2025-09-18@06:59:03 GMT
إجمالي نتائج البحث: 270

«faduwar farashin»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da matakin da kasar Yemen ta dauka na haramtawa jiragen ruwan Isra’ila shiga tekun Bahar Maliya Bayan sanarwar da kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen ta fitar na cewa za ta dawo da haramcin da ta yi wa jiragen ruwan Isra’ila na tsallakawa tekun Bahar Rum, Hamas ta fitar da sanarwa inda ta yi maraba da matakin. ta bayyana wannan mataki a matsayin wanda ke nuna hakikanin matsayin al’ummar Yemen da gwamnatin kasar na goyon bayan gwagwarmayar al’ummar Falastinu. Har ila yau kungiyar ta yi kira ga dukkanin kasashen Larabawa da na Musulunci da kuma ‘yantatun kasashe a duniya da su kara zage damtse wajen matsin lamba ga ‘yan mamaya da magoya bayansu...
    Cikin kasa da wata guda, an yi asarar hannayen jari da darajarsu ta kai dala triliyan 4, inda damuwar da duniya ke da shi kan manufofin haraji na Amurka ke haifar da fargaba a kasuwar hannayen jari ta kasar. Wani nazari da kafar CGTN ta gudanar tsakanin jama’ar duniya masu amfani da intanet ya nuna cewa, mutane na bayyana shakku kan manufofin haraji na sabuwar gwamnatin Amurka, kuma sun damu ainun da mummunan tasirinta kan kasuwar hannayen jari ta kasar dake tafiyar hawainiya. Wani mai bayar da amsa cikin nazarin ya kuma bayyana cewa, sanya haraji kan dukkan kayayyakin kasashen wajen, bai taba haifar da da mai ido ba. A baya bayan nan, shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa,...
    Jami’ar kula da manufofin ketare ta Tarayyar Turai, Kaya Kalas, ta tabbatar da cewa, EU za ta iya sake kakaba takunkumi kan kasar Syria, idan aka samu tabarbarewar lamurra, tana mai nuni da yadda ake cin zarafin fararen hula a gabar tekun Syria. Kaya Kalas ta shaidawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa, “Muna shirye-shiryen mayar da takunkumi kan Syria, idan muka ga tabarbarewar lamurra na ci gaba, inda ta jaddada cewa, dole ne mika mulki ya kasance cikin lumana da kuma hadin kai, kuma dole ne a kare fararen hula a kowane hali.” Ta bukaci dukkan masu ruwa da tsaki na waje da su mutunta hadin kan Syria, da kuma iko da iyakokinta.”
    An gargaɗi mazauna da su kwana cikin shirin daƙile yaɗuwa cutar Sanƙarau a yayin da cututtuka masu alaƙa da ita suka soma bayyana a wasu ƙananan hukumomin Jihar Sakkwato. Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Faruk Umar Wurno ne ya yi wannan gargaɗi haɗi da bayar da shawarar a wani jawabi da ya fitar a ranar Talata. Lakurawa sun kashe mutum 13 a ƙauyukan Kebbi Tsohon shugaban Philippines ya faɗa komar ’yan sanda Kwamishinan ya yi bayanin cewa ya zama wajibi duk wasu alamomi da aka gani a ɗauka a shiga da su ɗakin gwaje-gwaje a bincika domin a tabbatar ko ƙoshin lafiyar al’umma. Dakta Faruk Umar ya ce ma’aikatarsa za ta saka ido kan jami’an lafiya na gwamnati da masu...
    Masana na gargaɗin cewa idan NNPC ta daina sayar wa matatar Dangote mai a naira, hakan na iya haifar da hauhawar farashin man fetur, maimakon rage farashin da ake tsammani. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An haife shi a ranar 21 ga Fabrairu, 1949, kuma ya yi karatu a Jami’ar Ohio da ke Athens a Amurka, a 1981, da Jami’ar Leicester ta ƙasar Birtaniya a 1987.   Ya yi aiki a kamfanin jaridun New Nigerian, da hukumar talbijin ta NTA, da Ofishin Yaɗa Labarai na Amurka (USIS). Haka kuma ya yi koyarwa a Kaduna Polytechnic, ya yi aiki a Bankin Arewa da kuma Bankin Union inda a nan ya yi ritaya a ranar 26 ga Yuni, 2005.   A cikin saƙon ta’aziyyar sa a ranar Asabar, Minista Idris ya bayyana rasuwar Malam Kabir Ɗangogo a matsayin babban rashi ga Nijeriya da fannin sadarwa a nahiyar Afirka.   Ya ce: “Mutuwa ta ƙwace mana ƙwararren ma’aikaci...
    Ofishin jakadancin kasar Sin dake Nijeriya, ya shirya taro domin bikin ranar mata ta duniya da ake gudanarwa a ranar 8 na watan Maris din kowacce shekara. Taron mai taken “Labarinta, Makomarta” wanda ya gudana ranar Juma’a a cibiyar raya al’adu ta kasar Sin dake birnin Abujan Nijeriya, ya hada mata daga dukkan bangarorin rayuwa, inda suka yi waiwaye kan ci gaban da suka samu da ma tsara hanyar tabbatar da daidaiton jinsi.   Da yake jawabi yayin taron, jakadan Sin a Nijeriya Yu Dunhai, ya nanata muhimmancin bikin na wannan shekara kasancewar ya zo daidai da cikar Yarjejeniyar Beijing ta tabbatar da daidaiton jinsi ta MDD, shekaru 30 da kulluwa. A Mai Da Duniya Ta Zama Ta Kasa Da Kasa...
    Damuwar IMF akan kalubalen tattalin arzikin Najeriya yaudara ne – Farfesa Yushau AngoWani masani kan harkokin kudi, Farfesa Yushau Ibrahim Ango, ya ce damuwar da asusun lamuni na duniya IMF ke yi kan kalubalen tattalin arzikin da kasar ke fuskanta a halin yanzu yaudara ce.   Farfesa Yushau Ango ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a Kaduna. Ya kuma jaddada bukatar hukumar ba da lamuni ta duniya IMF ta gabatar da shawarwari masu inganci don magance kalubalen da ke haifar da cire tallafin man fetur, wanda manufofinsa suka yi tasiri.   Masanin harkokin kudi ya bayyana raguwar farashin kayan abinci a matsayin na wucin gadi sai dai idan ba a samar wa manoman kasar...
    Wata koto a nan Tehran ta ci gwamnatin Amurka taran dalar Amurka biliyon $12.6 saboda hana wadanda suke fama da cutar ‘Talamessia” a kasar. Tashar talabijin ta Presstv  a nan Tehran ta ce a shekara ta 2018 ne gwamnatin kasar Amurka ta fice daga yarjeniyar JCPOA ta shirin Nukliyar kasar sannan ta dorawa kasar Iran takunkuman tattalin arziki mafi muni, wanda ya hada da magungunan cutar Talassemia. Labarin ya kara da cewa Kotu mai lamba 55 wanda yake kula da kararraki na kasa da kasa a jiya Laraba ta yanke hukun kan wasu jami’an gwamnatin Amurka wadanda suke da hannun kasi tsaye na wajen dorawa kasar takunkuman tattalin arziki har da magungun wannan cutar. Kafin haka dai masu fama da...
    Wata mummunar gobara ta ƙone shaguna sama da 17 a ɓangaren ’yan teloli da masu hada-hadar kayan abinci a tsohuwar kasuwar garin Gombe. Gobarar, wadda ta fara da misalin ƙarfe 2:00 na dare, ta jefa ’yan kasuwa cikin jimamin asarar dukiya mai tarin yawa da aka kiyasta ta kai miliyoyin naira. Mijina bai hana ni waƙa ba sai dai… – Fa’iza Badawa Ramadan: Abubuwa goma ga ma’aurata Wasu da lamarin ya faru a kan idonsu, sun bayyana cewa gobarar ta bazu cikin sauri, inda ta riƙa laƙume kaya da kadarori kafin ’yan kwana-kwana su iso wurin. Ko da yake ba a tabbatar da musabbabin tashin gobarar ba, amma wasu ’yan kasuwar na zargin cewa matsalar wutar lantarki ce ta haddasa...
    A Talatar nan ne ofishin yada bayanai na majalissar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da takardar bayani game da batutuwan da suka shafi sinadarin Fentanyl. Takardar mai taken “Shawo kan sinadarai masu alaka da sinadarin Fentanyl-Gudummawar kasar Sin.” Ta yi fashin baki game da yadda a ‘yan shekarun baya bayan nan, kasar Sin ke ta kara dora muhimmanci kan matakan shawo kan bazuwar sinadarai dangin Fentanyl, kana take ta karfafa hadin gwiwa da sauran sassan kasa da kasa, wajen dakile bazuwar miyagun kwayoyi, da zurfafa hadin kai da sauran kasashe masu ruwa da tsaki, ciki har da Amurka, wajen shawo kan bazuwar sinadarai dangin Fentanyl, da sinadaran da ake samar da shi daga gare su, inda kuma aka cimma manyan...
    Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Nasarawa da Toto daga Jihar Nasarawa, Honorabul Abdulmumin Ari ya ba da cekin Naira miliyan 45 don biyan kuɗin jarabawar WAEC ga daliban sakandare a mazaɓarsa. Da yake jawabi a wajen taron a garin Keffi, Abdulmumin Ari ya bayyana cewa kimanin shekara biyar ke nan yake aikin agaza wa daliban mazaɓar a duka matakai don cika alkawura da ya yi a baya. Ya ce ya yanke shawarar yin haka ne don tallafa wa iyayen ɗalibai marasa galihu don ba su damar cimma burinsu na samar wa ’ya’yansu ilimin zamani dana addini. Ya ce kawo yanzu ya kashe sama da Naira miliyan 500 a cikin shekara biyar da duka gabata a kan irin wannan aiki....
    Shugabar kasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan ta bayyana a jiya Juma’a cewa, tashar jirgin ruwa ta Tanga da kasar Sin ta inganta yanzu tana jigilar sama da tan miliyan 1.2 na kaya a duk shekara, adadin da ya karu daga jigilar tan 400,000 a kowace shekara. “Habaka tashar ta Tanga ya inganta ayyukanta.” a cewa Hassan a jawabinta ga kasar a karshen ziyararta a yankin Tanga. Tana mai cewa, babban kamfanin gine-gine mallakin kasar Sin wato China Harbor Engineering Compnay, shi ne ya yi aikin inganta tashar ta Tanga. Ta kara da cewa, inganta tashar da aka yi ya kuma samar da ayyukan yi ga matasan yankin, tare da shirye-shiryen mayar da tashar ta zama cibiyar jigilar takin zamani da...
    Ana fargabar cewa wata gobara ta laƙume aƙalla shaguna 100 a Kasuwar Kara da ke Jihar Sakkwato. Gobarar wadda ta tashi tun da Asubahin wannan Asabar ɗin ta shafe sa’o’i 9 tana ta’adi. An raba wa ma’aikatan gona babura 200 a Yobe Yadda farashin kayan abinci ya sauka a kasuwannin Arewa Wani ɗan kasuwar da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce tun da misalin ƙarfe 6:30 amma sai wurin ƙarfe 3:30 na rana aka samu nasarar kashe ta. A cewarsa, gobarar ta yi ta’adi a ɓangaren shagunan masu sayar da abinci da suka haɗa da gero, dawa da masara da shinkafa. Haka kuma, majiyar ta ce wutar ta yi ɓarna a ɓangaren masu ƙyamare da layin maƙera da masu...
    Wata gobara ta sake tashi a fitacciyar Kasuwar Kara da ke Sokoto, wacce aka fi sani da sayar da hatsi da kayan abinci, inda ta cinye gaba ɗaya kasuwar tare da mayar da shaguna da wuraren ajiyar kaya toka. Gobarar ta fara ci ne da safiyar Asabar, inda jami’an kwana-kwana suka yi ƙoƙarin shawo kanta amma ta gagara. Har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba. Turji Ya Ƙaƙaba Wa Ƙauyen Mataimakin Gwamnan Sokoto Da Wasu Biyan Harajin Miliyan 22 Gwamnatin Sokoto Za Ta Kashe Naira Miliyan 998 A Cibiyoyin Ciyarwa Na Ramadan A halin yanzu, masu shaguna da gidaje da ke kusa da kasuwar na kwashe kayansu saboda tsoron sake ɓarkewar wutar. Hukumar kasuwar ba ta samu damar...
    Kakakin Majalisar dinkin MDD Stephane Dujarric ya bada sanarwan cewa yana makaranta a Gaza fiye da 100,000 suka fara karatu a makarantu a yankin a ranar 23 ga watan Fabrayrun da muke ciki. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jami’in MDD yana fadar haka a jiya Alhamis kwanaki huda da fara karatu a yankin na Gaza, bayan tsekon da aka samu saboda yakin da HKI ta dorawa kasar na tsawon shekara guda da watanni. Dujarric ya bayyana cewa a halin yanzu makarantu 165 suka bude kofofin su ga yan makaranta a gaza, kuma ga mafi yawansu wannan shi ne karo na farko da suka shiga aji a cikin watanni 16 da suka gabata. Jami’an gwamnati a Gaza...
    “A karkashin Shugabancin Dantsoho, ya taimaka wajen ganin ana sauke sundukan kayan da aka yo jigilarsu a cikin sauki, musamman a Tashar Lekki wanda hakan ya taimaka, wajen rage cunkso a Tashar.” A cewar Mahukuntan Mullar. Mahukuntan Mullar sun kara da cewa, sun zabo Dantso ne, ganin cewa, shi ne, na farko da aka zaba a mukamin Shugaba na Kungiyar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Gabas da yankin Afirka ta Tsakiya PMAWCA, inda zabarsa, ta kara daga kima da darajar Nijeriya, a fannin harkokin tafiyar da Tashohin Jiragen Ruwa, a yankin. A yayin da yake karbar babbar lambar yabon Mullar Dakta Dantsoho ya bayar da tabbacin cewa, zai kara zage damtse wajen shugabantar Hukumar, daidai da tsare-tsaren Miniatan bunkasa...
    “Mun yi jimamin asarar rai da aka yi, kuma mun yi tattaki zuwa ga iyalan mamacin don jajantawa tare da tabbatar musu da gudanar da cikakken bincike don tabbatar da adalci,” in ji shi.   Don haka, ya bukaci jama’a da su kwantar da hankulansu domin Rundunar tana aiki tukuru don zakulo gaskiyar lamarin tare da tabbatar da daukar matakan da suka dace. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sakamakon wannan ragin da aka samu, yanzu gidan mai na MRS zai sayar da man a jihar Legas a kan naira 860, sai mutanen da suke yankin kudu maso yamma kuma da za su saya a kan naira 870, sai kuma mutanen Arewa da za su saya a kan naira 880, sai mutanen kudu maso kudu da kudu maso gabas da za su saya akan naira 890. Kamfanin ya yi kira ga ‘yan kasuwa da su taimaka wajen ganin sauƙin ya je inda ake bukata, domin an yi ragin ne don sauƙaƙawa al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
    Yayin da aka fara tsinkar tumatari dan rani a Kano da sauran jihohin da ke samar da tumatar a fadin Nijeriya, rahotanni sun bayyana cewa, farashinsa ya fadi sosai fiye da yadda aka yi zato, lamarin da ya jefa manoman cikin damuwa. Binciken da Jaridar Aminiya ta gudanar ya nuna cewa, a halin yanzu, ana sayar da kwando daya na tumatir a kan Naira 3,500, yayin da ake sayar da babban kwando a kan Naira 10,000. 40% na matan Kano sun fuskaci cin zarafi a gida —Shugaban Majalisa Dan kwallon Najeriya ya mutu bayan fadowa daga bene a Uganda Wani manomin tumatir, Isah Bello Abba ya bayyana cewa, wannan yanayi ya sa manoma cikin fargaba saboda sun kashe kudade masu...
      Masu sharhi kan harkokin kudi a Cowry Asset Management suna tsammanin Naira za ta ci gaba da kasancewa kan yadda take a wannan makon, tare da hana matakan hana rugujewar ta a kasuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban hukumar Leken asiri na kasar Iraki Hamid al-Shatri ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iraki ta isar da sako ga sabuwar gwamnatin kasar Siriya dangane da samuwar ragowar mayakan kungiyar yan ta’adda ta Daesh a wasu yankunan kasar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta Nakalto Hamid al-Shatri ya na fadar haka ga kafafen yada labarai a birnin Bagdaza, sannan ya kara da cewa al-amuran tsaro a kasashen biyu suna hade juna ne, don haka dole ne gwamnatocin kasashen biyu su yi aiki tare don ganin bayan wadannan yan ta’adda, masu kafirta musulmi. Kamfanin dillancin labaran INA na kasar Iraki ya nakalto al-Shatri yana fadar haka a taro na 7TH na tattaunawar Bagadaza  a jiya Lahadi. Ya kara da...
    Ana zargin malamin makarantar Aliyu Mustapha Academy da ke Jimeta a Jihar Adamawa kan wuce gona da iri da kuma azabtar da wani ɗalibinsa a dalilin shan mangwaro a lokacin ‘break’ a harabar makarantar. Aminiya ta ruwaito cewa a lokacin da ake tsaka da hutun tara ne malamin yan kama ɗalibin yana shan mangwaro, inda ya lakaɗa wa ɗalibin dukan tsiya. Shaidu sun ce har da naushi malamin ya riƙa yi wa ɗalibin, lamarin da ya sa taron ya ƙuƙƙuje tare da barin sa da tabbai a jikinsa. Malamin yana tsaka da dukan ɗalibin ne mahaifin yaron ya je makarantar domin tabbatar da biyan kudin makarantar ɗan nasa. NAJERIYA A YAU: Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri Har yanzu Najeriya...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da ‘Sayyid Haassan Nasarallah’ shahidin Al-umma’ wanda aka yi jana’izar sa a ranar lahadin da ta gabata. Wanda ni tahir amin zan karanta. A ranar lahadi 23  ga watan Fabrayrun shekara ta 2025 ne aka gudanar da Jana’izar babbsan sakataren kungiyar Hibullah, sayyid Hassan nasaralla, da kuma magajinsa na tsawon kwanaki 6 Sayyid Hashim safiyyuda deen, kafin haka shi ne shugaban majalisar zartarwa na kungiyar Hizbullah.   An haifi sayyid Hassan nasaralla (r ) a ranar 31 ga watan Augustan shekara ta 1960  a wani kauye a kudancin kasar Lebanon, Sayyid ya tashi a cikin gida mai saukin rayuwa, ya fara karatu kamar yadda ko wani...
    Sin: Manufar Zuba Jarin Amurka Na Matukar Kassara Hadin Gwiwar Kasuwancin Kamfanonin Sin Da Amurka
    Kungiyar Hizbullahi ta bayyana cewa: Ba su yarda kasar Lebanon ta mika kai ga haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka ba Mataimakin shugaban majalisar zartaswar kungiyar Hizbullah Sheikh Ali Damoush ya jaddada cewa: Ba zasu amince kasar Lebanon, mai cin gashin kanta ta kasance karkashin dokar haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka a karkashin matsin lamba da barazanar kai hari kan filin jirgin saman Lebanon da sauran muhimman wuraren kasar ba. Sheikh Damoush ya jaddada a cikin hudubarsa ta Juma’a cewa “ya zama wajibi gwamnati ta magance matsalar jiragen Iran zuwa kasar Lebanon, domin wannan batu na farko da na karshe yana da alaka ne da ‘yancin kai da kuma martabar kasar Lebanon, kuma hakan na nuni da kwace ‘yancin matakin da...
    Karamar hukumar Birnin Kudu dake Jihar Jigawa ta ce za ta dauki nauyin dalibai ‘yan asalin yankin su 80 da ke kwalejin Ilmi ta tarayya ta Jama’are a Jihar Bauchi, da kwalejin fasaha ta Dutse da kuma kwalejin fasahar sadarwa ta Kazaure. Shugaban Karamar Hukumar, Dr. Muhammed Uba Builder ya bayyana haka ga manema labarai a Birnin Kudu. Dr Muhammad Uba, yayi bayanin cewar, an zabo mutum uku-uku daga kowace mazaba goma sha daya dake yankin. Yana mai cewar, Karamar Hukumar ta yanke shawarar hakan ne domin bai wa dalibai damar karatu cikin sukuni. Dr Muhammad Uba Builder, ya kara da cewar nan gaba kadan Karamar Hukumar za ta kara zabo wasu daliban dan tafiya manyan jami’o’i dake kasar nan....
    Gwamnatin Tarayya, ta bayyana cewa ba ta shigo da kayan abinci daga ƙasashen waje ba, duk da cewa farashin kayan abinci ya ragu a kasuwanni. Ministan Aikin Gona da Samar da Abinci, Farfesa Abubakar Kyari, ya bayyana cewa, ko da yake gwamnatin ta yi tunanin shigo da abinci a lokacin da farashinsa ya yi tashin gwauron zabo, daga bisani ta janye wannan shawarar. An ƙwace miliyoyin daloli, gidajen da ke da alaƙa da Emefiele Babban mai kai wa Bello Turji makamai ya shiga hannu Ministan ya danganta saukar farashin kayan abinci da ƙoƙarin manoma da suka koma gonaki a daminar bara, wanda ya sa amfanin gona ya yi yawa. Ya kuma buƙaci ‘yan kasuwa da su rage farashi domin jama’a...
    Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja a ranar Laraba, Ogbugo Ukoha, Babban Darakta a sashen rarraba mai tare da adanawa na NMDPRA, ya ce matakin ya biyo bayan karuwar firgicin hadurran da ke tattare da manyan motocin dakon man.   “Kwamitin fasaha na masu ruwa da tsaki ya gana a yau don cimma wasu muhimman kudurori guda 10 da nufin rage karuwar yawan hadurran tankokin mai da ke janyo asarar rayuka,” in ji Ukoha.   An cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa da manyan masu ruwa da tsaki da suka hada da DSS, hukumar kashe gobara ta tarayya, hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), kungiyar masu sufurin mota ta kasa (NARTO), kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas...
    Mutane Da Dama Sun Jikkata Sakamakon Fashewar Wani Abu A Kasuwar Zamfara
    An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labarai da yada labarai na gidan gwamnatin Kano, Sanusi Tofa, ya fitar ranar Talata.   A nasa jawabin, gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatinsa na samar da romon dimokuradiyya da habaka ci gaban zamantakewa da tattalin arziki a jihar.   Ya kuma nuna jin dadinsa da goyon baya da hadin kai da mazauna Kano ke bai wa gwamnatinsa, ya kuma bukace su da su ci gaba da jajircewa kan manufofin gwamnatin.
    Abin ban takaicin shi ne duk wannan hauhawar farashi da karin harajin zai haifar a kan talakawa zai kare, domin kuwa farashin kayayyakin da ake kerawa daga irin wadannan ma’adanai na Karafa da Sanholo zai yi tashin gwauron zabo. A bayyane take cewa kasashen da wannan karin haraji ya shafa ba za su rungume hannuwansu ba su sanya ido Amerika ta ci karenta ba babbaka, babu shakka su ma za su dauki matakan ramuwar gayya, ta hanyar kakaba haraji a kan kayayyakin da Amerika ke fitarwa. Wannan lamari zai haifar da yakin ta fannin kasuwanci, abin da ba zai amfanawa kowa ba.
    ’Yan kasuwa da abokan hulɗa da dama sun jikkata yayin da gubar harsashi ta tarwatse wannan Talatar a Jihar Zamfara. Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a babbar kasuwar garin Talatan Mafara wadda ke ci duk ranar Talata. Galibi waɗanda lamarin ya rutsa da su ’yan kasuwar ne da kuma wasu abokan hulɗarsu da suka samu ƙonuwa da raunika daban-daban. Hotuna da wakilinmu na naɗa ya hasko waɗanda lamarin ya shafa suna kwance ana kawo musu agaji, inda galibi sun ƙone a ƙafafu da cinya har zuwa mazaunai.  
    Ministan tsaron HKI Israel Katz ya bayyana cewa gwamnatin HKIba zata bar a kafa kasar Falasdinu ba, saboda hakan barazana ce ga samuwar HKI. Israek Kazt ya bayyana haka ne a lokacin ganawar jami’an gwamnatin HKI da tawagar kasar Amurka. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a taron su da tawagar kasar ta Amurka a yau. Ya kuma kara da cewa abubuwan da HKI ta sa a gaba sun hada da ganin kasar Iran bata mallaki makaman Nukliya ba, da shafe kungiyar hamas, sakin fursinoni a hannun Hamasa da kuma samar da huldar jakadanci da kasar Saudiya. Wasu kafafen yada labarai sun nakalto wasu manya manyan jami’an sojojin kasar suna tunanin dakatar da...
    “Mutanen nan sun matsa mana iya matsi, suna kafa sabbin sansanoni, duk wanda ke yankin nan babu wanda bai san shi ba, kuma jami’an tsaronmu na iya bakin kokarinsu.” BBC ta tuntuɓi kakakin rundunar Fansar Yamma, Laftanar-Kanal Abubakar Abdullahi ta waya domin jin ko sun san da wannan sabon sansani, sai dai ba mu same shi ba, duk da an tura masa sakon kar-ta-kwana game da lamarin. A kwanan nan dai rahotanni daga jihar ta Zamfara na cewa ana ci gaba da samun gagarumar nasara wajen yaƙi da ‘yan bindiga, sai ga shi yanzu wasu al’umma na bayyana cewa sabbin mahara na sake dawowa.
    Shi kuwa tsohon Janar Manaja na Hukumar ta NPA Joshua Asanga, ya jaddda mahimmancin amincewa da karin biyan harajin wanda ya sanar da cewa, sahalewar za ta taimaka wajen samar da kayan aiki a Tashar Jiragen Ruwan, inda kuma shi ma wani mai ruwa da tsaki a fannin ya yi kira da a zuba hannun jari a wasu bangarori na Tashar. Mahukunta a bangaren tafiyar da Tashohin Jiragen Ruwa a fadin duniya, sun dogara ne, wajen samar da kudaden shiga domin su samu damar ci gaba da kula da kayan gudanar da ayyukansu da kuma kara tabbatar da tsaro, a Tashohin Jiragen Ruwan su. Bugu da kari, wasu kararru a fannin sun bayyana cewa, harajin da Hukumar NPA ke karba...
    An yi nasarar watsa liyafar bikin fitilu na gargajiya na Sin na 2025 ta CMG jiya Laraba a mabambantan dandamali, lamarin da ya samu yabo sosai. Alkaluman masu kallo ta talabiji da sauran kafofi na zamani sun karu sosai fiye da bara. Kididdiga ta nuna cewa, an kalli liyafar da aka watsa kai tsaye ta kafofi daban daban sau miliyan 459, karuwar kaso 30 kan na bara. Kana an kalli liyafar ta talabijin har sau miliyan 189, karuwar kaso 12 idan aka kwatanta da bara. Baya ga haka, kallon liyafar kai tsaye ta kafofin zamani, ya kai sau miliyan 270, karuwar kaso 47 idan aka kwatanta da bara. A bangaren kasashen waje kuwa, kafar yada labarai ta CGTN wadda ke...
    A lokacinda yake ganawa da masana masu fasaha a masana’antun makamai na kasar da kuma manya-manyan Jami’an sojojin Kasar Iran, Jagoran Juyin Juya Halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa fitowar mutane a zanga-zangar cika shekaru 46 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar, a ranar litinin da ta gabata, wata alama ce ta hadin kan mutanen kasar Iran, har’ila yau jawabi ne ga barazanar da makiya JMI suke mata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jagoran yana fadar haka bayan ya zagaya ya ga sabbin makamai wadanda masana’antun makamai na kasar suka kera. Ya kuma yaba da irin ci gaban da masana’antun suka samu. Imam Khaminae ya kuma yaba da ayyukan da masu...
    Kasar Saudiyya ta jaddada matsayinta na yin watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da korar Falasdinawa daga muhallinsu Saudiyya ta jaddada cewa: Tana yi watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da neman tilastawa al’ummar Falasdinu yin hijira daga yankunansu, kuma ta nuna cewa ba za a samu dawwamammen zaman lafiya ba sai dai ta hanyar amincewa da tsarin zaman lafiya da zai kai ga samar da kasashe biyu na Falasdinawa dana yahudawan sahayoniyya. Hakan ya zo ne a yayin taron majalisar ministocin Saudiyya da yarima mai jiran gado kuma fira ministan kasar Mohammed bin Salman ya jagoranta, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Saudiyya SPA ya ruwaito. Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na...
