da sauyin yanayi. A wajen taron, shugaban tawagar kasar Sin a taron COP30, kana mataimakin ministan muhallin halittu na kasar, Li Gao, ya ce sauyin yanayin duniya wani babban kalubale ne da daukacin bil Adama ke fuskantarsa, inda a nata bangare, kasar Sin ta tsaya kan mai da hankali kan...
Richard A falk Tsohon mai bincike kan laifukan yaki da HKI ta tafka kan alummar Gaza da majalisar dinkin duniya ta nada ya fuskanci matsalar a kasar kanada inda aka tsare shi tare da yi masa tambayoyi a wata tafiya da yayi don halartar taron dake da alaka da yankin Gaza. Falka dan shekara 92 da haihuwa, hukumar kula da hakkin dan adam ta majalisar dinkin duniya ta nada shi a shekara ta 2008 na tsawon shekaru 6 a matsayin dan rahoton musamman don gudanar da bincike kan laifukan yaki da HKI ta tafka a yankin falasdinu. Falk ya bayyana cewa dalilin yin tambayoyi na tsawon lokaci ga manyan masana da ba sa yin wata barazanar tsaro a filin saukar...
Rahotanni sun nuna cewa tsohon ministan harkokin wajen kasar iran mohammad Javad zarif yace isra’ila ce kawai gwamnatin dake ayyukan nukiliya ba bisa kaida ba a yammancin asiya, amma take sukar iran duk da cikakken hadinkai da take bayarwa ga dokokin hukumar nukiliya kuma wadda ke da tarihi mafi girma na binciken hukumar nukiliya ta duniya, Zarifi ya fadi haka ne a wajen taron international iranology da aka gudanar a birnin Tehran, kuma ya bayyana matsayin iran na dogon lokaci inda isra’ila take kokarin haifar da barazana a yankin domin kawar da kokarin deiplomasiya da ake yi na yarjejeniyar JCPOA. Har ila yau ya jaddada cewa batun danganta shirin iran da barazanar tsaro wani makirci ne da aka kulla domin...
Amfani da jami’an tsaro: Abu na farko dai dole ne kungiyoyi su yi aiki tare da yansanda, NSCDC, da jami’an tsaro na sirri wajen tsara tsare-tsaren tsaro a ranar da za su buga wasa, domin kuwa Bahaushe na cewa, “tun za a, ake shiri ba sai an dawo ba”, hakazalika yana da mahimmanci a tura isassun masu aikin kwantar da tarzoma (ba yansanda kawai ba) don sa ido kan magoya baya, lura da wuraren shiga/fita, da kuma taimakawa wajen rage turmutsitsi yayin wasa. Amfani da CCTV: Yawancin filayen wasa na gasar NPFL ba su da isasshen tsarin kyamarar CCTV, a cikin filayensu cewar bincike, samar da kyamarori masu sa ido na iya rage tashin hankali a cikin...
Ɓangaren Shari’a a Nijeriya, yana da alhakin bayyana dokoki, kare kundin tsarin mulki, da kuma tabbatar da adalci. An tsara tsarin shari’a a karkashin jagorancin Kotun Ƙoli inda Alƙalin Alƙalan Nijeriya (CJN) ke kula da ita, sannan Kotun Ɗaukaka Ƙara da Manyan Kotuna a matakin jiha da tarayya. Daga cikin manyan haƙƙoƙin da suka rataya akan ɓangaren Shari’a, akwai fassara kundin tsarin mulki da dokoki don amfani da su a shari’o’i. Sulhunta masu saɓani da kare haƙƙin ‘yan ƙasa da kuma tabbatar da cewa, sauran sassan gwamnati suna aiki a cikin iyakokin kundin tsarin mulki. Amma, mu tambayi kanmu, wai me ke faruwa a ɓangaren Shari’a, ake samun hukuncin Shari’a ɗaya masu karo da juna? An...
Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan
Kalaman tayar da husuma na firaministar Japan Sanae Takaichi, dangane da batun yankin Taiwan na kasar Sin, na ci gaba da shan suka da Allah wadai daga sassan kasa da kasa. Wani sakamakon kuri’un jin ra’ayin al’umma da kafar CGTN ta gabatar ya nuna yadda akasarin masu bayyana mahanga suka amince da cewa, matakin na Takaichi tsoma baki ne cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, kuma akwai bukatar gaggauta sanya ido kan karuwar burikan wasu jagororin Japan masu tsattsauran ra’ayi, na ruguza odar kasa da kasa ta bayan yakin duniya na biyu. Kaso 91.1 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin na ganin kamata ya yi Japan ta gyara tarihin ta’asar da ta aikata ta hanyar aiwatar da matakai na hakika,...
Kamar ‘yan wasa da masu horarwa, an hana jami’an wasa shiga ayyukan yin caca bisa ga ka’idojin TFF, da kuma na FIFA da hukumar gudanarwa ta Turai (Uefa), masu gabatar da kara na Turkiyya sun bayar da umarnin tsare mutane 21 ciki har da alkalai 17 da shugabannin kungiyoyin kwallon kafa biyu a wani bangare na babban bincike kan yin caca da kuma shirya yadda sakamakon wasa zai iya fitowa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Ina Son Kasancewa Cikin Koshin Lafiya Kafin Buga Gasar Kofin Duniya Na Shekarar 2026 – Messi November 15, 2025 Wasanni Shakirat Ta Tsallaka Mataki Na Ƙarshe Na Zama Gwarzuwar Ƴar Wasan Afrika November 15, 2025 Wasanni Kofin Duniya: Nijeriya Za Ta Fafata Da...
An haife ni a garin Kano, karamar hukumar Nasarawa, Giginyu, Mahaifana ‘yan Sakkwato ne. Na yi aure a Kano ina da yara na guda uku, namiji daya mata guda biyu. Na yi firamare da Sakandare, a garin Kano. Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma harkar fim? A baya ban taba jin zan yi fim ba dan bana ra’ayi, ban taba jin abun yana burgeni ba, ban kuma taba sa shi a raina ba har in ce zan yi ba. Amma sakamakon ina tare da ‘yan fim din ina dan harkar turarurruka, kayayyaki, ‘yan dai abubuwa ina dan kai musu, har na shaku dasu, na ga yadda suke yi. Har wata rana bana mantawa ana ‘shooting’ din wani fim,...
Jaridar “ma’ariv’ ta buga labarin dake cewa Fira minista Netanyahu yana rayuwa cikin zullumi da tsoro mai tsanani akan hukuncin da kotu za ta yanke masa. Jaridar ta ‘yan sahayoniya ta kuma ce yadda ake yin matsin lamba daga waje domin ganin an yafe wa Netanyahu,yana nuni ne da yadda Fira ministan yake cikin tsoro da razana akan hukuncin da kotun za ta yanke a kansa. Kwanaki kadan da su ka gabata ne dai shugaban kasar Amurka ya aike da wasika zuwa ga shugaban Haramtacciyar kasar Isra’ila Ishaq,,, yana bukatar ya yi wa Netanyahu afuwa.Ana tuhumar Netanyahu ne daaii da cin hanci da rashawa. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to...
Kungiyar “Oil Change International” mai zaman kanta ta bayyana cewa da akwai kasashe 25 da su ne su ka rika sayar wa da “Isra’ila” man fetur a tsawon lokacin yakin Gaza. Rahoton wannan jaridar ya yi ishara da kasashe 25 da su ne madogarar Haramtacciyar Kasar Isra’ila” wajen samun makamashin da ta rika amfani da shi a motocinta nay akin Gaza. Jaridar “al-Ahbar” wacce ta buga wannan rahoton da kungiyar “ Oil Change International” mai zaman kanta ta watsa a yayin taron da ake yin a muhalli a kasar Brazil, ta ce; Kasashen Azerbaijan da kuma Kazakhstan ne a gaba da su ka bai wa ‘yan sahayoniya kaso70% na man fetur din da motocinsu na yaki su ka rka amfani...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Jakadan Sin A Japan Ya Bayyana Matukar Adawa Da Kalaman Firaminista Takaichi Dangane Da Kasar Sin November 15, 2025 Daga Birnin Sin Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya November 14, 2025 Daga Birnin Sin Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba November 14, 2025
Jakadan kasar Sin a Japan Wu Jianghao, ya gana da mataimakin ministan harkokin wajen Japan Takehiro Funakoshi a jiya Juma’a, inda ya bayyana matukar adawar kasarsa, da korafi a hukumance, dangane da kalamai marasa dacewa da firaministar Japan Sanea Takaichi ta furta dangane da kasar Sin. Jakada Wu, ya ce munanan kalamai masu tayar da husuma na Takaichi, dangane da yankin Taiwan na Sin, wadanda aka jiyota tana yi kwanan baya, a majalissar dokokin kasarta sun sabawa hankali, sun tsallaka jan-layin kasar Sin, kana barazanar nuna karfi ne da neman takalar yaki. Kazalika, firaministar ta Japan ta ki amincewa da kuskurenta, ta ki janye kalaman, ko sassauta mummunan tasirinsu. Don haka matakin nata ya shaida matukar kaucewa gaskiya, da fankamar...
Kifi mai nama ko naman rago, Ataruhu da tattasai, Barkono ja, Albasa, Daddawa, Gauta (baobab leabes),Yaji, gishiri da maggi, Manja ko man gyada. Yadda ake hada miyar: A wanke kifi ko naman da kyau, a nika attaruhu, tattasai, barkono ja da albasa a hade. A zuba kifi ko naman a tukunya tare da dan ruwa, gishiri da maggi. A bar shi ya tafasa har ya fara laushi. Sannan a zuba nikakken kayan miya a cikin tukunyar. A bar su su dahu har su gauraya da naman ko kifin. Sannan sai a zuba daddawa a cikin miya. A juya sosai sannan a bar shi ya tafasa na ‘yan mintuna. Sai a wanke gauta sosai kafin a zuba a cikin miya....
Ki cire kwallon da ke cikin dabino, sai ki hada kwakwa da aya da dabinon, ki markada su waje daya. Bayan haka, ki kawo zuma mai kyau, mai dan yawa da kuma nonon rakumi kamar kofin shayi daya. Ki hada da kwakwar da kika markada da dabino da aya. Ki juya su waje daya sosai har sai sun hadu. Yadda ake amfani da shi: Ki adana hadin a wuri mai tsafta, sannan ki rika sha da safe da yamma. Idan hadin ya kare, za ki iya sake yin wani. Kada ki yi da yawa domin kada ya lalace kafin ki gama shan sa. Ki yi hadin kamar na kwanaki bakwai kawai. Wannan hadin na masu aurene. Don maganin tsatsatsagewar gaba:...