Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa sojansu daya ya halaka a Gaza yayin da wasu 4 su ka jikkata bayan da aka kai wa motar da take dauke da su mai sulke hari.
Majiyar ta kuma ce ana ci gaba da yin fada mai tsanani a tsakanin sojojin Isra’ilan da kuma ‘yan gwagwarmaya a yankunan daban-daban na zirin Gaza.
Majiyar Falasdinawa ta ce; ‘yan gwgawarmaya sun tarwatsa wata tankar yakin HKI ta hanyar tashin wani bom da aka ajiye a kan hanya.
An ga jiragen yakin HKI masu saukar angulu suna jigilar daukar wadanda su ka jikkata sanadiyyar harin.
A gefe daya, Falasdinawa da dama sun yi shahada a wasu hare-hare da ‘yan sahayoniya su ka kai akan yankin na Gaza. Tun da safiyar yau Asabar ne dai ‘yan sahayoniyar su ka rika kai hare-haren wanda ya yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa 30.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Saudiya Ta Yi Allawadai Da Kissan Kiyashin Da HKI Take Yi A Gaza A Gaban Kutun ICJ
Gwamnatin kasar Saudiya ta yi allawadai da HKI a kissan da take wa falasdinawa a Gaza, a jiya talata a gaban kutun ICJ. Saudiya ta bayyana cewa gwamnatin HKI ta sabawa dokokin kasa da kasa da dama a kissan kiyashin da take yi a Gaza.
Wakilin kasar a gaban kotun Muhammad Saud Al-Nasser, ya kara da cewa, HKI ta ci gaba ta sabawa wadannan dokoki, amma kuma bata da dalilan saba masu.
Banda kissan kiyashin da take yi a Gaza, Al-Nasser ya ce HKI ta maida Gaza kofai, ta rusa mafi yawan gine-ginen yankin, sannan ta hana shigowar abinci da ruwa da magunguna zuwa yankin, wadanda ko wane daya daga cikinsu take hakkin bil’adama ne wanda yake kaiwa ga laifin yaki.
Gwamnatin Saudiya ta gabatar da wannan jawabin ne a rana ta biyu da bude zaman da kotun ta ICJ tayi don tattaunwa da kuma jin ra’ayin kasashe dangane da take hakkin bi’adaman da HKI take yi a Gaza. A halin yanzu fiye da kwamaki 50 kenan da gwamnatin HKI ta ke hana shigowar abinci da magunguna da kuma bukatun falasdinawa zuwa yankin.
Har’ila yau kotun ta girka wannan zaman ne don tattauna yadda HKI take mu’amala da umurnin ta danganda take hakkin bil’adama a Gaza.