Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-09-18@09:07:23 GMT

NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawa Na 2025

Published: 18th, September 2025 GMT

NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawa Na 2025

Hukumar shirya jarabawar ta kasa NECO ta fitar da jarabawar SSCE dalibai dubu 818, 492 suka sami kiridit 5 zuwa sama da suka hada darasin Ingilishi da Lissafi.

 

Adadin bisa ga sakamakon ya nuna dalibai kashi sittin da biyu sun smai nasara.

 

Magatakardar NECO kuma Babban Jami’in Hukumar, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi ne ya bayyana haka a lokacin da yake fitar da sakamakon jarabawar SSCE na shekarar 2025 a hedkwatar NECO da ke Minna babban birnin Jihar Neja.

 

Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi ya bayyana cewa adadin dalibai miliyan daya da dubu dari da arba’in da hudu da dubu dari hudu da casa’in da shida da ke wakiltar maki tamanin da hudu da suka zana jarrabawar sun samu kiridit 5 ko sama da haka ba tare da la’akari da harshen Ingilishi da lissafi ba.

 

A cewar Farfesa Danteni “. A yayin gudanar da jarrabawar kammala sakandare ta shekarar 2025, (SSCE), an gano makarantu talatin da takwas suna yin magudin zabe) a jihohi talatin, yana mai jaddada cewa, za a gayyace su zuwa majalisar domin tattaunawa, bayan haka za a sanya takunkumin da ya dace.

 

Shugaban Hukumar NECO ya yi nuni da cewa an ba manya jami’ai Tara, Uku a Kogi, Daya a Niger, Uku a F.C.T, Daya a Kano da Daya a Jihohin Osun takardar gargadi saboda rashin kulawar da ake yi, wanda ya sa aka samu makara, rashin da’a, cin zarafi, da rashin biyayya.

 

Ya ce a lokacin Jarrabawar an samu rikicin kabilanci wanda ya haifar da bullar takardun jarrabawar a Jihar Adamawa daga ranar 7 zuwa 25 ga watan Yulin 2025 da ya shafi makarantu Takwas (8), inda ya ce jimillar darussa goma sha uku da takardu ashirin da tara (29) ne wannan lamarin ya shafa, sannan kuma dalibai dari biyar da casa’in da tara ne abin ya shafa.

 

NECO ta fara tattaunawa da jihar Adamawa da nufin gudanar da jarrabawar makarantun da abin ya shafa, inda ya nuna cewa ba za a iya fitar da sakamakon makarantun takwas a yanzu ba.” Inji magatakardan NECO.

 

Farfesa Dantani Wushishi ya bayyana cewa an fitar da sakamakon jarrabawar cikin gida na SSCE kwanaki hamsin da hudu bayan rubuta na karshe a watan Agusta, 2025, wanda ke nuni da cewa an kammala dukkan matakan da suka kai ga samun nasarar fitar da sakamakon cikin gida na 2025 SSCE.

 

Ya kara da cewa, fitar da sakamakon na cikin 2025 na SSCE cikin sauki, shaida ne na ma’aikatan Hukumar Jarrabawar bisa kwarewa, da’a da kuma ci gaba da neman nagartarsu, da sanin ya kamata, da kula da inganci, da jajircewa wajen bin ka’idojin da’a, sun tabbatar da cewa NECO ta samar da sakamakon da ya dace kuma dalibai, cibiyoyi da sauran jama’a suka amince da su.

 

 

Farfesa Dantani ya bayyana matukar godiya ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinuba bisa jajircewarsa wajen ganin an inganta ilimi ya samar da kyakkyawan yanayi ga hukumar NECO ta samu ci gaba, ya kuma yabawa ministan ilimi Dr Maruf Tunji Alyssa da karamin ministan ilimi Farfesa Suwaiba Said Ahmad bisa goyon baya da fahimtarsu.

 

COV ALIYU LAWAL.

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: fitar da sakamakon Farfesa Dantani

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno

Sojojin Najeriya sun kashe aƙalla mayakan ƙungiyar ISWAP 8, ciki har da manyan kwamandojinta biyu a Jihar Borno.

Wata majiyar leƙen asiri daga rundunar haɗin kai ta OPHK ta bayyana cewa an kashe ’yan ta’addan ne a wata arangama da suka yi da sojojin a kan hanyar Maiduguri zuwa Baga a safiyar ranar Litinin.

DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala

A cewar majiyoyin, an yi arangamar ce a kusa da Garin Giwa da ke gab da ƙauyen Kauwa, lokacin da ’yan ta’addan suka yi wa dakarun da ke sintiri kwanton ɓauna.

“A yayin wannan artabu, an kashe ’yan ta’adda takwas, ciki har da Munzirs biyu (kwamandojin filin daga na ƙungiyar) da kuma Qaid ɗaya (shugaban sashe).

“An kashe Modu Dogo, Munzir daga Dogon Chukun, wani Munzir da ba a bayyana ba, da Abu Aisha, shugaban sashe (Qaid) daga Tumbun Mota,” in ji wata majiya.

Majiyar ta ƙara da cewa wasu mayaƙa da dama sun samu raunuka, musamman waɗanda suka tsere da ƙafa bayan sun yi watsi da babura 14 da sojojin suka ƙwato.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwara ETF Ya Dauki Nauyin Karatun Fitattun Dalibai A Matakin Sakandare
  • Manyan Ma’aikatan FIRS 4 Sun Rasu Sakamakon Gobarar Da Ta Tashi A Ginin Afriland A Legas 
  • NECO ta saki sakamakon jarabawar 2025
  • NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2025
  • Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi
  • Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
  • Bida Poly ta kawo sojoji su kula da jarrabawar ɗalibai
  • An Karrama Farfesa Adamu Gwarzo Kan Gudummawarsa Ga Bunƙasa Ilimin Jami’a A Nijeriya
  • Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada Sakamakon Kisan Kiyashin ‘Yan Sahayoniyya A Gaza Ya Kusaci 65,000