Zargin Ganduje: Za mu sanar da lokacin yanke hukunci —Kotu
Published: 17th, April 2025 GMT
Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu ta Babbar Kotun ta Jihar Kano ta ce za ta yanke hukunci nan gaba a shari’ar cin hanci da rashawa da ake yi wa Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Abdullahi Ganduje, da matarsa Hafsat, da wasu mutane da kamfanoni shida.
Gwamnatin Jihar Kano ta tuhumi waɗannan mutane da kamfanoni da laifuka guda takwas da suka haɗa da karɓar rashawa, yin amfani da kuɗin jama’a ta haramtacciyar hanya, da kuma satar kuɗin gwamnati.
Ganduje ya yi gwamnan Jihar Kano daga shekarar 2015 zuwa 2023.
Lauyan Ganduje ya roki kotu da ta ba shi karin lokaci a shari’ar amma lauyan gwamnati ya soke wannan roko kuma ya bukaci kotu da ta yi watsi da shi.
Ka dawo Najeriya ka magance matsalar tsaro —Obi ga Tinubu Gwamnatin Tarayya ta buƙaci ’yan jarida su daina kawo rahoton ayyukan ’yan ta’adda Hisbah ta kama matashi yana ‘lalata’ da Akuya a KanoLauyoyin wasu mutane da kamfanoni da ake tuhuma a shari’ar sun kuma gabatar da wasu batutuwa kuma sun roki kotu da ta na su gaskiya tare da umartar gwamnati da ta biya su diyya.
Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu ta dakatar da sauraron ƙarar kuma ta ce za ta sanar da dukkan waɗanda abin ya shafa ranar da za ta yanke hukuncinta daga baya.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar
Antoni Janar na Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke birnin Yamai a Nijar, ya bayyana cewa an kama tsohon Ministan Harkokin Waje, Ibrahim Yacoubou, bisa zargin hannunsa a cikin wata aika-aika ta kisan kai domin yin tsafi.
A cewar Maazou Oumarou, lamarin ya samo asali ne daga wani binciken ’yan sanda da aka fara gudanarwa tun a ranar 29 ga Yuli, 2025.
KEDCO ya ƙaryata asibitin AKTH kan mutuwar majinyata saboda ɗauke wuta Dole sai mun tantance wa’azi kafin a yi —Gwamnan NejaYa bayyana cewa, an soma gudanar da binciken ne dangane da yunƙurin kisa a wani yanki da ke wajen birnin Yamai, lamarin da ya kai ga cafke ababen zargin a garin Dosso.
Wani mutum mai suna Mahamadou Noura ne ya bayyana cewa shi ne ya yi yunƙurin kisan, tare da wasu kashe-kashe guda shida da ya aiwatar a baya, bisa umarnin wasu mutane, ciki har da tsohon ministan Ibrahim Yacoubou.
Mutumin ya shaida wa mahukunta cewa ya aikata hakan ne domin yin tsafi da gawarwakin, a madadin wasu mutane da suka haɗa da: Issa Ali Maiga da Ismael Morou Karama da Elhadji Bilya da kuma Issa Seybou Hama.
TRT ya ruwaito cewa tuni dai an cafke duk ababen zargin, yayin da Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta umurci ’yan sanda da su ci gaba da bincike tare da ɗaukar ƙarin matakan da za su tabbatar da gaskiya.
Sanarwar ta ce: “Manufar wannan mataki na shari’a ita ce a tattara cikakken rahoto da ke ƙunshe da dukkan abubuwan da suka faru, sannan a miƙa shi ga ɓangaren gurfanarwa.”
Mai shigar da ƙara a ɓangaren gwamnati ya ce, la’akari da girman wannan lamari, wajibi ne a gudanar da bincike cikin gaggawa.
Haka kuma ya buƙaci al’umma da su mutunta ’yancin kotu tare da bayar da cikakken goyon baya domin fayyace gaskiya.
Ana iya tuna cewa, Ibrahim Yacoubou na daga cikin manyan jami’an da aka kama bayan juyin mulkin Nijar na ranar 26 ga Yuli, 2023, sai dai daga bisani an ba shi beli na wucin gadi a cikin watannin baya.