Aminiya:
2025-05-01@00:24:34 GMT

An Kashe Shanu 36, an ba 42 guba a Filato

Published: 17th, April 2025 GMT

Shanu 36 sun mutu baya ga wasu 42 da ake zargin an ba su guba guba a kusa da yankin mahaɗar Tafi Gana a Ƙaramar Hukumar Bassa ta Jihar Filato.

Shugaban Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) a Karamar Hukumar Bassa, Ya’u Idris, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na yamma lokacin da shanun ke kiwo a yankin.

Ya’u ya ƙara da cewa an sanya guba ne a cikin gauta, waɗanda aka warwatsa a kewayen wurin kiwon kuma shanun suka ci.

Ya ci gaba da cewa sun kai rahoton lamarin ga dukkan hukumomin tsaro ciki har da Hukumar DSS, da ’yan sanda, ya kuma  Babban Kwamandan Rundunar ta kuma din ya ziyarci wurin da abin ya faru.

Wannan lamarin ya faru ne kwanaki biyu kacal bayan wani mummunan hari a kauyen Zikke, a cikin wannan ƙaramar hukumar ta Bassa, inda aka kashe mutane 52 tare da jikkata wasu da dama. An kuma kona gidaje da dama a harin.

Mazauna yankin da aka kai harin sun zargi makiyaya da hannu a kashe-kashen da aka yi a ranar Litinin, zargin da makiyayan suka musanta.

Kakakin rundunar tsaro ta Operation Safe Haven, Manjo Samson Zhakom, bai amsa saƙon da wakilinmu ya aike masa ba game da lamarin a lokacin da ake rubuta wannan rahoto.

An haramta kiwon dare da hawa babur

A sakamakon ƙaruwar rashin tsaro, Gwamna Caleb Mutfwang a ranar Laraba ya haramta kiwon dabbobi da daddare, da kuma jigilar shanu da hawa babura bayan ƙarfe 7 na yamma. Wannan matakin na daga cikin hanyoyin da gwamnatin jihar ta ɗauka domin hana ci gaba da samun sabani tsakanin makiyaya da manoma.

Gwamnan, a cikin wani jawabi da ya yi wa al’ummar jihar a ranar Laraba, ya bayyana cewa a makon da ya gabata, an kai hari kauyen Zikke inda aka kashe mutane da dama.

Sai dai, wannan dokar ta haifar da ce-ce-ku-ce, musamman ma daga direbobin manyan motocin da ke Jos, waɗanda suka bayyana haramcin jigilar shanu bayan karfe 7 na yamma a matsayin wanda ya ci karo da wata doka da ta riga ta hana zirga-zirgar manyan motoci tsakanin karfe 6 na safe zuwa 9 na yamma. Sun kuma roƙi gwamnatin da ta sake duba wannan doka.

Haka kuma, kungiyar MACBAN ta nuna damuwarta game da wannan doka, inda ta bayyana cewa lokacin da aka ƙayyade zai iya shafar rayuwar makiyaya, musamman wadanda za su iya kasancewa tare da shanunsu a kasuwanni bayan karfe 7 na yamma.

Sun cewa suna goyon bayan dokar domin tabbatar da zaman lafiya, amma suna roƙo gwamnan da ya ɗaga lokacin zuwa karfe 8 na dare domin mutanensu su samu damar komawa gida lafiya.

Laifin gwamnatocin baya ne — Gadgi

A nasa ɓangaren, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Pankshin Kanke da Kanam a Jihar Filato, Yusuf Adamu Gagdi, ya bayyana cewa abin takaici ne yadda yankunan da suka yi fice wajen noma a Bokkos, Bassa, Wase, da Mangu suka zama filin daga.

Ya zargi gazawar gwamnatocin baya wajen ba kama shugabannin hukumomin tsaro da laifin  gazawarsu wajen samar da tsaro a yankunansu da ta haifar da karuwar matsalar tsaro a kasar.

Gadgi ya kuma alaƙanta ƙaruwar hare-hare a Filato da tserewar da ’yan bindiga ke yi daga jihohi Zamfara da Sakkwato zuwa dajin Filato sakamakon ragargazarsu da sojoji suka tsananta.

Za mu dawo da zaman lafiya — ’yan sanda

Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan Sanda (DIG) Kwazhi Bzigu Dali ya ziyarci yankunan da aka kai hari domin tantance halin da ake ciki, inda ya gudanar da sintiri ta sama da ƙasa tare da ganawa da shugabannin ƙananan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki.

Ya kuma tabbatar wa mazauna yankin da cewa Sufeto-Janar na ’Yan Sanda ya ƙudiri aniyar dawo da zaman lafiya, inda ya sanar da tura karin jami’an tsaro da kayan aiki.

Dattawan Arewa sun fusata

Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta yi kakkausar suka ga kashe-kashen da ake yi a Filato, inda ta bayyana su a matsayin abin kunya ga ƙasa.

Sun soki rashin ɗaukar mataki da Gwamnatin Tarayya ke yi, suna masu kira da a tura jami’an tsaro da kayan aiki nan take tare da tabbatar da an yi adalci.

Haka kuma, Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta nuna baƙin cikinta game da sake ɓarkewar rikicin a Filato, inda ta yi kira ga shugabannin al’umma da na addini da su tallafa wa Gwamna Mutfwang wajen kwantar da hankula da kuma gina zaman lafiya mai ɗorewa.

Gwamnatin Tarayya ta sake nanata ƙudirinta na kawo ƙarshen rashin tsaro a faɗin ƙasar, inda ta bayyana ƙoƙarin da ake yi na ƙarfafa tsaron kasa.

Tsohon ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya yi kira ga gwamnatin da ta daina magana ta fatar baki kawai, ta ɗauki matakai na zahiri don kare ’yan Najeriya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Makiyaya Mutfwang Tsaro zaman lafiya

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda ’yan Tifa da baƙin direbobi ke haddasa haɗari a Abuja

Rayukan al’umma gami da dukiya musamman na ababen hawa na ci gaba da salwanta a Mahadar hanya ta yankin Tipper-garage da ke Dutse-Baupma, da ke kan titin da ya tashi daga garin Dutsen-Alhaji ya nufi garin Bwari, a yankin Birnin Tarayya Abuja.

Titin da ke mastayin tagwaye ya haɗa yankin da garin Jere da ke Jihar Kaduna.

Hanyar na ci gaba da ganin ƙaruwar kwararan motoci a sakamakon ingancinta da kuma karancin matsalar tsaro, idan a ka kamanta ta da babban titi Abuja zuwa Kaduna.

Rawar da Arewa za ta taka a Zaɓen 2027 An ɗaure ’yar shekara 80 a kurkuku saboda dukan jikarta da silifas

Adadin motoci da ke bin titin ya kara dagawa a bayabayan nan a dalilin mummunan cunkushewar hanya da ake fuskanta a garin Zuba Abuja da kuma Madalla da ke Jihar Neja, a sakamakon rufe hannu guda na hanyar biyo bayan fara aikinsa da wani sabon kamfani ke yi, bayan karbe aikin daga kamfanin Bega.

Baya ga motoci na matafiya da ke yawan ratsawa ta hanyar, akwai kuma motocin tifa da ke daukar duwatsu daga kamafanonin fasa duwatsu biyu da ke kusa da mahadar hanyan suna kai wa yankuna daban-daban na Abuja dama kewaye.

Aminiya ta ba da labarin cewa hatsarin mota na baya bayan nan da a ka fuskanta a hanyar su ne wanda ya auku a ranar Asabar 5 ga wannan watan na Afrilu, 2025, inda a ka rasa rayukan mutum biyar, bayan wata babbar mota tirela da ta fito ta kusurwan Bwari ta fuskanci matsalar tsinkewar birki a yayin da ta ke gangarowa daga hayin madatsar ruwa na Usuma dam da ke kan titin.

Tirelar ta taka kekunan adaidaita sahu guda biyar da ke daukar fasija a gefen hanayar, baya ga wani adadi na baburan acaba.

Kwana biyu bayan aukuwar hatsarin, an sake fuskantan wani a ranar Litinin da ta biyo baya inda wata babbar mota irin ta daukar bulo da ke dauke da albasa daga wata jiha ta Arewa ta rasa birki a yayin saukowa daga gangarar hanyar.

Ta buge kekunan kafin ta kife a kusa da wani magudanan ruwa da ke jikin hanyar.

An bada labarin rasa mutum biyu a yayin hatsarin, baya ga wasu da su ka tsira da raunuka.

Asarar rayuka da ta dukiya da muka yi — Masu tukin adaidaita sahu

Malam Fahad Musa na cikin shugabannin kungiyar ’yan yuniyon na masu sana’ar tukin Keken Adaidaita sahu da ke aiki a wurin.

Ya ce hatsarin farko ya faru ne da misalign karfe 7 na dare inda ya ce sun rasa mambobinsu uku, sai kuma dan acaba guda, a yayin da mutum na biyar din kuwa ya rasa ransa ne a dalilin harbinsa da bindiga da ake zargin wasu da suka taho cikin ayarin motoci suka yi, kamar yadda majiyoyi daban-daban suka shaidawa Aminiya.

Shugaban na ’yan yuniyon ya shaida wa wakilinmu a yayin ziyara a wajen cewa an kuma rasa kekune biyar a yayin hatsarin bayan motar ta bi ta kansu.

Ya ce faduwar motar ta farko ta yi sanadiyyar rufe hannu guda sannan ba a kai ga cire ta ba sai bayan hatsari na biyu a ranar Litinin.

Ya ce, a lokacin da ake kokarin zakulu mutane da suka mutu da kuma wadanda suka yi raunukan daga karkashin ababan hawan a ranar Asabar, an rufe daukacin tagwayen titin biyu da lamarin ya kai ga jawo takaddama bayan ayarin jami’an tsaro sun bulla ta wajen.

Wani da ya shaidi lamarin, ya shaida wa Aminiya cewa, a lokacin da ayarin motocin suka bullo, wani babba a cikin tawagar ya fito daga cikin mota tare da neman da a bude masu daya hanyar, amma sai ’yan asalin al’ummar yankin suka ki amincewa da bukatar hakan.

Ya kara da cewa, matasan sun bi motocin ayarin da jifa bayan sun kutsa ta daya hanyar da nufin wucewa, kuma a nan ne sai wasu daga cikin jami’an tsaron suka yi harbi cikin iska, a yayin da wani kuma ya harbi daya daga cikin matasa ’yan asalin yankin mai suna Timothy John, da ya mutu nan take.

Bayan nan, ayarin sun wuce da motocinsu cikin hanzari, kamar yadda aka bayyana wa Aminiya.

A yayin zantawarsa da Aminiya shugaban n ’yan yuniyon na masu sana’ar tukin adaidaita sahu ya ce, daya daga cikin direbobinsu mai suna Yusuf Auwal na cikin wadanda harsashin bindiga ya bi ta jikinsa.

Ya ce, bayan nan an garzaya da shi zuwa garinsu inda yake cigaba da jinya a yanzu.

Babban Kwamandan Hukumar Kare Hadurra na FRSC mai kula da yankin Dutsen-Alhaji, Mista Luka Wuna, ya tabbatar da faruwan haduran biyun, da kuma rasa rayukan, a yayin zantawarsa da wakilinmu a kan lamari.

Akwai bukatar ilimantar da direbobin Tifa

Binciken Aminiya ya bayyanan cewa, matsalar da tifofi ke samu ta shanyewar burki a yayin da suka ɗauko kaya kuma suka sukwano gangarar da daga ita sai marabar titin ita ce a mafi yawan lokaci ke haddasa munanan hadurra a wannan mahada.

Da yawan direbobin tifa matasa ne da basu san dokokin tuki ba sannan kuma suna tukin da ganganci tamkar suna tuka kananan motoci.

Don haka mafi yawa ba sa kula da yadda suke shawo wannan gangara ta la’akari da cewa, burkin tifa iska ce.

Wani masanin harkokin sufuri da ba ya son a ambaci sunansa ya ba da shaara cewa, ya kamata hukumomin da abin ya shafa su rinka shirya wa direbobin musamman na Tifa bita kan ka’idojin tuki da alamomin hanaya da kuma hatsarin da ke tattare da burkin mota mai dauke da iska.

Abinda ke jawo hatsari a wajen

Malam Anas Mu’azu na cikin ma’aikatan tattara haraji na Karamar Hukumar Bwari da ke ba da tikiti a wajen.

Ya ce, yawancin direbobi da ke fuskantar hatsarin baki ne da ke bi ta gangaren hanyar ba tare da cikakken masaniya a kan yadda wajen yake ba.

Ya ce, ”wutar ba da umarnin wucewa a wajen da ke da kusurwa 4 na bukatar tsayawar mota na wani lokaci a duk ta inda ta fito saboda dogon layi da motoci ke yi, sannan indan wutar ta haska don wucewa, adadi kadan ne na motoci ke iya wucewa kafin ta sake bukatar tsayar da mota,” in ji shi.

Malam Anas ya kara da cewa yawancin bakin direbobi da ke bin hanyar ba su da masaniya a kan tsarin wutar da kuma yanayin hanyar kasancewar babu allunan alamomi na hanya da ke fadakarwa a kan titin.

Ya ce, haka kuma a baya an cire kunyar kan titi da ke sa motoci rage gudun mota. ”A baya akwai kunyar titi na rage gudun da adadinsu ya kai kamar guda biyar, amma sai a ka cire su a lokaci guda ta hanyan kankare su daga kan hanyar,” in ji shi.

Ya ce, ko da Ministan Birnin Abuja Mista Nyesom Wike ya ba da aikin sake gina hanyar a bayabayan nan, ba a maida kunyar titin ba, har zuwa lokacin da haduran baya-bayan nan su ka auku..

Yadda za a magance matsala —Masu Tifa

Haka kuma Aminiya ta zanta da daya daga shugabannin masu motocin tifa da kuma harkar sayar da duwatsu daga kamfanoni biyu na fasa dutsi da ke yankin mai suna Kwamred Ose Idasho inda ya ba da shawarwaari kan yadda ya ke ganin za a magance yawaitar haduran, da ya ce sun bayar a yayin wani zama na musamman da Jami’an Hukumar Magance Hadurra ta FRSC a yankin.

Ya ce, “abu na farko shi ne bukatar a sa alamomin hanya tun daga kamar kilo mita uku kafin mahadar hanyar da zai rika sanar da direba hatsarin wajen tare da bukatar da ya yi takatsantsan.

“Sai kuma a sa abubuwa da ke sa rage gudun mota na kunyar hanya samfurin roba ba na siminta ba, da zai rika yin kara idan direba ya yi yunkurin yin gudu sosai. Hakan zai kara wa direba karsashi ko da ya fara yin gyangyadi.

“Mun kuma bukaci jami’an na FRSC da nemi dauki daga Hukumar Kula da Gine-gine ta Abuja kan su kawar da wuraren da ke sa mutane na tsayawa ta wurin, tare da mayar da shi sarari, sai kuma samar da wurearen yin lodi da kuma hana yin lodi a gefen titin.

“Haka kuma akwai bukatar a gyara wasu daga cikin fitilun ba da hannu da suka daina yin aiki, kamar wanda ya shiga ta bangaren Bamuko ta inda motocin tifa ke shiga da kuma yawan fita.

Sai kuma uwa-uba a gina gadar sama a wajen da zai rage girman gangarowar motoci da ke fitowa ta kusurwar Bwari ko DutsenAlhaji inda motocin za su bi ta saman gada,” in ji jagoran masu motocin tifa.

Ya kamata a gina gadar sama

Shi ma a zantawarsa da Aminiya, Sakataren Hakimin yankin na Dutse-Baupma mai suna Simon Luka da ya yi bayani a madadin hakiminsu, ya ce, hatsarin motoci a wajen ya jima yana jawo masu fargaba da kuma asarar rayuka da dukiya.

Ya buƙaci Ministan Birnin Tarayya Mista Nyesom Wike da ya taimaka wajen yin aikin gadar sama a wajen don magance matsalar.

Ya ce, tarihin farawar matsalar ba za ta gaza shekara 20 bayan an yi aikin hanyar.

Ya ce, matashin da aka kashe bayan jami’an tsaro sun buɗe wuta a wajen mai suna Timothy John, bai wuce shekara 20 ba kuma lamarin ya faru ne kasa da mako guda bayan mai gidansa ya yaye shi daga aikin walda da ya ke yi, inda yake shirin buɗe na kansa.

Ya kara da cewa, “sai dai har zuwa lokacin ziyarar nan babu wata ta’aziyya ko ta jaje da muka samu daga jamiu’an tsaro ko kuma hukuma, kan mutuwar matashin.”

Aminiya ta tuntubi Babbar Jami’ar Hulda da Jama’a a Sakatariyar da ke Kula da Sufuri a yankin Birnin Tarayya Abuja mai suna Misis Lecita Wogu, inda ta buƙaci lokaci don yin tsokaci a kan lamarin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Araghchi : Za’ayi Tattaunawar Iran da Amurka ta gaba a Rome bayan taron E3
  • Yadda ’yan Tifa da baƙin direbobi ke haddasa haɗari a Abuja
  •  Bom Da Ya Tashi A Arewa Maso Gabashin Najeriya Ya Kashe Mutane 6
  • Wani abin fashewa ya kashe mutum 26 a Borno
  • Ta yi wa saurayinta ƙaryar shekarunta 27 maimakon 47
  • Gwamnatin Yobe Na Ƙoƙarin Inganta Tsaro – Hon. Idi Gubana
  • Sojoji Sun Ceto Mutum 50 Da Aka Sace, Sun Ƙwato Shanu 32 A Katsina
  • Har Yanzun Ana Zaman Dar-Dar A Burkina Faso Bayan Kokarin Juyin Mulkin Da Bai SamiNasara Ba
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Ci Gaba Da Killace Gaza Da Kashe Mutane, Laifi Ne Da Ba A Taba Yin Irinsa Ba
  • Kissoshin Rayuwa: Imam Al-Hassan 114