Kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC reshen jihar Kano ta yabawa gwamnatin jihar Kano kan kudirin ta na daidaita bashin da ake bin ‘yan fansho da ya haura naira biliyan 16.

 

 

 

Da yake jawabi yayin bikin ranar ma’aikata da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar Mata a Kano, shugaban kungiyar kwadago ta NLC, Kwamared Kabiru Inuwa, ya bukaci ma’aikatan Nijeriya da su jajirce wajen tabbatar da adalci da walwala.

 

 

Kwamared Inuwa ya bayyana cewa duk da nasarorin da gwamnatin ta samu wajen horas da ma’aikata, har yanzu akwai bukatar karin ma’aikata masu tallafawa a ma’aikatun gwamnati da na kananan hukumomi.

 

 

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatin sa na samar da yanayi mai kyau ga ma’aikatan gwamnati.

 

 

“Duk da kalubalen tattalin arziki, gwamnatin jihar na tabbatar da biyan albashin ma’aikata a kan lokaci domin kara kwarin gwiwar ma’aikata don samar da ingantaccen aiki.”

 

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa ta farfado da ma’aikatan jihar Kano ta hanyar bin ka’idojinta da tsarin aiki.

 

 

Gwamna Yusuf ya jadadda cewa, bisa fifikon da aka ba wa garambawul na fansho a jihar, shaida ce karara na jajircewar gwamnatin na ganin cewa kokarin da sadaukarwar da manyan ‘yan kasa ke yi ba a bar su a banza ba.

 

 

Ya bukaci ma’aikata da su mayar da biki ga kokarin gwamnati ta hanyar sadaukar da kai da jajircewa wajen gudanar da ayyukan da aka dora musu.

 

A yayin bikin wakilan kungiyoyin kwadago daban-daban sun gudanar da fareti mai ban sha’awa don murnar zagayowar ranar ma’aikata.

 

Taron ya samu halartar gwamna Abba Kabir Yusuf, mataimakinsa, yan majalisar zartarwa na Kano, shugaban kungiyar da sauran masu ruwa da tsaki.

 

 

Cover /Abdullahi jalaluddeen/Kano

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Za mu ci gaba da shirye-shiryen babban taronmu — PDP

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa za ta ci gaba da shirin gudanar da babban taronta wanda za a yi a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba a Ibadan da ke Jihar Oyo.

Tun da farko, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta hana jam’iyyar gudanar da taron, inda ta ce PDP ta karya dokokinta na cikin gida.

’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi Kotu ta dakatar da gudanar da babban taron PDP

Mai shari’a James Omotosho, wanda ya jagoranci shari’ar, ya umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), da kada ta karɓi ko ta wallafa sakamakon taron har sai PDP ta cika dukkanin sharuɗan da doka ta tanada.

Sai dai a cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar da yammacin ranar Juma’a, kakakinta na ƙasa, Debo Ologunagba, ya ce jam’iyyar ba za ta dakatar da shirin gudanar da taron ba.

Ya bayyana hukuncin kotun a matsayin tauye haƙƙin dimokuraɗiyya a Najeriya.

Ologunagba, ya ce hukuncin ba zai hana PDP ci gaba da shirye-shiryenta na zaɓen sabbin shugabanni da za su jagoranci jam’iyyar na tsawon shekaru huɗu masu zuwa ba.

Ya yi nuni da cewa Kotun Ƙoli ta tabbatar da cewa jam’iyyu na da ’yancin tafiyar da harkokinsu na cikin gida.

“PDP na kira ga mambobinta da shugabanni a faɗin ƙasar nan da su kuma ci gaba da shirye-shiryen babban taron jam’iyyar,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa jam’iyyar mai bin doka ce, kuma ta umarci lauyoyinta da su ɗaukaka ƙara game da hukuncin kotun.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci
  • Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3
  • Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
  • Za mu ci gaba da shirye-shiryen babban taronmu — PDP
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar
  • Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai
  • Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa
  • NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Daliban Makarantar Kudi Suka Fi Na Gwamnati Kokari