Jonathan ya tattauna da Peter Obi kan tsayawa takara a 2027
Published: 12th, September 2025 GMT
Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, sun gana ranar Alhamis a Abuja, a yayin da ake ci gaba da hasashen kafa kwakkwaran kawancen adawa gabanin zaben shugaban kasa na 2027.
Manyan ’yan siyasar na Kudancin Najeriya dai sun mamaye tattaunawa a bakunan jama’a a baya-bayan nan a matsayin wadanda za su iya kalubalantar Shugaba Bola Tinubu na jam’iyyar APC.
Kodayake har yanzu Peter Obi yana cikin LP, amma yana mu’amala da jam’iyyar kawancen adawa ta ADC ke jagoranta.
NAJERIYA A YAU: Masu Nau’in Jinin AS Sun Fi Masu Nau’in AA Lafiya 2027: Malamai sun gudanar da addu’o’in nasarar Tinubu-Barau a KanoJonathan kuwa, wanda har yanzu dan jam’iyyar PDP ne a hukumance, bai cika shiga al’amuran jam’iyyar ba tun bayan faduwarsa neman tazarce a 2015.
Kodayake ba a bayyana ainihin abin da taron na ranar Alhamis ya tattauna ba, sai dai Obi, wanda tsohon gwamnan jihar Anambra ne, ya wallafa hotunan ganawar a shafinsa na X, inda ya bayyana cewa sun tattauna kan al’amuran ci gaban kasa da halin da Najeriya ke ciki.
Ya rubuta cewa: “A yau a Abuja, na gana da yayana, jigo kuma jagora, tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan @GEJonathan. Mun yi muhimmiyar tattaunawa a cikin sirri, inda muka tattauna kan halin da ƙasarmu ke ciki. – PO.”
Majiyoyi da suka san da taron sun shaida wa Aminiya cewa ganawar ci gaba ce kan tattaunawar da suka fara tun da dadewa kan shirye-shiryen tunkarar zaben 2027.
“Wannan shi ne karo na uku ko na hudu da suka gana tun lokacin bukukuwan Ista, amma duk ganawar da suka yi a baya an boye ta. Babban batun shi ne wanda zai janye wa wani a matsayin dan takarar shugaban kasa na kawancen,” in ji wata majiya.
An ce dukkansu sun fahimci cewa suna da tarin magoya baya a yanki ɗaya, kuma idan kowannen su ya tsaya takara shi kadai, zai iya ba wa Tinubu damar samun nasara cikin sauki.
“Ka san yawancin kuri’un da Obi ya samu a 2023 sun fito ne daga Kudu, musamman Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu, da kuma yankin Tsakiyar Najeriya (Middlebelt) wanda shi ma Jonathan ya fi karfi a 2011. Sun gane cewa ba za su iya shiga zabe mai zuwa ba tare da hadin kai ba.”
“Wani batu kuma shi ne jam’iyya. Wasu shugabannin PDP sun roki Jonathan da ya tsaya takara a jam’iyyar su, amma yana da shakku kan rikicin cikin gidan da yake addabar ta. Yana jiran samun tabbaci tukunnan,” in ji majiyar.
A cewar majiyar, bangaren Obi ma ya nuna damuwa kan yadda ake kokarin watsar da su a cikin kawancen da suka taimaka wajen gina shi.
“ADC ba ta iya gamsar da magoya bayan Peter Obi cewa jam’iyyar ba an shirya ta ne don share wa Atiku wajen yin takara ba,” in ji ta.
Batutuwan dai a cewar majiyoyin na cikin abubuwan da tattaunawar ta ranar Alhamis ta tabo, inda wasu makusantan Jonathan suka ce ana dab da cimma matsaya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: a jam iyyar
এছাড়াও পড়ুন:
Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar
“Sauran motocin da ke cikin ayarin, ciki har da wacce ke ɗauke da shugaban majalisar, da ƙyar suka iya tsayawa wanda tsakaninsu mitoci kaɗan ne daga wurin da haɗarin ya afku,” in ji wani ganau.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa, an garzaya da jami’an ‘yansandan da suka samu raunuka zuwa babban asibitin Gumel a sume amma daga baya sun farfaɗo.
Da yake magana kan lamarin, mataimakin shugaban majalisar, Aqeel Akilu, ya yi godiya ga Ubangiji cewa, ba a rasa rayuka ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp