Kasar Sin Za Ta Yi Ramuwar Gayya Kan Takunkumin Biza Da Amurka Ta Kakaba Wa Jami’anta
Published: 2nd, April 2025 GMT
A yau Talata, kasar Sin ta bayyana cewa, za ta dauki matakan ramuwar gayya domin mayar da martani game da sanarwar da Amurka ta fitar ta saka takunkumin biza a kan jami’an kasar Sin, bisa hujjar hana izinin shiga yankin Xizang mai cin gashin kansa, da ke kudu maso yammacin kasar Sin.
A yayin taron manema labarai da aka saba yi a-kai-a-kai, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun ya bayyana cewa, yankin Xizang a bude yake ga kowa da kowa, kuma ba a hana baki daga kasashen waje shiga ba, inda ya kara da cewa, yankin yana karbar dimbin matafiya da sauran al’ummomi da dama daga sassa daban-daban a kowace shekara, domin ko a shekarar 2024 kadai, akalla baki 320,000 ne suka shiga yankin.
Jami’in ya ce, kasar Sin tana kira ga Amurka da ta mutunta alkawuran da ta dauka kan batutuwan da suka shafi Xizang, da daina hada baki ko goyon bayan masu gwagwarmayar “’yancin kai” na Xizang, da kuma dakatar da amfani da batutuwan da suka shafi Xizang wajen yin katsalandan a harkokin cikin gidan kasar Sin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ƴan Bindiga Sun Sace Malamin Krista Na Ɗarikar Katolika A Kogi
Haka kuma, wannan na faruwa ne makonni biyu bayan yin garkuwa da Pastor Friday Adehi na Christian Evangelical Fellowship of Nigeria (CEFN) tare da wani abokin cocinsa bayan kammala wa’azi. Wannan ya kara nuna yadda matsalar garkuwa ke ta’azzara a yankin Kogi East.
A gefe guda, kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA), reshen Idah, ta bukaci gwamnati a matakai daban-daban da ta dauki matakan gaggawa don kawo karshen satar mutane a jihar. Shugaban kungiyar, Barr. James Michael, ya ce yawaitar garkuwa a kan titunan yankin ya jefa rayukan jama’a cikin hatsari, don haka gwamnati ya kamata ta dauki tsauraran matakai domin kare lafiyar al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp