An fara samun masu zawarcin kujerar Firaministan Japan
Published: 8th, September 2025 GMT
An fara samun masu zawarcin kujerar Firaministan Japan da ya yi murabus, inda tsohon Ministan Harkokin Waje ya bayyana takarar neman kujerar mai tasiri a kasar wadda take sahun gaba na kasashe masu arziki a duniya.
Tsohon Ministan Harkokin Wajen kasar Japan, Toshimitsu Motegi ya zama mutum na farko da ya nemi ’yan majalisar dokoki na jam’iyya mai mulki ta Liberal Democratic Party (LDP) su ba shi damar zama sabon Firaminista, domin ya maye gurbi Firamnista Shigeru Ishiba mai barin gado wanda ya bayyana yin murabus daga kan mukamin.
Aminiya ta ruwaito cewa a jiya Lahadi ce Firaministan Japan, Shigeru Ishiba, ya sanar da murabus dinsa a matsayin shugaban jam’iyyar Liberal Democratic Party (LDP), watanni kaɗan bayan jam’iyyarsa ta sha mummunan kaye a zaɓen watan Yuli.
Ishiba ya sanar da matakin duk da cewa a baya ya yi ƙoƙarin kaucewa matsin lambar ‘yan jam’iyyarsa da ke neman ya sauka sakamakon rashin nasarar zaɓen, inda ya dage cewa yana son tabbatar da yarjejeniyar haraji da ƙasar ta ƙulla da Amurka ta fara aiki yadda ya kamata.
“Tun da Japan ta sanya hannu kan wannan yarjejeniya, kuma shugaban Amurka ya rattaba hannu a matsayin doka, mun tsallake babban ƙalubale,” in ji shi.
“Lokaci ya yi da zan miƙa wa sabon jini tutar shugabanci,” ya ƙara da cewa.
Duk da murabus ɗinsa daga shugabancin jam’iyyar, Ishiba zai ci gaba da zama Firaminista har zuwa lokacin da za a gudanar da zaɓen cikin gida domin zaɓen sabon shugaban LDP.
Gidan Talabijin na Al-Jazeera ya ruwaito cewa wannan mataki ya ƙara jefa Japan, wacce ita ce ƙasa ta huɗu mafi girman tattalin arziƙi a duniya, cikin ruɗanin siyasa.
Tun bayan hawansa mulki a watan Oktoba da ya gabata, ɗan siyasar mai shekara 68 ya gamu da manyan ƙalubalai da suka yi sanadin kawar da rinjayen ’yan jam’iyyarsa a majalisun biyu na ƙasar.
Rashin nasarar, wanda aka danganta shi da ƙorafin jama’a kan tsadar rayuwa, ya sa gwamnatin Ishiba ta kasa aiwatar da manufofinta yadda ta tsara.
Yayin da ƙasar ke ƙara faɗawa cikin ruɗanin siyasa, manyan ‘yan jam’iyyarsa musamman daga bangaren ’yan ra’ayin mazan jiya sun matsa masa lambar yin murabus, waɗanda suka ɗora masa alhakin rashin nasara a zaɓen majalisar dattawa na Yuli.
Rahotanni sun ce Ministan Aikin Noma na Japan tare da tsohon Firaministan sun gana da shi a daren ranar Asabar domin shawartarsa da ya yi murabus.
A taron manema labarai da ya kira ranar Lahadi, Ishiba ya tabbatar da murabus ɗinsa, tare da bayyana cewa ya fara shirye-shiryen neman wanda zai gaje shi.
Yayin da ƙasar ke ƙara nutsewa cikin rudanin siyasa, manyan ‘yan jam’iyyarsa musamman daga bangaren ’yan ra’ayin mazan jiya sun matsa masa lamba da ya sauka, suna zarginsa da alhakin sakamakon zaben majalisar dattawa na Yuli.
Rahotanni sun ce Ministan Aikin Noma na Japan tare da tsohon Firayim Minista sun gana da shi a ranar Asabar da dare don shawarce shi ya sauka.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan jam iyyarsa
এছাড়াও পড়ুন:
‘An Kashe Masu Zanga-zanga Akalla 500 a Tanzania’
Jami’an diflomasiyya a Tanzania sun ce akwai kwararan hujjoji da ke tabbatar da an kashe akalla mutum 500 a cikin kwana biyu da barkewar zanga-zangar kin amincewa da sakamakon zaben da aka gudanar a ranar Laraba.
Sai dai a wani bangaren kuma, alkalumman Yan’adawa sun zarta haka.
Wakiliyar BBC ta ce ministan harakokin wajen Tanzania Mahmoud Kombo Thabit ya musanta rahotannin, amma wani jagoran adawa John Kitoka ya ce ‘yansanda da wasu sojojin haya na kasashen waje ne suka aiwatar da kisan mutane cikin dare.
Majalisar Dinkin Dauniya ta yi kiran gudanar da bincike kan zargin amfani da karfin da ya wuce kima a kan masu zanga-zangar.
BBC