2025-11-27@22:59:05 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4794
«Abu Musa Ya»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Kwamitin Tsaro Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Amurka ta bukaci duba kudurin da aka gabatar na neman kafa rundunar kasa da kasa a Gaza Rahotannin daga Amurka sun bayyana cewa: Gwamnatin Amurka ta Trump tana neman amfani da rikicin Gaza wajen kwace makaman kungiyar Hamas da take amfani da ramuka wajen yakar ‘yan sahayoniyya, don aiwatar da wani tsari na kwace makamai daga hannun ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa. A ƙarƙashin tutar tsaro da kwanciyar hankali, Amurka, da kuma Isra’ila, suna ƙoƙarin kafa sabon tsari a Gaza wadda ke neman murkushe ‘yan gwagwarmaya, tare da tabbatar da tsarin babakeren ‘yan mamaya karkashin wani tsari mai sauƙi, da zai buɗe sabon babi na iko a kan yankin. A tsakiyar tambayoyi game da...
Muhimmin fadakarwa daga Sayyid Muqtada al-Sadr kwanaki kafin zaɓen kasar Iraki Malamin Tafarkin Shi’a na Iraki Muqtada al-Sadr ya umurci magoya bayansa a ranar Alhamis da su dakatar da duk wani zaman dirshan da zanga-zanga har zuwa lokacin zaben ‘yan majalisa dokokin kasar mai zuwa. A cikin wata sanarwa, ofishin al-Sadr ya ce ya yi nazari kan ayyukan da suka hada da tarurrukan kabilanci da na matasa da ke goyon bayan shawararsa ta kauracewa zaben kuma ya yi tsokaci, “Daga yanzu har zuwa ranar zabe, babu bukatar wani karin zanga-zanga.” Wannan shawarar ta ci gaba da tsarin al-Sadr na nisantar da kansa daga tsarin zaben tun bayan sanarwarsa a watan Yunin shekara ta 2022 na janye kansa gaba daya daga...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro November 6, 2025 Manyan Labarai Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu November 5, 2025 Manyan Labarai ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya November 5, 2025
Ministan Harkokin Wajen Iran ya yaba da juriyar da kasar ta nuna yayin hare-haren Amurka da Isra’ila, wanda ya tilasta musu rokon a tsagaita wuta ba tare da shiri ba. Da yake jawabi a yammacin ranar Laraba a taron Majalisar Gudanarwa ta Lardin Hamadan, Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa abokan gaba sun gaza a dukkan manufofinsu a lokacin yakin na kwanaki 12. Kalaffafen yakin na kwanaki 12 ya bamu babban darasi inji shi, saboda mun fi karfi da a ranar 13 ga watan Yuni. A karon farko, an yi amfani da makamai masu linzami na Iran a wani rikici na gaske, wanda hakan ya ba da damar gano ƙarfi da rauninsu. A yau, Iran tana...
Osimhen, wanda ya koma Galatasaray daga Napoli, ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarorin ƙungiyar ta ƙasar Turkiyya, ciki har da lashe kofin ƙalubale. A yanzu haka, shi ne ɗan wasan da ya fi ci wa Galatasaray ƙwallaye a dukkanin da ta ke bugawa a bana, ya bar sauran fitattun ’yan wasa irin su Leroy Sane da Mauro Icardi a baya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba November 2, 2025 Wasanni Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara November 2, 2025 Wasanni Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar? November 2, 2025
Mataimakin ministan harkokin wajen Iran kan harkokin ƙasa da ƙasa da shari’a ya jaddada muhimmancin kara karfafa dangantakar da ke tsakanin Tehran da Riyadh, yana mai cewa ci gaban kyakkyawar alaƙa tsakanin Tehran da Riyadh ba wai kawai yana da amfani ga ɓangarorin biyu ba ne, har ma zai kara karfafa zaman lafiya a yankin da ma a duniya. Kazem Gharibabadi ya yi wannan furuci ne bayan ziyarar da ya kai Saudiyya da nufin fadada haɗin gwiwa da haɗin kai tsakanin manyan ƙasashen biyu. Mataimakin ministan harkokin wajen ya jaddada cewa Iran da Saudiyya, waɗanda ke da alaƙa ta tarihi suna da kyakkyawan matsayi don yin hidima ga al’ummarsu da kuma taka domin ci gaban zaman lafiya a yanking abas...
Tawagar masu sa ido ta Tarayyar Afirka ta sanar a ranar Laraba cewa zaɓen Tanzania “bai cika ƙa’idodin dimokraɗiyya ba,” tana mai tsokaci kan zaɓen da aka yi jayayya a kansa wanda ya haifar da zanga-zanga mai tsanani kwanan nan. An ayyana Shugaba Samia Suluhu Hassan a matsayin wadda ta lashe zaɓen da gagarumin rinjaye a zaɓen da aka gudanar a ranar 29 ga Oktoba, amma ‘yan adawa sun zargi gwamnati da yin magudi a zaɓen, kuma zanga-zangar ta ɓarke bayan da aka soke manyan abokan hamayyarta. Tawagar ta ƙara da cewa “a wannan matakin farko, tawagar ta kammala da cewa babban zaɓen 2025 a Tanzania bai yi daidai da ƙa’idodin Tarayyar Afirka da tsarin ƙa’idoji na kasa da kasa...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cutar basir na daga cikin cututtukan da mutane da dama ke da mabanbantan ra’ayoyi akan ta. A lokuta da dama za ka ji yadda mutane ke fadin dalilai daban daban da ke janyo cutar basir, yayin da wasu ke ganin yawan zama ne ke kawo ta, wasu kuwa gani suke yi zaki da maiko ne ke kawo ta. Wannan shine abun da da yawa daga cikin mutane suka sani kan wannan cuta, sai dai masana kiwon lafiya na da nasu fahimtar daban kan wannan cuta. NAJERIYA A YAU: Rashin aikin yi da hanyoyin magance su a Najeriya DAGA LARABA: Yadda ‘Yanbindiga Ke Amfani Da Hakar Zinare Wajen Mallakar Makamai Shirin Najeriya A...
“Wannan babban shiri ne da zai sake fasalin Zamfara, ya tabbatar da ci gaba mai ɗorewa tare da inganta rayuwar al’umma,” inji shi. Ya ƙara da cewa, a mafi yawan ƙananan hukumomin jihar ana gina sabbin hanyoyi na kilomita biyar a cikin birane, baya ga Gusau wadda ake gudanar da manyan ayyuka na musamman. Ya ce hakan zai rage cunkoso, ya haɗa al’umma, ya kuma farfaɗo da kasuwancin ƙauye da birane. A fannin lafiya, gwamnati ta ƙaddamar da gina sabon babban asibiti a Nasarawa Burkullu a ƙaramar hukumar Bukkuyum, tare da sabunta cibiyoyin kiwon lafiya da dama a yankunan karkara, domin sauƙaƙa samun ingantaccen magani. An kuma sanar da ci gaba da gyaran makarantu a dukkan...
Li Chenggang, wakilin cinikayyar kasa da kasa na ma’aikatar kasuwanci kuma mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin, ya gana da tawagar cinikayyar kayan noma ta Amurka a birnin Beijing a jiya Talata 4 ga watan Nuwamb, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra’ayoyi kan huldar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, da cinikayyar kayayyakin noma, da sauran batutuwa masu alaka. Li Chenggang ya bayyana cewa kyakkyawar alaka ta tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka tana da alfanu ga kasashen biyu da kuma duniya baki daya. Tun daga watan Mayu na wannan shekarar, tawagogin tattalin arziki da cinikayya na bangarorin biyu sun tattauna har sau biyar bisa jagorancin muhimmiyar matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, wanda...
A gaskiya wannan yanayi ya yi matukar burge ni, kuma sai na zaci ko don saboda ina bako ne, amma yayin da na ga wasu Sinawa suna daukar hotunan bishiyoyin, sai na ce to, babu makawa wannan yanayi ne mai burge kowa da kowa, bako da dan gari kuma ciki har da dattawa. Nan take ni ma na zaro wayata, muka ci gaba da kashe hotuna ni da abokin aikina. Na yi kokarin nuna kawaici a kan yadda yanayin ya shaukantar da ni, amma sai na ga abokin nawa ya fi ni “jazabancewa”, domin shi ya fi ni yawan yin “style” na daukar hoton da kuma yawan hotunan da muka dauka. Wani abu da na lura da shi...
Dantsoho ya bayyana cewa, a taron Tashoshin Jiragen Ruwa na Duniya da aka yi a Kobe, Kasar Japan, shugabannin tashoshin jiragen ruwa na Afirka sun yi alƙawarin haɓaka ci gaban Tashoshin yankin ta hanyar tsarin dabaru uku – aiwatar da manufofi, sabunta haɗin gwiwa, da sauƙaƙe ciniki, wanda wannan shi ne abin da NPA ta ƙuduri aniyar aiwatarwa. Shugaban na PMAWCA ya kuma yaba wa gwamnati da mutanen Jamhuriyar Congo saboda ɗaukar nauyin taron kuma ya yaba wa sakatariyar ƙungiyar bisa jajircewa wurin tabbatar da dandamalin tattaunawar tsakanin yankunan da kuma yadda ake samar da sabbin tsare-tsare a shugabancin kungiyar mai kula da teku. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A...
Kamfanin dillanacin labarun Faransa ya ambato wata majiyar shari’a tana cewa; ‘yan jaridar da aka kama su ne; Ibro Shu’aibu na gidan talbijin din Sarauniya, sai Yusuf Sariba na wani Shafin watsa labaru na Niger Ecoh da kuma Umaru Kano na jaridar “Errison.” Dukkanin ‘yan jaridar uku an kai su kurkukun Kolo wanda yake da nisan kilo mita 50 daga babban birnin kasar Yamai. A ranar Asabar din da ta gabata ne dai aka kama wadannan ‘yan jaridar da kuma wasu abokan aikinsu. Ana tuhumar ‘yan jaridar da fallasa bayanan gwamnati da shi ne bukatar samarwa da gwamnatin taimakon kudi daga ‘yan kasa. Bayan watsa labarin da aka zargi tashar talabijin din Sarauniya da yi, labarin ya watsu a cikin...
Shugaban kasar Mali Assimi Goita ya yi wa al’ummar kasar jawabi akan karancin man fetur da ake fama da shi a kasar da kuma yadda masu ikirarin Jihari suke killace motocin dakon makamashi. An fara samun kamfar man fetur ne a kasar Mali wacce ba ta da iyaka ruwa, da masu ikirarin jihadi su ka tare kan iyaka da hana tankokin man fetur shiga cikin kasar. Goita ta bayyana cewa: “ A duk lokacin da za a dauko motocin dakon mai, mutane suna mutuwa, ana yin kwanton bauna akan hanya,ana kona motocin da mutane a cikinsu har su kone kurmus.” Goita ya bayyana haka ne a lokacin dake halartar bikin bude wurin hako ma’adanin “Lithium” a yankin Bougouni a kudancin...
Firaministan kasar Georgia Irakli Kobakhidze da firaministan kasar Serbia Duro Macu da shugaban majalisar wakilan kasar Najeriya Tajudeen Abbas, sun halarci taron bude bikin tare da ba da jawabai. Haka kuma wakilai kimanin 1500 daga sassan siyasa, kasuwanci da ilmi na kasashe da yankuna da kungiyoyin kasa da kasa 155 su ma sun halarci taron.(Tasallah Yuan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka November 5, 2025 Daga Birnin Sin CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika November 5, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika November 4, 2025
Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Don Yaki da Laifuffuka A Maiduguri Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya mika motocin sintiri 63 ga hukumomin tsaro da kuma Rundunar Hadin Gwiwa ta Farar Hula (CJTF) da ke aiki a Maiduguri da kewaye. Daga cikin motocin 63, an ba da motocin 30 ga sassa daban-daban na Sibiliyan JTF, 16 ga Jami’an tsaron kai daukin gaggawa don dakile masu aikata laifukan cin Zarafi, 10 ga kungiyoyin tsaro, 6 ga mafarauta da kuma daya ga jami’an Hukumar Kula da Fataucin Mutane (NAPTIP). Rarraba motocin yana da nufin inganta karfin yin sintiri da mayar da martanin gaggawa musamman ga ‘yan sanda, sauran jami’an tsaro, da rundunar hadin gwiwa ta farar hula wajen magance barazanar...
Ya ƙara da cewa wannan mataki wani ɓangare ne na gyaran tattalin arziƙi da kuma dawo da amincewa ga tsarin kwangilolin gwamnati. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya November 5, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86 November 5, 2025 Manyan Labarai Ɗan Majalisar Amurka Ya Zargi Kwankwaso Da Hannu A Kisan Kiristoci A Nijeriya November 5, 2025
Daga Khadijah Aliyu An fara shirye-shirye gudanar da taron shekara-shekara karo na 2 da bikin shigar da sabbin mambobi na Ƙungiyar Masana Harkokin Yada Labarai ta Najeriya (SNB), bayan an kaddamar da Kwamitin Shirya Taron (LOC) a Kano. An tsara gudanar da taron ne daga ranar 20 zuwa 21 ga watan Nuwamban 2025. Shugaban Ƙungiyar, Farfesa Umaru A. Pate, ya umarci kwamitin da ya gudanar da aikinsa da himma da jajircewa domin tabbatar da nasarar taron, wanda shi ne irinsa na farko da za a yi a Kano. Ya bayyana cewa ana sa ran masana sama da 400 da sabbin mambobi daga ciki da wajen jihar za su halarta. Farfesa Pate ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kano kan jajircewarta wurin...
Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kwara ta ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su ba tare da wata illa ba, a kauyen Igbonla. A cikin wata sanarwa da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta rundunar, SP Adetoun Ejinre-Adeyemi, ta fitar, ta ce rundunar ta samu kiran gaggawa cewa wasu ’yan bindiga sun kutsa cikin wani gida, suna harbi a sama, sannan suka tafi da wasu daga cikin mazauna gidan. Daga nan ne rundunar ’yan sanda tare da ’yan banga da masu farauta suka isa yankin cikin gaggawa, lamarin da ya kai ga ceto sun hada da Fatima Wasiu da Kudus Wasiu da jaririya mai watanni shida, ba tare da jin rauni ba. Sai dai har yanzu ana ci gaba...
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga sun kai hari kan ayarin dan majalisar tarayya mai wakiltar Mazabar Agwara/Borgu a Jihar Neja, Honarabul Jafaru Mohammed Ali. Rahotanni sun bayyana cewa harin ya faru ne a jiya, a kauyen Kubul, kan hanyar Agwara zuwa Babana, a cikin Karamar Hukumar Borgu, yayin da dan majalisar ke hanyarsa ta zuwa ganawa da jama’arsa kan muhimmin shirin ci gaba. Bayan harin, Honarabul Jafaru da tawagarsa sun samu rauni, inda aka garzaya da su asibiti, kuma suna karbar kulawar likitoci a halin yanzu. A halin da ake ciki, jami’an tsaro sun isa yankin domin fatattakar ‘yan bindigar da kuma kare rayukan jama’a. Duk da haka, babu wata sanarwa ta hukuma a hukumance a yanzu game da...
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jinjinawa rundunar Sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro bisa gaggawar daukar mataki kan hare-haren ‘yan bindiga da suka faru a wasu sassan jihar. Gwamnan ya yi wannan yabo ne a lokacin da Babban Hafsan Runduna ta 1, wato GOC 1 Division da ke Kaduna, Major Janar Abubakar Sadiq Muhammad Wase, ya kai masa ziyara a Gidan Gwamnati Kano. Gwamna Yusuf ya bayyana jin dadinsa da yadda sojoji ke gudanar da aikinsu cikin kwarewau, jajircewa da kishin kasa, tare da bayar da tabbacin ci gaba da hadin kai tsakanin gwamnati da hukumomin tsaro. Ya kuma gode wa Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu, bisa nada manyan hafsoshi masu kwarewa da suka himmatu wajen yaki...
Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya umarci Ma’aikatar Ilimi don tabbatar da cewa, daliban jami’a suna ci gaba da karatunsu ba tare da wani cikas ba, yana mai cewa, Gwamnatin Tarayya tana yin duk abin da ya dace don hana Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) tsunduma wani yajin aiki a nan gaba. Da yake magana da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja, a ranar Talata, Ministan ya ce Shugaba Tinubu ya umarce shi da ya nemo mafita mai ɗorewa ga duk wata matsala da ka iya kawo cikas ga ayyukan ilimi a manyan makarantun kasar nan. Kamar yadda na gaya muku, Shugaban Ƙasa ya umarce mu da cewa, ba ya son ASUU ta sake...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kiyasi ya nuna cewa Najeriya tana asarar sama da dala biliyan 9 a duk shekara sakamakon ayyukan masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, kuma kaso mafi tsoka shi ne fannin zinare. Rahotanni sun ce hakan na karawa ‘yan ta’adda karfi, inda suke amfani da wannan dama wajen tara muggan makamai a yankin Arewa maso Yamma da ke fama da matsalar tsaro. ‘Yan bindigar sun yi ikirarin suna samun kimanin naira miliyan 300 duk mako daga haramtattun wuraren hakar ma’adinai. NAJERIYA A YAU: Rashin aikin yi da hanyoyin magance su a Najeriya DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa PDP Ta Ki Sayarwa Sule Lamido Fom Din Takarar Shugaban Jam’iyya Shirin Daga Laraba na...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Tinubu Ya Umarci Ma’aikatar Ilimi Ta Kawo Ƙarshen Yajin Aikin ASUU November 4, 2025 Labarai 2027: Ko Kano Ta Zauna Lafiya Ko Ta Hautsine, Sai Mun Sauke Gwamna Abba — Shugaban APC November 4, 2025 Labarai Zargin Kisan Kiyashi Ga Kiristoci: Trump Bai San Ƙalubalen Tsaron Da Najeriya Ke Ciki Ba — Ndume November 4, 2025
A halin yanzu, sashen saukar kumbuna da dukkan na’urori da tsare-tsaren da ke aikin tallafa wa saukar kumbo suna ci gaba da shirye-shiryen tarbar ‘yan sama jannatin, kamar yadda Hukumar Kula da Zirga-zirgar Kumbuna ta kasar Sin ta bayyana. (Abdulrazaq Yahuza Jere) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar November 4, 2025 Daga Birnin Sin Li Qiang Ya Zanta Da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya November 4, 2025 Daga Birnin Sin Tsohon Jami’in Diflomasiyyar Nijar: Baje Kolin CIIE Muhimmin Dandali Ne Na Bunkasa Hadin Gwiwa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa November 4, 2025
Ya ƙara da cewa: “Mun cika dukkan buƙatunsu. Yanzu mun koma teburin tattaunawa, yanzu haka na zo wurin shugaba Tinubu ne don zayyana masa inda muka tsaya da ASUU.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai 2027: Ko Kano Ta Zauna Lafiya Ko Ta Hautsine, Sai Mun Sauke Gwamna Abba — Shugaban APC November 4, 2025 Labarai Zargin Kisan Kiyashi Ga Kiristoci: Trump Bai San Ƙalubalen Tsaron Da Najeriya Ke Ciki Ba — Ndume November 4, 2025 Manyan Labarai Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Ga Hukumomin Tsaro A Borno November 4, 2025
Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta yi tsokaci game da matakin Amurka na sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ake da damuwa a kansu, inda ta jaddada matsayin Sin na matukar goyon bayan gwamnatin Najeriya, wajen jagorantar al’ummarta zuwa turbar neman ci gaba bisa yanayin da kasar ke ciki. A ’yan kwanakin nan ne shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar da sanya Najeriya cikin jerin kasashen da kasarsa ke kara mayar da hankali a kansu, bisa zargin barazanar da ya ce mabiya addinin Kirista na fuskanta a kasar. Trump ya kara da cewa, idan har gwamnatin Najeriyar ta gaza shawo kan kisan Kiristoci, to Amurka za ta hanzarta dakatar da dukkanin tallafin da take baiwa kasar, kana...
A yau Talata ne firaministan Sin Li Qiang, ya gana da kakakin majalisar wakilan tarayyar Najeriya Tajudeen Abbas, wanda ya isa birnin Shanghai don halartar baje kolin CIIE karo na takwas. Yayin zantawarsu, Li Qiang ya bayyana aniyar kasar Sin ta karfafa salon wanzar da ci gaba bisa manyan tsare-tsare tare da Najeriya, da zage damtse wajen aiwatar da wasu muhimman matakai goma na bunkasa kawance tsakanin Sin da kasashen nahiyar Afirka, da hada hannu wajen gina shawarar “Zira Daya Da Hanya Daya” mai inganci, da bunkasa matakin hadin gwiwa a sassan gargajiya, da fadada hadin gwiwa a sabbin masana’antu, da kara kyautata gina tattalin arziki da zamantakewar al’ummun sassan biyu. Li Qiang ya kara da cewa, akwai bukatar kasashen...
Majalisar Wakilai ta dakatar da zamanta na tsawon mako guda, sakamakon zanga-zangar da wasu ’yan kwangila suka gudanar a ƙofar shiga ginin majalisar dokoki ta ƙasa da ke Abuja, saboda rashin biyan kuɗaɗen ayyukan da suka kammala tun shekarar 2024. Rahotanni sun ce ’yan kwangilar sun yi dandazo ne a ƙofar shiga majalisar a ranar Talata, domin nuna rashin jin daɗinsu kan yadda gwamnati ta gaza biyansu haƙƙoƙinsu duk da cewa sun kammala ayyukan da aka ba su. China ta yi martani kan barazanar Trump ta kai hari Najeriya Kotu ta sahale wa PDP gudanar da babban taronta a Ibadan Bayanai sun ce masu zanga-zangar sun rufe hanyoyin shiga da fita na majalisar, abin da ya tilasta shugaban majalisar da sauran...
Kakakin Dakarun Kare Juyin Juya Halin Mususluni na bayyana yaƙin kwanaki 12 kan Iran ya tabbatar da cewa ba za a taɓa amincewa da Amurka ba Kakakin Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) ya tabbatar da cewa: Yakin kwanaki 12 da aka yi da Iran ya nuna rashin amana ga masu yanke shawara na Amurka, kuma al’ummar Iran sun san halin da ake ciki kuma sun haɗu wuri ɗaya, inda suka samar da garkuwar da ba za a iya ratsawa ba. Birgediya Janar Ali Mohammad Na’ini, kakakin Dakarun kare juyin juya halin Musulunci {IRGC}, ya yi jawabi ga mahalarta taron gangamin Ranar Yaƙi da Girman Kai na Duniya a Karaj, yana mai nuna godiyarsa ga kasancewar mutane masu aminci...
Mataimakin ko’odinetan sojojin Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan Sahayoniyya ba ta kai matakin da zata samu damar yaƙar Iran ba Mataimakin ko’odinatan sojojin Iran, Admiral Habibullah Sayyari, ya bayyana cewa: Yahudawan Sahayoniyya ba su da ikon yaƙar Iran, kuma bayan Iran ta fara murkushe su, Amurka ta hanzarta shiga cikin yaki, wanda ita ma ta dandana kudarta.” Da yake jawabi a wani taron jama’a don tunawa da Ranar Yaƙi da Girman Kai ta Duniya, Admiral Sayyari ya ce: “Girman kai yana da halaye uku; na farko shine yana sa ƙasashe su gaza ci gaba, kuma yana mai da hankali sosai kan hakan musamman dangane da Iran.” Ya ƙara da cewa: “Halayya ta biyu ta girman kai ita ce: Kokarin...
Shugaban Majalisar Dokokin Lebanon ya bayyana cewa; Gwagwarmaya ta tilastawa gwamnatin mamayar Isra’ila rashin girke sojojinta a kan iyakar da ke tsakanin Isra’ila da Lebanon Kakakin Majalisar Dokokin Lebanon Nabih Berri ya tabbatar da cewa: “Gwagwarmaya ta yi cikakken biyayya ga sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wuta, kuma sojojin Lebanon sun tura sojoji da jami’ai sama da 9,000 a yankin da ke kudancin Kogin Litani.” Ya ƙara da cewa “sojojin suna da ikon tura sojoji a kan iyakokin da ƙasashen duniya suka amince da su tsakanin Labanon da Isra’ila, amma abin da ke kawo cikas ga wannan shi ne ci gaba da mamaye yanki mai girma na kudancin Lebanon da sojojin mamayar Isra’ila suka yi, kamar yadda Rundunar UNIFIL da rahotanninta na...
Tsohon mataimakin shugaban Amurka da ya kasance wanda ya tsara mamayar Iraki, ya mutu a yau Tsohon Mataimakin Shugaban Amurka Dick Cheney, wanda ya yi aiki a karkashin Shugaba George W. Bush, ya rasu a yau Talata yana da shekaru 84 a duniya, a cewar rahotannin kafafen yada labarai na Amurka. Cheney ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban kasa a gwamnatin Bush daga 2001 zuwa 2009. Kafafen yada labaran Amurka sun bayyana shi a matsayin babban mai tsara “Yakin Ta’addanci,” wanda ya jagoranci Amurka ta mamaye Iraki a shekara ta 2003 bayan hare-haren 11 ga watan Satumban shekara ta 2001 da suka kashe dubban ‘yan Iraki. Cheney, wanda kuma ya yi aiki a matsayin Sakataren Tsaro kuma Babban Jami’in...
Yayin da yake gabatar da motocin, Gwamna Zulum ya sake nanata kudirin gwamnatinsa na samar da tallafin kayayyaki ga jami’an tsaro a kowane lokaci. Ya jaddada cewa, tsaro wani bangare ne na muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba. Zulum ya kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu da jami’an tsaro kan kokarin da suke yi na dawo da zaman lafiya a Borno. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya November 4, 2025 Manyan Labarai Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike November 4, 2025 Manyan Labarai Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi November...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan Rasha Mikhail Mishustin yau Talata a birnin Beijing, inda suka yi kira da inganta dangantakar kasashen biyu a bangarori daban-daban da kyautata hadin gwiwarsu kan dabarun samun ci gaba. Ya ce tun daga farkon bana, Sin da Rasha ke gudanar da harkokinsu cikin nutsuwa duk da yanayi na hargitsi da suke fuskanta a waje, inda suka mayar da hankali kan ingantattun muradun ci gaba. Ya ce karfafawa da daukakawa da ci gaba da gudanar da hulda tsakanin kasashen biyu, muhimmin zabi ne da bangarorin biyu suka yi. Da yake bayyana cewa an tsara taswirar bunkasa dangantakar kasashen biyu ne yayin taron da suka yi da shugaba Vladimir Putin a bana, shugaba...
Ya ƙara da cewa yana cikin farin ciki ganin yadda Gwamna Douye Diri ya fice daga jam’iyyar, inda ya ce, “Shi da Makinde sun taɓa cewa ba za su bari a lalata PDP ba ko a jawo ta ƙasa, amma ga su yanzu; su ne suka faɗi ƙasa.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi November 4, 2025 Manyan Labarai Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja November 4, 2025 Manyan Labarai Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo November 4, 2025
Natasha ta bayyana dakatar da ita a matsayin mataki wanda ba na doka ba, tana mai cewa hakan ya nuna yadda tsoro da barazanar siyasa ke rinjayar halayen jami’an gwamnati. An dakatar da Sanata Natasha a watan Maris saboda zargin da ya shafi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, amma ta koma kujerarta a watan Satumba bayan kammala wa’adin dakatarwar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai “Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan Trump November 3, 2025 Manyan Labarai Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna November 1, 2025 Siyasa Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar October 31, 2025
rahotanni suna nuna cewa mai ba shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu ya gana da manyan hafsoshin tsaron Najeriya da jagororin sassan tattara bayanan sirri kan barazanar Shugaban Amurka Donald Trump. Trump ya yi zargin cewa ana yi wa kiristoci kisan kiyashi a Najeriya, inda ya ce yana so gwamnati ta dauki matakin gaggawa ko kuma ya turo sojoji domin su yaki maharan da ya bayyana da ƴanbindiga masu ikirarin jihadi. A sanarwar, ya ce, “na ba sashen yaki umarni su fara shirin daukar mataki. Idan har za mu kai hari, to za mu kai harin ne cikin sauri ba tare da bata lokaci ba, kamar yadda ƴan ta’addan nan suke kai hari kan kiristoci,” in ji...
Ya jaddada cewa gwamnati tana tabbatar da tsaron kowa ba tare da bambanci ba. Kalaman Trump sun haifar da ruɗani da cece-ku-ce a tsakanin ‘yan Nijeriya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya November 3, 2025 Manyan Labarai Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro November 3, 2025 Manyan Labarai Kwamishinan Ƴansanda Na Kano Ya Karrama Sabbin Jami’an Da Aka Ƙara Wa Matsayi November 3, 2025
Gwamnatin Kaduna Da Hadin Gwiwar UINL Da FHFL Sun Gina Gidaje 100 Ga Mutanen Da Rikici Ya Raba Da Muhallans Daga Abdullahi Shettima Gwamnatin Jihar Kaduna tare da haɗin gwiwar kamfanin Ummi International Nigeria Ltd (UINL) da Family Homes Funds Ltd (FHFL), bisa tallafin Ma’aikatar Tsare-tsare da Kasafin Kuɗi ta Tarayyar Najeriya, sun kammala ginin gidaje 100 domin mutanen da rikici ya raba da muhallansu da kuma marasa galihu a cikin jihar. Wannan aiki ya gudana ne a yankin Rigachikun, inda kamfanin Ummi International Nigeria Ltd ya bayar da fili, yayin da Gwamnatin Kaduna, Family Homes Funds, da Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsare suka ɗauki nauyin ginin gidajen gaba ɗaya. A yayin ƙaddamar da ginin da kuma miƙa ma waɗanda...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na fadada ayyukan ci gaban karkara, tare da aiwatar da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar al’umma. Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi bakuncin jami’in kula da shirin rage radadin illar da annobar cutar Korona ta haifar, wato (NG-CARES), Dakta Abdulkareem Obaje, wanda ya kai masa ziyara ta ban girma a Dutse. Dakta Obaje ya yaba wa gwamnan da gwamnatin jihar Jigawa bisa goyon bayan da suke bai wa shirin NG-CARES tun daga lokacin da aka ƙaddamar da shi a shekarar 2021. Ya bayyana cewa an kirkiro shirin ne a shekarar 2020 sakamakon tasirin annobar COVID-19, domin taimaka wa jihohi su...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya November 3, 2025 Ra'ayi Riga Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki November 3, 2025 Manyan Labarai Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro November 3, 2025
Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Lebanon ta sanar a yau Litinin cewa; Jirgin sama maras matuki na HKI ta kai wa wata mota hari a kusa da garin “Sharqiyya”. Kamfanin dillancin labarun kasar Lebanon kuwa ya sanar da cewa; Jirgin sama maras matuki na HKI ya jefa bom a kusa da wata motar Buldoza a garin Khayyam, sai dai babu wanda ya jikkata. Haka nan kuma kamfanin dillancin labarun ya ce; Jirgin saman maras matuki ya jefa wasu bama-baman guda uku akan hanyar Zafta. A cikin kwanakin bayan na HKI tana kara tsananta kai hare-hare a kudancin Lebanon, lamarin da yake nuni da kokarin sake dawowar yaki gadan-daban. Tun bayan tsagaita wutar yaki a Lebanon shekarar da ta gabata HKI...
Wasu rahotanni na cewa dakarun RSF a kasar Sudan, sun hallaka fararen hula kusan 2000 a birnin El Fasher, fadar mulkin jihar arewacin Darfur. Kuma tuni MDD, da kungiyar tarayyar kasashen larabawa ta AL, da kungiyar tarayyar Afirka ta AU, da ma wasu karin hukumomin kasa da kasa suka fara mayar da hankali kan yanayin jin kai da ake ciki a birnin na El Fasher, suna masu Allah wadai da muggan ayyukan da ake aikatawa kan fararen hula. Game da hakan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a Litinin din nan, yayin taron manema labarai cewa, Sin na Allah wadai da duk wasu ayyuka dake illata fararen hula, tana kuma fatan Sudan...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 19, Sun Ƙwato Makamai A Kano November 3, 2025 Manyan Labarai Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka Ga Nijeriya: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yaba Wa Kwankwaso November 3, 2025 Manyan Labarai Kano Ta Amince Da Naira Biliyan 8.2 Don Ayyukan ilimi, Samar Da Ruwa, Da Makamashi November 3, 2025
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas ta ayyana ɗan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, a matsayin wanda take nema ruwa a jallo. Wannan mataki da rundunar ta ɗauka na zuwa ne bayan zargin Sowore da yunƙurin ta da zaune tsaye da kawo hargitsi da sunan zanga-zanga a Jihar Legas. Kano Pillars ta koma ƙarshen teburin Gasar Firimiyar Nijeriya An rantsar da Samia Suluhu Hassan a wa’adin mulki na biyu a Tanzaniya Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Olorundare Jimoh, ya bayyana cewa tun da fari rundunar ta gargaɗi Sowore kan kada ya jagoranci wata zanga-zanga da aka gudanar kan wani rusau da hukumomi suka gudanar a yankin Oworonshoki na jihar. Sai dai rundunar ta bayyana cewa Sowore ya yi...
A ranar Litinin jami’an tsaro da dama sun hallara a hedikwatar jam’iyyar PDP da ke Abuja yayin da Abdulrahman Mohammed Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Kasa (Arewa ta Tsakiya), ya yi ikirarin cewa, ya karɓi mukamin Muƙaddashin Shugaban Jam’iyyar na Kasa a yayin da rikicin shugabancin Jam’iyyar ke kara tsananta. Kwamitin gudanarwar jam’iyyar na ƙasa (NWC) da ke ƙarƙashin jagorancin Samuel Anyanwu ne ya naɗa Mohammed a matsayin muƙaddashin Shugaban Jam’iyyar na ƙasa bayan sauke Umar Damagum, da Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba, a matsayin wani mataki na adawa da NWC da Damagum ke jagoranta suka yi a baya. Kafin isa sakatariyar PDP da ke Wadata Plaza, Mohammed da magoya bayansa sun taru a ofishin jam’iyyar na...
Kwankwaso, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na NNPP a zaben 2023, ya fitar da wata sanarwa mai karfi yana gargadin cewa kalaman Trump na iya kara ruruta wutar rikicin addini da kuma kara ta’azzara rashin tsaro a kasar. A shafinsa na X, tsohon gwamnan ya yi Allah-wadai da matakin Trump na ayyana Nijeriya a matsayin “kasar da ke da matukar damuwa,” wanda kuma ya yi zargin ikirarin “kisan kare dangi ga Kiristoci.” Kwankwaso, ya yi kira ga Amurka da ta taimaka wa Nijeriya da tallafin fasaha da leƙen asiri maimakon barazana, sannan ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta zurfafa hulɗar diflomasiyya ta hanyar naɗa wakilai na musamman domin tattaunawa. “Ga ‘yan uwana ‘yan ƙasa,...
Daga Aminu Dalhatu Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa Shugaban Karamar Hukumar Gusau, Alhaji Abubakar Imam, bisa shirin tallafawa jama’a domin dogaro da kai da kuma inganta rayuwarsu. Ta yi wannan yabo ne yayin bikin kaddamar da kayan tallafi a Gusau, babban birnin jihar Zamfara. Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta bayyana cewa, kayayyakin da aka raba sun haɗa da motoci, babura, injinan dinki, injinan niƙa, keken guragu, kayan abinci da kuma tallafin kuɗi a fadin ƙaramar hukumar. Ta bayyana shirin a matsayin abin yabo da ke tallafawa iyalai, wanda ke karfafa dogaro da kai, tare da rage matsin tattalin arziki a tsakanin al’umma. Uwargidan Gwamnan ta taya waɗanda suka amfana da shirin...
Daga Aliyu Muraki Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta Kasa reshen Jihar Nasarawa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya Lafia ta bi umarnin ƙungiyar ta ƙasa wajen shiga yajin aiki na ɗindindin. Wakilinmu wanda ya ziyarci asibitin koyarwar, ya bayar da rahoton cewa likitocin sun bar wuraren aikinsu domin matsin lamba ga gwamnatin tarayya ta biya dukkan hakkokinsu da ke karuwa zuwa biliyoyin naira. A yayin ziyarar, ya ruwaito cewa nas nas da ungozoma ne kawai ke kula da marasa lafiya, musamman a sashen bada kulawar gaggawa, inda suke ƙoƙarin taimaka wa waɗanda ke cikin mawuyacin hali, yayin da ake tura waɗanda lamuransu ke neman kulawar likitoci zuwa wasu asibitoci domin samun kulawar gaggawa. Haka zalika su ma likitocin ...
“Wannan yajin aikin yana nan yana gudana, har sai an biya duk buƙatunmu mafi ƙaranci,” in ji shi. NARD ta fara yajin aiki na sai baba-ta-gani a duk faɗin ƙasar a ranar Asabar, 1 ga Nuwamba, 2025, bayan abin da ta bayyana a matsayin gazawar gwamnati na cika jerin “mafi ƙanƙancin buƙatunta.” Wannan matakin dai tuni ya riga ya kawo cikas ga ayyuka a asibitoci mallakar gwamnatin tarayya da na jiha a faɗin ƙasar. A halin yanzu, Ma’aikatar Lafiya da Jin Daɗin Jama’a ta Tarayya, a cikin wata sanarwa da Shugaban Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Alaba Balogun ya fitar, ya nace cewa, gwamnati ta saki kuɗaɗe kuma tana ci gaba da haɗin gwiwa da ƙungiyoyin...
Daga Usman Mohammed Zaria Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu, Injiniya (Dr.) Muhammad Uba, ya yaba wa Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, bisa amincewa da sabbin ayyukan gina hanyoyi a fadin jihar, ciki har da na Birnin Kudu. Ya ce wannan mataki na cikin ajandar gwamnati 12, musamman wajen inganta ci gaban ababen more rayuwa. A cewarsa, Birnin Kudu za ta amfana da gina hanyoyi masu tsawon kilomita 113, wanda ya hada da hanyoyin kauyuka da wadanda ke hada al’umma da sauran sassan jihar. Dr. Uba ya bayyana aikin a matsayin babban ci gaba wajen saukaka zirga-zirga, inganta harkokin tattalin arziki da samun sauki ga muhimman ayyuka ga jama’a. Ya bayyana tabbacin cewa za a dade ana cin moriyar aikin...
Wani magidanci, Malam Jibrin Rabi’u, ya bayyana yadda matarsa, Khadijat Ado, ta ɓace a gidansu da ke unguwar Life Camp a Abuja a ranar Alhamis da ta gabata, sannan kuma aka gano ta a Sakkwato washegari. Ya shaida wa wakilinmu da yammacin Lahadi, cewa ya dawo gida a ranar Alhamis, sai ya tarar da matarsa ba ta nan. Malam Jibril ya ce, ya kira wani abokinsa ɗan sanda, wanda ya sanar da ofishin ’yan sanda na Life Camp, Gwarinpa da sauran sassan yankin bayan bincike na farko ya gagara gano inda take. A cewarsa, na’urar CCTV da ke gidansu ta nuna yadda matarsa ta fita daga gidan cikin natsuwa, har sai da ta fita daga inda kyamarar ke iya ɗauka....
A wata hira da kafar watsa labarai ta iran press ta yi da jagoran harkar musulunci a najeriya shaikh Ibrahim zakzaki yayi tir da ci gaba da kashe mutane da ake yi a kasar sudan inda kungiyar RSF ta kasashe sama da mutane 2000 a garin el-fishar, ya zargi kasar hadaddiyar daular larabawa da ruruta wutar yaki a madadin kasashen masu girma na duniya. Yakin basasar dake ci gaba da gudana a kasar sudan ya dauki mummunan yanayi yayin da kungiyoyin masu samun goyon bayan kasashen waje ke kara kai hare-hare kan fararen hula da basu ji ba basu gani ba, bayanan na shaikh zakzaki sun kara haskaka yanayin siyasar da ke mayar da kasashen afrika fagen yaki don rarrabasu,...
Kwankwaso ya kuma buƙaci gwamnatin Tarayya da ta ƙarfafa hulɗar diflomasiyya da Amurka ta hanyar naɗa jakadu na musamman da kuma jakadun dindindin domin kare muradun Nijeriya a matakin ƙasa da ƙasa. “Ya kamata gwamnatin Nijeriya ta naɗa jakadu na musamman da kuma jakadun dindindin domin wakiltar muradunmu yadda ya kamata a kasashen waje,” in ji shi. A ƙarshe, yayi kira ga ƴan Nijeriya da su zauna cikin haɗin kai da juriya, yana mai cewa lokaci ne da ya kamata a fifita zumunci fiye da rarrabuwar kai. “Yan uwa ƴan Nijeriya, lokaci ne da muke buƙatar haɗin kai fiye da komai. Allah ya taimaki Nijeriya,” in ji Kwankwaso. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba November 2, 2025 Manyan Labarai 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su November 2, 2025 Manyan Labarai Wadi Al-Salam: Maƙabartar Musulmai Mafi Girma A Duniya November 2, 2025
Allah Ya yi wa fitaccen jarumin Kannywood, Mato Na Mato, wanda aka fi sani da Malam Nata’ala a cikin shirin Dadin Kowa rasuwa. Wannan na cikin wani saƙo da fitacciyar marubuciya, Fauziyya D. Sulaiman ta wallafa a shafinta na Facebook a daren ranar Lahadi.
Shugaba Xi ya kara da cewa, a halin da ake ciki yanzu, duniya na fuskantar sauye-sauye irin wadanda ba a taba gani ba kuma cikin sauri. Don haka, kamata ya yi kasashen biyu masu dadaddun wayewar kai su zurfafa koyi da juna, da shigar da sabon kuzari cikin gina cikakken salon hadin kai, bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu, kana su tattaro karfin wayewar kai don gina al’umma mai makomar bai daya ga dukkanin bil’adama. A wani ci gaban kuma, wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping wato ministan raya al’adu da yawon bude ido na kasar Sun Yeli, ya halarci bikin bude babban gidan adana kayan tarihin na GEM bisa gayyatar gwamnatin Masar. Kafin bikin, shugaba al-Sisi ya...
A 2022, kasashe shida ne suka daina yanke hukuncin kisa, ko dai gaba daya ko kuma wani bangare. Hudu daga cikinsu; Kazakhstan, Papua New Guinea, Saliyo, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, sun jingine shi kwatakwata. Ekuatorial Guinea da Zambia sun ce za a rika amfani da shi ne kawai kan laifuka mafiya kololuwar muni. A watan Afrilun 2023, majalisar dokokin Malaysia ta kada kuri’ar daina amfani da shi a matsayin tilas kan laifuka 11, ciki har da kisa da kuma ta’addanci. Majalisar dokokin Ghana ma ta kada kuri’ar soke hukuncin kisa a watan Yulin 2023. Wadanne kasashe ne suka fi yanke hukuncin kisa? Kasashe 20 ne suka zartar da hukunbcin kisa a 2022, idan aka kwatanta da 18 da suka...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik November 2, 2025 Daga Birnin Sin An Bude Sabon Babin Huldar Sin Da Koriya Ta Kudu November 2, 2025 Daga Birnin Sin Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya November 1, 2025
Ga yadda ake hada Fab biskit (wani irin biskit mai dandanon madara da sukari, mai taushi da dan kamshi kamar na “shortbread”). Da farko za ki samu roba haka sai ki zuba sukari da Bota, ki cakuda su da cokali ko maburkaki har sai sun hade jikinsu kuma sun yi laushi. Sannan ki fasa kwai a ciki, ki zuba filaibo, ki ci gaba da cakudawa. A wani kwano ko robar daban, ki hada fulawa, bakin fauda, madara, da dan gishiri. Sai ki zuba wannan hadin a cikin wancan kayan da kika fara hadawa. Ki gauraya su sosai har sai ya zama kullu mai laushi, ba mai taurin gaske ba. Idan ya yi tauri, ki kara dan madarar ruwa ko dan...
An ture Mataimakin Gwamna Gefe, Tsarin karba-karba Na Goyon Bayan Kwara ta Arewa. Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazak, zai kammala wa’adinsa na biyu a shekarar 2027, amma babu wata alamar cewa mataimakinsa, Mista Kayode Alabi, zai gaje shi. Yanayin siyasa a jihar na nuna cewa yankin Sanatocin Kwara Arewa ne ake sa ran zai samar da gwamna na gaba; Alabi yana daga Kwara Kudu. Kwara ta Arewa ba ta samar da gwamna da tun daga 1999, yayin da Kwara Kudu ta rike kujerar siyasa ta farko a jihar na tsawon shekaru takwas, kuma zuwa 2027 Kwara Tsakiya za ta kasance ta rike kujerar na shekaru 20. Masu nazarin siyasa guda biyu, Comrade Abdul-Rahoof Bello-Labelabe da Comrade AbdulLateef Ishowo, sun bayar...
Manajar ofishin na NIWA, da ke a jihar ta Legas Injiniya Sarat Braimah ta bayyana cewa, tura ma’ikatan hukumar domin yin aikin, zai taimaka wajen gudanar da aikin a cikin inganci. Kazalika, ya sanar da cewa, hakan zai kuma bayar da damar yin safarar kaya a cikin sauki da kuma safarar matafiya da ke bin hanyar ruwa ta yankin na Ikorodu. “Mun yi nazari a cikin kwanciyar hankali kan yadda za a tabbatar da an cire fulawar da ke a cikin kasan ruwan ba tare da wata miskila ba tare da kuma bai wa jiragen ruwan damar yin zirga-zirgarsu a hanyoyin ruwan, ba tare da wata matsala ba, “ Inji Injiya Braimah. “ Aikin ya wuce batun fannin samar da...
A yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan kalaman Shugaban Amurka Donald Trump da ke zargin gwamnatin Nijeriya da watsi da batun kisan Kiristoci a ƙasar, Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta bayyana cewa ta fara shirin kai farmaki a Nijeriya. Sakataren Ma’aikatar, Pete Hegseth, ne ya tabbatar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, yana mai cewa ma’aikatarsa “na shirye-shiryen ɗaukar mataki” bayan umarnin da Trump ya bayar. Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan Tinubu zai gana da Trump kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya “Muna shirye-shirye don ɗaukar mataki a Nijeriya. Idan gwamnatin Nijeriya ba ta kare Kiristoci ba, za mu kai hari, mu kawar...
Majiyar ta kara da cewa, bayan yunkurinsu bai yi nasara ba a Tsanyawa, maharan sun sake wani sabon shiri, inda suka kai hari a kauyen Yar Tsamiya da ke gundumar Faruruwa, karamar hukumar Shanono, da misalin karfe 1:30 na dare, inda suka kashe mutane uku suka, tare da sace wasu uku. Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima November 1, 2025 Manyan Labarai Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori November 1, 2025 Manyan Labarai Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da...
Rahotanni da muka samu sun nuna cew wasu yan ta’adda sun kashe wasu dakarun sa kai guda biyu a kudu masu gabashin iran a yankin sisitan Baluchistan. Jami’In huda da jama’a na dakarun kare juyi yayi karin harke game da harin da aka kai, yace an kashe mutane ne yayin da suke kokarin ketare da jami’an tsaro suna tafiya akan babbar hanyar da ta hada birnin kashsh dake lardin da kuma babban birnin zahidan An bayyana cewa wanda abin ya shafa sun hada da Esma’il shavarzi da kuma mukhtar shahouze da kuma wadanda suka samu mummuan rauni a lokacin kai harin Lardin sistan baluchestan na da iyaka da kasar Pakistan da ya dade yana fuskantar tashe tashen hankula kan fararen...
Bug da kari Tinubu ya jinjina wa Shugaban jami’ar, Farfesa Wahab Olasupo Egbewole (SAN)da ‘yan tawagarsa wajen maida hankalin da suka yi na bunkasa Jami’ar da kumna kudurinta na muradun ci gaban da ake bukata. Shi ma anashi jawabin Shugaban Jami’ar Sarkin Katsina, Alhaji. Abdulmumin Kabir Usman, wanda Wazirin Katsina, Sanata Ibrahim Idah ya wakilta, ya nuna jin dadinsa kan irin kokarin da UNILORIN saboda bunkasar ilimi da kumasamar wuraren koyon kaaratu masu kyau da kuma suka dace. Ya yi ma kallon ayyukan da ak kaddamar a matsayin“ irin abubuwan da ake bukatar gani ke nan”da za su taimakawa lamarin koyarwa, koyo,da kuma bincike, inda ya kara da cewa yadda Jami’ar ta maida hankalinta wajen bunkasa dabarar koyon yin abubuwa...
Wannan mataki ne awanni kaɗan bayan ɓangaren Damagum ya dakatar da Anyanwu da wasu mutane uku, lamarin da ya ƙara ta’azzaea rikicin shugabanci a cikin jam’iyyar PDP. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami November 1, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su November 1, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Martani Kan Iƙirarin Trump Na Kisan Ƙare Dangi Ga Kiristoci November 1, 2025
Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
Ya ce Sin tana maraba da kamfanonin dake fuskantar kalubale su tuntubi ma’aikatar ko hukumomi masu ruwa da tsaki, yana cewa, ma’aikatar za ta nazarci ainihin abubuwan dake faruwa da kuma bayar da damar fitar da kayayyaki ga wadanda suka cancanta. (Mai fassara: FMM) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya November 1, 2025 Daga Birnin Sin Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar November 1, 2025 Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung November 1, 2025
Jagoran ‘yan hamayyar siyasar kasar Kamaru Issa Chiroma Bakary ya kira yi magoya bayansa da su dakatar da dukkanin harkoki domin a tsayar da kasar wuri a matsayin ci gab da nuna kin amincewa da sakamamon zabe. A can garin Marwa dake a matsayin babban birnin Arewacain kasar,dukkanin harkokin yau da kullum sun tsaya kacokau. Wani dan kasuwa ya bayyana cewa, rufe kasuwa a wurinsu abu ne mai wahala,amma za su yi ne saboda tsoron kar a kona musu shaguna. Haka nan kuma ya ce, kasuwar ma ta tsaya cak saboda babu masu saye da suke zuwa. Da akwai garuruwa da dama da su ka zama kango, saboda kaurewa harkokin yau da kullum da mutane su ka yi a ci...
Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta sanar da cewa daga lokacin da aka tsayar da wuta zuwa yanzu adadin Falasdinawan da HKI ta kashe sun kai 200, yayin da wasu kusan 600 sun jikkata. Sanarwar ta ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta kuma ci gaba da cewa; A cikin sa’o’i 48 da su ka gabata,an sami shahidai 22, biyar daga cikinsu basu dade da yin shahada ba, sai kuma 17 da aka tono su daga karkashin baraguzai. Haka nan kuma na kai wasu 9 zuwa asibitocin da suke a yankin. Wani sashe na sanarwar ma’aikatar kiwon lafiyar ta Gaza ya ce, har yanzu da akwai shahdai masu yawa da suke a karkashin baraguzai, wasu kuma a kan hanyoyi, saboda rashin...
Shugaban kasar Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya fada wa Shugaban Amurka Donald Trump cewa; a Nigeria ba a lamunta da duk wani rikicin addini. Shugaban na kasar Najeriya ta mayar wa da Tinubu martani ne saboda yadda ya bayyana Najeriya a matsayin kasa mai jawo damuwa ta musamman”, bisa zargin cewa Mabiya addinin kiristanci suna fuskantar barazanar karewa, ya kuma yi alkawalin cewa Amurkan za ta ba su kariya. Donald Trump ya ce; Kiristoci suna fuskantar barazanar karar da su a Nigeria, an kuma kashe dubban kiristoci a kasar.” A yau Asabar, kwana daya daga wancan zancen na Tinibu ne dai shugaban kasar ta Nigeria Bola Ahamd Tinubu mayar da martanin da ya kunshi cewa: Nageria kasa ce ta Demokradiyya,...
Ofishin kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ce, an harba kumbon Shenzhou-21 mai dauke da ‘yan sama jannatin kasar Sin 3 cikin nasara, a daren jiya Juma’a, agogon Beijing. Daga baya kumbon ya sarrafa kansa wajen hade jikinsa da na tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, ta yadda ‘yan saman jannatin suka shiga tashar, inda tsoffin ‘yan saman jannati 3 da suka dade a cikin tashar, suka yi musu maraba. Hakan ya shaida haduwar sabbi da tsoffin ‘yan sama jannatin kasar Sin karo na 7 a tashar binciken sararin samaniya ta kasar. Bisa shirin da aka yi, wadannan ‘yan sama jannati 6 za su kwashe kimanin kwanaki 5 suna aiki tare a cikin...
A wannan rana, a gun taron manema labarai da aka gudanar bayan kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC, Lee Jae-myung ya ce hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Sin da Koriya ta Kudu yana da matukar muhimmanci, ya kuma yi imanin cewa birnin Shenzhen na kasar Sin zai karbi bakuncin kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC cikin nasara a shekara mai zuwa.(Safiyah Ma) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik November 1, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka October 31, 2025 Daga Birnin Sin Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu...
Daga Abdullahi Shettima Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya wakilci Nijeriya a taron ƙoli na biranen Asiya da ya gudana a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), inda ya gabatar da kudirorin sauyin ci gaban Kaduna. Taron ya samu halartar manyan baki daga ƙasashe sama da 150, ciki har da gwamnoni, shugabannin birane da jagororin kasuwanci daga Asiya, Fasifik, Turai da Afirka. Taken taron shi ne “Haɗin Gwiwa. Ƙarfafawa. Sauyi.” A jawabinsa mai taken “Gina Haɗin Gwiwa Domin Ci Gaban Kowa,” Gwamna Uba Sani ya bayyana yadda Kaduna ke samun nasara a fannoni da dama kamar gyaran birane, bunƙasa noma da tallafawa jama’a. Ya ce tsarin ci gaban jihar yana dogara ne kan faɗaɗa damar tattalin arziki, kare marasa ƙarfi,...
A wani bidiyo daban da PUNCH Metro ta gani a Facebook, wanda Mc Pee ya wallafa, wani mutum da ake zargin dalibi ne na jami’ar ya bayyana abin da ya faru. A cewarsa, marigayin ya roki a bar shi ya rayu kafin daga bisani wanda ake zargin ya kashe shi. Ya ce: “Nanpon ya riga ya yanke Peter a kumatunsa yayin da yake rokon a bar shi. Lokacin da muka shiga tsakani muka ce ya daina, sai ya yi barazanar yanka duk wanda ya kusanto shi. “Da Peter ya ga ba ya sauraron rokonsa, sai ya rungume shi yana rokonsa da kuka. “Mun fita neman taimako amma babu wanda ya amsa mana. Da Peter ya yi kokarin tserewa sai ya...
Daga Usman Muhammad Zaria Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar. Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya karɓi sabbin motoci 10 kirar Toyota Hilux da Gwamna Umar Namadi ya bai wa rundunar a Dutse, babban birnin jihar. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, CP Dahiru Muhammad ya yaba da jajircewar Gwamna Umar Namadi wajen tallafa wa hukumomin tsaro domin sauke nauyin da ke kansu a jihar....
Daga Usman Muhammad Zaria Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar. Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya karɓi sabbin motoci 10 kirar Toyota Hilux da Gwamna Umar Namadi ya bai wa rundunar a Dutse, babban birnin jihar. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, CP Dahiru Muhammad ya yaba da jajircewar Gwamna Umar Namadi wajen tallafa wa hukumomin tsaro domin sauke nauyin da ke kansu a jihar....
Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’ar nuna goyan baya ga wani kudiri da ya jaddada cewa shirin da Morocco ta gabatar kan Yammacin Sahara shi ne mafita ‘’mafi dacewa” ga yankin da ake takaddama a kai. Kudirin ya nuna goyan bayan kasashe mambobin kwammitin ga shirin na Morocco, tare da bayyana cewa ikon masarautar kan yankin zai iya kasancewa mafita mafi dacewa. Kan hakan ne kwamitin yaya kira ga Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres da wakilinsa na musamman kan wannan batu, Staffan de Mistura, da su gudanar da tattaunawa “bisa ga” wannan shirin don cimma yarjejeniya da kowa zai aminta da ita. Aljeriya wacce ta ke kaddama da Morocco kan yankin ta kaurace kada...
Harkokin siyasa na Kudancin Kaduna ya dauki wani salo yayin da dan majalisar da ke wakiltar mazabar Jema’a/Sanga a majalisar tarayya, Hon. Dan Amos, ya sanar da komawarsa jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar PDP, yana mai cewa ya dauki wannan mataki ne domin ya hada kai da gwamnatocin jiha da na tarayya don cigaban yankin. Yayin da yake jawabi ga manema labarai a Kafanchan kafin karbar sa a hukumance tare da Sanata Marshall Katung, Amos ya bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan dogon shawarwari da aka yi da shugabannin al’umma, kungiyoyin addini, kwararru da kuma sarakunan gargajiya a fadin mazabarsa. Ya ce jam’iyyar PDP, wacce a da take da karfi sosai a Kaduna, ta ragu saboda rikice-rikicen cikin...
Shugaba Samia Suluhu Hassan, wadda ke neman wa’adin ta na farko a hukumance bayan ta gaji marigayi John Pombe Magufuli a 2021, ta tsaya takara ƙarƙashin jam’iyyar CCM mai mulki. Sai dai rashin shigar manyan ‘yan adawa da aka hana tsayawa ko aka daure ya jefa shakku kan ingancin zaɓen da aka gudanar, inda masu zanga-zanga suka yi kira da a kafa gwamnatin riƙon ƙwarya da zai shirya sahihin zaɓe a gaba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3 November 1, 2025 Manyan Labarai Yadda Gwamnatin Tarayya Ta Dakile Yaɗuwar Ɓarkewar Cutar Dabbobi A Jihar Jigawa November 1, 2025 Manyan Labarai Jerin Gwarazan...
Sanata Sunday Marshall Katung, wanda ke wakiltar mazabar Kaduna ta Kudu a majalisar dattawa, ya sanar da hukuncin da ya yanke na komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yana mai cewa wannan mataki ne da ya dace domin inganta aikin wakilci da kuma tabbatar da ƙarin haɗin kai ga al’ummar mazabarsa. A cikin wata sanarwa mai taken “Sabon Babin Rayuwa: Saƙon Haɗin Kai da Manufa Ɗaya,” Sanata Katung ya bayyana cewa wannan shawara ta biyo bayan dogon shawarwari da aka yi da mazauna mazabarsa, jagororin siyasa, iyalansa da abokan aikinsa. Ya ce, “Wannan sauyin matsayi yana fitowa ne daga niyyar gaskiya ta yin wa mutanenmu hidima cikin inganci, da tabbatar da cewa muryarmu tana da ƙarfi kuma ana jin ta...
A wani rahoto da miami herald ya wallafa a jiya jumaa ya nuna cewa kasar Amurka na shirin kaiwa kasar Venuzuwela hare hare, yayin da Donald trump shugaban kasar Amurka yake musantawa cewa babu wani shiri na daukar matakin soji a kasar ta latin Amurka. Yace gwamnatin trump ta yanke shawarar kai hari kan wasu wuraren soji a kasar, a kowanne lokaci. Yace duk da yakin da washington ke yi kan miyagun kwayoyoi gwamnatinsa ba ta la’akari da kai hare-haren sojin kan venuzuwela yana nuna a akwai karo da juna a kalamansa na makon da ya gabata Da manema labarai suka tambayeshi ko hare-haren da Amurka takai a yan kwanakin nan kan jiragen ruwa a yankin karebiya da aka ce...
A cewarsa, ta hanyar wadannan shirye-shirye, kasar Sin ta nuna goyon baya mai dorewa ga kasashe masu tasowa kuma tana ba da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban duniya a karkashin tsarin hadin gwiwar kasashe masu tasowa. (Abdulrazaq Yahuza Jere) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace October 31, 2025 Daga Birnin Sin Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC October 31, 2025 Daga Birnin Sin Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare October 31, 2025
“Amurka ba za ta tsaya kawai tana kallo ba yayin da irin waɗannan ta’addancin ke faruwa a Nijeriya da sauran ƙasashe. “Mun shirya, muna da ƙarfi da niyyar kare Kiristoci a faɗin duniya,” in ji Trump. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano October 31, 2025 Manyan Labarai Makarantar Kogi Poly Ta Bankaɗo Masu Ƙirƙirar Takardun Kammala Karatu na Bogi October 31, 2025 Manyan Labarai Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar October 31, 2025
Ya kuma bayyana cewa kasar Sin wuri ne mai kyau ga harkokin zuba jari ga ‘yan kasuwa na duniya. Ya ce hadin gwiwa da kasar Sin yana nufin hadin gwiwa da damammaki, imani da kasar Sin yana nufin imani da kyakkyawar makoma, zuba jari a kasar Sin yana nufin zuba jari mai riba ta dogon zango.(Safiyah Ma) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare October 31, 2025 Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi October 31, 2025 Daga Birnin Sin An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da...
Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da fasinjoji a cikin wasu motocin bas Toyota guda biyu a titin Itobe zuwa Ajegwu-Anyigba a Ƙaramar hukumar Ofu ta jihar Kogi. An samu rahoton cewa, lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 5 na asubahi a tsakanin ƙauyukan Ojiwo’-Ajengo da Mamereboh da ke kan babbar hanyar. Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai Kotu ta dakatar da babban taron PDP na ƙasa An ce masu garkuwa da mutanen sun yi amfani da wata tirela da aka kama wajen tare hanyar bayan shingen binciken jami’an tsaro, da ke kusa da wurin da lamarin ya faru. Shedun gani da ido sun ce...
A jawabinsa yayin taron, Gwamna Sani ya gabatar da kasida mai taken: “Gina Haɗin Gwiwa Domin Ci Gaban Kowa”, inda ya bayyana yadda Jihar Kaduna ke ci gaba da samun nasara a fannoni da dama kamar gyaran birane, bunƙasa noma, da tsarin tallafiwa jama’a. Gwamnan Ya ce tsarin ci gaban jihar yana dogara ne kan faɗaɗa damar tattalin arziki da kare marasa ƙarfi, da ƙarfafa jama’a su samu nasara a rayuwarsu. Gwamna Uba Sani, ya kuma halarci shirin baje koli na birnin Dubai mai taken : “Sauya Arewa a Nijeriya: Jagoranci, Ƙirƙira, da Tasirin Zamantakewa”, inda nan ma ya jaddada cewa jagoranci mai nagarta da amfani da fasaha a mulki suna da matuƙar muhimmanci wajen buɗe damarmaki ga...
