2025-06-15@17:55:54 GMT
إجمالي نتائج البحث: 229

«Alƙawari»:

    Majalisar wakilai za ta binciki yadda aka samu mummunar faduwa a jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire (UTME) ta 2025 da hukumar shirya jarabawar (JAMB) ta gudanar kwanan nan. Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da dan majalisa, Adewale Adebayo ya gabatar a zauren majalisar a ranar Alhamis. Da yake gabatar da kudirin, ya...
    Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta bayyana cewa hauhawar farashi a Najeriya ya sauka kaɗan a watan Afrilu 2025 zuwa kashi 23.71, daga kashi 24.23 da aka samu a watan Maris. Wannan na nuna cewa hauhawar farashi ya ragu idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, inda a watan Afrilun 2024 aka samu kashi...
    Wutar lantarki ta kashe wani wanda ake zargin ɓarawon wayar rarraba wutar ne a harabar Sabuwar Sakatariyar Jihar Jigawa. ’Yan sanda sun sanar cewa an tsinci gawar mutumin ta maƙale ne a karkashin kankare da manyan wayoyin lantarkin ke ciki. Kakakin ’yan sanda a Jihar Jigawa, Shiisu Lawal Adamu ya ce a safiyar ranar Alhamis...
    Shugaban kasar Amurka wanda yake Ziyara a kasar Katar ya sanar da cewa gwamnatinsa tana son ganin tattaunawar da ake yi da Iran ta yi nasara, kuma ya yi Imani da cewa ana gab da kulla yarjejeniya da ita. Shugaban kasar ta Amurka ya kuma ce da akwai ci gaba sosai a cikin tattaunawar da...
    A yau ne za a gudanar da tattaunawar zaman lafiya kan yaƙin da ke tsakanin Ukraine da Rasha a birnin Istanbul da ke ƙasar Turkiyya, – amma fadar Kremlin ta bayyana cewa shugaban Rasha, Vladimir Putin, ba ya cikin jerin jami’an da za su halarci tattaunawar. Rahotanni daga kafafen yaɗa labarai sun ce shugaban Amurka...
    Ɗaliban da suka rubuta jarabawar shiga jami’a (UTME) na shekarar 2025 da Hukumar Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta gudanar sun buƙaci a soke sakamakon ɗungurungum. Ɗaliban sun bayyana haka ne bayan da Hukumar JAMB ta amsa laifin kurakurai da aka samu da suka haifar da yawan rashin ƙoƙarin ɗalibai a jarabawar. Rashin kyawun sakamakon...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta yi amai ta lashe. Bayan ta musanta duk zarge-zargen da aka yi cewa tana da hannu a rashin kyawun sakamakon jarabawar da ta shirya, shugaban hukumar ya fito ya amsa laifin. Yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai,...
    Shugaban Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB), Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana cewar an samu kura-kurai a sakamakon jarrabawar UTME ta shekarar 2025 da aka saki kwanan nan. A yayin wani taron manema labarai a Abuja, Farfesa Oloyede, ya fashe da kuka yayin da yake bai wa ɗalibai haƙuri, inda ya nuna nadamarsa kan...
    Oloyede, wanda ya bayyana tangardar a matsayin “zagon kasa” ga shirin jarabawar UTME ta 2025, ya ce, wadanda abin ya shafa za su fara samun sako a wayar salularsu daga Hukumar daga ranar Alhamis, 15 ga Mayu, 2025.   Daga cikin dalibai miliyan 1.9 da suka zana jarabawar UTME ta shekarar 2025, sama da miliyan...
    Wannan matsala, in ji bankin, na shafar samar da abinci da kuma ƙara hauhawar farashin kayan masarufi a kasuwa. Bankin Duniya ya yaba wa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu bisa matakan da ta ɗauka tun bayan da ya hau mulki a watan Mayun 2023, musamman cire tallafin man fetur da yunƙurin ƙarfafa darajar Naira. Amma bankin...
    Wannan matsala, in ji bankin, na shafar samar da abinci da kuma ƙara hauhawar farashin kayan masarufi a kasuwa. Bankin Duniya ya yaba wa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu bisa matakan da ta ɗauka tun bayan da ya hau mulki a watan Mayun 2023, musamman cire tallafin man fetur da yunƙurin ƙarfafa darajar Naira. Amma bankin...
    Bankin Duniya ya sanar da cewa duk da ƙalubalen hauhawar farashin da Nijeriya take fuskanta, tattalin arzikin ƙasar ya ƙaru a shekarar da ta gabata. Babban bankin ya ce tattalin arzikin Nijeriyar ya samu haɓaka a kusan shekaru goma a 2024, inda a watanni uku na karshen 2024 aka samu haɓaka sosai. HOTUNA: Trump na...
    Kasar Siriya ta rikide daga Jihadi da zaluncin gwamnatin mamayar Isra’ila zuwa ga kulla kyakkyawar alaka da gwamnatin ‘yan mamaya Gaskiya ta fara bayyana daya bayan daya, sannan makirci da makarkashiyar kungiyoyin masu dauke da makamai bisa da’awar gudanar da jihadi a Siriya suka fara bayyana ga al’umma, masu da’awar jihadi sun kama hanyar fitar...
    Hukumar JAMB mai shirya jarrabawar neman shiga makarantun gaba da sakandire a Nijeriya, ta sanar da sakin sakamakon jarrabawar da ɗalibai suka zana a bana. Wata sanarwa da shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ya fitar ranar Juma’a, ta ce an riƙe sakamakon ɗalibai 39,834 wanda a cikin wannan adadi tana bincike kan sakamakon ɗalibai 1,426....
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ma’aikatar kula da harkokin cinikayya ta kasar Sin, ta ce sabuwar gwamnatin Amurka ta dauki jerin matakan kakaba haraji na ba gaira ba dalili, lamarin da ya kawo tsaiko ga dangantakar cinikayya da tattalin arziki tsakanin kasashen biyu da ma tsarin cinikayya da tattalin arziki na duniya, tare da kawo kalubale mai tsanani ga farfadowar...
    Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya yi zargin cewa sojoji da sauran jami’an tsaro na bayar da gudunmawar aikata miyagun laifuka da cin zarafin jama’a a Nijeriya. Zulum ya faɗi hakan ne yayin da yake haramta sayar da barasa a birnin Maiduguri da kewaye. Ka-ce-na-cen da ya biyo bayan ziyarar Tinubu a Katsina DAGA...
    Ministan Ilimi a Nijeriya, Tunji Alausa ya ce hana satar amsa ne ya janyo faɗuwar ɗalibai a jarawabar shiga manyan makarantu da JAMB ke shiryawa a kowace shekara. Tunji ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da gidan talabijin na Channels a ranar Talata. ‘Raini ne ya sa ake ƙalubalantar yunƙurin kafa ƙungiyar Hausawa zalla’ Majalisar...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaaei ya bukaci kasashen turai da su shiga a dama da su kan tattaunawa dangane da shirin nukliyar kasar Iran na zaman lafiya. Ya kuma jaddada cewa Iran tana turjiya ga dukkan tunanin Amurka na wargaza shirin Nukliyar kasar Iran kwata-kwata. Baghaei ya kara da cewa duk da...
    Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu a Nijeriya (JAMB) ta fitar da alƙaluman sakamakon jarabawar UTME ta shekarar 2025, inda ta bayyana cewa yawancin daliban da suka zauna jarabawar sun gaza samun maki 200 daga cikin maki 400. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar yayin wani taron manema labarai da ta...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta bayyana cewa tattaunawar sulhu a Gaza ba ta da wani tasiri a wannan mataki. Ofishin kungiyar, ya yi kira ga kasashen duniya da su matsa lamba kan gwamnatin Netanyahu don kawo karshen laifukan yunwa, kishirwa da kisan kai a Gaza, in ji wani babban jami’in kungiyar. Halin da ake...
    A wani bangare na wasikar na cewa, “An umurce ni da in isar da amincewar Gwamnati na fitar da jimillar kudi Naira miliyan 15,227,272.72 a asusun kowace karamar hukuma domin gyaran motoci biyu tare da siyo karin wasu guda hudu ga Majalisar masarautar Kano wanda kamfanin Sottom Synergy Resources Ltd zai dauki nauyin siyowa.  ...
    Gwamnan Sakkwato, Dokta Ahmad Aliyu ya bayyana ƙarara cewa gwamnatinsa ta kasa cika alƙawarin da ta yi wa ma’aikatan gwamnatin jihar kusan shekara ɗaya kenan. Gwamnan ya bayyana hakan a yayin bikin Ranar Ma’aikata da aka gudanar a makon da ya gabata. Lakurawa sun kashe ’yan bijilanti 11 a Sakkwato Ya kamata a zuba jari...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci matasan kasarsa da su zage damtse, wajen bayar da gudummawar cimma nasarar zamanantar da kasa, ta hanyar yin dukkanin sadaukarwa da kasar ke bukata daga gare su.   Shugaba Xi, ya yi wannan tsokaci ne cikin martanin wasikar da ya aike ga rukunin malamai masu aikin sa kai,...
    Shugaba Bola Tinubu ya yi alƙawarin ƙwato dazuzzuka da sauran yankuna a Arewa-Maso-Yamma da sauran sassan Nijeriya, yayin da yake jawabi a wata liyafa da tsofaffin shugabannin Katsina suka shirya. Ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ƙara amfani da fasahar sa ido don yaƙar ta’addanci da ƴan fashi. A cewar sanarwar kakakin shugaban ƙasa, Tinubu...
    Limamin da ya jagoranci sallar Jumma’a a nan Tehran Hujjatul Islam kazim Sadiki ya bayyana cewa kasar tana da kwararru wadanda suke da kwarewa a sanin fasahar nukliya da kuma hanyoyin dublomasiyya a tattaunawar da Iran take da Amurka dangane da shirin Nukliyar kasar. Tashar talabijin ta Al-alam a nan Tehran ta nakalto limamin yana...
    Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen gina jihar da ma’aikata za su bunkasa, samar da ayyukan yi masu nagarta, da baiwa kowane bangare damar bayar da gudunmawa mai ma’ana ga ci gaban jihar.   Gwamna AbdulRazaq a cikin sakonsa na bikin ranar ma’aikata ta duniya na shekarar 2025, a Ilorin,...
    Jakadan kasar Sin ya bayyana cewa, kasar tana kiran a samar da hanyar kawar da makaman nukiliya wacce a karkashinta ba za a iya raba tsaro na kashin kai da tsaro na bai daya ba, tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. Babban darektan sashen kula da makamai na ma’aikatar harkokin...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Sanata Atiku Bagudu tare da hadin guiwar Kyakyawar Gate Handicapped Centre Jos, sun bayar da tallafin keken guragu guda dari da talatin ga masu bukata ta musamman a Birnin Kebbi na jihar Kebbi.   Kakakin Ministan, Sadiq Nura Maiyaka, ya ce Ministan ya kuduri aniyar taimakawa masu bukata...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce za a yi taro karo na hudu na shawarwari tsakanin Tehran da Washington kan shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a birnin Rome na kasar Italiya a ranar Asabar mai zuwa. M. Araghchi ya fadawa manema labarai a gefen taron majalisar ministocin gwamnatin kasar na mako-mako yau...
    Gwamnatin tarayya ta ɗauki nauyin dukkanin buƙatun ɗaliban na zana jarabawar, ciki har da abinci da wurin kwana, har na tsawon kwanaki uku. Kwamishinan ilimi na jihar Bauchi, Dakta Lawal Mohammed Rimin Zayam, ya yaba da wannan mataki na JAMB, yana mai kira ga iyaye da su tura ‘ya’yansu dake da lalura ta musamman makaranta...
    Gwamnatin tarayya ta umarci hukumar shirya jarrabawar WAEC da NECO da su fara amfani da cikakken tsarin amfani da Komfuta (CBT) ga dukkan jarabawar su nan da shekarar 2026. Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ne ya bayar da wannan umarnin a ranar Litinin yayin ziyara da kuma duba yadda ake gudanar da gwaje-gwaje na CBT...
    Mataimakin ministan harkokin waje mai kula da bangaren siyasa, ya bayyana cewa; Ko kadan ba a bijiro da batun dakatar da tace sanadarin uranium a Iran ba, ko kuma batun makamanta masu linzami. Mataimakin ministan harkokin wajen na Iran ya tabbatar da cewa, wadannan abubuwan biyu wato dakatar da ci gaba da tace sanadarin uranium...
    A ganawarsa da wata jami’ar Amurka, al-Julani ya yi alkawarin ba zai cutar da tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila ba! Barbara Leaf, tsohuwar mataimakiyar sakatariyar harkokin wajen Amurka mai kula da harkokin gabas ta tsakiya, ta tabbatar da cewa shugaban rikon kwarya a Siriya, Mohammed al-Julani (al-Shara’a), “ya bayyana fahimtar matsalolin tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila,” a...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu ya yaba da yadda tattaunawa da Amurka kan shirin Nukliyar kasar yana tafiya kamar yadda ta dace. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya nakalto Aragchi yana fadar haka bayan, bayan ya fito daga taron tattaunawa ta ukku wanda aka gudanar...
    Mai ba da shawara ga Jagoran juya juya halin Musulunci kan harkokin siyasa ya bayyana cewa: Tattaunawar Muscat wata dama ce ta samun zaman lafiya kan batutuwa masu sarkakiya Ali Shamkhani mai ba Jagoran juyin juya halin Musulunci shawara kan harkokin siyasa ya yi tsokaci kan tattaunawar ba na kai tsaye ba da ake yi...
    A nasa bangare kuma, firaministan kasar Senegal Ousmane Souko ya bayyana cewa, kasar Senegal tana son hadin gwiwa da cibiyar nazarin ilmin kimiyyar zamantakewar al’umma ta kasar Sin don kara cudanyar juna da gudanar da ayyukan nazarin ilmi tare, baya ga samar wa kasashen dake yammacin nahiyar Afirka dabarun neman samun ci gaba.   Bugu...
    Hon. Ibrahim ya yi nuni da cewa a karkashin jagorancin Gwamna Abba an samu ci gaba sosai wajen tabbatar da samar da ingantaccen ilimi ga kowa da kowa da kyautata harkar lafiya da sufuri da biyan ma’aikata da ‘yan fansho hakkokinsu ba tare da jinkiri ba.   Kwamishinan ya jaddada goyon bayansa ga irin ayyukan...
    A kokarinta na ganin an gudanar da jarrabawar hadin gwiwa ta hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta JAMB, gwamnatin jihar Kano ta dakatar da aikin tsaftar muhalli na watan Afrilun 2025.   An dauki wannan matakin ne bayan nazari da tuntubar masu ruwa da tsaki, a kokarin baiwa daliban jihar Kano damar rubuta jarabawarsu ba...
    Kasar faransa ta jaddada anniyar na ci gaba da tattaunawa kan shirin nukiliyar iran. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Faransa ya bayyana a ranar Alhamis cewa, Faransa na ci gaba da jajircewa wajen ganin an warware matsalar nukiliyar Iran ta hanyar diflomasiyya, kuma a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da Tehran. A yayin taron...
    Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa ba tabbas ko za’a iya kawar da cutar zazzabin cizon sauro nan da shekarar 2030, musamman a nahiyar Afrika. Fiye da mutane miliyan 263 ne suka kamu da cutar a cikin 2023, kuma kusan 600,000 ne suka mutu sanadin cutar a cewar alkalumman na MDD. Musamman a wannan lokacin...
    Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah sayyid Ali Khamnei wanda ya gabatar da jawabi dangane da zagayowar ranar shahadar Imam Ja’afar Assadiq ( a.s) ya bayyana cewa: Tafarkin Imaman Ahlul-Bayti (a.s) ya kasance na gwgawarmaya da jajurcewa, kuma koyarwarsu ta ginu ne akan mandiki da kafa dalili. Jagoran juyin musuluncin na Iran ya ce; rayuwar...
    Ya buƙaci jama’a da su ci gaba da tallafa wa jami’an tsafta domin tabbatar da tsaftar muhalli a jihar. Aikin tsaftar muhalli na wata-wata, wanda ake yi a ƙarshen kowane wata, ana dakatar da zirga-zirgar ababen hawa na wasu awanni domin tsaftace muhalli a faɗin Kano. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
    Babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya ba da umarnin ga rundunar sojin Najeriya da ta fatattaki ‘yan bindigar da ke addabar al’ummar kananan hukumomin Baruten da Kaiama na jihar kwara da Borgu da ke dajin Kainji a jihar Neja cikin wata guda.   A jawabin da ya yi wa dakarun rundunar soji...
    Da yake jawabi a fadar Mai Tangele (Sarkin Billiri), Danladi Sanusi Maiyamba, ya bayyana lamarin da matukar bakin ciki tare da fatan samun makoma mai kyau ga wadanda suka rasu, ya kuma warkar da wadanda suka samu raunuka da gaggawa.   Daga nan sai Gwamna Inuwa ya sanar da bayar da gudummawar Naira miliyan 2...
    Iran ta sanar da dage tattaunawar da aka shirya gudanarwa yau Laraba tsakanin tawagar kwararu ta kasar da kuma na Amurka a kasar Oman a wani bangare na ci gaba da tattaunawar da ake tsakanin kasashen biyu kan shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ya bayyana cewa, an dage tattaunawar...
    Ana kallon Cunha a matsayin wani da zai iya bayar da gudunmawa wajen dawo da Manchester United kan ganiyarta, Cunha ya kasance wanda ya fi zurawa Wolverhampton kwallaye a raga a kakar wasa ta bana inda ya zura kwallaye 16 a dukkanin gasa.   United na shirin fuskantar gogayya daga kungiyoyi da dama na gasar...
    An tsinci gawar wani matashi da budurwarsa a tube bisa gado a cikin dakinsa a yakin Alo da ke Karamar Hukumar Ankpa a Jihar Kogi. An tsinci gawara masoyan ne a gidan hayan da saurayin ke zama ranar Juma’a da ta gabata. Mai gidan hayan mai suna Salisu Ibrahim ne ya nemi agajin jama’a sakamakon...
    Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa tace uranium din ta tamakar jan layi ne a tattaunawar dake wakana tsakaninta da Amurka. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar ne Kazem Gharibabadi ya bayyana hakan, inda ya ce hakkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne inganta sinadarin Uranium, yana mai jaddada cewa, wannan batu a matsayin jan layi...