2025-05-07@00:10:03 GMT
إجمالي نتائج البحث: 317
«tawagar wanzar da zaman lafiya»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, jami’an hukumar tsaron farin kaya daga jamhuriyar Nijar ne suka biyo wanda ake zargin ɗan bindigar ne a kan babbar hanyar Zurmi/Kauran Namoda a jihar Zamfara. Da yake duba makaman da aka kama, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin sojojin da gwamnatin jihar Zamfara wajen yaƙi da ‘yan bindiga. “Dole ne in yaba wa sojoji, DSS, da ‘yan sanda, musamman ma Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya, bisa nasarar aiwatar da wannan gagarumin kame. “Ina so in jaddada cewa waɗannan nasarori da aka samu tare da wasu na daƙile ‘yan bindiga a jihar, sun samo asali ne daga haɗin kai da goyon bayan da gwamnatin jihar Zamfara ke baiwa ɗaukacin...
Assalamu alaikum masu sauraro, sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da rashin amincewar kasashen masar da Jordan kan maida Falasdnawa cikin kasashensu wanda ni tahir amin zan karanta. A makon da ya gabata ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fadawa kafafen yada labarai a lokacinda yake cikin jirgin fadar shugaban kasa ko ‘Air Force 1, kan cewa yana duba yiyuwar kwasar Falasnidawa a Gaza zuwa kasar Masar sannan sauran falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan da kuma sauran wurare a kasar Falasdinu da aka mamaye zuwa kasar Jordan. Wannan zancen dai ba sabuwa bace, a rikicin gabas ta tsakiya, shuwagabanin Amurka a baya, sun yi wannan maganar amma bata yuba. A halin yanzun babu wata kasa, ya...
Jaridar “Le Monde” ta kasar Faransa ta dauki labarin da yake cewa iyalai masu yawa sun fice daga HKI baki daya zuwa kasashen Portugal,Cyprus, da kuma Girka. Rahoton ya ci gaba da cewa; Dalilan yin hijirar daga HKI zuwa kasashen waje sun kunshi yaki, rashin tsaro da kuma siyasar gwamnatin Benjemine Netanyahu. Har ila yau, jaridar ta kasar Faransa ta ce, dubban ‘yan share wuri zauna ne suke ficewa daga Falasdinu dake karkashin mamaya a wasu lokutan iyalai ne kaco kau suke ficewa. Kwanaki kadan da su ka gabata wasu iyalai da suke kunshe da mutane 20 da su ka hada iyaye, kakanni da jikoki sun yi hijira zuwa Cyprus domin su rayu a can. A cikin kafafen sadarwa na...
Babban kwamishinan hukumar kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya “UNRWA” ya bayyana wa kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya cewa: Aiwatar da dokokin Isra’ila kan hukumar UNRWA zai zama bala’i Babban Kwamishinan Hukumar Kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA), Philippe Lazzarini, ya ce: Aiwatar da cikakken dokar Majalisar Dokokin Haramtacciyar kasar Isra’ila ta Knesset kan hukumar UNRWA zai zama masifa, yana mai gargadin cewa: Rage ayyukan hukumar ta “UNRWA” a wajen tsarin siyasa, kuma a daidai lokacin da kwarin gwiwa daga kasashen duniya ya yi kadan, wanda hakan zai kawo cikas ga yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza. Shafin watsa labaran Falasdinu na “Wafa” ya bayar da rahoton cewa: A jawabin da...

Dan Majalisar Dattijan Amurka Ya Mayar Da Martani Kan Kalaman Trump Na Tilastawa Falasdinawa Gudun Hijira
Dan Majalisar Dattawan Amurka ya bayyana kiran da shugaban Amurka ya yi tilastawa Falasdinawa gudun hijira Falasdinawa da cewa kokari ne na shafe wata al’umma daga kan doron kasa Dan Majalisar Dattawan kasar Amurka Sanata Bernie Sanders a jiya Litinin ya fara mayar da martani ga shugaban Amurka Donald Trump inda ya bayyana kiran da Trump ya yi na korar Falasdinawa daga Zirin Gaza zuwa kasashen da ke makwabtaka da su a matsayin kokarin “Shafe wata al’umma ce daga kan doron kasa kuma laifin yaki ne” inda ya bukaci dukkan Amurkawa da su yi Allah wadai da wannan furuci. A ranar Asabar da ta gabata ce shugaban Amurka Donald Trump ya ba da shawarar mayar da Falasdinawa daga zirin Gaza...
Dan Majalisar Dattawan Amurka ya bayyana kiran da shugaban Amurka ya yi tilastawa Falasdinawa gudun hijira Falasdinawa da cewa kokari ne na shafe wata al’umma daga kan doron kasa Dan Majalisar Dattawan kasar Amurka Sanata Bernie Sanders a jiya Litinin ya fara mayar da martani ga shugaban Amurka Donald Trump inda ya bayyana kiran da Trump ya yi na korar Falasdinawa daga Zirin Gaza zuwa kasashen da ke makwabtaka da su a matsayin kokarin “Shafe wata al’umma ce daga kan doron kasa kuma laifin yaki ne” inda ya bukaci dukkan Amurkawa da su yi Allah wadai da wannan furuci. A ranar Asabar da ta gabata ce shugaban Amurka Donald Trump ya ba da shawarar mayar da Falasdinawa daga zirin Gaza...
Runduna daya ta sojojin Najeriya ta gudanar da bikin jana’izar marigayi Mascot, Sajan Dalet Danfari Akawala, a shalkwatar rundunar dake jihar Kaduna. Wanda dokin sojojin ne. A wata sanarwa da mukaddashin Daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta daya, Laftanar Kanar Musa Yahaya ya fitar, ya ce Kanar Akabike ne ya jagoranci jana’izar, wanda ya wakilci babban hafsan rundunar, Manjo Janar Mayirenso Lander David Saraso. A cewar sa, Marigayi Sajan Dalet Danfari Akawala ya yi hidimar sashen sadaukarwa da aminci, tare da nuna jajircewa da juriya a gidan Soja. “Bikin shi ne hanyar mu na girmamawa ta ƙarshe ga wani wanda ya kawo sauyi da farin ciki da aiki tukuru da kuma daukaka sashen da yayi...
A cim ma burin Gwamna Umar Namadi na ci gaban bil’adama a cikin ajandar mai dauke da abubuwa 12, majalisar zartaswar jihar Jigawa ta kafa wani kwamiti mai mambobi 10 domin samar da hanyoyin da za a bi wajen nemo masu hazaka domin karfafa kirkire-kirkire a tsakanin matasa masu tasowa a jihar. Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu na jiha Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana haka bayan taron majalisar da aka gudanar a Dutse. Ya ce, kwamitin ya kunshi kwamishinonin lafiya, muhalli, kananan hukumomi yayin da kwamishinan ilimi mai zurfi zai zama shugaba. Sauran mambobin sun hada da masu ba da shawara kan fasaha, ICT da tattalin arziki na dijital, ilimi mai zurfi, aikin gona,...
Ofishin yada labarai na gwamnati a zirin Gaza ya sanar da cewa Falasdinawa kusan 300,000 da suka rasa matsugunansu ne suka koma gida a gabar tekun a ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma da kungiyar Hamas. “Wannan ya zo ne bayan kwanaki 470 na kisan kiyashi da sojojin mamaya na Isra’ila suka yi,” in ji sanarwar, wanda ya yi sanadin shahadar Falasdinawa akalla 47,000 tare da lalata wargaza yankin Falasdinawan. An bayyana cewa sama da kashi 90%, yankin ya lalace sakamakon hare haren Isra’ila. An ruguza duk wasu wurare da cibiyoyi masu matukar mahimmanci kama daga asibitoci, makarantu, gidajen jama’a wuraren samar da ruwan sha da wutar lantarki. A yanzu Falasdinawan dake komawa wannan yankin...
Kwamitin zaman lafiya da tsaro na Tarayyar Afirka ya sanar da cewa zai gudanar da zaman gaggawa yau Talata kan halin da ake ciki a gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango (DRC). Kwamitin na (PSC) zai gudanar da wani zaman gaggawa a yau Talata kan halin da ake ciki a yankin, wanda ke fama da yakin da ake yi tsakanin dakarun Kongo da mayakan M23″ in ji Paschal Chem-Langhee, mai magana da yawun kwamitin, yayin da al’amura ke kazanta a Goma, babban birnin gabashin DRC. Kafin nan daruruwan ma’aikatan MDD da fararen hula a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongo sun tsere zuwa makociyar kasar, Rwanda, yayin da gomman sojojin Kongo din suka “mika wuya” ga jami’an tsaron Rwanda a ranar Litinin, bayan ‘yan...
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, ya yaba da irin gudunmawar da darikar Tijjaniyya ke bayarwa wajen samar da hadin kai a tsakanin al’ummar musulmin kasar nan. Mataimakin shugaban kasar ya yi wannan yabon ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron Mauludin bana 2025 na marigayi Sheikh Ibrahim Nyass, jagoran darikar Tijjaniyya a filin wasa na Sani Abacha dake Kano. Mataimakin wanda ya samu wakilcin Alhaji Babagana Fannami, Ya yabawa kungiyar musulmi bisa tsayin daka a tsawon karnukan da suka gabata akan koyarwar addinin musulunci na gaskiya. Shettima wanda shi ne babban bako na musamman a wajen taron, ya yaba da tsarin jagoranci na darikar ‘Sufi’ ga bil’adama. Babban bako na musamman ya jaddada...
Bikin Bazara Na Kasar Sin Na Samun Karbuwa Daga Masu Yawon Shakatawa Na Duniya
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bukaci masu tsara manufofi a fannin ilimi a Najeriya da su dauki kwararan matakai don magance gibin da ke tattare da zamantakewa da al’adu da ababen more rayuwa da manufofin da ke haifar da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar. Shugabar ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Farah, ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025. Ya yi nuni da cewa, Jihohin Kano, da Jigawa da Katsina suna da adadin yara miliyandaya da dubu dari takwas da sittin da uku, da dari biyu da bakwai (1,863,207) da ba sa zuwa makaranta a matakin firamare, da...
Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa. Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta...
Kungiyar kwamishinonin kudi ta kasa ta jinjinawa kokarin gwamnatin jihar Jigawa na bunkasa Ilmin ya’ya mata. Shugaban kungiyar kuma kwamishinan kudi na jihar Ekiti, Mr Akim Oyebode ya bayyana hakan a lokacin da suka ziyarci Gwamna Umar Namadi a gidan gwamnati dake Dutse. Mr Akim Oyebode ya ce kungiyar tana alfahari da ayyukan raya kasa da Gwamna Umar Namadi ya aiwatar tun hawansa karagar mulki, a sassan jihar ta Jigawan. Yana mai cewar sun ziyarci jihar Jigawa ne domin yi wa Gwamnan ta’aziyyar rashin da aka masa. A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi ya yaba musu bisa wannan ziyara tare da fatan za su koma jihohinsu lafiya. Usman Mohammed Zaria
Gwamnatin Jihar Jigawa ta yaba da kokarin ‘yan Nigeria mazauna kasar Saudiyya bisa gudunmawar da suke bayarwa ga harkokin kiwon lafiyar al’ummar jihar. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a lokacin rangadin duba aikin idanu da ‘yan Nigeria mazauna kasar Saudiyya da hadin gwiwar gwamnatin jihar ke gudanarwa a babban asibitin Dutse. Gwamnan wanda ya zagaya wuraren da aka kwantar da wadanda aka yi wa aikin idanun, ya nuna jin dadinsa da gamsuwa da yawan mutanen da aka yi wa aikin. Daga cikin wadanda suka amfana da aikin sun hada da masu matsalar ido su 500 da aka yi wa tiyata, sai kuma mutane 300 da aka baiwa gilashi. Kazalika, mutane 400 kuma suka...
Shugaban Amurka Donald Trump ya zayyana wani ra’ayi mai manufar tsarkake zirin Gaza. Trump na mai cewa yana son aikewa da Falasdinawa daga yankin zuwa kasashen Masar da Jordan “na dan lokaci” ko kuma “a cikin dogon lokaci”. don samun zaman lafiya. Ana dai ganin tamakar Trump na kwatanta yankin Falasdinu da “wurin rushewa nan gaba” bayan watanni 15 na yakin da Isra’ila ta kadamar kan Gaza.