Sai dai don neman cimma burinta na “sake mayar da kasar Amurka zakaran gwajin dafi”, kasar Amurka ta sha daukar matakai na dakile ci gaban kasar Sin, ciki har da katse huldar tattalin arziki da ita da ma sanya takunkumai ga kamfanoninta masu ci gaban kimiyya da sauransu, duk da hakan, kasar Sin ta kiyaye bunkasar tattalin arzikinta yadda ya kamata, har ma karuwar tattalin arzikinta ta kai kaso 5.2% a cikin watanni tara na farkon bana, lamarin da ya shaida inganci da juriya na tattalin arzikin kasar. A kwanan nan, kasar Sin ta zartas da shawarwarin da aka gabatar game da tsara shirin raya tattalin arziki da zaman al’umma cikin shekaru biyar masu zuwa, kuma bisa ga shawarwarin, za...
Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Ƙulla Alaƙa Ta Kut-da-kut Tsakanin Hukumar Shige Da Fice Da Kwastam – Babandede
“Iyakar kasa ba wai kawai yanki ne na tsaro ba. Yanki ne na al’adu; yanki ne na tarihi; haka nan ma yanki ne na tattalin arziki. Kula da shige da fice na da matukar amfani ga ci gabanmu. Wajibi ne Nijeriya ta zuba jari a kan kula da nau’in mutanen da take tacewa wajen shiga kasa da kuma irin mutanen da muke tacewa wajen fita daga kasa. “Dole ne mu yi nazarin nau’in ayyukan da bakin-haure ke yi da kuma yadda suke shafar tattalin arzikinmu. Muna bukatar tsame mutanen da ke kawo cikas ga ci gabanmu”, in ji Babandede. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki October 31, 2025 Labarai...
Sudan ta yi kira ga Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya da ya sanya rundunar Rapid Support Forces (RSF) a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda bisa ga ka’idojin yaki da ta’addanci na duniya, sannan ya dauki mataki a kan duk wanda ya yi mu’amala da ita, ko ya samar mata da makamai da sojojin haya, ko jiragen sama marasa matuki, ko kuma kasar da ta bar ta ta tsallaka iyakokinta. A cikin wata sanarwa da ya fitar a lokacin zaman gaggawa na Kwamitin Tsaro don tattauna yanayin da ake ciki a Sudan, Wakilin dindindin na Sudan a Majalisar Dinkin Duniya, Al-Harith Idris, ya bukaci Majalisar da ta yi Allah wadai da kisan kiyashin da ‘yan bindigar RSF, sojojin haya na kasashen waje,...
Gwamna Inuwa ya kuma jaddada bukatar bin ka’idojin kariya a harkokin sufurin ruwa, inda ya yi kira ga shugabannin kananan hukumomi, da shugabannin al’umma, da direbobin kwale-kwale da hukumomin da ke da ruwa da tsaki da sauran wadanda suka dace su kara kaimi wajen ganin ana kiyaye duk ka’idojin kariya don magance sake afkuwar ibtila’in a nan gaba. Ya umurci Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jiha (SEMA) da Majalisar. Karamar Hukumar Nafada su bayar da duk wani tallafin da ya dace ga iyalan da abin ya shafa tare da hada hannu da hukumomin da abin ya shafa don inganta tsaro da wayar da kan al’ummomin da ke yankunan kogi. Gwamna Inuwa Yahaya ya yi addu’a yana mai cewa “A madadin...
“A lokacin, mun yi lissafin adadi a Babban Bankin. Na tashi na kafa sharuda bisa ga ka’idodi, inda na ce a cire tallafin yau. Farashin kaya zai tashi daga kashi 11 zuwa kashi 13, zan rage shi a cikin shekara guda. Ba za mu samu hauhawar farashin kaya na kusan kashi 30 ba,” in ji shi. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Allah Ya Kai Manzon Allah (SAW) Muƙami Na Babban Yabo A Cikin Komai October 31, 2025 Manyan Labarai Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP October 31, 2025 Manyan Labarai Matsalar Talauci Da Rashin Tsawon Rai Da ‘Yan Nijeriya Ke Fuskanta October 31, 2025
Idan ka duba tarihin duniya gabadaya da tarihin annabawa, tarihi ne na wayewar duniya tun daga Annabi Nuhu (S.A.) har zuwa Manzon Allah (S.A.W.) kamar duniya tana ‘yar makaranta ce ta fara da Nazare, ta zo Firamare zuwa Sakandire har zuwa Jami’a, sannan aka yaye ta, yanzu da zuwan Manzon Allah an yaye duniya, yanzu duniya ba ta bukatar sai an aiko annabi, ba ta bukata sai an aiko ma’aiki, a’a wanna abu da Manzon Allah ya zo da shi za mu iya kafa dalili da shi mu shirya kanmu ba sai da annabi ba. Wannan abu da Manzon Allah ya zo da shi yanzu ya kafa dalili da shi, da shi muka karantar da kanmu ba sai da Annabi...
Shugaba Xi ya kuma bayyana cewa, cikakken zama na 4 na kwamiti na 20 na JKS ya amince da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15. Sin za ta yi amfani da wannan damar don ci gaba da gyare-gyaren tattalin arzikinta, da kuma fadada bude kasuwancinta mai zurfi ga ketare, ta haka za ta ci gaba da ba da sabbin damammaki ga yankin Asiya da Pasifik da sauran kasashen duniya ta hanyar zamanantar da al’ummarta. (Amina Xu) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo October 30, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Fitar Da...
Shugabannin Rundunar tsaro da Tinubu ya sallama sun hada da shugaban rundunar tsaro ta kasa Janar Christopher Musa da shugaban sojojin ruwa, Emmanuel Ikechukwu Ogalla da shugaban sojojin sama Hassan Abubakar. Wadanda suka maye gurbin su da idanu ya koma kan hobbasar kwazon da za su nuna su ne shugaban rundunar tsaro Olufemi Oluyede, shugaban sojojin kasa Waidi Shaibu, shugaban sojojin ruwa Idi Abbas da shugaban sojojin sama S.K Aneke sai kuma shugaban rundunar leken asiri, EAP Undiendeye wanda ya ci-gaba da rike kujerar sa. Yan Nijeriya sun jima suna kukan duk da kwarewa da gogewar jami’an sojojin Nijeriya da irin makuddan kudaden da gwamnati ke kashewa a sha’anin tsaro a kowace shekara amma matsalar kullum gaba- gaba take kara...
Shugaban Lebanon Joseph Aoun ya yi Allah wadai da keta hurumin kasarsa da Isra’ila ke yi a kudancin kasar, yana mai kira da a dauki tsauraran matakai kan duk wani kutse da sojojin mamaye za su yi a nan gaba a cikin Lebanon. A lokacin wata ganawa da Kwamandan Rundunar Soja Rodolphe Heikal, Shugaba Aoun ya bayyana cewa dole ne Lebanon ta “fuskanci duk wani kutse da Isra’ila ta yi wa yankunan kudancin da aka ‘yantar don kare filayenmu da kuma tsaron ‘yan kasa.” Wannan jawabi ya zo ne bayan harin da Isra’ila ta kai wa gundumar Blida, inda sojojin Isra’ila suka kashe wani ma’aikacin gundumar a lokacin wani hari da suka kai kan ginin ofishin karamar hukuma. Daga baya,...
Shugaban Lebanon Joseph Aoun ya yi Allah wadai da keta hurumin kasarsa da Isra’ila ke yi a kudancin kasar, yana mai kira da a dauki tsauraran matakai kan duk wani kutse da sojojin mamaye za su yi a nan gaba a cikin Lebanon. A lokacin wata ganawa da Kwamandan Rundunar Soja Rodolphe Heikal, Shugaba Aoun ya bayyana cewa dole ne Lebanon ta “fuskanci duk wani kutse da Isra’ila ta yi wa yankunan kudancin da aka ‘yantar don kare filayenmu da kuma tsaron ‘yan kasa.” Wannan jawabi ya zo ne bayan harin da Isra’ila ta kai wa gundumar Blida, inda sojojin Isra’ila suka kashe wani ma’aikacin gundumar a lokacin wani hari da suka kai kan ginin ofishin karamar hukuma. Daga baya,...
Madagascar ta sanar da kafa sabuwar gwamnati wadda ta kunshi fitattun ‘yan adawa guda uku a manyan mukamai na ministoci. An gabatar da majalisar ministoci mai mambobi 29, wacce ta kunshi mata 10, a wani biki da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Yavoloha da ke babban birnin kasar, Antananarivo. Shugaban rikon kwarya Michael Randrianireina ya bayyana a lokacin bikin cewa manyan abubuwan da sabuwar gwamnatin ta sa gaba sun hada da yaki da rashin adalci, aiwatar da matakan tsuke bakin aljihu, da kuma samar da yanayin kasuwanci mai dorewa. Ya kara da cewa kowane minista dole ne ya samar da sakamako mai kyau cikin watanni biyu, yana mai gargadin cewa rashin yin hakan a cikin wannan lokacin zai zama gazawa...