2025-08-01@22:45:33 GMT
إجمالي نتائج البحث: 314
«Jam iyyar APC ta»:
A yanzu haka dai ratotannin sun tabbatar da cewa APC da ADC suna gogayya wajen neman samun goyon bayan mutanen arewa kafin babban zaɓen 2027 ya ƙariso. A ranar 1 ga Yuli, manyan ƴan adawa da suka hada da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi da dan takarar shugaban ƙasa a APC a 2023, Rotimi Amaechi, da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, sun gabatar da ADC a matsayin hadakar jam’iyyar adawa domin ƙalubalantar Tinubu a 2027. Shugabannin ADC sun ci gaba da yin ƙoƙari don samun goyon bayan mutanen arewacin Nijeriya da sauran yankuna tun bayan buɗe jam’iyyar. A taron, Mark ya buƙaci shugabannin arewacin Nijeriya da...
Shugaban jam’iyyar NNPP na Jihar Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa, ya ce farin jinin jam’iyyar adawa ta PDP ya dusashe a jihar. Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mayar da martanin da wasu jam’iyyun adawa suka yi, wajen zargin gwamnatin jihar da rashin bayyana yadda ta ke kashe kuɗaɗen da aka ware wa ilimi, lafiya, da gine-gine. Haɗarin tirela ya yi sanadin asarar awaki sama da 100 a Zariya Martani: Har yanzu muna ci gaba da yajin aiki — Ma’aikatan jinya Dungurawa, ya ce waɗannan zarge-zargen siyasa ce kawai, ba su da tushe ko makama. Ya ce waɗanda ke sukar gwamnati su ne suka gaza lokacin da suka yi mulki a Kano. “Da farko, muna gode musu da...
Bayan shekar 22 da kuɓutar da Nijeriya daga mulkin soja, dimokuraɗiyya na ci gaba da fama da rauni mai tsanani. Alamun cutar sun bayyana ne a cinikin baragurbin wakilai (delegates), amfani da kuɗin ƙasa da aka wawure ta hanyar haram wajen gudanar da yaƙin neman zaɓe, maƙudan kuɗin da ake ware wa Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC), ƙarancin yawan masu kada ƙuri’a, sayen ƙuri’u a bainar jama’a, tashin hankali yayin zaɓe, da kuma yaɗuwar fargaba, musamman a tsakanin matasa, cin amana na ƴan siyasa, canja sheƙa da zaɓaɓɓu ke yi, da dai sauran makamantansu. Asalin matsalar ita ce, rashin shiga cikin gudanar da gwamnati a siyasance (eɗclusion) na masu gaskiya da riƙon amana, matasa, mata, masu fama da naƙasa, ƴan...
Sai dai girma, kima da ɗaukakar da matasa ke da ita ga al’umma ta ja baya ƙasa sosai a bisa ga yadda rayuwarsu ke iyo da ninƙaya a kogin zubar da mutunci ta hanyar aiwatar da abubuwan da ke da alamar ayar tambaya. Matasa da dama a yau ba su ganin kowa da gashi, ba su girmama kowa, ba su ganin mutuncin kowa, ba su daraja kowa ballantana har a tsawata masu ko a ba su shawara da ɗora su kan hanyar yadda za su daidaita rayuwar su daga gurɓatacciyar hanya zuwa madaidaiciyar hanya. Abin takaici ne da matuƙar damuwa yadda matasa suka gurɓata rayuwarsu mamakon amfani da lokaci da damar da suke da ita amma sai suka zaɓi biyewa...
Ɗaya daga cikin jigo da suka kafa Jam’iyyar PDP, Farfesa Jerry Gana ya yi iƙirarin cewa tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi zai kayar da duk wani ɗan takara a jihohin Arewacin Najeriya idan ya tsaya takara a PDP. Da yake bayabni a tashar talabijin ta Arise TV a ranar Laraba, Gana ya ce, “Ni mai nazari ne, kuma ina nazarin ra’ayoyi, a jihohin Arewa Peter Obi a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP zai doke duk wani ɗan takara, saboda mutanenmu suna da gaskiya.” Mun yi asarar shanu 340 a hannun ɓarayi a Yuli — Miyetti Allah Tinubu ya tsawaita wa’adin aikin shugaban hukumar Kwastam Peter Obi ya fice daga Jam’iyyar PDP a watan Mayun 2022 inda ya jagoranci Jam’iyyar LP a...
Melaye wanda shi ne dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a zaben jihar Kogi a 2023, har yanzu bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba a nan gaba. Sai dai rahotanni na nuni da cewa, yana iya sauyawa zuwa jam’iyyar ADC – wata gamayyar jam’iyyar adawa da a baya-bayan nan ta jawo hankalin wasu jiga-jigan masu sauya sheka da suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Abdullahi ya ce tun kafin a kafa haɗakar, wasu sun riga sun fara yaɗa cewa an shirya ta ne domin Atiku. Ya ƙara da cewa: “Ni ina da shekara 56, wa ya ce ba zan iya tsayawa takarar shugaban ƙasa ba?” Da aka tambaye shi game da Peter Obi, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Abdullahi ya ce Obi na cikin haɗakar har yanzu. Amma ya ce bai zama cikakken ɗan jam’iyyar ADC ba har yanzu. Ya bayyana cewa jam’iyyar ADC ta bai wa Obi da kuma tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, dama su fice daga jam’iyyunsu na yanzu wato LP da SDP. Ya kuma ce Obi ba zai koma jam’iyyar PDP ba, duk da cewa jam’iyyar...
Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara, ta bayyana matukar damuwarta kan yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara a jihar, inda ta bayyana hakan a matsayin abin ban tsoro da rashin fahimta. A wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren yada labarai na jam’iyyar, Yusuf Idris Gusau, jam’iyyar APC ta ce yawaitar ‘yan fashi da makami, garkuwa da mutane da kashe-kashe a Zamfara ya kai matakin da ba a taba ganin irinsa ba, yayin da ta zargi gwamnatin jihar a karkashin Gwamna Dauda Lawal da nuna halin ko in kula. A cewar sanarwar, jam’iyyar ta damu matuka da wani faifan bidiyo na baya-bayan nan inda aka ga sama da mutane 200 mazauna Kaura Namoda suna rokon a taimaka musu biyo...
Kwanan baya, kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya shirya taron bita tare da wadanda ba ’yan jam’iyyar ba, dangane da yanayin tattalin arzikin kasar, da kuma ayyukan tattalin arziki da za a aiwatar a rabin shekarar bana ta biyu, domin sauraren ra’ayoyinsu. Xi Jinping, babban sakataren jam’iyyar ne ya shugabanci taron tare da ba da muhimmin jawabi, inda ya ce, dole ne a zage damtse wajen gudanar da ayyukan tattalin arziki a rabin shekarar bana ta biyu, kuma a tabbatar da gudanar da ayyukan ba tare da tangarda ba, kana a aiwatar da cikakken sabon tunanin raya kasa daga dukkan fannoni, da gaggauta kafa tsarin raya kasa, da kiyaye aiwatar da manufofi ba tare da matsala ba, da...

Rashin Nasarar DPP A Zagayen Farko Na Kuri’ar Kiranye Ya Nuna Rashin Amincewar Al’ummar Taiwan Da Salon Mulkin Jami’yyar
Kakakin ofishi mai lura da harkokin yankin Taiwan a majalisar gudanarwar kasar Sin Chen Binhua, ya ce kalaman da aka jiyo jagoran yankin Taiwan na kasar Sin Lai Ching-te na yi dangane da sakamakon zagayen farko na kuri’ar kiranye da al’ummar Taiwan suka kada, ya nuna rashin gamsuwarsu da salon mulkin jam’iyyar DPP mai mulkin yankin. Chen Binhua, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Larabar nan, ya ce kalaman Lai na cike da yaudarar kai, sun kuma fayyace manufar da ya dage a kanta ta “neman ’yancin kan Taiwan”. Kazalika, mummunan kayen da DPP ta sha a kuri’un da aka kada ranar Asabar din karshen makon jiya, ya fayyace ajandarta ta yin fito-na-fito da Sin, tare da fafutukar...
Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta taya sabon mai martaba Sarkin Katsinar Gusau, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello, murnar hawansa karagar mulki a matsayin Sarkin Katsinan Gusau na 16. Jam’iyyar a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaranta, Yusuf Idris Gusau, ta bayyana sabon sarkin a matsayin mai tarihi da kuma nadin sarautar Allah, wanda ya zo ne jim kadan bayan rasuwar mahaifinsa, marigayi sarki, Alhaji Ibrahim Bello. Sanarwar ta nuna cewa Alhaji Abdulkadir kyawawan halaye na gaskiya, kwazonsa, sadaukarwa, biyayya ga mahaifinsa da ya rasu, da kuma mutunta al’umma ta kowane hali, sun nuna shi ne wanda ya cancanta. A cewar sanarwar, wannan shi ne karo na farko a tarihin masarautar da wani...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

SDP: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yi Wa El-Rufai Shaguɓe Da Ayyana Shi A Matsayin Ɗan Gudun Hijirar Siyasa
Jam’iyyar ta bayyana cewa bayan bincike daga reshen jam’iyyar na jihar Kaduna, ya tabbatar da cewa El-Rufai ba halataccen ɗan SDP bane. Saboda haka, Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar na Ƙasa ya kafa masa takunkumin shekaru 30, har zuwa shekarar 2055, ya hana shi sake neman zama mamba ko hulɗa da jam’iyyar ta kowace fuska. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jam’iyyar ta buƙaci hukumar INEC da sauran hukumomi da su lura cewa El-Rufai ba ɗan jam’iyyar ba ne, kuma bai da hurumin wakiltar ta a kowanne mataki. SDP ta kuma jaddada ƙudurinta na kare dimokuraɗiyya ta cikin gida da kuma adawa mai tushe da gaskiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Muƙaddashiyar Shugabar Jam’iyyar LP, Sanata Nenadi Esther Usman, ta ce gwamnatin APC ce ta fi jefa ’yan Najeriya cikin talauci sama da kowace gwamnati a tarihin ƙasar nan. Da ta ke zantawa da manema labarai a Jihar Kaduna, Sanatan ta ce jam’iyyar LP ta shirya tsaf don gyara kurakuran da gwamnatin APC ta tafka. Gwamna Bauchi ya sasanta manoma da makiyaya a Darazo Ambaliya ta yi ajalin mutane, ta lalata gidaje a Adamawa Ta roƙi ’yan Najeriya da su bai wa LP goyon baya, inda ta ce jam’iyyar za ta kawo canji na gaskiya. Ta ce halin da ake ciki na wahala a ƙasar nan ya yi muni ƙwarai, kuma ta d6ora alhakin hakan kan gwamnatin APC. Game da sauya...
Shugabar riƙo ta jam’iyyar Labour (LP) ta ƙasa, Sanata Nenadi Usman, ta ce jam’iyyarsu ta shirya tsaf domin gyara manyan kura-kurai da gazawar da gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki ta jefa Nijeriya a ciki. Sanata Usman ta bayyana hakan ne a wata ganawa da manema labarai a ƙarshen mako a Jihar Kaduna dangane da abinda da ke faruwa a cikin jam’iyyar LP. Rashin abinci mai gina jiki ya kashe yara 650 a Katsina — MSF Za mu ba da damar shigar da kayan agaji a Gaza — Isra’ila Sanatar ta buƙaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da goya musu baya domin a cewarta, jam’iyyar LP ce za ta farfaɗo da fatan da al’umma ke da shi da kuma ɗaga...

Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya
A baya-bayan nan Robert Tarjan, Ba’amurke masanin kimiyyar na’ura mai kwakwalwa, wanda ya taba lashe lambar yabo ta “Turing”, ya ce Sin ta kafa tsarin bunkasa ilimin kimiyya a matakin farko, a matsayin dabara ta tsawon lokaci da kasar ke baiwa fifiko, kuma hakan abu ne mai matukar ban sha’awa. Kazalika, a halin yanzu, Sin ta cimma manyan nasarori, yayin da a gaba kuma, ake sa ran ganin karin ci gaba da kasar za ta cimma. Tarjan wanda ya bayyana hakan yayin wata zantawa da kafar CMG ta Sin, ya ce a matakan ingiza ci gaban basirar AI, Sin na da manyan damammakin takara, wadanda suka hada da dagewa wajen cimma burika na tsawon lokaci, da tsarin bayar da ilimin...
Shugaban riƙon ƙwarya na jam’iyyar ADC, David Mark, ya ce Arewacin Najeriya na cikin mawuyacin hali, kuma jam’iyyarsu ce kaɗai za ta iya warware waɗannan matsaloli idan aka zaɓe ta. Ya bayyana hakan ne a taron jam’iyyar ADC da aka yi a Abuja Continental Hotel, inda mambobi da magoya bayan jam’iyyar daga sassa daban-daban suka halarta. Dole gyaran kundin tsarin mulki ya haɗa kan ƙasa da shugabanci na gari — Abba Za a ɗauke wuta na tsawon kwanaki 25 a Legas — TCN David Mark, wanda tsohon Shugaban Majalisar Dattawa ne, ya gabatar da jawabi mai taken: “Haɗin kai da zaman lafiya su ne mafita ga matsalolin Arewa”. Ya ce Arewa na fuskantar matsaloli masu tsanani kamar su rashin tsaro,...
Wasu yan bindiga wadanda ake dangantasu da kungiyar Jaishul-Zulum sun dauki alhakin kai hare-hare a cikin wata kotu a birnin Zahidan babban birnin lardin Sistab Baluchistan a yau Asabar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa yan ta’addan sun shigo da motarsu har zuwa a wata kotu a garin da Zahidan, sannan suka sauka suna son shiga kotun amma jami’an tsaro a kotun suka hanasu shiga. Daga nan kawai suka fara jefa nakiya irin da yaki a kansu. An yi ta musayar wuta tsakaninsu da jami’an tsaro zuwa wani lokacin suka sami nasarar halakasu. Amma kuma sun kai mutane 6 ga shahada uku daga cikinsu jami’an tsaron kotun da kuma wani yaru da kuma wata mata yar...
Mai magana da yawun jam’iyyar na wucin gadi ya ki janye ikirarinsa na cewa ADC na fuskantar manyan matsaloli a bangaren shari’a. “Muna da tabbaci kan doka a kowane mataki da muka dauka. Mun tabbatar mun rufe duk wata baraka da jam’iyya mai mulki za ta iya amfani da ita a kanmu,” ya kara da cewa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kwanan nan jam’iyyar PDP ta gudanar da taron kwamitin zartarwa karo na 100 da aka gudanar ranar 30 ga Yuni, PDP ta warware rikicin da ya dade yana ci mata tuwo a kwarya na batun mukamin sakataren jam’iyyar na kasa wanda ta tabbatar da Sanata Samuel Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyyar. Duk da wannan warware batun, Atiku da wasu magoya bayansa sun fice daga jam’iyyar sakamakon rashin warware rikicin gida na jam’iyyar. A ranar 1 ga Yuli, Atiku da Peter Obi da Rotimi Amaechi da Nasir El-Rufai, da wasu sun kulla hadaka a karkashin jam’iyyar ADC, sun ce sun yi wannan hadakar ne domin kalubalantar APC a zaben 2027. A matsayin wani bangare na wannan yunkurin hadin gwiwa, sun nada...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi alhinin rasuwar Sarkin Gusau, Dokta Ibrahim Bello na Jihar Zamfara. Sarkin ya rasu da safiyar Juma’a yana da shekaru 71. An yanke wa mutum 3 hukuncin kisa kan kisan kai a Gombe HOTUNA: Yadda Kwankwaso ya karɓi ’yan APC zuwa NNPP a Kano Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin watsa labarai, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa. Ya ce Sarkin mutum ne da ya sadaukar da rayuwarsa don hidimta wa al’ummarsa. Shugaba Tinubu ya ce rasuwar Sarkin babban rashi ne, ba wai kawai ga mutanen masarautarsa ba, har da ƙasa baki ɗaya. Ya yaba da jajircewarsa, kyakkyawan shugabancin da sadaukarwarsa ga jama’a. Shugaban ƙasa ya miƙa ta’aziyyarsa ga...
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a 2023, ya karɓi ’yan APC zuwa jam’iyyar NNPP a Jihar Kano. Kwankwaso, ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a ta shafinsa na X, inda ya ce waɗanda suka sauya sheƙar ’yan jam’iyyar APC ne. An kai hari a ƙauyuka uku da kashe mutum 7 a Imo An kashe mata da yara a sabon harin Filato “Jiya rana ce mai muhimmanci,” in ji shi. “Na karɓi dubban mutane da suka bar jam’iyyar APC suka dawo NNPP.” Ya ce taron ya gudana ne a gidansa da ke Kano, inda ya yi wa sabbin mambobin maraba da kuma alƙawarin adalci da haɗin kai a cikin jam’iyyar. An wallafa hotunan taron a shafukan...
“Rasuwar Sarkin Zamfara babban rashi ne ga al’ummar jihar Zamfara, Arewa da ma ƙasar nan baki ɗaya. “Sarkin ya sadaukar da rayuwar sa a shekarun nan 10 da ya ya yi hana mulki a matsayin Sarkin Gusau na 15, wanda ya hau a ranar 16 ga watan Maris na shekarar 2015. Ya yi mulki cikin jajircewa da sadaukarwa. “Marigayin, kafin ya zama Sarki, ƙwararren ma’aikacin gwamnati ne, wanda har sai da ya kai matsayin Babban Sakatare a gwamnatin tsohuwar jihar Sakkwato da ta Zamfara. “Na rasa murshidin Uba mai basira, wanda ke nuna mani hanya, tare da sauran shugabanni a jiha. Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki ya gafarta masa kura-kuran sa, ya sa aljanna ce ce makoma. Daga kanmu,...
An sami hatsarin tashin gobara a cikin wani rumbun ajiyar makamai a garin Mu’arrah dake gundumar Idlib ta Arewa, wanda ya yi sanadiyyar mutuwa da jikkatar mutane da dama. Majiyar lafiya ta kiwon kasar Syria ta bayyana cewa; Mutane 2 sun rasa rayukansu, yayin da wasu 70 su ka jikkata sanadiyyar fashewar rumbun makamai a garin Mu’arrah Masrin. Hukumar agjin gaggawa ta kasar Syria ta ce; Har yanzu babu cikakken dalili akan abinda ya haddasa wannan gobarar ta Mu’arrah Msarin. Ma’aikatan kwana-kwana sun nufi wurin da gobarar ta tashi domin kashe wuta da kuma dauke mutanen da su ka jikkata.
Kwamitin zartaswa na Jam’iyyar APC na ƙasa ya naɗa Ministan Jin-ƙai da Yaƙi da Talauci, Farfesa Nentawe Yilwatda, a matsayin sabon shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa. Nan take aka rantsar da Nentawe Yilwatda a wajen taron. Kwalara: Mutum 13 sun mutu sama da 236 na jinya a Neja Jirgin Rasha mai dauke da mutum 50 ya yi hatsari a China Nentawe ya yi rantsuwar ne da misalin ƙarfe 02:50 na rana a gaban manyan jiga-jigan jam’iyyar yayin taron NEC karo na 14 da ya gudana a ɗakin taro na fadar gwamnati da ke Abuja, ranar Alhamis. Nentawe, wanda ya fito daga Jihar Filato, shiyyar Arewa ta Tsakiya, shi ne ɗan takarar Gwamna na Jam’iyyar APC a zaɓen 2023.
An cimma matsaya kan zaɓensa bayan wata ganawa da aka yi a Abuja tsakanin Shugaba Bola Tinubu da gwamnonin APC. Ana sa ran manyan shugabannin jam’iyyar za su tabbatar da naɗinsa a yau Alhamis. Farfesa Yilwatda, ya fito ne daga Jihar Filato da ke yankin Arewa ta Tsakiya, yankin da suke da alhakin riƙe kujerar shugabancin jam’iyyar. Wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar sun ce kasancewarsa Kirista zai taimaka wajen daidaita shugabanci, duba da cewa shugaban ƙasa da mataimakinsa Musulmai ne. Shugabannin jam’iyyar na fatan Farfesa Yilwatda zai kawo sabon salo, tare da haɗa kan jam’iyyar kafin tunkarar zaɓe mai zuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
Matukar ba a sami sauyin tsare-tsare ba, akwai yiwuwar Ministan Jinkai da Yaki da Talauci, Farfesa Nentawe Yilwatda ya zama sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa a yau Alhamis. Majiyoyi da dama a daren jiya sun shaida wa Aminiya cewa Nentawe ne ke kan gaba a cikin mutanen da ake so su dare shugabancin jam’iyyar mai mulki. Sai dai a cewar wasu majiyoyin, tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Umaru Tanko Almakura shi ma na daga cikin wadanda ake duba yiwuwar ba kujerar. Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram Ibn Khalid a Borno NAFDAC ta gano dakin ajiye kayayyaki makare da sinadaran hada bam a Kano A daidai lokacin da ya rage ’yan sa’o’i gabanin taron Kwamitin Zartarwa na jam’iyyar, majiyoyi...
Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC kuma Gwamnan Jihar Imo, Sanata Hope Uzodimma, ya bayyana cewa Gwamnonin APC sun gudanar da wata muhimmiyar ganawa da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Fadar gwamnati da ke Abuja. Da yake zantawa da manema labarai na Fadar Shugaban Ƙasa bayan kammala taron, Gwamna Uzodimma ya bayyana ganawar da cewa “tattaunawa ce mai muhimmanci da Shugaban Ƙasa domin ƙarfafa jam’iyyar da kuma inganta ikon ta na samar da nagartaccen shugabanci ga ‘yan Najeriya”. Ya ƙara da cewa, a matsayin su na gwamnoni, sun haɗu da Shugaban Ƙasa domin daidaita matsayin al’amuran jam’iyya da kuma muhimman abubuwan da suka shafi shugabanci. Da aka tambaye shi ko ana sa ran yanke wasu manyan shawarwari ko takaddama a...
Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya zargi Shugaba Bola Tinubu da amfani da hukumomin gwamnati wajen danne ’yan adawa. Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da manema labarai a Kano. Uwa ta kashe ’ya’yan cikinta biyu saboda kuncin rayuwa An kone babur din ‘barayin waya’ a Kano Lamido, ya ce hukumomi irin su EFCC ana amfani da su ne wajen matsa wa ’yan adawa lamba. Ya bayar da misalin tsohon Gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, wanda ke fuskantar tuhuma kan zargin aikata almundahana. A cewarsa bayan Okowa ya koma jam’iyyar APC, an daina tuhumarsa. Ya kafa misali da wata magana da Sanata Adams Oshiomhole ya taɓa yi. Ya ce: “Da zarar ka shiga APC, an yafe...
Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Tinubu ta karɓo bashin ƙasashen waje da ya haura dala biliyan 21 domin aiwatarwa da cike giɓin kasafin kuɗin shekarar 2025 zuwa 2026. Majalisar ta bayyana cewa za a yi amfani da bashin ne wajen aiwatar da muhimman ayyukan ci gaban ƙasa, musamman a fannonin ababen more rayuwa, da tsaro, da noma da kuma gina ɗan Adam. UNICEF na zargin Gwamnatin Nijeriya da cin zarafin ƙananan yara Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 151 a Nijeriya bana — NCDC Shugaban kwamitin Majalisar Dattawa kan basussukan cikin gida da na waje, Sanata Aliyu Wamako ne ya gabatar da rahoton karbar bashin yayin zaman majalisar a yau Talata. Sanata Wamakko wanda yake wakiltar shiyyar Sakkwato...
Ya ce ya zagaya dukkanin ƙananan hukumomin Jihar Bauchi domin goyon bayan Gwamna Bala yayin yaƙin neman zaɓe, duk da cewa yana ci gaba da aiki a matsayin Sakataren Gwamnatin Jiha. A watan Janairu 2025, Kashim ya yi murabus daga matsayin SSG, inda ya ce gwamnan ne ya umarce shi da yin hakan. Rahotanni na nuna cewa Kashim na da niyyar sake tsayawa takarar gwamna a nan gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta zabi Hon. Kamilu Sa’idu (Wamban Kasuwar Daji) a matsayin dan takararta na Majalisar Dokokin Jihar Kaura Namoda ta Kudu da za a yi ranar 16 ga Agusta, 2025. A wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC na Jihar, Yusuf Idris Gusau ya fitar, ya ce Kamilu ya fito ne ba tare da hamayya ba bayan janyewar wasu ‘yan takara uku Bashir Muhammad Madaro (Walin Kurya), Anas S/Fada, da Alhaji Ashiru Hamisu Habibu—a lokacin zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar a makarantar firamare ta Kasuwar Daji. Sanarwar ta ce, ‘yan takarar ukun sun sauka ne domin nuna goyon bayansu ga Kamilu Sa’idu inda suka yi alkawarin samun nasararsa da...
Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Nijeriya, Femi Gbajabiamila ya ce haɗakar ’yan siyasa a jam’iyyar ADC alheri ce ga siyasar Nijeriya. Ya bayyana cewar haɗaka ’yan adawar za ta taimaka wajen hana ƙasar faɗawa cikin siyasar jam’iyyar ƙwaya ɗaya tal. WFP ya dakatar da tallafin abinci a Yammaci da Tsakiyar Afirka Za a sa zare tsakanin Amurka da Turai kan harajin kasuwanci Gbajabiamila ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomin da aka yi a Jihar Legas a jiya Asabar a mazaɓarsa da ke Surulere. Sai dai tsohon shugaban Majalisar Wakilan ya bayyana shakkunsa kan haɗakar, inda ya ce ce ba ya tunanin za ta yi wani tasirin a-zo-a-gani. “Muna maraba da samar da haɗakar....
A bisa umarnin sakatariyar kungiyar ‘yan jarida ta kasa NUJ, an yi nasarar gudanar da zaben majalisar jihar Zamfara a ranar Asabar din da ta gabata cikin kwanciyar hankali da lumana, inda aka dawo da dukkan mukamai ba tare da hamayya ba. Mukamin daya tilo da aka fara takaddama a kai ya sa daya daga cikin masu neman takarar, Rabi Yusuf ta janye bisa radin kanta, wanda a hukumance ta sauka ta hanyar mika takarda ga kwamitin tantancewa, tare da aika kwafin ga mataimakin shugaban shiyyar da Sakatare. Wakilai daga Sakatariyar NUJ ta kasa ne suka jagoranci gudanar da zaben da kuma kaddamar da taron wanda suka hada da mataimakin shugaban shiyyar A, Muhammad Tukur Umar da sakataren...
Sanata Ireti Kingibe, wacce ke wakiltar Babban Birnin Tarayya, ta fice daga jam’iyyar LP zuwa ADC. Da ta ke magana da ’yan jarida a Abuja, ta ce wannan matakin nata wani shiri ne na tunkarar babban zaɓen 2027. Abin da ya faru tsakani na da DSS bayan kama ni — Ɗan Bello DSS ta saki Ɗan Bello bayan ta kama shi a Kano “Ni cikakkiyar mamba ce ta ADC yanzu,” inji ta. Da aka tambaye ta ko tana da ƙwarin gwiwa game da shugabancin ADC da haɗin gwiwar da suke ƙoƙarin ginawa, ta ce jam’iyyar na ci gaba da samun tagomashi. Tace kowace tafiya a sannu ake binta wanda daga bisani ta ke girma. Wasu sun nuna damuwa cewa wannan...
Sanata Ireti Kingibe, wacce ke wakiltar Babban Birnin Tarayya, ta fice daga jam’iyyar LP zuwa ADC. Da ta ke magana da ’yan jarida a Abuja, ta ce wannan matakin nata wani shiri ne na tunkarar babban zaɓen 2027. Abin da ya faru tsakani na da DSS bayan kama ni — Ɗan Bello DSS ta saki Ɗan Bello bayan ta kama shi a Kano “Ni cikakkiyar mamba ce ta ADC yanzu,” inji ta. Da aka tambaye ta ko tana da ƙwarin gwiwa game da shugabancin ADC da haɗin gwiwar da suke ƙoƙarin ginawa, ta ce jam’iyyar na ci gaba da samun tagomashi. Tace kowace tafiya a sannu ake binta wanda daga bisani ta ke girma. Wasu sun nuna damuwa cewa wannan...
Wata majiya ta tabbatar da cewa, a yayin da tsohon shugaban majalisar dattawan ya je Jihar Binuwai domin daurin auren jikarsa, “watakila zai yi ganawa da shugabanni da masu goyon bayan tafiyar a shiyyar.” Aregbesola ya samu tarba daga magoya bayansa a lokacin da ya isa Jihar Legas jim kadan bayan kaddamar da jam’iyyar a Abuja. A nasa bangaren, Atiku ya gana da wasu jiga-jigan jam’iyyar ADC na jihar Gombe a Abuja karkashin jagorancin tsohon minista kuma Sanata Idris Abdullahi a Abuja, a yammacin ranar Juma’a. Wata majiya ta shaida wa LEADERSHIP Sunday cewa shugabannin jam’iyyar “sun dawo ne domin tuntubar yankunansu tare da kafa hanyar kulla alaka da jama’a yadda ya kamata.” “Yan Nijeriya sun riga sun yi taro,...
Rahotanin sun bayyana cewa Shettima ya ziyarci Kano ne don yin ta’aziyyar rasuwar hamshakin dan kasuwa, Alhaji Aminu Dantata, wanda ya rasu kwanan nan, da kuma jajanta wa mutanen Kano kan wannan rashi. Haka kuma rahotannin sun bayyana cewa a irin wadannan manyan taruka a Nijeriya, an saba ganin shugabannin jam’iyya da goyon baya su tarbi manyan jami’ai kamar mataimakin shugaban kasa, amma lamarin ya bambanta yayin ziyarar Shettima, wanda ya haifar da zazzafar muhawara. Da yake musanta cewa akwai rikice-rikice na cikin gida a jam’iyyar, sakataren APC a Kano, Ibrahim Zakari Sarina, ya shaida cewa rashin halartar shugabannin jam’iyyar a ziyarar ta’aziyya da mataimakin shugaban kasa ya kawo Kano ya faru ne sakamakon rashin sadarwa. “Mun san cewa ziyarar...
Sojojin Sahayoniya suna ci gaba da yi wa mutane Gaza kisan kiyashi a kwana na 643 a jere. Sojojin sahayoniyar suna amfani da dukkanin kayan yaki da su ka hada jiragen masa masu matuki da marasa matuki, da kuma manyan bindigogi. Tun da safiyar yau Alhamis ne dai sojojin HKI su ka fara kai hare-hare da tankokin yaki bayan kutsawarsu cikin yankin “Bi’irut-Turki” da “maslakh” dake kudancin Khan-Yunus. Tankokin sun rika bude wuta akan mai uwa da wabi da gidajen mutane a cikin yankin, da hakan ya yi sanadiyyar jikkatar mutane da yawa.” Majiyar Falasdinawa ta tabbatar da shahadar mutane 16, da su ka hada mata da kananan yara a wuruin da suke jiran karbar abincin agaji a shataletalen al-Dhayyarah,...
Tsohon jigo a Jam’iyyar LP, Kenneth Okonkwo, ya ce dole ADC ta tsayar da ɗan Arewa takara idan tana son ta kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027. A cikin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, Okonkwo, ya ce idan ADC ta tsayar da ɗan Kudu takara, Tinubu zai sake lashe zaɓe ba tare da wata tangarɗa ba. Biza: UAE ta ƙaƙaba wa ’yan Najeriya sabbin takunkumai Yara miliyan 5.4 na fama da karancin abinci a jihohin arewa 9 – Red Cross Ya ce dole ne ’yan adawa su yi aiki da hikima da dabaru idan suna son yin nasara. “Shirina a wannan karon shi ne zan goyi bayan ɗan Arewa a 2027,”...
Jam’iyyar ADC ta musanta labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa wasu shugabanni daga yankin Kudu sun buƙaci Atiku Abubakar, da ka da ya fito takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027. A cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar, ta ce wannan labari ƙarya ne, wanda aka ƙirƙira don haddasa rikici , musamman a wannan lokaci da ake ƙoƙarin haɗa kan ‘yan adawa da kuma ƙarfafa dimokuraɗiyya a Nijeriya. Amurka Ta Tsaurara Matakan Bai Wa ‘Yan Nijeriya Biza Kofin Duniya: Chelsea Ta Kai Wasan Ƙarshe Bayan Ta Doke Fluminense Jam’iyyar ta ce: “Ba mu taɓa zama da wasu wakilai daga Kudu domin yin irin wannan magana ba. “Wannan rahoto ba kawai ƙarya ba ne, yana kuma...
Matar tsohon Gwamnan jihar Adamawa, Zainab Boni Haruna, ta fice daga tsohuwar jam’iyyarta ta PDP zuwa jam’iyyar hadakar ’yan adawa ta ADC. Zainab, wacce asalinta ta fito ne daga karamar hukumar Nangere a Jihar Yobe ta bayyana haka ne a wani taro da mata magoya bayan jam’iyyar ta ADC da aka gudanar a Damaturu, babban birnin jihar ta Yobe. Masu ƙwacen waya sun kashe ma’aikaciyar ofishin jakadancin Ghana a Abuja Kaso 90 na ’yan bindigar da suka addabi Katsina ’yan asalin jihar ne – Radda Zainab Boni ta kuma zargi jam’iyyar APC mai mulki karkashin jagorancin Shugaban Kasa Bola Tinubu kan rashin tsaro, wahalhalu, cin hanci da rashawa da kuma rashin shugabanci na gari a kasar nan. “Mutane suna shan...
An kaddamar da jam’iyyar African Democratic Party, ADC a Gombe mako guda bayan wasu jiga-jigan ‘yan adawa sun hada kai cikin jam’iyyar. Shugaban jam’iyyar ADC a jihar Gombe kuma tsohon ministan sufuri Alh. Idris Abdullahi, ya ce makasudin shiga jam’iyyar shi ne ceto kasar nan daga kangin tattalin arziki da dora ta kan turbar ci gaba. A cewarsa gamayyar jam’iyyun adawa sun zabi jam’iyyar ADC a matsayin jam’iyya daya tilo da za ta samar da hanyar kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2027. Sanata Idris Abdullahi ya jaddada kudirin kungiyar a Gombe na ci gaba da kasancewa da hadin kai domin cimma burin ta. Shugaban jam’iyyar ADC na jihar Gombe Alh. Auwal Barde ya ce...
Aminu Dahiru Ahmad, hadimin tsohon shugaban jam’iyar APC na kasa, Abudllahi Umar Ganduje, ya ce jam’iyyar za ta gane ta yi kuskure kan saukarsa daga shugabancin. A wata doguwar wasika da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana takaicinsa kan rashin nuna wa Ganduje halasci, duk da irin ci gaban da ya kawo jam’iyar wanda ya ce ba a taba samun makamancinsa ba. “Tarihin APC ba zai manta da Ganduje ba — Shi ya kai ta matsayin da take kai yanzu,” inji shi. Gwamnatin Tinubu na shirya mana zagon ƙasa — ADC An ƙayyade maki da shekarun shiga jami’a a Nijeriya Aminu ya ba da misali da yadda aka dinga tururuwar shiga APC a lokacin mulkin Ganduje da kuma...
Tsohon Ministan Sufuri, Idris Umar, ya bayyana cewa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ce za ta ceto Najeriya daga halin da take ciki, tare da mayar da APC jam’iyyar adawa a Zaɓen 2027. Yayin wani taron haɗin gwiwar jam’iyyu na adawa a Gombe, an amince da amfani da ADC a matsayin dandalin siyasa na bai ɗaya domin fuskantar zaɓen 2027. Gwamnatin Tinubu na shirya mana zagon ƙasa — ADC NAJERIYA A YAU: Sarƙaƙiyar da ke gaban Haɗakar ADC: Atiku ko Peter Obi Taron ya gudana a Shugleez Event Centre wanda ya samu halartar fitattun ‘yan adawa daga sassa daban-daban na jihar. Idris ya ce za su yi haɗakar ce ba wai kawai don karɓar mulki ba, sai dai domin ceton...
Jam’iyyar ADC ta zargin Fadar Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinuba da shirya mana wata kutungwila mai hadarin gaske domin kawo cikas ga hadakar ’yan adawan da ke kara samun farin jini. Sakataren Yada Labarai na ADC na Kasa, Malam Bolaji Abdullahi, ya ce a sakamakon haka gwamnatin APC a matakin kasa ta kira wani taron sirri tsakanin wasu manyan jami’an gwamnati da shugabbanin jam’iyyar ADC na jihohi da kuma kusoshinta daga yankin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas. Bolaji Abdullahi ya ce, “muna da sahihan bayanan sirri cewa manufar taron ita ce domin razanawa da tursasa wadannan shugabannin jam’iyar su shirya wa ’yan adawar makarkashiya. Wannan ba siyasa ba ce, tsurku ce.” Ya ci gaba da cewa, hadafin taron...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wannan lamari ya buɗe sabon shafi a siyasar ƙasar nan, inda ƴan adawa suke ci gaba da cewa zuwan sabuwar jam’iyyar wani sauyi ne da za a samu a cikin ƙasar. Wani mai sharhi a kan siyasa, Sani Kabo, ya bayyana abin da ya samu shafin yanar gizon jam’iyyar a matsayin wata ƴar manuniya ga irin buƙatar da ake da ita wajen sauya sheƙa da kuma haɗin kan ƴan adawa, inda ya misalta abin da yake faruwa da shekara ta 2013, lokacin da aka samar da jam’iyyar APC wadda ta kawo karshen mulkin jam’iyyar PDP a wancan lokaci. Shima wani masanin siyasa a Nijeriya wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce wannan ya nuna yadda al’ummar ƙasar suke buƙatar...
Elon Musk, wanda ya taɓa zama mashawarcin Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce zai kafa sabuwar jam’iyyar siyasa mai suna America Party. Ya bayyana hakan ne a shafinsa na X (Twitter), makonni bayan wata taƙaddama da ta ɓarke tsakaninsa da Shugaban Amurka. Tinubu ya umarci sojoji su murƙushe ’yan ta’adda a faɗin Najeriya Mutum 21 sun rasu a hatsarin mota a kan hanyar Zariya–Kano Musk, wanda attajirin mai kuɗi sosai, ya ce jam’iyyarsa za ta kasance wata hanya ta daban daga jam’iyyu biyu da ake da su yanzu, wato Republican da Democrat. Amma har yanzu ba a bayyana ko hukumar zaɓen Amurka ta amince da rajistar jam’iyyar ba. Amma Musk bai bayyana wanda zai jagoranci jam’iyyar ko irin manufofinta ba....
Ɗaya daga cikin hadiman gwamnan jihar Yobe, Hon. Babagana Yakubu Mohammed, ya ajiye muƙaminsa na mai taimakawa gwamna na musamman ya kuma fice daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar ADC. Babagana, ya sanar da ajiye aikin nasa ne cikin wata wasiƙa da ya aikewa Sakataren Gwamnatin Jihar, Baba Malam Wali. Ba Ni Da Niyyar Barin APC Zuwa Wata Jam’iyyar — Gwamna Zulum Ranar Talata Mai Zuwa Zan Koma Zauren Majalisar Dattawa – Sanata Natasha A kwafin wasiƙar da LEADERSHIP ta samu, Babagana ya bayyana matuƙar damuwarsa kan yadda aka yi watsi da wanda suke hidimtawa gwamnati da taimaka mata. “Don haka ina sanar da ajiye aiki na a hukumance daga matsayin mai taimakawa gwamna na musamman” cewarsa. A ƙarshe, ya godewa...
Zalum ya kuma shawarci gidajen jaridu da su dinga tantance labarai kafin su yaɗa shi domin kaucewa labaran ƙanzon kuregen da wasu suke yaɗawa. A ƙarshe gwamnan ya ce ya duƙufa wajen hidimtawa al’ummar jihar Borno a ƙarƙashin jam’iyar mai albarka ta APC . Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa zai bar jam’iyyar APC zuwa ADC tare da wasu gwamnoni biyar. A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Dauda Iliya, ya fitar, Zulum ya ce wannan labari ƙarya ne, kuma wasu ne kawai ke ƙirƙirarsa domin cimma wata manufa ta ƙashin kansu. Gwamna ya gargaɗi sarakuna kan mamaye filayen kiwo a Gombe Majalisar Dattawa ta gindaya sharaɗin dawo da Sanata Natasha Ya ce yana nan daram a jam’iyyar APC kuma yana biyayya ga jam’iyyar a matakin jiha da ƙasa baki ɗaya. Sanarwar ta ce, “Mun ji wani labari da ake yaɗawa cewa zan koma jam’iyyar ADC tare da wasu gwamnoni biyar. “Wannan...

Iran ta Bukaci Gudanar da Bincike Kan Sacewar jami’ar Diblomasiyyar kasar A Lebanon Shekaru 43 Da Suka gabata
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi tir da ci gaba da riki jami’an diblomasiyyar kasar 4 wanda HKI take yi tun shekaru 43 da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar tana fadar haka a wata sanarwa da ta fitar shekaru 43 cur da sacewar wadanda Jami’an diblomasiyyar kasar a birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon a ranar 4 ga watan Yuli n shekara 1982. Jami’an diblomasiyyar suna ne Seyed Mohsen Mousavi, Ahmad Motevaselian, Kazem Akhavan, and Taghi Rastegar Moghadam, wadanda wata kungiyar yar ta’adda wacce HKI take goyon bayanta ta kamasu ta kuma mikawa HKI a lokacinda take mamayae da kasar Lebanon. Rahoton ya yabawa gwamnatin kasar Lebanon kan hadin...
Ibrahim ya bayyana cewa, sun rarraba mukamai na rikon jam’iyyar a tsakaninsu, kafin babban taro na kasa a nan gaba. Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai ya tabbatar cewa; hadakar ta ADC, ta zabi Aregbesola a matsayin sakatarenta na kasa na riko, har ma ya wallafa a jawabin karbar mukamin da ya yi a shafukan sada zumunta. Matakin ‘yan adawar na shiga ADC, na zuwa ne bayan kasa cimma bukatarsu ta yi wa sabuwar kungiyar mai suna ‘All Democratic Alliance’ (ADA), rajista a matsayin jam’iyyar siyasa, sakamakon jan kafa da suka rika samu daga babbar hukmar zabe ta kasa (INEC). Haka zalika, Atiku Abubakar da wasu manyan jam’iyar PDP, sun nemi ‘yan jam’iyyar da su hada hannu da su wajen shiga...
Rahotanni daga kudanci Lebanon sun ce, sau uku jiragen yakin HKI su ka kai hare-hare a kan gidajen mutane da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya da kuma jikkatar wasu da dama. A garin Shaqra’dake yankin Bint-jubail, jiragen sama marasa matuki sun kai hare-hare da ya yi sanadiyyar jikkatar mutane biyu da raunuka, kamar yadda ma’aikatar kiwon lafiya ta Lebanon ta sanar. Har ila yau wani jirgin maras matuki na abokan gaba ya kai wani harin akan wata mota a yankin “Safful-Hawa” da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya. A garin Shab’a kuwa ‘yan sahayoniyar sun kai hari akan wani gida, wanda ya yi sanadiyyar jikkatar mutanen dake cikinsa. Majiyar asibiti a garin Marja’iyyun ta ce an kai...
Dakarun kare juyin musulunci na Iran sun fitar da bayani a lokacin tunawa da sace jami;an diplomasiyyar Iran 4 a birnin Beirut, wanda ya kunshi cewa: Ya zama wajibi ‘yan sahayoniya su kwana da sanin cewa; Duk laifukan da su ka aikata a baya za a yi musu sakamako a kansa,kuma duk wani sabon wuce gona da iri, zai gaggauta zuwa karshensu ne.” Sanarwar ta kuma ce: Muna tunawa ne da zagayowar cikar shekaru 42 daga wancan aikin ta’addanci, da a yanzu kwanaki kadan ne su ka wuce na kawo karshen yakin da HKI da Amurka su ka kallafa mana na tsawon kwanaki 12. Yaki ne wanda martani mai karfi da jamhuriyar musulunci ta Iran ta mayar yake kara fito...
Jam’iyyar NNPP, ta bayyana cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya yi mata takarar shugaban ƙasa a 2023, ba zai tsaya takara a 2027 ba. Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dokta Agbo Major, ne ya bayyana haka a wata sanarwa, inda ya mayar da martani kan wata magana da Buba Galadima ya yi. Tinubu ko ɗansa zai naɗa shugaban INEC, APC sai ta faɗi zaɓen 2027 — Dalung Tsadar rayuwa ta sa ’yan Nijeriya na siyan abincin da ya lalace Galadima, ya ce har yanzu Kwankwaso yana cikin NNPP kuma zai tsaya takara a 2027. Galadima ya shaida wa manema labarai cewa: “Babu wani tabbaci da ke nuna cewa Kwankwaso yana shirin komawa APC. Za mu ci gaba da zama a...
Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya ce duk wani yunƙuri da Shugaba Bola Tinubu, zai yi ba zai hana jam’iyyar APC faɗuwa a zaɓen 2027 ba. Yayin wata hira da aka yi da shi a Jos, a Jihar Filato, Dalung, ya ce ko da Tinubu zai naɗa ɗansa Shugaban Hukumar Zaɓe (INEC), ko matarsa ta zama Babbar Alƙalin Alƙalai ta Ƙasa, hakan ba zai taimaka wa APC ba. Tsadar rayuwa ta sa ’yan Nijeriya na siyan abincin da ya lalace Mutanen unguwa sun kama masu ƙwacen waya a Kano Ya ce gwamnatin APC ta gaza, kuma ta jefa ‘yan Najeriya cikin ƙunci da yunwa ta hanyar manufofinta marasa kan gado. Dalung ya ce: “Ko duk gwamnonin jihohi 36...
Salim Sani Shehu Jam’iyyar NNPP ta bayyana a hukumance cewa tsohon ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ba zai sake yin takarar shugaban ƙasa karkashin jam’iyyar a zaɓen 2027 ba. Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Agbo Major, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin da yake mayar da martani ga kalaman Buba Galadima, wanda ya ce Kwankwaso zai ci gaba da zama cikin jam’iyyar kuma zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027. Major ya ce jam’iyyar ta riga ta kori Kwankwaso da Galadima bisa zargin aikata laifukan cin amanar jam’iyya, don haka ba su da ikon magana da sunan NNPP, balle su wakilci jam’iyyar a a duk wani sha’anin siyasa. “Tun da dadewa NNPP...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yan Najeriya da dama na ta bayyana mabanbantan ra’ayoyi kan sabon hadakar ‘yan siyasa zuwa sabuwar jami’yyar ADC. A yayin da wasu ke ganin wannan hadaka za ta cire musu kitse daga wuta, wasu kuwa gani suke yi duk kanwar ja ce. A ranar laraban nan ne dai gaggan ‘yan siyasa daga jamiyyu daban daban suka hadu don dinkewa wuri daya da niyyar kalubalantar jamiyya mai mulki ta APC, a cewar su za su ceto Najeriya daga halin da jamiyyar ta jefa su a ciki. NAJERIYA A YAU: Ɓoyayyun Ƙalubalen Da Sabuwar Haɗakar ADC Za Ta Iya Fuskanta DAGA LARABA: Cutukan Da Sinadaran Yin Burodi Ke Haifarwa Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan...
Daga safiyar yau juma’a, Falasdinawa 17 sun yi shahada sanadiyyar hare-haren da HKI ta kai wa Falasdinawa ‘yan hijira a yankin Mawasi dake Kudancin Khan-Yunus. Tun da safiyar yau ne dai jiragen yakin HKI su ka kai hare-hare a gabashin birnin Gaza, haka nan kuma ‘yan sahayoniyar sun yi amfani da jirgin sama maras matuki nau’in Code Copter ” wajen bude wuta akan wannan yankin. A cikin unguwar Shuja’iyya kuwa, sojojin sahayoniyar sun tarwatsa da rusa gidajen Falasdinawa. A sansanin ‘yan hijira na Jabaliya dake arewacin Gaza ma dai jiragen yakin HKI sun kai jerin hare-hare masu tsanani da hakan ya yi sanadiyyar shahadar da dama daga cikinsu. A daren jiya Alhamis ‘yan sahayoniyar sun yi kisan kiyashi akan Falasdinawan...
Dele Momodu, sanannen ɗan jarida kuma jigo a jam’iyyar PDP, ya bayyana cewa yawancin magoya bayan jam’iyyar sun fara ficewa daga cikinta, suna barin tsarin jam’iyyar a hannun ministan babban birnin tarayya. Dele ya bayyana hakan ne yayin wani shiri a Channels TV, inda ya nuna cikakken goyon bayansa ga sabon ƙawancen jam’iyyun adawa da suka rungumi jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) domin fuskantar zaɓen 2027. Momodu ya ce, duk da Wike yana PDP, kasancewarsa a gwamnatin APC na nuna rashin amanna kuma ya janyo rikici cikin jam’iyyar. A cewarsa, “mutane suna barin gawar PDP ga Wike da ƙawayensa kawai.” Ya zargi APC da shirya makirci na tura mutanenta cikin jam’iyyun adawa don rage musu ƙarfi a 2027, yana mai...
A ci gaba da sauya sheƙar da ’yan Majalisar Wakilai na Tarayya ke yi a ranar Alhamis wasu mambobi bakwai daga Jihar Akwa Ibom sun sanar da sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar APC mai mulki. Cikin waɗanda suka sauya sheƙa sun haɗa da shida daga Jam’iyyar PDP da kuma ɗaya daga Jam’iyyar YPP. ’Yan Najeriya sun fara begen Buhari saboda azabar Tinubu – Amaechi Gwamnatin Yobe ta rufe kasuwanni 3 saboda matsalar tsaro Shugaban Majalisar Wakilan Tarayya Tajudeen Abbas ne ya karanta wasiƙunsu na sauya sheƙa a zauren Majalisar a ranar Alhamis yayin zaman majalisar. ’Yan majalisar dai sun yi nuni da ƙara samun rarrabuwar kawuna da rigingimun cikin gida a cikin Jam’iyyar PDP a matsayin dalilin da ya sa suka...
Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce wahalhalu sun yi yawa a Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, wanda har ya sa mutane suka fara fatan dawowar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari. Yayin da yake magana a birnin Abuja, Amaechi ya ce Najeriya ta taɓarɓare matuƙa, inda ya ce sauyin gwamnati ne kawai zai magance matsaloli. Gwamnatin Yobe ta rufe kasuwanni 3 saboda matsalar tsaro Ɗan wasan Liverpool, Diogo Jota, ya mutu a hatsarin mota “Farashi kayayyaki ya tashi sosai. Mutane ba za su iya siyan abinci ba. Babu kuɗi. Komai ya lalace,” in ji shi. Ya ƙara da cewa rayuwa ta yi tsanani har mutane sun fara tunawa da zamanin Buhari da muradin dawowarsa kan mulki. “Yanzu mutane na so Buhari ya...
Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce wahalhalu sun yi yawa a Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, wanda har ya sa mutane suka fara fatan dawowar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari. Yayin da yake magana a birnin Abuja, Amaechi ya ce Najeriya ta taɓarɓare matuƙa, inda ya ce sauyin gwamnati ne kawai zai magance matsaloli. Gwamnatin Yobe ta rufe kasuwanni 3 saboda matsalar tsaro Ɗan wasan Liverpool, Diogo Jota, ya mutu a hatsarin mota “Farashi kayayyaki ya tashi sosai. Mutane ba za su iya siyan abinci ba. Babu kuɗi. Komai ya lalace,” in ji shi. Ya ƙara da cewa rayuwa ta yi tsanani har mutane sun fara tunawa da zamanin Buhari da muradin dawowarsa kan mulki. “Yanzu mutane na so Buhari ya...
Babbar jam’iyyar hamayya a Nijeriya, PDP ta ce za ta ɗauki tsattsauran mataki kan mambobinta da ke ƙoƙarin shiga sabuwar haɗaka da jam’iyyar ADC. Yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan taron kwamitin amintattun jam’iyyar, shugaban jam’iyyar na ƙasa Ambasada Iliya Damagum ya ce jam’iyyar tana gargaɗi ’yan’yanta da ke shirin shiga sabuwar haɗakar ADC. Damagum ya ce ƙoƙarin da haɗakar ke shirin yi ba zai yi tasiri ba, yana mai cewa da dama daga cikin mambobin haɗakar za su koma jam’iyyunsu. “Yana da kyau su sani cewa babu inda ya kamata a haɗu domin tunkarar gwamnatin APC da ya wuce jam’iyyar PDP, amma in suna ganin ba haka ba, to su je su gwada su gani, amma dai...
Jagoran sabuwar jam’iyyar ADC, Ralph Nwosu, ya bayyana cewa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, zai jagorance su wajen karɓar mulki daga hannun Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027. Jam’iyyar haɗakar, wacce ta ƙunshi fitattun ’yan siyasa, ta naɗa David Mark a matsayin Shugaba, tare da tsohon Gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola, a matsayin Sakatare. ’Yan sanda sun kama wani mutum da jabun kuɗi a Gombe Ambaliya: Zulum ya bada umarnin tallafa wa mutanen Damboa da Askira-Uba A wajen babban taron da ta gudanar a cibiyar Yar’Adua da ke Abuja, Nwosu ya ce: “Mun sauka daga muƙamanmu domin mu bai wa David Mark dama ya jagoranci wannan tafiya zuwa fadar shugaban ƙasa.” Ya yaba wa Aregbesola, wanda ya taɓa kasancewa...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
‘Yan tawagar jam’iyyar UDA ta kasar Kenya da suka kawo ziyara kasar Sin sun kwatanta jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin da bishiyar kuka, suna cewa, “Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin tamkar bishiyar kuka ce, wadda ke da ingantattun saiwoyi da ma babban karfi na warkar da kanta, tana ta fid da furanni da ‘ya’ya ba tare da tsayawa ba” “bishiyoyin kuka suna da tsawon rai na sama da shekaru dubu”. Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin tana cikin karfinta, kuma za ta ci gaba da kokartawa domin bauta wa jama’a, tare da dogara da jama’a don cimma karin nasarori. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
Wasu manyan ƴan siyasa daga jam’iyyun adawa sun hallara a Cibiyar Yar’Adua da ke Abuja a yau Laraba da rana don taron ƙaddamar da sabbin shugabannin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), a wani mataki na shiryawa zaɓen shekarar 2027. Taron ya samu halartar manyan fitattun ’yan takara da tsofaffin gwamnoni daga sassa daban-daban na ƙasa. Cikin waɗanda suka halarta akwai Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP; Peter Obi na LP; tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai; da tsohon Ministan Sufuri kuma gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi. Haka kuma, Solomon Dalung, Dino Melaye, Dele Momodu, Sanata Gabriel Suswam, da Sanata Ireti Kingibe sun samu halarta. Emeka Ihedioha da Air Marshal Sadique Abubakar (rtd.) suma sun bayyana. David Mark Da Aregbesola Sun Zama Shugaba...
Majalisar Dokokin Jihar Filato ta zaɓi Nanloong Daniel a matsayin sabon Kakakin Majalisar, bayan da Gabriel Dewan ya yi murabus. Zaɓen sabon kakakin ya gudana ne a wani zaman gaggawa da majalisar ta gudanar ranar Laraba. David Mark ya fice daga PDP, ya shiga haɗaka don ƙalubalantar Tinubu Najeriya ta kammala dawo da alhazan da suka yi Aikin Hajjin bana Zaman ya gudana ne a harabar tsohon gidan gwamnatin jihar. Hon. Nanloong Daniel, wanda ke wakiltar mazaɓar Mikang wanda kuma tsohon jagoran masu rinjaye ne a majalisar ta tara, ya samu amincewar dukkanin ’yan majalisar 24 don jagorantar su. Daniel shi ɗan jam’iyyar APC ne. Zaɓen nasa ya biyo bayan wani zaman sirri da aka yi tsakanin Gwamna Caleb Mutfwang,...
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, ya fice daga jam’iyyar adawa ta PDP. A cikin wata wasiƙar da Aminiya ta gani, David Mark ya bayyana cewa ya fice daga jam’iyyar ne saboda rikice-rikicen shugabanci da aka gaza magancewa. Najeriya ta kammala dawo da alhazan da suka yi Aikin Hajjin bana Kotu ta yanke hukuncin rataya ga dalibin da ya kashe malaminsa a Jos Ya ce waɗannan matsalolin sun kawo wa jam’iyyar naƙaso kuma sun jawo mata abun kunya a idon jama’a. A daren ranar Talata, an naɗa David Mark da tsohon Gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola, a matsayin shugabannin riƙon kwarya (Shugaba da Sakatare) na wata sabuwar jam’iyyar ADC. Wannan jam’iyya wadda ta haɗa manyan ’yan adawa na da niyyar...
Ya ce kamar yadda mutane suka karanta a jarida, shi ma ya karanta, amma babu gaskiya cikin batun. Ya ce a yanzu, kowa ya san yana cikin PDP kuma yana da matsayi a jam’iyyar, bai bar ta ba kuma da yardar Allah zai ci gaba da zama a cikinta. Ya ce dalilin da ya sa wasu ke son ya koma APC shi ne domin jam’iyyar APC a Filato ba ta da shugabanni nagari, shi ya sa suke kallon shugabannin PDP da fatan su shiga jam’iyyar domin kawo gyara. Ya ƙara da cewa wasu daga cikin mambobin APC na ƙasa suna sha’awar abubuwan da PDP ta yi a Filato, kuma suna ganin irin waɗannan ayyuka na buƙatar shugabanni masu nagarta. Amma...
Aregbesola, wanda shi ne tsohon Gwamnan Jihar Osun, ya ƙara da cewa jam’iyyar siyasa bai kamata ta zama hanyar neman mulki kawai ba ko wata dama ga wasu tsiraru ba. Ya ce jam’iyya ta gaskiya ita ce wadda ke da tsari da manufa, kuma wadda ke aiki don jama’ar da ta ke wakilta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugabannin jam’iyyar APC a matakin gunduma na Gayam, cikin ƙaramar hukumar Lafia, sun dakatar da shugaban jam’iyyar a matakin jiha, Hon. Aliyu Bello. Sun zarge shi da aikata abubuwan da suka saɓa da kundin tsarin mulki na jam’iyyar, musamman sashe na 21 (D)(i–iii), wanda ya haɗa da cin amanar jam’iyya da goyon bayan ɗan takarar wata jam’iyya daban. Shugaban gundumar, Ibrahim Ilyasu, ya bayyana cewa matakin dakatarwar ya fara aiki nan take, kuma Hon. Bello ba zai iya wakiltar kansa ko amfani da matsayin sa a matsayinsa na mamba na APC daga Gayam ba, har sai an warware batutuwan da aka gabatar. Sun kuma zarge shi da jawo wa jam’iyyar tozarci da keta mutuncinta a idon jama’a. Haɗakar Jam’iyyun Adawa...

Fahimtar Sabon Tunani: Yadda Sin Ta Samu Bunkasa A Tarihi Ta Hanyar Juyin Juya Halin Da Take Yi Wa Kanta
Yau Talata ita ce ranar cika shekaru 104 da kafuwar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS. A cikin lokacin sanyi na shekarar 2012, jama’ar kasar Sin sun wayi gari da ganin motocin gwamnati kalilan ne ke kai-komo a kan tituna, kuma an daina amfani da kudin gwamnati wajen shirya liyafar cin abinci a gidajen cin abinci masu tsada, kana hatta kyautar da ake bayarwa ta kek, watau “Mooncake” lokacin bikin tsakiyar kaka an rage girmanta daga dan karamin akwati zuwa wani karamin kunshi. Wannan shi ne sauyin da aka samu bayan aiwatar da shahararrun “Ka’idoji Takwas” na jam’iyyar JKS. Matakin da aka dauka na dokoki ya zama tamkar wani magani mai karfi wanda ke warkad da “cututtukan” da suka...

Xi Jinping Ya Jaddada Niyyar Gina Babbar Kasuwar Kasa Ta Bai Daya, Tare Da Raya Tattalin Arziki Na Teku Mai Inganci
Yau Talata da safe, shugaban kasar Sin, kana babban darektan kwamitin harkokin kudi da tattalin arziki na kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, Xi Jinping ya jagoranci taro karo na 6 na kwamitin harkokin kudi da tattalin arziki na kwamitin tsakiyar JKS, inda aka yi nazari kan yadda za a gina babbar kasuwar kasa ta bai daya, tare da raya tattalin arziki na teku mai inganci da dai sauransu. A yayin taron, shugaba Xi ya jaddada cewa, kafuwar babbar kasuwa ta bai daya a ciki kasar Sin ta dace da bukatunmu na bullo da sabon tsarin neman ci gaba da samun bunkasa mai inganci, don haka ya kamata a aiwatar da aikin bisa manufar kwamitin tsakiya, da daidaita ayyuka...
A bisa jagorancin Alhaji Mustapha Junaid, iyalan mamacin, da suka haɗa da matan sa da ‘ya’ya da jikokin sa, sun tarbi tawagar, kuma sun yi masu godiya. Minista Badaru ya miƙa saƙon ta’aziyya daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana cewa, “Rasuwar Baba Aminu ta taɓa Shugaba Tinubu matuƙa. Yana addu’ar Allah ya yi masa sakayya da gidan Aljannar Firdausi, kuma yana ba dukkan iyalan sa haƙurin su yi jimirin jure wannan babban rashi.” Jakaden Nijeriya a Saudi Arebiya, Ambasada Ibrahim Modibbo, da Babban Jagoran Aikin Jakadanci, Ambasada Mu’azam Ibrahim Nayaya, da Jami’in Kula da Tsaro a Ofishin Jakadanci, Manjo Janar Adamu Hassan, duk suna cikin tawagar. Malaman da aka je da su kuma duk sun yi addu’o’i ga marigayi...
Adadin mambobin JKS na ci gaba da karuwa, inda rassanta ke ci gaba da ingantuwa. Baya ga haka, sassanta a matakin farko na kara karfi. Wannan na kunshe ne cikin rahoton kididdiga da sashen shirye-shirye na kwamitin kolin jam’iyyar ya fitar yau Litinin, gabanin bikin cika shekaru 104 da kafuwar jam’iyyar. Zuwa karshen 2024, jam’iyyar na da mambobi sama da miliyan 100.27, karuwar kusan miliyan 1.09 kan na shekarar 2023. Zuwa karshen 2024 kuma, JKS na da sassa miliyan 5.25 a matakin farko, karuwar 74,000 idan aka kwatanta da shekarar 2023. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
Jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya ta tsayar da 24 ga watan Yulin bana a matsayin ranar da za ta gudanar da taronta na Majalisar Zartarwa. Mataimakin Sakataren jam’iyyar, Barista Fetus Fuanter ne ya tabbatar wa manema labarai hakan a yau Litinin a Abuja. Magidanci ya kashe matarsa da adda a Yobe Jami’an tsaro sun hana taron kwamitin amintattun PDP Fuanter ya ce kusoshin jam’iyyar za su gana kafin gudanar da taron Majalisar Zartarwar. Taron da za a gudanar shi ne na biyu ta fuskar girma a cikin jerin tarukan da jam’iyya ke zaman yanke shawara da daukar wasu muhimman matakai bayan babban taronta na kasa. Wannan dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba cece-kuce tun bayan murabus...
Jami’an tsaro sun hana mambobin Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar Adwa ta PDP gudanar da taron da suka tsara gudanarwa. A safiyar Litinin din nan ne jami’ai da yawa ne suka kutsa cikin zauren da aka tsara gudanar da taron inda suka bukaci wadanda suka hallara da su watse. Jami’an tsaro da aka jibge a hedikwatar babbar jam’iyyar adawar sun hana mambobin kwamitin amintattu gudanar da taronsu a hedikwatar jam’iyyar. Har zuwa lokacin hada da wannan rahoto, wasu daga cikin ’yan kwamitin amintattun na PDP suna tattaunawa a kan halin da ake ciki. Mun samu rahotannin cewa jami’an sun umurci mambohin su bar ofishin jam’iyar domin ganin ba a gudanar da wani taro a ofishin jam’iyar ba.
Sabon Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Ali Bukar Dalori, ya shiga ofis, inda a halin yanzu yake jagorantar taron Kwamitin Gudanarwa na jam’iyyar.
Magoya bayan Kwankwaso, wadanda aka fi sani da Kwankwasiyya, sun yi ikirarin cewa Ganduje ya bai wa mutanen Kano kunya, shi ya sa ya yi murabus. Shugaban jam’iyyar NNPP na Kano, Hashimu Dungurawa, wanda ya yi magana a madadin magoya bayan Kwankwaso, ya bayyana murabus din Ganduje a matsayin kwaso abin kunya ga Kano. Ya bayyana cewa, an sami Ganduje ne da son yin almundahana, musamman a lokacin zaben shugabannin jam’iyyar da aka kammala kwanan nan. Dungurawa ya yi wannan ikirarin ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake amsa tambayoyi daga LEADERSHIP game da matakin da jam’iyyar za ta dauka na gaba bayan faruwar wannan lamari. Ya ce, kafafen yada labarai sun...
Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Rwanda sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya bayan shafe shekaru 30 suna rikici Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Rwanda sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, shekaru talatin bayan rikicin da ya barke a shekara ta 1994 da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane daga bangarorin biyu. An rattaba hannu kan takardar ne a gaban sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ministar harkokin wajen Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Teresa Kayumba, da na Rwanda Olivier Nduhungirehe. Yarjejeniyar da Amurka da Qatar suka wakilci shiga Tsakani ta hada da tanade-tanade kan mutunta yankunan kasa, haramta ayyukan soji, kwance damarar makamai da hadewar kungiyoyin da ba na gwamnati ba, da kuma samar da wani tsari na hadin gwiwa don daidaita...
Wannan ne ma dalilin da yasa wasu ke ganin hadakar za ta iya yin karfi kwarai da gaske, kasancewar ta samu wakilci a sassa daban-daban na wannan kasa. Dalili kuwa shi ne, ‘yansiyasa ne da a baya suka samu damar rike manya-mnyan mukamai, sannan kuma har zuwa yanzu yana da tasiri a fagen siyasar kasar yadda ya kamata. Manya-manyan jiga-jigan da ake gani a cikin wannan sabuwar tafiya ta hadakar jam’iyyar sun hada da: Jagoran adawa a kasar, wanda a baya ya sha yin takarar shugabancin kasa, sannan kuma ko a shekarar 2023 shi ne ya zo na biyu bayan da ya samu kuri’a kusan miliyan bakwai. Alhaji Atiku Abubakar, wanda a yanzu dan jam’iyyar PDP ne; ya kasance guda...
Jam’iyyar PDP a Jihar Kebbi, ta bayyana shirinta na haɗa kai da sauran jam’iyyu da ƙungiyoyi domin karɓe mulki daga hannun APC a zaɓen 2027, a matakin jiha da kuma tarayya. An bayyana wannan matsaya ne a garin Birnin Kebbi ranar Asabar, yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, inda aka jaddada buƙatar yin sulhu da warware rikicin cikin gida da ke damun PDP. Mutanen Sakkwato na neman ɗaukin gwamnati game da Bello Turji An samu amincewar yi wa Dantata jana’iza a Madina Jigo a jam’iyyar, Ibrahim Mera, ya ce sun amince su haɗa kai da kowa domin a samu nasarar kawar da APC a jihar. “Za mu yi aiki tuƙuru don ganin haɗakar ta yi tasiri. Mun...
Jagoran wannan sabuwar tafiya kuma tsohon sakataren gwamnatin Jihar Katsina, Mustapha Inuwa ne ya bayyana haka a lokacin da tsaffin ‘yan takarar suka je ofishinsa domin jadadda goyon bayansu kan sabuwar tafiya. Shi ma da yake magana a madadin sauran ‘yan takarar majalisar dokokin jiha a zaben 2023, Hon. Jamilu Yahaya ya bayyana cewa sun fice daga jam’iyyar PDP ne saboda yadda aka nisantar da su daga al’umma wanda su ne ke yin zabe. A nashi bangaren, shugaban ‘yan takarar shugabancin kananan hukumomi, Hon. Yasir Ibrahim ya ce sun shiga wannan hadaka ne saboda irin yaudarar shugabanci da aka yi masu a tsohuwar jam’iyyar PDP da ke fama da rikice-rikice. Da yake nasa tsokaci, shugaban tsaffin ‘yan takarar kansiloli na...
Matsalolin Da Muke Fuskanta: Bayan shekar 22 da kubutar da Nijeriya daga mulkin soja, dimokuradiyya na ci gaba da fama da rauni mai tsanani. Alamun cutar sun bayyana ne a cinikin baragurbin wakilai (delegates), amfani da kudin kasa da aka wawure ta hanyar haram wajen gudanar da yakin neman zabe, makudan kudin da ake ware wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), karancin yawan masu kada kuri’a, sayen kuri’u a bainar jama’a, tashin hankali yayin zabe, da kuma yaduwar fargaba, musamman a tsakanin matasa, cin amana na ’yan siyasa, canja sheka da zababbu ke yi, da dai sauran makamantansu. Asalin matsalar ita ce, rashin shiga cikin gudanar da gwamnati a siyasance (edclusion) na masu gaskiya da rikon amana, matasa, mata, masu...
Ganduje, wanda ya kasance Gwamnan Jihar Kano daga 2015 zuwa 2023, ya zama shugaban APC a watan Agustan 2023 bayan murabus ɗin tsohon shugaban jam’iyyar, Sanata Abdullahi Adamu daga yankin Arewa ta Tsakiya. Tun daga wannan lokacin ne wasu daga cikin mambobin jam’iyyar suka fara sukar jagorancinsa, suna ganin naɗa shi ya karya tsarin raba muƙamai na cikin gida da jam’iyyar ke bi. Dama tuni wasu manyan dattawan jam’iyyar da shugabannin yankuna daban-daban suka bayyana rashin jin daɗinsu, inda suka dk ga kira ga jam’iyyar da ta gyara wannan tsari. Majiyoyi sun ce saukar Ganduje za ta samar da haɗin kai a cikin jam’iyyar, da kuma gyara matsalolin rabon muƙamai don sake farfaɗo da APC kafin babban zaɓen 2027. A...
Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi murabus daga shugabancin jam’iyyar. Murabus ɗin nasa ya fara aiki nan take. Sojoji sun yi wa ’yan bindiga luguden wuta a Neja ’Yan sanda sun kama ɓarayi 5, sun ƙwato kuɗi da makamai a Gombe Ganduje, wanda tsohon Gwamnan Jihar Kano ne, ya bayyana rashin lafiya a matsayin dalilin da ya da ya ajiye muƙaminsa. Ganduje ya zama Shugaban APC a watan Agustan 2023, a lokacin da jam’iyyar ke fama da rikicin cikin gida. Lokacin da ya kwashe a matsayin shugaban jam’iyyar na cike da cece-kuce da suka. Dalilin murabus ɗinsa Ko da yake Ganduje ya ce rashin lafiya ce ta sa ya yi murabus, wasu majiyoyi sun bayyana cewa...
Rigimar shugabanci a jam’iyyar adawa ta PDP, ta lafa yayin da Sanata Samuel Anyanwu ya samu umarnin komawa bakin aikinsa a matsayin sakataren jam’iyyar na ƙasa. Muƙaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Umar Damagum, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Laraba a hedikwatar jam’iyyar da ke Wadata Plaza, Abuja. Gwamnan Sakkwato Ya Kaddamar Da Aikin Gina Gidaje 500 Don Rage Matsalar Rashin Gida KAROTA Ta Kama Matasa 5 Kan Ɗaukar Bidiyo A Kan Hanya A Kano Damagum ya kuma bayyana cewa an soke taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) karo na 100 da aka shirya yi, saboda wasu matsaloli. Maimakon haka, jam’iyyar za ta gudanar da wani taro a ranar 30 ga...
Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta mayar da na hannun damar Ministan Abuja Nyesom Wike, wato Samuel Anyanwu kan kujerarsa ta Sakataren jam’iyyar na ƙasa. Mai riƙon muƙamin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Iliya Damagum ne ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Laraba. Isra’ila da Iran sun ci gaba da musayar wuta duk da sanarwar tsagaita wuta Bello Turji ya kashe ’yan sa-kai sama da 40 a Zamfara Yayin taron dai, shugaban na tare da Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar. Damagum ya ce yanke shawarar dawo da Anyanwu cikin kwamitin zartarwar jam’iyyar na ƙasa shawara ce mai...
Ya nemi ‘yan jarida da su riƙa amfani da kafafen su wajen haska labarai da ke nuna sauye-sauyen da aka samu a hukumomi, yadda jama’a ke shiga cikin harkokin gwamnati, cigaban ababen more rayuwa da bunƙasar tattalin arziki, a matsayin wani ɓangare na rawar da kafafen ke takawa wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya. “Yayin da muke bikin shekaru 26 na ci gaba da mulkin dimokiraɗiyya a Nijeriya, dole ne kafafen yaɗa labarai su riƙa yaɗa labaran da ke bayyana nasarorin da dimokiraɗiyyar ƙasar nan ta samu, irin su gyaran hukumomi, gina ababen more rayuwa, shiga jama’a cikin harkokin gwamnati, da kuma cigaban tattalin arziki,” inji shi. Idris ya ƙara da cewa yayin da kafafen yaɗa labarai suke haska waɗannan nasarori ta hanya...
A cikin takardar, ƙungiyar ta bayyana cewa ta yanke shawarar kafa sabuwar jam’iyya maimakon haɗaka da wasu. Sun bayyana cewa sun zaɓi suna All Democratic Alliance (ADA) kuma taken jam’iyyar shi ne “Justice for All” wato “Adalci ga Kowa.” Sun kuma haɗa da adireshin babban ofishin jam’iyyar a cikin takardar. Sun gabatar da wasu muhimman takardu da suka haɗa da tambarin jam’iyya, tsarin kundin mulki, tutar jam’iyyar, da manufofinta. Tambarin jam’iyyar ya ƙunshi kayan hatsi irin su masara da launuka masu ma’ana. Kundin tsarin mulki kuma ya ƙunshi manufofi, tsari da dokokin jam’iyyar, bisa ga tsarin dokokin Najeriya da ƙa’idar dimokuraɗiyya ta duniya. Takardar ta ƙare da girmamawa, inda ta ke roƙon INEC da ta ɗauki mataki na gaba wajen...
Jagororin jam’iyyun adawa na Najeriya a ƙarƙashin ƙungiyar hadaƙa ta Nigeria National Coalition Group (NNCG) na neman yin rajistar All Democratic Alliance (ADA) domin ta zama sabuwar jam’iyyar da za su yi amfani da ita don tunkarar Jam’iyyar APC a zaɓen 2027. NNCG ta riga ta miƙa takardar neman rajistar jam’iyya ga Hukumar Zaɓe mai zaman kanta INEC a hukumance don babban zaɓe na gaba. Jami’an tsaro sun ƙwato makamai da kama mutane 398 a Kaduna Wani ya kashe mahaifiyarsa mai shekara 71 a Akwa Ibom Takardar wadda suka aika zuwa ga shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu a ranar 19 ga watan Yuni, wanda shugaban ADA na ƙasa Cif Akin Ricketts da sakataren riƙo Abdullahi Musa Elayo ne suka...
Wasu na ganin jita-jitar ta samo asali ne bayan wani abokin aikinsa na baya, Sani Sidi, ya koma jam’iyyar APC tare da magoya bayansa a Kaduna. Amma Sambo ya ce hakan bai shafe shi ba. Hakazalika, an shirya Sambo zai halarci bikin ƙaddamar da asibiti mai gadaje 300 da ke Kaduna a ranar Alhamis, 19 ga watan Yuni, 2025. Ya halarci bikin kuma hakan ba yana nufin ya goyi bayan wata jam’iyya ba ne. Ƙungiyarsa ta nanata cewa Sambo yana nan daram a cikin jam’iyyar PDP, kuma labarin sauya sheƙar nasa ƙarya ce da aka ƙirƙira domin tayar da hankali da ƙoƙarin cimma wasu muradu na siyasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce matsalar da ke addabar jam’iyyar PDP ba ta tsaya kan Atiku Abubakar kaɗai ba, face tana da nasaba da girman kai tsakanin shugabannin jam’iyyar. Da yake magana da manema labarai a ranar Laraba, Gwamna Lawal ya ce: “Kowa yana da nasa matsalar; ba kan Atiku Abubakar kawai ba ne; ta wuce hakan.” An ɗaure mutum 7 kan yi wa ɗan sanda rauni a Kano ’Yan bindiga sun kashe manoma 24 a Katsina “Matsala ce daga cikin gida… Na ga matsalar tana da alaƙa da girman kai, ba a bar kowa a baya ba.” Da aka tambaye shi ko yana daga cikin masu haddasa matsala a cikin jam’iyyar, ya amsa cewa yana ciki. Gwamna...

Motoci Masu Aiki Da Lantarki Kirar Sin Sun Samar Da Sabuwar Hanyar Sufuri Ga Al’Ummun Kasashen Shiyyar Tsakiyar Asiya
A watan Afrilun bana, wata farar mota kirar bas mai tsawo mita 12, ta yi tafiya a kan titunan Ashgabat, hedkwatar kasar Turkmenistan. Bas din da kamfanin Yutong na kasar Sin ya kera ta dace da ma’aunin kiyaye muhalli da kasar ta tanada, kuma tana dauke da na’urar ba da jagorancin sufuri mai amfani da tauraron dan Adam, da na’urar biyan kudi ta yanar gizo, matakin da ya bullo da sabuwar hanyar zirga-zirga ga jama’ar wurin. A wannan shekara, Sin za ta samar da irin wannan bas har 700 ga Ashgabat, matakin da zai biya bukatun zirga-zirgar jama’ar kasar da yawansu ya zarce miliyan 1. Tun da aka bude taron koli na Sin da kasashen shiyyar tsakiyar Asiya karon farko...