Bude Kofa Da Hadin Gwiwa Da Juna Kalmomi Ne Mafi Dadi
Published: 5th, April 2025 GMT
Har ila yau a kan batun haraji, a karshen bara, kasar Sin ta cire harajin kwastan a kan dukkanin kayayyakin da take shigowa da su daga kasashen da suka fi fama da koma bayan tattalin arziki, wadanda suka kulla huldar diplomasiyya da ita, ciki har da wasu kasashe 33 dake nahiyar Afirka, matakin da a hannu guda ya saukaka hanyoyin shigowar amfanin gona na kasashen Afirka cikin kasuwar kasar Sin don biyan bukatun gidanta, a dayan hannu kuma, ya taimaka ga saukaka fatara da ma bunkasuwar sana’o’i a kasashen Afirka.
Lallai kashe fitilun wasu ba zai taimaka ga samar da haske ga wasu ba. A zamanin dunkeluwar tattalin arzikin duniya, tuni kasa da kasa sun zamanto masu matukar alaka da juna a tattalin arzikinsu, kuma ko kadan ba zai yiwu ba su katse huldar tattalin arziki da juna.
Ba shakka, bude kofa da hadin gwiwa da juna kalmomi ne mafi dadi, wanda a baya an shaida hakan, kuma zai ci gaba da tabbata a gaba. (Lubabatu Lei)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Amurka ta sake laftawa wasu kamfaninin mai na Iran takunkumi
Amurka ta sanar da kakaba takunkumi kan wasu kamfanoni 7 da ta ce suna da hannu wajen siyar da man kasar Iran, a wani mataki na kara matsin lamba duk da tattaunawar da aka yi kan shirin nukiliyar Iran.
Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar ta ce, bangarorion da takunkumin ya shafa sun hada da kamfanonin kasuwanci guda biyar, hudu da ke Hadaddiyar Daular Larabawa, daya kuma a kasar Turkiyya, wadanda suka sayar da albarkatun man fetur na kasar Iran ga kasashe uku, da kuma wasu kamfanonin jigilar kayayyaki guda biyu.
A cikin sanarwar da sakataren harkokin wajen kasar ta Amurka Marco Rubio ya fitar, ya ce “Matukar dai Iran na son samar da kudaden shiga na man fetur da sinadarai don samar da kudaden gudanar da ayyukanta na tabarbarewar zaman lafiya, da kungiyoyin da ya bayyana da na ta’addanci to Amurka za ta dauki matakin laftawa Iran da dukkan kawayenta alhakin kaucewa takunkumi.”
Matakin na zuwa ne jim kadan bayan Iran ta sanar da cewa za a sake gudanar da zagaye na hudu na tattaunawa da gwamnatin shugaba Donald Trump a birnin Rome a ranar Asabar 3 ga watan Mayu a karkashin jagorancin kasra Oman.