Limamin Jumma’a A Nan Tehran Ya Ce Iran Tana Da Masu Tattaunawa Da Amurka Kwararru
Published: 2nd, May 2025 GMT
Limamin da ya jagoranci sallar Jumma’a a nan Tehran Hujjatul Islam kazim Sadiki ya bayyana cewa kasar tana da kwararru wadanda suke da kwarewa a sanin fasahar nukliya da kuma hanyoyin dublomasiyya a tattaunawar da Iran take da Amurka dangane da shirin Nukliyar kasar.
Tashar talabijin ta Al-alam a nan Tehran ta nakalto limamin yana fadar haka a khudubobinsa na sallar Jumm’a.
Hujjatul Islam Sadiki ya kara da cewa tawagar Iran a wannan tattaunawar, suna amfani da tajruban da suke da shi a tattaunawar baya, sannan sauran jami’an gwamnati suna sanya ido suna kuma kula da yadda tattaunawar take. Sannan ko way a san cewa wannan tattaunawar tana dimfare da makaman JMI ganin yadda kasar Amurka take barazanar faraway Iran da yaki sannan tana karawa kasar Takunkuman tattalin arziki ana cikin tattaunawar.
Har’ila yau limamin yana yi magana dangane da ranar ‘Malami” a kasar Iran wanda yayi dai-dai da ranar shahadin daya daga cikin jaga-jigan malaman da suka jagoranci juyin juya halin musulunci a kasar a shekara 1979. Wato Aya. Shahid Murtada Muttahari.
Wata batacciyar kungiyar wacce ake kira furkan ce ta kashe Aya. Shahid Muttahari wataki bai 80 da nasarrar juyin juya halin musulunci a kasar.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: a tattaunawar
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa
A cewarsa, ta hanyar wadannan shirye-shirye, kasar Sin ta nuna goyon baya mai dorewa ga kasashe masu tasowa kuma tana ba da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban duniya a karkashin tsarin hadin gwiwar kasashe masu tasowa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA