Ministan harkokin wajen Iran ya sanar da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ci gaba da ake samu a shawarwari makamashin nukiliyar Iran tsakanin Amurka da Iran amma ana buƙatar gaskiya da hangen nesa daga ɗayan ɓangaren

A yammacin jiya Juma’a ne ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Araqchi ya tattauna ta wayar tarho da Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres, inda suka yi musayar ra’ayi da musayar mahanga da kuma tattaunawa kan ci gaban yankin da kuma kasa da kasa.

Araqchi ya kuma yi wa Guterres bayani kan sabbin abubuwan da ke faruwa a shawarwarin da ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, da kuma shirye-shiryen da masarautar Oman ta yi na tsara zagaye na gaba na wadannan shawarwari.

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya yi nuni da matakin daukar nauyi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi wajen zabar tafarkin diflomasiyya don warware takaddamar shirinta na makamashin nukiliya ta hanyar lumana, yana mai jaddada cewa, ci gaba kan wannan tafarki na bukatar kuduri na gaskiya da hangen nesa daga daya bangaren. Ya jaddada cewa Iran a matsayinta na mamba a yerjejeniyar hana yaduwar makaman kare dangi, ta himmatu wajen aiwatar da alkawurran da ta dauka, sannan ta dage kan hakkin al’ummar Iran na amfana da makamashin nukiliya domin zaman lafiya, wanda ke bukatar hakkin sarrafa sinadarin yuraniyom.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

An Bude Dandalin Tattauna Batutuwan Tsaro Na Xiangshan Karo Na 12 A Beijing 

Da safiyar yau 17 ga watan Satumba, aka bude dandalin tattauna batutuwan tsaro na Xiangshan karo na 12 da zai dauki kwanaki 3, daga raneku 17 zuwa 19 ga wannan nan, bisa jigon “daukaka tsarin duniya da inganta neman ci gaba cikin lumana”, a nan birnin Beijing.

Tawagogi sama da 100 na gwamnatocin kasashe daban-daban da yankuna da wakilan kungiyoyin kasa da kasa ne ke halartar taron, inda yawan masu rajista ya wuce 1,800.

Da safiyar yau, taron ya shirya tarukan tattaunawa guda 6 bisa jigon “ma’anar cimma nasarar yakin duniya na kin tafarkin murdiyya” da “madaidaitan hanyoyi da manyan kasashe za su bi na yin mu’ammala”, da “hanyoyin warware rikice-rikicen shiyya-shiyya”, da “cika shekaru 80 da kafuwar MDD: samun ci gaba cikin sauye-sauye”, da “amfani da sarrafa sabbin fasahohi”, da kuma “kirkire-kirkire a bangaren kimiyya da fasaha da sauye-sauyen yanayin yaki”. (Amina Xu)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Bude Dandalin Tattauna Batutuwan Tsaro Na Xiangshan Karo Na 12 A Beijing 
  • Guterres: Jerin Shawarwarin Da Sin Ta Gabatar Sun Cika Ka’idar Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya
  • Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki Guda 5 A Wajen Taron Kolin kere-kere .
  • Pezeshkian: Saudiyya Na Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Samar Da Hadin Kan Kasashen Musulmi
  • Baqa’i: Kowace Kasa A Duniya Tana Da Hakkin Mallakar Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya
  • An Fara Taron Hukumar Makamashin Nukliya Ta Duniya IAEA Karo Na 69 A Birnin Vienna
  • Ministan Tsaron Kasar venezuela Ya Gargadi Amurka Dangane Da Kokarin Juyin Mulki A Kasar
  • Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Shuka Kiyayya Da Tashin-Tashina A Tekun Kudancin Sin
  • Ɗan Majalisar Tarayya Ya Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-haren Ta’addanci A Sakkwato 
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Qatar, Turkiyya, Pakistan Da Labanon A Doha