Harin ’Yan bindiga: Mun yi asarar shanu sama da miliyan 4 – Miyetti Allah
Published: 20th, February 2025 GMT
Ƙungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) ta yi iƙirarin cewa wasu ’yan bindiga sun sace sama da shanu miliyan huɗu na mambobinta musamman a yankin Arewa maso Yamma.
Shugaban Ƙungiyar MACBAN na ƙasa, Baba Usman ne ya bayyana hakan a yayin ƙaddamar da sababbin zaɓaɓɓun shugabannin ƙungiyar na jiha a Jihar Kebbi.
Ya ce, ɓarayin shanu na yawan kai wa Fulani makiyaya hari, lamarin da ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.
Usman ya jaddada cewa, ana yawan sauya fahimtar Fulani makiyaya da kuma yin kuskuren sanya su a matsayin masu tayar da fitina, inda ya buƙaci jama’a su riƙa ganin su a matsayin ’yan Najeriya masu son zaman lafiya.
Ya kuma yi kira ga makiyaya da su guji shiga gonaki, su kuma zauna lafiya da manoma domin hana rikice-rikice.
Usman ya kuma yabawa gwamnatin tarayya da na jihohi bisa kafa ma’aikatar kiwo, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen magance matsalolin da makiyaya ke fuskanta.
Ya kuma yabawa gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris bisa ayyukan da suka inganta rayuwar al’ummar Fulani.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Fulani makiyaya
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun sace mutum 40 a masallaci a Zamfara
Aƙalla masallata 40 ’yan bindiga suka sace a wani masallaci da ke Gidan Turbe a Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara da safiyar wannan Litinin.
Majiyoyi sun ce an yi awon gaba da masallatan ne zuwa dazukan Gohori da ke yankin Tsafe.
Hauhawar farashi ya ragu a watan Agusta — NBS NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a LegasWannan harin dai kai tsaye masu ruwa da tsaki na kallonsa a matsayin kawo ƙarshen yarjejeniyar sulhu tsakanin ’yan bindigar da mahukuntan jihohin Zamfara da Katsina.
A baya-bayan nan ne jihohin Katsina da Zamfara suka ƙulla yarjejeniyar sulhu tsakaninsu da ’yan bindigar da suka addabi al’ummar jihohin arewa maso yammacin Najeriyar.
Yarjejeniyar sulhu da aka cimma a dajin Wurma ta samu halartan manyan ’yan bindiga irinsu Alhaji Usman Kachalla Ruga da Muhindinge da Yahaya Sani ( Hayyu ) da kuma Shu’aibu.
A ɓangaren mahukunta, akwai Maradin Katsina da Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi da kuma shugaban ƙaramar hukuma Babangida Abdullahi Kurfi.
’Yan bindiga sun saki wasu mutane da suke garkuwa da su a lokacin yarjejeniyar sulhun, tare da barin al’umma zuwa gonakinsu ba tare da wata fargaba ko tsangwama.
To sai dai kuma, ƙasa da wata guda bayan cimma wannan yarjejeniya, rahotanni sun ce ’yan bindiga sun kutsawa wani ƙauye a Zamfara tare da awon gaba da masallata.
Shaidun gani da ido sun ce, maharan sun yi wa masallacin ƙawanya da misalin ƙarfe 5:30 na safe, daidai lokacin da jama’a ke sallar asuba.