Al-Houthi: Kisan jami’an fararen hula manuniya ce kan gazawar Isra’ila
Published: 1st, September 2025 GMT
Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyed Abdul Malik al-Houthi ya yi kakkausar suka kan harin wuce gona da iri da Isra’ila ta kai a birnin San’a wanda ya kai ga shahadar firaministan kasar Yemen da wasu jami’an farar hula da dama.
A cikin wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin na jinjinawa shahidai, al-Houthi ya bayyana cewa, “laifi na kai hari kan ministoci da ma’aikatan farar hula ya kara tabbatar da laifukan Haramtacciyar Kasar Isra’ila a yankin,” yana mai jaddada cewa dukkan wadanda suka yi shahada suna gudanar da ayyukansu ne a fagagen da ba na soja ba.
Da yake mika ta’aziyyarsa ga iyalan shahidai, abokan aikinsu, da al’ummar kasar Yemen, ya tabbatar da cewa wuce gona da iri ba zai karya azamar al’ummar kasar Yemen ba.
Al-Houthi ya tunatar da cewa, wannan sabon harin wani bangare ne na wuce gona da iri, yana mai cewa: “Wadannan suna daga cikin irin munanan laifuka da Isra’ila take aikatawa a kan al’ummar Palastinu, Lebanon, Siriya, Iraki da Iran.” Ya yi tir da irin wanann zaluncin da kekasar zuciya, yana mai cewa, Isra’ila ta wuce dukkanin iyakoki, kuma dole ne ta fuskanci sakamakon ayyukanta.”
Ya jaddada cewa irin wadannan laifuffukan suna nuna mahimmanci da wajabcin yin gwagwarmaya domin dakile manufofinta a cikin yankin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka GCC: Batun Kafa Isra’ila Babba Hadari Ne Mai Girma Ga Kasashen Larabawa September 1, 2025 Jagora: Yarjejeniyar Da Iran Ta Cimma Da China Tana Da Muhimmanci Don Haka A Hanzarta Aiwatar Da Ita August 31, 2025 Pezeshkian: Taron Kolin Shanghai Wata Muhimmiyar Dama Ce Ta Bunkasa Alakar Bangarori Da Dama Na Yankin August 31, 2025 Mataimakin Babban Kwamandan “IRGC”: Makiya Sun Kasa Cimma Munanan Manufofinsu Kan Iran August 31, 2025 Jagoran Kungiyar Ansarullah Ta Kasar Yemen Ya Ce: Dakarunsa Zasu Ci Gaba Da Yaki Da Isra’ila August 31, 2025 Gwamnatin Kenya Ta Ci Gaba Da Tono Gawarwakin Da Masu Tsaurin Addinin Kirista Da Suka Kashe Kansu A Kenya August 31, 2025 Kissoshin Rayuwa: Siratuh Imam Al-Hassan (a) 135 August 31, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 137 August 31, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 136 August 31, 2025 Iran Ta Sami Nasarar A Kan Amurka A Gasar Volleyball Na Kasa Da Kasa August 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Yemen
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Qatar Ta Ba Da Tallafin Gaggawa Ga Al’ummar Sudan Bayan Gumurzun El-Fasher
Qatar ta bayar da tallafin gaggawa ga mutanen da suka rasa matsugunansu a Sudan
Gwamnatin Qatar ta aika da agajin gaggawa da tallafin jin kai zuwa birnin Ad-Dabba da ke Jihar Arewacin Sudan domin rage wa dubban mutanen da suka rasa matsuguninsu da ke tserewa daga El Fasher, babban birnin Jihar Arewacin Darfur.
Ma’aikatar Harkokin Waje ta Qatar ta bayyana cewa: “Wannan tallafin ya zo ne a cikin tsarin jajircewar Qatar na tallafawa ‘yan uwantaka na Sudan, musamman idan aka yi la’akari da mawuyacin halin jin kai da fararen hula ke ciki, ciki har da karancin abinci mai tsanani da kuma karuwar bukatar matsugunai da kayan masarufi.”
Sanarwar ta kara da cewa wannan tallafin wani bangare ne na kokarin da Qatar ke yi na tsayawa tare da ‘yan uwantaka na Sudan da kuma rage musu wahalhalun da rikicin yaki da makamai ya haifar. Haka nan ya kunshi rawar da Qatar ke takawa wajen karfafa martanin jin kai da kuma gina gadoji na hadin kai da al’ummar da abin ya shafa a fadin duniya.
Tallafin ya kunshi kimanin buhuhunan abinci 3,000, tantuna 1,650, da sauran kayayyakin bukatu, wanda Asusun Ci Gaban Qatar da kuma Hukumar Ba da Agaji ta Qatar suka bayar, don tallafawa wadanda suka rasa matsuguninsu daga El Fasher da yankunan da ke kewaye. Ana sa ran sama da mutane 50,000 za su amfana daga wannan tallafin, wanda ya haɗa da kafa sansanin agaji na musamman na Qatar mai suna Qatar Charity.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya November 2, 2025 Amurka : zamu dauki matakin soja idan Najeriya ta gaza kawo karshen kashe Kiristoci November 2, 2025 Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza November 2, 2025 Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran November 2, 2025 Sojojin Amurka Na Kara Fuskantar Venezuwela Adaidai Lokacin da Trump Ke Musanta Batun Kai Hari November 2, 2025 Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon November 2, 2025 Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya November 2, 2025 Shugaban AmurkaTrump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya November 2, 2025 Kamaru: Jagroan ‘Yan Hamayya Ya Yi Kira Da A Tsayar Da Harkoki A Fadin kasar November 1, 2025 MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania November 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci