Na bar APC saboda Tinubu bai cika alƙawarin da ya yi ba — Marafa
Published: 29th, August 2025 GMT
Sanata Kabiru Garba Marafa tsohon ɗan Majalisar Dattawa da ya wakilci yankin Zamfara ta tsakiya jigo a Jam’iyar APC a jihar ya fice daga jam’iyar.
Sanata Marafa ya bayyana ficewarsa a wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafin Facebook a ranar Jumu’a ya ce bayan tattaunawa da magoya bayansa sun cimma matsayar barin Jam’iyyar APC kan ta zalunce su.
“Bayan mun yi waiwaye a shekara biyu da rabi da suka gabata mun gano cewa, APC a matakin ƙasa da jiha ta zalunce mu, a matakin jiha lalacewar jam’iyar ya kai matuƙa tun bayan kafa kwamitin riƙon ƙwarya har zuwa yanzu ba a taɓa zama ko na minti biyar ba, don tattauna halin jam’iya, kuma ita ce ta fasa jam’iya gidan wane da gidan wane a haka ake tafiya.
“Shekara biyu da rabi ba a ɗunke baraka ba, don haka mun barwa ɓangaren Sanata Abdul’aziz Yari da Minista Bello Matawalle jam’iyar.
“Matsalar tsaro da ke addabar jihar na cikin abin da ya sa muka yi zama don duba halin da ake ciki, yanda APC ta yi na tilas sai ta yi nasara a zaɓen Ɗan Majalisa na Ƙaura da aka yi baya cikin alƙawarin da aka yi mana, shugaban ƙasa ya yi mana alƙawalin zai duba lamarin tsaro na Jihar Zamfara, hakan ya sa ya ɗauki jihohi biyu da ya ci zaɓe, ya ba su ministocin tsaro, a Zamfara ba abin da aka yi mana.”
Kan kalaman da ake yi sun bar APC ne don ba a ba su muƙami ba ne? Ya ce haka ne, ai suna siyasa ne don su samu muƙami su amfanar da al’ummarsu, “don me wani zai tsaya takara mu yi kamfe a zaɓe shi a ƙarshe ya ce shi ba abin da zai ba mu, wannan ba adalci ba ne don haka mun jingine Jam’iyar APC.
“A nan gaba za mu sanar da jam’iyyar da muka koma, sai a yi yaƙin gaba da gaba kana can ina nan,” kalaman Kabiru Marafa.
Sakataren yaɗa labarai na Jami’iyar APC a Zamfara Yusuf Idris, ya ce ba za su ce komai ba kan kalaman Sanata Kabiru Marafa domin bai rubuta masu ya sanar da su ya bar APC ba tun daga kan mazaɓarsa har zuwa matakin jiha.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Bello Matawalle Sanata Kabiru Marafa Zamfara
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Masallata Tare Da Garkuwa Da Mutane A Zamfara
Yarjejeniyar, a cewar daukacin mahalarta taron, ta nuna wani gagarumin mataki na kawo karshen tashe-tashen hankula, garkuwa da mutane da satar shanu a Arewa maso Yamma, da kuma yankin Arewa.
Yarjejeniyar wacce Mai Maradin Katsina da Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi, da shugaban karamar hukumar, Babangida Abdullahi Kurfi suka shirya, ta gudana ne a dajin Wurma, inda ake fama da rashin tsaro.
Manyan jagororin ‘yan bindigan da suka hada da Alhaji Usman Kachalla Ruga da Sani Muhindinge da Yahaya Sani (Hayyu) da kuma Alhaji Shu’aibu duk sun yi alkawarin tsagaita wuta.
Daga baya suka sako mutanen da suka kama kuma suka bar manoma su koma gonakansu ba tare da wata barazana ba.
Sai dai kasa da wata guda da kulla yarjejeniyar, an tattaro cewa ‘yan bindigar sun sake kai hari a Zamfara inda suka yi awon gaba da masallata da dama.
Wata majiya ta cikin garin, ta shaida cewa, harin ya afku ne a lokacin sallar asuba da misalin karfe 5:30 na safe, inda ‘yan bindigar suka afkawa masallacin, suka kewaye shi, sannan suka tattara masallatan zuwa daji.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp