2025-06-07@13:18:18 GMT
إجمالي نتائج البحث: 813
«Lawal Uwais»:

Batun Zuba Hannun Jari A Amurka Ne Babbar Ajandar Ziyarar Shugaba Donald Trump Zuwa Kasashen Larabawan Yankin Tekun Pasha
A yau Talata ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya isa kasar Saudiyya domin fara ziyarar aiki a karon farko tun da ya zama shugaban kasa. Baya ga kasar Saudiyya shugaban kasar ta Amurka zai kuma kai Ziyara zuwa kasashen Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa da zummar bunkasa alaka da larabawan yankin tekun Pasha kamar...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Tattaunawar Iran da Amurka ba zata shafi matakin jan layi da Iran ta gindaya ba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa da gaske kasarsa tana tattaunawa da Amurka, kuma tana neman cimma matsaya, amma batun neman yin watsi da cibiyoyin nukiliyarta wani zabi ne da ba za...
Sojojin mamayar Isra’ila sun aiwatar da mummunan kisan kiyashi a garin Jabaliya, tare da janyo shahada da jikkatan wasu a Khan Yunis A rana ta 56 da sake komawa yaki ta hanyar kai hare-haren wuce gona da iri kan Gaza, sojojin mamayar Isra’ila sun ci gaba da yin luguden wuta kan wasu wuraren zama, da...
Masana kimiyya suna ƙoƙarin fahimtar yadda garken awaki ke rayuwa a wani tsibiri da ke Arewa maso gabashin Brazil fiye da ƙarni biyu (shekara 200) ba tare da samun tsaftaccen ruwan sha ba. Ba a fayyace yadda ainihin awakin suka hau saman tsaunin Santa Barbara tun a farko ba, wanda ɗaya ne daga cikin tsibirai...
Yayin da a wannan Litinin ake bikin ranar jami’an jinya ta Duniya ta shekarar 2025, hukumar lafiya ta Duniya WHO ta ce akwai kashi 42 cikin 100 na ma’aikatan jinya a Afirka, dake cike da burin ficewa daga nahiyar saboda rashin cikakkiyar kulawa da kuma albashi mara tsoka. A jawabin da ya gabatar akan ranar...
Kungiyar Kurdawan Turkiya PKK ta sanar da cewa za ta ajiye makamanta ta kuma rusa kanta. Kamfanin dillancin labarum “Furat” mai kusanci da kungiyar ta PKK, ya nakalto cewa; Kungiyar ta yanke zartar da wannan matakin ne a yayin taron da ta yi kaso na 12 da ta yi kwanaki kadan da su ka gabata....
Shugaban Asibitin ido dake Gaza, Dr. Abdussalam Sabah, ya sanar da cewa, adadin Falasdinawan da su ka rasa ganinsu sanadiyyar yaki sun kai 1500. Dr. Abdussalam ya kuma yi gargadin cewa da akwai wasu Falasdinawa da sun kai 4000 da suke fuskantar barazanar rasa idanunsu saboda rashin kayan aiki a asibiti da kuma magani. Likitan...
Kungiyar Hamas wacce take iko da yankin Gaza, ta bada sanarwan cewa a shirye take ta saki fursina mai suna Edan Alexander wanda yake da jinsiyar Amurka da HKI don bude kofa ga tattaunawar tsagaaita wuta a gaza da kuma bude kofar rafa don samar da kayakin abicni a gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na...
A yayin da ta bayyana cewar a shiri na gaba za a zakulo matan karkara sosai ta ce ta jagoranci shirin ne ba wai a matsayin kashin kan ta ba, sai dai domin ta karfafawa mutum mai kishin al’umma da hangen nesan inganta rayuwar su. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
Iran ta bayyana cewa tattauanwa ta hudu data wakana tsakaninta da Amurka tana da wahala amma kuma tana da amfani. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya ce zagaye na hudu na tattaunawar da Amurka abu ne mai wahala amma mai amfani ce. M. Baghaei ya bayyana hakan ne a wani sako da ya...
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana fatan ganin kasashen India da Pakistan sun kai zuciya nesa, tare da warware sabani ta hanyar shawarwari da tattaunawa, kana su gujewa sake rura wutar tashin hankali. Wang ya bayyana hakan ne a jiya Asabar, yayin tattaunawa ta wayar tarho da mashawarcin gwamnatin India ta fuskar...
Falasdinawa mazauna yankunan Khan-Yunus dake kudancin zirin Gaza suna fama da matsananciyar yunuwa, a lokaci daya suna fuskantar hare-hare masu tsanani daga sojojin HKI. Mata mazauna yankin sun fi fuskantar matsaloli saboda kananan yaran da suke tare da su, alhali kuma an rushe gidajensu. A tsawon yakin kisan kiyashin da HKI take yi, matan da...
Jakadan JMI a MDD ya musanta zargin kamfanin dillancin labaran reuters dangane da rotohonsa na cewa JMI tana aika makamai masu linzami zuwa kasar Rasah don taimakawa kasar Rasha yakin da take fafatwa da kasar Ukraine fiye da shekaru 3 da suka gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ofishin jakadancin JMI...
Wani babban hafsan sojin Yemen ya bayyana dabarun Yemen da suka tilastawa Amurka dakatar da kai hare-hare kan kasar Yemen Kwararren kan harkar sojin kasar Yemen kuma kwararre kan harkar yaki Birgediya Janar Aziz Rashid ya jaddada bunkasar karfin sojan kasar Yemen, yana mai nuni da dalilan da suka sanya aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta...
Fira ministan kasar Pakistan Shahbaz Sharif ya kira yi Majalisar kasa wacce take kula da makaman Nukiliyar kasar da su yi taro. Wannan matakin da ake yi wa Kallon mai hatsari yana faruwa ne a daidai lokacin da kasar ta Pakistan take yaki da Indiya. Ita dai Majalisar kasar Pakistan dake kula da makaman Nukiliya...
A wani lokaci a gobe Asabar ne ake sa ran ministan harkokin wajen Iran zai fara wata ziyara a kasashen Saudiyya da kuma Qatar. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa, ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi zai ziyarci Saudiyya da Qatar a, bayan rahotannin da ke cewa akwai yiwuwar yin wata sabuwar tattaunawa...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce za a gudanar da zagaye na hudu na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka ranar Lahadi. Araghchi ya bayyana a yau Juma’a cewa Oman ce, zata kasance mai shiga tsakani, kuma ita ce ke tantance lokaci da wurin da za a yi tattaunawar. Ya kara da cewa bisa...
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni a ranar Alhamis ya ziyarci sojojin Hedikwatar Task Force Brigade ta 27 Buni Gari, domin jajantawa waɗanda aka kashe kan harin da ’yan tada ƙayar baya suka kai. A cikin jawabinsa Gwamna Buni ya bayyana cewa, abin takaici ne ga sake ɓarkewar tashe-tashen hankula da kuma hare-haren da ake...
Hukumar jindadin Alhazai ta jihar jigawa ta gudanar da taro da shugabanin shiyya shiyya da kuma jami’an alhazai na kananan Hukumomi Jihar 27 a shelkwatar hukumar dake Dutse gabannin fara jigailar maniyatan aikin hajjin bana. A lokacin da yake jawabi, Darakta Janar na Hukumar Alhaji Ahmed Umar labbo ya ce taron yana da muhimmanci kasancewar...

Iran Ta Yi Tsokaci Kan Jita-Jitar Da Ake Yadawa Cewa: Shugaban Kasar Iran Zai Gana Da Shugaban Amurka
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi tsokaci kan jita-jitar cewa: Shugaban kasar Iran zai gana da shugaban kasar Amurka Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya yi watsi da jita-jitar da ake yadawa game da batun cewa shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian zai yi wata ganawa da shugaban Amurka Donald Trump a mako mai...

Falasdinawa Sun Yi Shahada A Hare-Haren Da Sojojin Isra’il Suka Kai Gidan Cin Abinci Da Kasuwa A Gaza
Falasdinawa da dama ne suka yi shahada tare da jikkata sakamakon hare-haren bama-bamai da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gidan abinci da wata shahararriyar kasuwa a Gaza Akalla Falasdinawa 20 ne aka kashe tare da raunata wasu da dama a jiya Laraba a wani sabon kisan kiyashi da jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar...
Fira ministan kasar Siriya ya bayyana cewa: Kasar Siriya zata gudanar da tattaunawa ba na kai tsaye ba da haramtacciyar kasar Isra’ila! Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Siriya Abu Mohammed al-Julani ya sanar a jiya Laraba cewa: Kasar Siriya zata gudanar da zaman tattaunawa ba na kai tsaye ba da gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar...
Wani rahoto na musamman da HKI ta gudanar akan asarar da ta fuskanta sanadiyyar yaki da Hizbullah, ya bayyana cewa, a fagen aikin gona kawai sun yi asarar dalar Amurka miliyan 108 wacce ta fara daga 8 ga watan Oktoba 2023. Kungiyar ReGrow Israel” ta ce, yakin da aka yi da Hizbullah ya yi barna...

Sharhin bayan Labarai: Mahangar Iran Dangane Da Tattaunawa Kan Shirinta na Makamashin Nukliya Na Zaman lafiya
Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayana labarummu na yau zai yi magana dangane da ‘Mahangar Jumhuriyar Musulunci na Iran ta yadda za’a kai ga fahintar juna a tattaunawanta da kasar Amurka da suke yi wanda ni tahir amin zan karanta. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a wata tattaunawa ta wayar tarho da tokwaransa...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk shekara, dalibai kan rubuta jarabawa a matakai daban-daban na makarantu daban-daban. Ɗaya daga cikin nau’ukan jarabawa da ɗaliban Najeriya suke yi ita ce Jarabawar Neman Shiga Manyan Makarantu, wato UTME. Kamar kowace shekara, a bana ma ɗalibai sun rubuta wannan jarabawa kuma a cewar Hukumar Shirya Jarabawar...
Kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ta mabiya Al-Houthi ta sanar da cewa: Sanarwar da shugaban Amurka ta fitar kan Yemen gazawa ce ga Netanyahu Kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ta sanar a jiya Talata cewa: Sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi dangane da kasar Yemen gazawa ce ga Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar...
Shugaban tawagar kasar Yemen, Mohammed Abdul Salam, ya sanar da cewa ayyukan Yemen na tallafawa Gaza ba zai tsayawa ba Shugaban tawagar shiga Tsakani na kasar Yemen Abdul Salam ya bayyana cewa: Yemen ta samu sakon bukatu daga Amurka ta hanyar masarautar Oman, kuma wanda ya sauya matsayinsa Amurka ce, ba Yemen ba. Ya kara...
Kasar Sudan ta yanke huldar jakadancinta da kasar Hadaddiyar Daulart Larabawa tana mai ayyana UAE a matsayin ‘kasa mai cin zali’ Kamfanin dillancin labaran Sudan (SUNA) ya watsa rahoton cewa: Kwamitin tsaro da kula da matakan tsaron kasar Sudan ya sanar a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata cewa: Sudan ta yanke...
Majalisar Dattawa ta kafa kwamiti mai mambobi 18 domin sanya idanu kan yadda gwamnan riƙo na Jihar Ribas Vice Admiral Ibok Ete Ibas mai ritaya ke tafi da aikinsa. Majalisar ta ce ta ɗauki matakin ne a wani yuƙuri na ƙarfafa shugabanci na gari ba tare da rufa-rufa ba a jihar da ke kudu maso...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hanyar deblomasiyya ce kadai zata warware matsakar shirin nukliyar kasar iran da kasashen yamma. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a zantawa ta wayar tarho da jami’a mai kula da al-amuran harkokin waje na kungiyar tarayyar Turai Kaja...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaaei ya bukaci kasashen turai da su shiga a dama da su kan tattaunawa dangane da shirin nukliyar kasar Iran na zaman lafiya. Ya kuma jaddada cewa Iran tana turjiya ga dukkan tunanin Amurka na wargaza shirin Nukliyar kasar Iran kwata-kwata. Baghaei ya kara da cewa duk da...
A yau, rukunin farko na tawagar wanzar da zaman lafiya da martanin gaggawa na kasar Sin kashi na biyu wadda za ta je yankin Abyei, ya tashi daga birnin Zhengzhou na kasar Sin, da jirgin saman soja domin gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya na tsawon watanni 12. Bugu da kari, ana shirin tura...
Kawamcen jam’iyyun siyasa na kasar Ivory Coast ya bukaci a sake lalen yadda aka tsara yadda ake ristar jam’iyyu a hukumar zaben kasar, ganin yadda ta hana rijistar wasu jam’iyyun saboda dalilai daban daban. Shafin yanar gizo na labarai Afirka news ya bayyana cewa an kafa kawancen ne wanda aka sanyawa suna CAP-CI a farkon...
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta kaddamar da manyan jami’an likitocin kasa a shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin shekarar 2025. Babban Daraktan Hukumar Alhaji Umar Ahmed Labbo ne ya bayyana haka a yayin bikin kaddamar da aikin da aka gudanar a Dutse babban birnin jihar. Ya bayyana cewa, hukumar ta kaddamar da...
A bidiyon da wani mai suna Nawab Sheikh ya fitar na nuna yadda ya hau motarsa, wacce yake tuka ta a kan titunan birnin Murshidabad a cikin ƙasar Indiya, don nishaɗantar da mahaya babur, wanda ya sa bidiyon yake ta yaɗuwa a shafin sada zumunta na Instagram. Babu wani wuri mafi kyawun nuna bajintar kirkira...
Wani matashi dan shekarar 20 ya fada hannun hukuma kan zargin kashe mahaifinsa da adda a Jihar Jigawa. Rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa ta kama wanda ake zargin kashe mahaifinsa mai shekara 57, da adda. Wanda aka kashe ya samu raunuka a kafadarsa da wuya da kirjinsa, kuma an kai shi Babban Asibitin Tarayya (FMC)...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta bayyana cewa tattaunawar sulhu a Gaza ba ta da wani tasiri a wannan mataki. Ofishin kungiyar, ya yi kira ga kasashen duniya da su matsa lamba kan gwamnatin Netanyahu don kawo karshen laifukan yunwa, kishirwa da kisan kai a Gaza, in ji wani babban jami’in kungiyar. Halin da ake...

Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Sha Alwashin Mayar Da Martani Cikin Gaggawa Kan Duk Wani Hari Kan Kasarta
Jamhuriayar Musulunci ta Iran ta sha alwashin mayar da martani cikin gaggawa ga duk wani kasadan ‘yan Sahayoniyya da Amurka kan kasarta Jakada kuma zaunannen wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani ya jaddada cewa: Duk wani kasadan harin soji da Amurka ko wakilliyarta gwamnatin ‘yan sahayoniyya suke yi, ko...
Falasdinawa fiye da 50 ne suka yi shahada yayin da wani adadi da dama suka jikkata a hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai Gaza a jiya Litinin Rahotonni sun bayyana cewa: Fiye da Falasdinawa 50 ne aka suka yi shahada wasu adadi da dama kuma suka jikkata sakamakon hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila ke...
A nasa jawabin, shugaban NAHCON ya bukaci tawagar da ta tunkari wannan aiki tare da himma da kwazo, tare da jaddada tsarkin aikin da ke gabansu. Wannan Tawagar ta musamman, ita ce ke da alhakin kafa harsashin gudanar da aikin Hajji baki daya, da suka hada da tsare-tsare na masaukai, ka’idojin karbar baki a...
A cikin wata daya kadai sojojin HKI sun rushe gidajen Falasdinawa 152 a yammacin Kogin Jordan. Majiyar Falasdinawa ta ambaci cewa a kudancin garin Khalil ‘yan mamayar sun rushe gidaje 25 da kuma wasu cibiyoyi, da hakan ya sa adadin gidajen da su ka rushe zuwa 152 kamar yadda hukumar Falasdinu ta ambata. Bugu da...
Kotun duniya ta yi watsi da karar da Sudan ta kai Hadaddiyar Daular Larabawa tana mai zarginta da hannu a kisan kiyashin da aka yi wa al’ummar wannan kasa. A yau Litinin ne kotun duniyar ta yi watsi da karar ta Sudan, tana mai wanke Hadaddiyar Daular Larabawa. Ita dai Sudan ta zargi Hadaddiyar Daular...
Yau Litinin ne kotun kasa da kasa ta ICJ za ta yanke hukunci kan karar da Sudan ta shigar kan Hadaddiyar Daular Larabawa. Khartoum ta kai karar UAE a gaban kotun kasa da kasa da ke birnin Hague, inda ta zarge ta da hannu wajen kisan kiyashin da ake yi wa al’ummar Masalit, sakamakon zarginta...
Ana ci gaba da gwabza kazamin fada a yammacin Sudan tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa na kasar Jiragen saman yaki marasa matuki ciki na dakarun kai daukin gaggawa sun kai hare-hare kan sansanin sojin sama na Osman Digna da ke gabashin Sudan, inda suka janyo bullar gobara a ma’ajiyar harsasai. Jiragen saman...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Argchi ya zanta ta wayar tarho da babban sakataren MDD Antonio Guterres inda ya fada masa inda aka kwana a tattaunawar da kasarsa take da Amurka ba kai tsaye ba. Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran ya nakalto Arigchi yana fadawa babban sakatarin kan cewa akwai bukatar bangarorin...
113-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau, shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantake tsaro da sauransu inda muke masu karin bayani sannan daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da...
Shugaban karamar hukumar Babura ta jihar Jigawa, Malam Hamisu Muhammad Garu, ya kaddamar da shirin karfafa aikin gona da nufin sanya matasa aikin noman shinkafa a wani bangare na kokarin inganta ayyukan yi da samar da abinci a yankin. Da yake jawabi yayin bikin kaddamar da aikin aka gudanar a garin Babura, shugaban ya...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya yaba da sadaukarwar da ‘yan jarida suka bayar da suke ba da labaran irin wahalhalun da Falasdinawa ke ciki A wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter na ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana jin dadinsa ga...
Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta tabbatar da cewa: Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon ayyukan ta’addancin ‘yan sahayoniyya ya karu zuwa 52,495 Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar a jiya Asabar 3 ga watan Mayu, shekara ta 2025 cewa: Falasdinawa 77 ne da suka yi shahada da suka hada da gawarwakin mutane 7 da aka...