Aminiya:
2025-09-17@21:31:45 GMT

Daruruwan magoya bayan NNPP sun tarbi Kwankwaso a Kalaba

Published: 11th, September 2025 GMT

Daruruwan magoya bayan jam’iyyar NNPP ne suka taru a birnin Kalaba na Jihar Kuros Riba, domin tarbar jagoran jam’iyyar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, a wata ziyarar sada zumunta da ya kai a jihar.

Kwankwaso ya fara irin wannan ziyarar ce daga yankin Kudu maso Gabas, kafin ya wuce zuwa Kudu maso Kudu, inda ya sauka a Kalaba domin ganawa da mambobin jam’iyyar.

Kotu ta yanke wa jagoran Ansaru hukuncin ɗaurin shekaru 15 Trump ya tiso ƙeyar rukunin farko na ’yan Najeriya daga Amurka

A yayin da yake jawabi ga taron magoya bayan jam’iyyar a Kalaba, tsohon Gwamnan Kano, ya bayyana cewa wannan ziyara ba ta da alaƙa da yaƙin neman zaɓe.

Sai dai ya ce uzuri ne ya kai shi yankin Kudu maso Gabas, kuma ya yanke shawarar tsayawa a Kalaba domin gaisawa da magoya bayan jam’iyya.

“Ziyarar da na kawo muku ba yaƙin neman zabe ba ne, domin lokacin kamfe bai yi ba. Na zo ne saboda wani uzuri da ya kawo ni wannan yanki, amma na ce sai na tsaya na ganku, mu gaisa, mu sada zumunci.”

Ya ja hankalin mambobin jam’iyyar da su zauna lafiya da jama’ar yankin da suke zaune da su, yana mai cewa: “A rayuwa dole mu riƙa zama lafiya da mutanen yankin da muke ciki.”

Kwankwaso ya kuma shawarci mambobin jam’iyyar da su tabbatar sun yi rajista ko sabunta katin zabe, domin kasancewa cikin shiri idan lokacin zabe ya yi.

A nasa jawabin, shugaban matasan jam’iyyar NNPP a Jihar Kuros Riba, Alhaji Muhammad Zanjuma, ya bayyana cewa jam’iyyar na da ɗimbin magoya baya a jihar.

“Wasu ma ba su san da zuwan jagoran ba, amma da ka ga yadda jama’a za su cika wurin nan, za ka san jam’iyyar na da ƙarfi. Idan aka kada gangar siyasa yau, lallai NNPP za ta taka muhimmiyar rawa,” in ji shi.

Shi ma a nasa bangare, jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar a jihar, kuma wakilin ‘yan Arewa, Umar Darki  wanda aka fi sani da Umar Police, ya ce wannan ziyara da Kwankwaso ya kawo ta ƙara jaddada cewa bai manta da ’yan Arewa mazauna Kudancin Najeriya ba.

“Muna godiya da irin kulawar da yake yi mana, musamman idan wani abu ya faru da ’yan Arewa a Kudu, yana shiga cikin lamarin. Allah Ya saka masa da alheri,” in ji Umar Police.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Rabiu Musu Kwankwaso magoya bayan

এছাড়াও পড়ুন:

Najeriya Na Asarar Dala Biliyan 10 Bayan Girbi Duk Shekara- Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na rasa sama da Dala Biliyan 10 duk shekara sakamakon asarar amfanin gona bayan girbi.

Ministan Noma  Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin Hanyar Inganta Noma da Kayayyakin Mire Rayuwa a Yankunan Karkara G.R.A.I.N a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta  Jihar Jigawa.

 

Ya ce asarar na faruwa ne saboda rashin ingantattun wuraren ajiya, karancin ababen more rayuwa, sauyin yanayi da kuma ambaliya.

Kyari ya bayyana cewa noma na bada gudunmawar kashi 24 bisa 100 na Jimillar Darajar Kayayyaki da Ayyuka da Kasa ta Samar a Cikin Shekara GDP, inda ƙananan manoma ke samar da sama da kashi 70 bisa 100 na abincin da ake ci a ƙasa.

Ya jaddada cewa gwamnati za ta tallafa musu da kayan noma na  zamani da wuraran kasuwanci domin inganta tattalin arziki.

A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi na Jigawa ya yaba da samun Cibiyar Cigaban Karakara ta Pulse ta farko a Jigawa, yana mai cewa za ta kawo sauyi a harkar noma da rayuwar jama’ar karkara.

Haka zalika, shi ma Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya ce haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu zai taimaka wajen ci gaban tattalin arziki.

Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu, Alhaji Builder Muhammad Uba, ya jaddada goyon bayansa ga shirin Renewed Hope Agenda na Shugaba Tinubu tare da yabawa gwamnatin Namadi kan sauya fasalin noma a jihar.

 

Usman Muhammad Zaria 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
  • An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
  • Gwamnatin Kano Ta Inganta Cibiyoyin Horas Da Sana’o’i Domin Dakile Aikata Laifuka Tsakanin Matasa
  • Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima
  • Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC Na Nasarawa, Aliyu Barde, Ya Rasu
  • Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
  • Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani
  • Najeriya Na Asarar Dala Biliyan 10 Bayan Girbi Duk Shekara- Gwamnatin Tarayya
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Malamin Krista Na Ɗarikar Katolika A Kogi
  • An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar