An tsinci gawar saurayi da buduwarsa a tube a cikin daki
Published: 22nd, April 2025 GMT
An tsinci gawar wani matashi da budurwarsa a tube bisa gado a cikin dakinsa a yakin Alo da ke Karamar Hukumar Ankpa a Jihar Kogi.
An tsinci gawara masoyan ne a gidan hayan da saurayin ke zama ranar Juma’a da ta gabata.
Mai gidan hayan mai suna Salisu Ibrahim ne ya nemi agajin jama’a sakamakon rashin ganin matashin ya bude kofarsa da safe kamar yadda ya saba.
Daga nan ne ya sanar da dan uwan matashin da kuma ’yan sanda, inda suka so aka balla kofar dakin, inda aka samu masoyan sun kwanta dama.
Mutanen da aka kashe a Binuwai sun ƙaru zuwa 72 HOTUNA: An yi zanga-zangar adawa da matsalar tsaro a Filato NAJERIYA A YAU: Matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa A Tsarin Mulkin Najeriya?Ya ce da shigan dan uwan mamamcin ya tsinci gawar masoyan biyu tsirara a bisa gado bayan da aka balla kofar dakin.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin ’yan sandan jihar Kogi, SP William Aya, ya ce suna gudanar da bincike domin gano hakikanin abin da ya faru.
Aya ya ce, ”DPO na Ankpa na ya tura jami’an da suka je aka gano gawarwakin aka kai su asbiti a Ankpa inda aka tabbatar rai ya yi halinsa.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gawa masoya Saurayi tsirara
এছাড়াও পড়ুন:
Tarayyar Afirka ta dage takunkumin da ta kakabawa Gabon
Kungiyar Tarayyar Afirka ta dage takunkumin da ta kakabawa kasar Gabon tare da maida ta a cikin cibiyoyinta.
AU, ta sanar da hakan ne yayin taron kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar yau Laraba a Addis Ababa.
Hakan dai ya karshen dakatarwar da aka yi wa kasar ta Gaban daga kungiyar, watanni 20 bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Agustan 2023.
Kwamitin zaman lafiya da tsaro na AU, ya yi la’akari da mika mulki da ya hambarar da Ali Bongo “gaba daya cikin nasara,” saboda haka ya yanke shawarar dage takunkumin nan take.
‘’Tsarin siyasar Gabon yana da ” gamsarwa” inji sanarwar kungiyar.
Wannan matakin na AU ya zo ne kwanaki uku gabanin rantsar da Janar Brice Oligui Nguema, wanda aka zaba a matsayin shugaban kasar a ranar 12 ga Afrilu.