2025-05-26@03:37:26 GMT
إجمالي نتائج البحث: 795

«Goyon Bayan»:

    Wata muhawara ta kunno kai a Jihar Kano da ma wajenta bayan gwamnatin jihar ta ba da umarni a cire naira miliyan 670 daga asusun ƙananan hukumomin jihar domin saye da kuma gyaran motocin Mai Martaba Sarkin Kano, Muhanmmadu Sanusi II. Gwamnatin jihar ta bayyana cewa za a kashe naira miliyan 50 daga cikin kudin...
    A Talatar makon jiya ce Inter Milan ta ƙara lalata wa Barcelona mafarkinta na ɗaukar Kofin Zakarun Turai a shekaran nan, bayan an yi kare-jini-biri-jini tsakanin kungiyoyin guda biyu a wasan kusa da na karshe. An tashi wasan ne da ci 4-3 a San Siro gidan Inter Milan bayan sun yi 3-3 a gidan Barcelona....
    Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya soki ’yan siyasar da ke sauya sheƙa daga jam’iyyar da a ƙarƙashinta suka samu nasarar lashe zaɓe zuwa wata. Kwankwaso ya bayyana lamarin a matsayin cin moriyar ganga, yana mai cewa hakan babban kuskure ne a siyasance. HOTUNA: An ƙaddamar da tashin sahun farko na maniyyatan Nijeriya...
    BBC ta rawaito cewa, babban abin da ke damun kamfanin na Meta shi ne, yadda al’amarin ya shafi Hukumar Kare Bayanan Sirri ta Nijeriya (NDPC), wanda kamfanin ke zargin karya dokokin kare bayanan sirrin kasar. Baya ga tarar Hukumar FCCPC, hukumar ta NDPC ta ci tarar kamfanin Meta dala miliyan 37.8, bisa zargin satar bayanan...
    Dubban daruruwan mutane a kasar Yemen sun fito kan tituna suna bayyana jin dadinsu da samun nasara a kan kasar Amurka a yakin da suka dau makokinni suka fafatawa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa an daw makonni jiragen yakin Amurka suna kai hare-hare kan wurare daban daban a kasar Yemen...
    Kotun tarayya da ke Abuja ta ɗage ƙarar tuhumar tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello kan zargin badaƙalar kuɗi da hukumar EFCC ta gabatar zuwa ranakun 26, 27 ga Yuni da 4, 5 ga Yuli don yanke hukunci kan buƙatar masu gabatar da ƙara ta “yi wa shaidar tambayoyi” da kuma ci gaba da shari’ar....
    Ƙungiyar Allied Group of Nasarawa Professionals (AGNP), wadda ta ƙunshi ’yan kasuwa da masu sana’o’in hannu, ta goyi bayan tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Mohammed Adamu, wanda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a 2027. A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ofishinta da ke Keffi, AGNP ta ce matakin...
    Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-husy ya bayyana cewa kisan kiyashin  da HKI take yi wa Falasdinawa a tsawon  watanni 19 a jere, shi ne laifi mani muni  akan bil’adama da ya faru a cikin karni daya. Sayyid Abdulmalik al-Husi ya kuma ce, abinda ya kara munin wannan laifin shi ne yadda...
    Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kasim, ya bayyana cewa mutanen kasar Lebanon zasu ci gaba da gwagwarmaya da HKI wacce ta ke mamaye da wasu kasashen larabawan yankin har zuwa nasara. Tashar talabijibn ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sheik Kasim yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar ta...
    Wasu yan jaridu masu bincike a kasar Amurka sun gano sunan sojan HKI wanda ya bindige yar rahoton tashar Aljazeera ta kasar Qatar a shekara ta 2022 a lokacinda take Shirin bada rahoton hare-harenn da sojojin yahudawan suke kaiwa kan wata unguwa ta Falasdinawa a birnin Jenin na yankin yamma da Kogin Jordan. Tashar talabijin...
    Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da shawarar yin amfani da fasahar zamani wajen yaƙi da ta’addanci da ’yan fashi a Nijeriya. Shugaban ya bayar da shawarar ne a ranar Larabar da ta gabata a lokacin da ya jagoranci mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na ƙasa a ziyarar jaje ga...
    Shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga taron musayar al’adu da cudanyar al’umma da aka shirya domin murnar cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiya da jama’ar kasar Sin suka yi a kan zaluncin Japan da kuma kazamin yakin ceton kasa na tsohuwar tarayyar Soviet. A cikin sakon nasa,...
    An kwantar da wasu matan aure kishiyoyin juna a asibiti bayan da suka sha maganin kara sha’awa domin burge mijinsu bayan ya auro mata ta uku. Kishiyoyin biyu da ke yankin Dakwa a Abuja sun sha maganin gargajiyan, wanda aka fi sani da kayan mata ne, kwana uku bayan amaryar da mijinsu ya auro ta...
    Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayana labarummu na yau zai yi magana dangane da ‘Mahangar Jumhuriyar Musulunci na Iran ta yadda za’a kai ga fahintar juna a tattaunawanta da kasar Amurka da suke yi wanda ni tahir amin zan karanta. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a wata tattaunawa ta wayar tarho da tokwaransa...
    Al’ummar garin Izge da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza ta Jihar Borno sun fatattaki ’yan ƙungiyar Boko Haram bayan kai musu hari a ranar Laraba. Ƙungiyar ‘yan ta’addan ta kuma kashe wani kaftin ɗin soji a harbin na ba zata. Jami’an tsaro na ba da gudunmawar aikata miyagun laifuka a Nijeriya — Zulum Jami’an tsaro na...
    Gwamnan Jihar Katsina Umaru Dikko Raɗɗa, ya ce ba shi da masaniyar wani allo da aka kafa mai ɗauke da saƙon ce wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu babu ƙorafi a Katsina ba kamar yadda ake ta muhawara a kai a ƙasar. Hakan na ƙunshe cikin wani saƙon murya ta gwamnan da aka fitar da...
    Gwamnatin Sudan ta katse dangantakar diflomasiyya da (UAE), bisa zarginta da goyan bayan dakarun RSF. A cikin jawabin da aka watsa a talabijin, Ministan Tsaron Sudan, Yassin Ibrahim ya bayyana cewa Sudan ta “katse dangantakar diflomasiyya da UAE,” tare da janye jakadanta da rufe ofishin jakadanci da konsulat dinta a kasar . Da yake magana...
    Kungiyar gwagwarmaya ta Ansarullah ta bayyana cewa yarjejeniyar tsagaiat wutar da ta cimma da Amurka, ba ta sauya matsayin kasar ba na kai wa Isra’ila hari. Kakakin kungiyar Ansarullah Mohammed Abdul-Salam ya jaddada cewa Dakarun Yeman za su ci gaba da kai hare-hare kan Isra’ila domin goyan bayan Falasdinawa a zirin Gaza. Yarjejeniyar da Amurka...
    Sai dai, rikice-rikicen cikin gida da matsalolin tsaro da tattalin arziƙi sun sa gwamnatin ke ci gaba da yin gyare-gyare don samar da hanyoyin da za su ba ta kariya da cikakken iko kan harkokin leƙen asiri da tsaro. Wannan mataki yana iya nuni da cewa Nijar na ƙoƙarin zama mai dogaro da kai a...
    Gwamnatin Sudan da ke da goyon bayan sojoji ta katse dangantakar diflomasiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), tana bayyana ƙasar a matsayin mai katsalandan, a cewar Ministan Tsaron Sudan, Yassin Ibrahim. A cikin jawabin da aka watsa a talabijin ranar Talata, Ibrahim ya bayyana cewa Sudan ta “katse dangantakar diflomasiyya da UAE,” tare da janye...
    Lamarin ya tayar da hankali a unguwar, inda wasu matasa suka yi yunƙurin kai farmakar Saudat. Amma jami’an tsaro sun isa wajen a kan lokaci, suka ceci amaryar tare da kai ta wajen hukuma. Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoto. Daga...
    Akalla mutum shida ne aka tabbatar da mutuwarsu a wani sabon hari Karamar Hukumar Barikin Ladi da ke Jihar Filato. ’Yan bindigar sun kuma jikkata mutane da dama a hare-haren da suka kai unguwannin  Marit da Gashish a ranar Litini. Aminiya ta samu labarin cewa an garzaya da wadanda suka ji raunin asibiti, bayan harin...
    Kungiyar Tarayyar Afrika (AU), ta yi tir da hari na baya-bayan nan da aka kai Port Sudan, muhimmin birni a kasar Sudan dake cikin ’yan kalilan da yakin da ake yi a kasar bai shafa ba. Port Sudan ya taka muhimmiyar rawa a matsayin cibiyar jigila da ayyukan agaji, yayin da ake ci gaba da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yin gwagwarmaya ko fafutuka wani abu ne da ke cikin jinin dan Adam, musamman idan yana kokarin ganin an samu sauyi ko cigaba a al’umma. Sai dai a Najeriya, sau da yawa ana danganta kalmar “gwagwarmaya” da rikici ko sabani da gwamnati. NAJERIYA A YAU: Abin da ke...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yin gwagwarmaya ko fafutuka wani abu ne da ke cikin jinin dan Adam, musamman idan yana kokarin ganin an samu sauyi ko cigaba a al’umma. Sai dai a Najeriya, sau da yawa ana danganta kalmar “gwagwarmaya” da rikici ko sabani da gwamnati. NAJERIYA A YAU: Abin da ke...
    Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da “Bankasar tattalin arzikin Iran duk tare da takunkuman tattalin arziki masu tsanani wadanda kasashen yamma musamman Amurka suka doramata, wanda ni tahir amin zan karanta. ////…A dai-dai lokacinda gwamnatin kasar Amurka take barazanar zata hana sayan danyen man fetur daga kasar Iran kwatakwata,...
    ’Yan bindiga sun kashe wata mata da suka sace tare da mijinta Yakubu Dada watanni bakwai da suka gabata a yankin Kontagora da ke Jihar Neja. Aminiya ta ruwaito cewa ’yan ta’addan sun halaka matar mai suna Lami bayan karɓar Naira miliyan 10 kuɗin fansa. ’Yan fashi sun kashe matashi a Kano Kwankwaso: Abba ya...
    Tashar talabijin din HKI ta channel: 12 ta nakalato sojoji suna sanar da kai wa Yemen hare-hare. Sanarwar ta kuma ce; jiragen yakin HKI sun kai hare-hare ne a wurare 9 a lokaci daya da su ka hada da tashar jiragen ruwa ta Hudaidah. Sojojin na HKI sun ce jirage 30 ne su ka kai...
    Jami’ar siyasar waje ta tarayyar turai Kaja Kallas ta bayyana cikakken goyon baya ga warware batun makamashin Nukiliyar Iran ta hanyar diplomasiyya. Jami’ar ta wallafa a shafinta na X cewa: Na tattauna da ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci domin tabbatar da goyon bayan kungiyar tarayyar turai akan aiki da hanyar diplomasiyya domin warware batun...
    Kotu ta yanke wa wani matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan kan laifin kashe wata karuwa bayan ya yi lalata da ita. Babban Kotun Jihar Ekiti ce ta yanke masa hukuncin bayan an gurfanar da shi kan zargin haɗa baki da kuma garkuwa da matar da kuma amfani da maganin kashe ciyawa wajen halaka...
    A yau 5 ga watan Mayu 2025 tsohon Shugaban Kasa Marigayi Umaru Musa ’Yar’adua ya cika shekaru 10 da rasuwa. ’Yar’Adua wanda ya rasu a bayan dogaruwar jinya yana daga cikin daidaikun zaɓaɓɓun shugabannin Najeriya da talakawa ke kewar su, saboda kyakkyawan kamun ludayin mulkinsa. Sai dai kuma an lura cewa shugabannin da suka fi...
    Iran ta yi kakkausar suka da kakkausar murya kan zargin Amurka da da na Isra’ila suka cewa ta na da hannu a hare-haren ramuwar gayya na kasar Yemen. Iran ta ce zarge zagren basu da tushe balle makama. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya fada a yammacin jiya Lahadi cewa, matakin da kasar...
    Yau Litinin ne kotun kasa da kasa ta ICJ za ta yanke hukunci kan karar da Sudan ta shigar kan Hadaddiyar Daular Larabawa. Khartoum ta kai karar UAE a gaban kotun kasa da kasa da ke birnin Hague, inda ta zarge ta da hannu wajen kisan kiyashin da ake yi wa al’ummar Masalit, sakamakon zarginta...
    Iran ta mayar da martani kan zargin da ake mata game da alakar ta da Yemen tana cewa; Taimakon da Yemen ke yi wa Falasdinu hukunci ne mai cin gashin kansa Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar da wata sanarwa dangane da zargin da ake yi wa Iran dangane da alakar da ke tsakaninta...
    Rahotonni na cewa mayaƙan Boko Haram sun kai kashe dakaru huɗu yayin wani hari da suka kai sansanin soji a Jihar Yobe. Aminiya ta ruwaito cewa ’yan bindigar sun ƙaddamar da hari kan sansanin soji na “27 Task Force Brigade” da ke garin Buni Yadi, a yankin Ƙaramar Hukumar Gujba da tsakar daren Asabar. Abin...
    Assalamu alaikum masu sauraro, sharhin bayan labarammu zai yi magana ne a kan Aya. Shahid Mttahari, shahidi na farko daga cikin malamai jagororin juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran a shekara 1979. A jiya Jumma ce 2 ga watan Mayu na wannan shekara ta 2025 aka yi juyayin shahadar malami na fadrko wanda...
    Cutar Mashaƙo ta ɓarke a unguwar Tukur-Tukur da ke garin Zaria ta jihar Kaduna, inda ta yi sanadiyar mutuwar yara biyu. Wannan ɓarkewar ta haifar da damuwa game da shirye-shiryen kiwon lafiya a Nijeriya. Abdulazeez Suleiman daga ƙungiyar Northern Elders Forum ya tabbatar cewa mutuwar ta faru cikin sa’o’i 48 bayan bayyanar alamun cutar. “Wannan...
    Cibiyar Binciken Aikin Gona ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Samaru Zariya ta hori manoma da kada su yi fargaba bisa yadda Gwamnatin Tarayya ke shigo da abinci daga ƙasashen waje. Shugaban Cibiyar, Farfesa Ado Yusuf ya ba da shawarar ce a yayin zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron bita da tsare-tsaren...
    An kamala gudanar da zabe a yankin jabal Lebanon na kasar Lebanon a safiyar yau Lahadi har an kuma an fara irge. Tashar talabijin ta Almanar ta kasar ta bayyana cewa an bude rumfunan zabe tun karfe 7 na safe, kuma an kamala zaben da yamma. Sannan ma’aikatar cikin gida da kuma kananan hukumomi ta...
    Mahajjata hudu – daya daga Maroko sauran kuma daga Sifaniya – sun isa kasar Saudiyya a kan dawakai a wannan makon da ya fice don gudanar da aikin Hajjin 2025, wanda hakan ke tunatar da al’ummar Musulumi tsarin zuwa aikin hajji a shekaru da dama da suka gabata. Mahajjatan sun isa zuwa kasar Saudiyya ne...
    Ƙafar Manchester United guda ta kai wasan ƙarashe na gasar Zakarun Turai ta Europa League bayan da ta doke Athletic Bilbao da ci 3-0 a Sifaniya. Da fari wasan ya nuna kamar ba zai yi wa United kyau ba, to amma bayan minta 30 sai wasan ya sauya bayan da Harry Maguire ya yi wata...
    Shugaban Amurka, Donald Trump na shan suka daga wasu jagororin mabiya ɗarikar Katolika, saboda wallafa hotonsa da ya samo daga manhajar ƙirƙirarriyar basira ta AI, sanye da kayan fafaroma. Mista Trump ya wallafa hoton ne a shafukan sada zumunta na fadar White House. Matakin na zuwa ne yayin da mabiyar ɗarikar Katolika, ke shirin zaɓen...
    Bishop Joseph Osifuwa, Bishop na jihar Kwara, ya ce Nijeriya za ta iya magance matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a sassan kasar nan idan har ta dauki matakin magance masu tada kayar baya.   Bishop Osifuwa ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen babban taron cocin karo...
    Dakta Abdulmalik ya ce, a halin yanzu gwamnatin jihar na da likitoci 99 kadai ne, wadanda ke kan tsarin albashi, ya kara da cewa; adadin da ake bukata kuma sun kai kimanin 180 zuwa 200.   “Likitoci ukun da suka bar aiki, sun dawo bayan karin albashin likitocin da gwamnan ya yi a baya-bayan nan....
    Ana gwabza kazamin fada a Sudan, inda dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka kashe fararen hula kusan 300 A tsakiyar bala’in Sudan, ana ci gaba da gwabza kazamin fada tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa, a daidai lokacin da ake fama da munanan ayyukan jin kai da ke ba da...
    A cikin jawabin sa a taron, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana wasu manyan fa’idoji da kuma irin barazanar da ke tattare wajen amfani da AI a cikin ɗakunan buga labarai.   Ya ce duk da cewa AI na taimaka wa ‘yan jarida a Nijeriya wajen saurin bayar da...
    Wakilinmu ya ce mayaƙan “Operation HADIN KAI” sun fafata da maharan lokacin da suka kai hari Buni Gari. Rundunar sojin ƙasa ta tabbatar da faruwar lamarin a shafinta na sada zumunta da safiyar yau Asabar. A cewarta, “Mayaƙan Operation HADIN KAI suna ci gaba da fafatawa da mayaƙan ISWAP a Buni Yadi.” Rahotannin sirri sun...
    Hedikwatar ’yan sandan Gada da ke Jihar Sakkwato ta gano wasu shanu 25 da ake zargin an sace ko kuma sun ɓace daga hannun masu su. An gano dabbobin ne a wani dajin da ke kan iyaka da ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar a ranar Alhamis, bayan da hukumomin yankin suka samu labarin. ’Yan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Cibiyar samar da kyakyawan yanayin yin kasuwanci na Fadar Shugaban Kasa da hadaka da NPA ne, suka shirya taron kaddamarwar,   “Ana sa ran a zangon farko na 2026, aikin na NSWP zai fara fara aiki wanda tuni, Fadar Shugaban Kasa ta amince da kwangilar domin a wanzar da aikin,” Inji Dantsoho.   Ya kuma...