    An gabatar da bikin mu’ammalar al’adu a jiya Litinin a birnin Harbin da ake wa lakabin “Birnin kankara”, yayin da ake gudanar da gasar wasannin motsa jiki na lokacin hunturu ta Asiya karo na 9 a birnin. An yi wannan gaggarumin biki ne bisa jigon “bikin sabuwar shekara ta kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato bikin bazara karo na farko bayan shigar da shi jerin bukukuwan gargajiya da aka gada daga kaka da kakanni a duniya, wanda ya zo a kan gabar gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Asiya.” ’Yan wasan motsa jiki 20 daga kasar Mongoliya da Thailand da Philipphines da Vietnam da Indiya da Nepal da dai sauran wakilan tawagogin wasannin motsa jiki da ’yan jarida...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta kara jaddada kudurinta na yin hadin gwiwa da wani kamfanin sarrafa dabino da kayan marmari domin inganta noman dabino da alkama a jihar. Gwamna Umar Namadi ya bada wannan tabbaci a lokacin da tawagar Babban Daraktan kamfanin, Dakta Abubakar Musa Bamai ta ziyarci shi a gidan Gwamnati dake Dutse, Babban Birnin Jihar. Ya bayyana cewar, Gwamnatin a shirye take ta yi aiki tare da kowace kungiya da ke da niyyar tallafa wa jin daɗin al’umma da ci gaban tattalin arzikin jihar jigawa. Malam Umar Namadi ya kara da cewar a zancen ma dai da ake yi a halin yanzu, Jihar Jigawa ta shahara wajen noman dabino kuma ita ce ta daya a noman...
    Yanzu haka, an kara tura manyan injuna domin gudanar da aikin ceto a wurin da zaftarewar kasa ta auku a lardin Sichaun na kasar Sin. Da farko za su kwashe duwatsu da kasa da suka lullube wurin, kuma da zarar an ga alamun gini, za a sanar da ma’aikatan dake wurin domin kara bincike. Zuwa karfe 11:00 na safiyar yau agogon Beijing, an tabbatar da kasa ta binne gidaje 10 da wata masana’ata 1, sanadiyyar zaftarewar kasar, wadda ta auku a gundumar Junlian ta birnin Yibin na lardin Sichuan. Haka kuma, mutum 1 ya rasa ransa yayin da 28 suka bata. Zuwa yanzu dai, ana ci gaba da gudanar da aikin ceto. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
    Wani matashi ɗan kasar Argentina mai shekara 23 ya rasa ransa a sakamakon daɓa masa wuƙa da budurwarsa ta yi saboda kawai ya gaisa da wata mata a kan titi. Kishi madaidaici zai iya zama abu mai masu alaka da juna, amma mafi yawanci na iya wuce kima! Abba ya naɗa sabon Sakataren Gwamnatin Kano Shigo da hatsi daga ƙetare ya karya farashinsa a Neja Idan aka dubi labarin Mariano Grinspun, ɗan shekara 23 daga González Catán, wani birni a lardin Buenos Aires na Argentina, wanda budurwarsa mai tsananin kishi ta caka masa wuka wanda ya yi sanadiyya mutuwarsa bayan ya gaisa da wata tsohuwar abokiyar karatunsa a titi, za a ga abin akwai ban mamaki. Abin ya faru ne...
    Shirin Inganta rayuwar al’umma na jihar Jigawa ya  raba katinan cire kudi na ATM a kananan hukumomi 10 daga cikin 27 domin al’umma su sami tallafin naira dubu saba’in da biyar biyar na gwamnatin Tarayya. Shugaban shirin na jihar, Malam Mustapha Umar Babura ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse, babban birnin jihar. Yayi bayanin cewar, ana rabon katinan karbar kudin ne ga wadanda za su sami tallafin inganta rayuwa na naira dubu sabain da biyar. A cewarsa, duk da korafe korafen da ake samu wajen rabon katinan, aikin na cigaba da  gudana yadda ya kamata. Mustapha Umar Babura ya ce ana ta kokarin warware duk matsalolin da ma’aikatan suke cin karo da su wajen rabon katinan ga al’umma....
    Kazalika, a Arewacin Nijeriya, Robar Tumatir mai nauyin kilo 25  yanzu, ana sanar da ita kan Naira 6,500. Shugabar kungiyar masu noman Tumatair da sarrafa shi ta kasa, Rabiu Zuntu ta sanar da cewa, an samu girbin Tumatir mai yawan gaske, duba da cewa; yanzu ana cikin watan Fabrairu, lokacin da ake samun yawaitarsa. A cewar tata, tarin yawan nasa ne ya sa aka samu faduwar farashinsa a kasuwanni, wannan dalili ne ma ya sanya, don gudun kada manoman su yi asara; suke sayar da shi kan farashi mai sauki. “Daga watannin Janairu, Fabrairu zuwa Maris; ana samun kwantan Tumatir, yanzu kuma muna da injinoni masu kyau na sarrafa Tumatirin, wanda hakan zai sa a samu raguwar farashin”, in ji...
    Kasashen Italiya da Spain sun ki amincewa da tilastawa Falasdinawa yin gudun hijira daga Zirin Gaza Ministan harkokin wajen kasar Italiya Antonio Tajani, a yayin wani taron manema labarai da takwaransa na haramtacciyar kasar Isra’ila Gideon Sa’ar a tashar jiragen ruwa ta Ashdod, ya jaddada kin amincewa da kakkausar murya da kasarsa ta yi na korar Falasdinawa daga zirin Gaza karkashin dabarar gudun hijira. Tajani ya bayyana cewa: Ba za a tilastawa Falasdinawan shiga kowane irin zabi ba, yayin da yake magana kan shirin da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar na neman kwace yankin Zaga. A cikin wani yanayi mai alaka da wannan batu, ministan harkokin wajen kasar Spain José Manuel Albares ya bayyana rashin amincewarsa da shawarar da...
    Ɗanbayan Manchester United Lisandro Martinez ba zai sake taka leda ba a sauran wasannin kakar nan saboda raunin da ya ji a guiwarsa, a ranar Lahadi. An fitar da ɗanwasan ne mai shekara 27, a karawar da United ta yi rashin nasara a gida a hannun baƙinta Crystal Palace, raunin da tun a lokacin kociyan ƙungiyar Ruben Amorim ya bayyana a matsayin babbar matsala. A ranar Alhamis ƙungiyar ta ce har yanzu ana duba yanayin raunin domin sanin yadda ya fi dacewa a yi masa magani da kuma tsawon lokacin da zai ɗauka yana jinya. Sanarwar ta ce kowa a ƙungiyar yana yi wa Lisandro Martinez fatan warkewa sarai, kuma za su ci gaba da tallafa masa a kodayaushe. Rashin...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Shin mene ne dalilin faɗuwar farashin tumatir warwas a kasuwa? Idan ba a manta ba, a watannin baya farashin tumatir ya yi tashin gwauron zabo wanda aka daɗe ba’a ga irinsa ba. A wancan lokacin, sai da farashin ya kai ga iyalai da dama sun haƙura da shi sun koma sayen na gwangwani ko na leda. NAJERIYA A YAU: Tasirin Yankan Angurya A Rayuwar Mata DAGA LARABA: Yadda Al’adun Aure A Ƙasar Hausa Suka Koma ‘Event Centre’ Wannan ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokacin zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
    Gwamnan ya bayyana haka a yayin wata ziyarar ta’aziyya da ya kai yankin na Rimin Zakara a yammacin ranar Alhamis 06, ga watan Febarairun 2025.   A yayin ziyarar l, gwamnan ya yi alkawarin gina wa jama’ar yankin na Rimin Zakara katafaren Masallacin Juma’a a matsayin sadaka jariya ga wadanda suka rasu a dambarwar filayan yankin da Jami’ar Bayero. Gwamnan ya yi kuma alkawarin samar da Asibitin sha-ka-tafi da samar musu da hanya da kai hasken wutar lantarki da rijiyoyin burtsatsai da bai wa iyalan mamatan jari da daukar dawainiyar karatun yaransu gwargwadon iko da kuma daukar nauyin jinyar wadanda suka ji rauni a yankin a yayin rusau da aka yi a makon da ya gabata.
    Shugaba Bola Tinubu, ya buƙaci hukumomin ilimi su tabbatar da cewa makarantun gwamnati da masu zaman kansu sun ɗauki matakan kare ɗalibai daga haɗura. Wannan kira na zuwa ne bayan da wata gobara ta yi ajalin almajirai 17 a wata makarantar tsangaya da ke garin Ƙauran Namoda, a Jihar Zamfara. Allah Ya yi wa Sheikh Ishaq Yunus rasuwa Tinubu ya yi sauye-sauye a Jami’ar Abuja Gobarar, wacce ta tashi da daddare a ranar Talata, ta kuma jikkata wasu almajirai bakwai, amma yanzu haka suna asibiti ana kula da su. Shugaba Tinubu ya jajanta wa Gwamnatin Jihar Zamfara da iyalan waɗanda da suka rasa ’ya’yansu a wannan iftila’in, tare da yin addu’ar samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata. Ya buƙaci makarantu...
    Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu da bai wa ‘yan’uwansu haƙurin jure wannan babban rashi, har ila yau gwamna Dauda Lawal ya yi addu’ar Allah ya bai wa wadanda suka samu raunuka lafiya. Gwamnati za ta yi bincike domin ta gano dalilin afkuwar wannan gobara, domin kaucewa hakan a nan gaba. A karshe ya ce gwamnati za ta bayar da duk wani taimakon da ake bukata da tallafi ga iyalan mamatan da kuma na asibiti.
    Wata gobara da ta tashi a wata makarantar tsangaya da ke Ƙaramar Hukumar Kaura-Namoda a Jihar Zamfara, ta yi ajalin almajirai 17. Dukkanin almajiran sun ƙone ƙurmus, ta yadda ba a gane kowa a cikinsu ba. Saura ƙiris Bello Turji ya zo hannu – Ministan Tsaro Tinubu ya ƙara kasafin kuɗin 2025 zuwa N54.2trn Shaidu sun bayyana cewa gobarar ta farq ne cikin daren ranar Talata, kuma ta ɗauki kimanin sa’o’i uku tana ci. Rahotanni sun bayyana cewar wasu almajirai 16 sun samu munanan raunuka a gobarar. Wani mazaunin yankin, Abdulrasaq Bello Kaura, ya bayyana cewa gobarar ta fara ne sakamakon kamawar wasu itatuwa da aka ajiye. Wani ganau ya shaida cewar, “Abin ya faru ne a makarantar Malam Ghali,...
    An yi kiyasin adadin tafiye-tafiyen fasinjoji tsakanin yankuna zai kai biliyan 4.8 a duk fadin kasar Sin daga ranar 14 ga watan Janairu zuwa ta 2 ga watan Febrairu, wato rabin farko na kwanaki 40 na zirga-zirgar bikin bazara.  Adadin ya nuna karuwar kashi 7.2 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara, a cewar tawagar aiki ta musamman da aka kafa don saukake ayyukan da suka shafi zirga-zirgar bikin bazara, wanda aka fi sani da chunyun. Hukumar FCTA Ta Rufe Asibitin Da Ke Aiki Ba Bisa Ka’ida Ba A Kuje Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Athletico Madrid Da Getafe Zirga-zirgar fasinjoji ya karu tun daga ranar 30 ga watan Janairu, inda adadin tafiye-tafiyen ya zarce miliyan 300 a...
    Guinea-Bissau Na Neman Karfafa Hadin Gwiwar Kafofin Yada Labarai Da Sin
    Uwargidan Gwamnan Jihar Jigawa, Hajiya Hadiza Umar Namadi ta kaddamar da wani katafaren  wurin shan shayi da taliya na zamani  a karamar hukumar Maigatari ta jihar. Hajiya Hadiza Namadi ta ce, wurin sayar da shayin da taliyar da aka zamanantar da shi wani yunkuri ne na karamar hukumar ta Maigatari.   Ta kara da cewa, an tsara wannan wurin na zamani ne domin samar da yanayi mai kyau da inganci ga mutane, inda za su ci abinci cikin gamsuwa, tare da bunkasa kasuwanci a yankin. Hajiya Hadiza ta kuma kaddamar wani tallafi ga mata 300 a karamar hukumar Maigatari.   An bayar da naira dubu talatin kowannensu, domin bunkasa kananan sana’o’i. Gidan rediyon Najeriya ya ruwaito cewa,...
    Haduwar farko shine wanda AC Milan ta yi nasara da ci 3–2 tsakaninta da Internazionale Milan a gasar Italian Football Championship a ranar 10 January, 1909.   Wanda yafi yawan jefa kwallaye: Andriy Shevchenko kwallaye 14.   Nasara mafi girma: inter Milan 0–6 Ac Milan a gasar Serie A (11 May 2001).   Dan wasan dayafi buga wasan Derbi Madonnina Paolo Maldini wasanni 56.   Haduwar da akafi jefa kwallaye Inter Milan 6-5 Ac Milan (6 Nuwamba 1949).   Dan wasan da yafi yawan kwallaye a wasa guda José Altafini kwallaye 4 (27 Maris 1960).   Dan wasa mafi shekaru daya jefa kwallo a wasan Zlatan Ibrahimović Shekaru 39 (26 Janairu 2021).   Gaba daya a tarihi, kungiyoyin biyu...
    ‘Yan gwagwarmayar Siriya sun sanar da fara kaddamar da hare-haren daukan fansa kan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila Sojojin mamayar Isra’ila sun yifuruci da cewa; Sun fuskanci bude wuta daga yankin kudancin Siriya, wanda kungiyar gwagwarmayar al’ummar Siriya ta yi ikirarin kai harin wanda shi ne irinsa na farko tun bayan da sojojin mamaya suka kutsa kai cikin yankunan Siriya bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad. Sojojin mamayar Isra’ila sun tabbatar da kai wani farmaki kan rundunar sojinsu a kudancin Siriya a jiya Juma’a. A jiya ne sojojin mamayar Isra’ila suka kai farmaki kauyen Taranja da ke yankin Quneitra a kudu maso yammacin kasar Siriya, inda suka kame mutane biyu. Wakilin gidan rediyon sojojin mamayar Isra’ila ya...
    Shekara 18 da fara aikin gina babban asibitin kwararru mai gado 300 a unguwar Sabuwar Kaduna (Millennium City) amma har yanzu aikin bai kammalu ba. Aikin wannan katafaren asibiti, wanda ake hasashen babu irinsa a fadin yankin Yammacin Afirka, ya yi zamani da gwamnoni biyar, kowannensu na sa lokacin kammala shi, amma har yanzu abin ya gagara. Sau hudu gwamnonin jihar daban-daban suna sa wa’adin kammalawa da kaddamar da wannan katafaren asibiti, ba tare da haka ba ta cimma uwa ba. A shekarar 2007 tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Muhammad Namadi Sambo tare da hadin gwiwar Bankin Raya Musulunci na Duniya suka assasa aikin ginin asibitin da wa’adin kammala shi a cikin shekara biyar, wato 2012. An yi fatan zai kasance...
    Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Mohammad Reza Aref ya jaddada muhimmancin karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da kasuwanci da kasar Kazakhstan a wata ganawa da firaministan kasar Kazakhstan Olzhas Bektenov. A yayin taron na ranar Alhamis, Aref ya bayyana bukatar samar da karin kwamitocin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu. Bayan goron gayyata day a samu a hukumance daga Bektenov, mataimakin shugaban kasar Iran na farko ya isa kasar Kazakhstan a ranar Alhamis domin halartar taron koli na shugabannin gwamnatoci mambobi a kungiyar tattalin arzikin Eurasia (EAEU) da taron Almaty Digital Summit 2025, wanda aka shirya gudanarwa daga ranar 31 ga watan Janairu zuwa 1 ga Fabrairu. Iran wadda a baya-bayan nan ta samu matsayin mamba mai sanya ido a...
    Kafafen yada labarai na kasar Sweden sun bayyana cewa an sami gawar Selwan Momika dan shekara 38 a duniya a wani gida daga kudancin birnin Stokhom na kasar. Selwan dai dan asalin kasar Iraki ne, wadanda yake gudun hijira a kasar ta Sweden tun, amma ya bayyana kansa a kafafen watsa labarai a shekara ta 2023 inda yake kona alkur’ani mai girma don wulakanta shi. Saboda kuma nuna kiyayyarsa ga addinin musulunci da musulmi. Gwamnatin kasar Sweden dai ta halattawa Selwan yin haka a karkashin dokar yencin fadin albarkacin baki wanda kasashen yamma musamman a turai suka amince da ita. Sai dai wannan aikin nasa ya gamu da fushin musulmi a duk fadin duniya. Yansan da a birnin Stokhom sun...
    Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya mika gaisuwar sabuwar shekara da fatan alheri ga kasar Sin yayin da ta shiga sabuwar shekarar gargajiya. Cikin sakonsa a jiya Laraba, Cyril Ramaphosa ya bayyana kwarin gwiwar shekarar Maciji za ta ci gaba da karfafa matsayin Sin na karfin samar da kyawawan abubuwa da hikima da wadata na bai daya ga duniya. Shi ma a jiyan, shugaban Zambia Hakainde Hichilema, ya aikewa shugaban kasar Sin Xi Jinping gaisuwar sabuwar shekarar gargajiya ta kasar, yana mai fatan samun ci gaban kasashen da al’ummominsu. Kotu Ta Bayar Da Belin Sowore Kan Naira Miliyan 10 Kafar CMG Ta Samu Nasarar Yayata Shirin Shagalin Murnar Bikin Bazara A Kasashen Waje A ranar Talata kuma, shugaban Angola...
    Ministan Harkokin Wajen Benin Ya Yi Wa Sinawa Gaisuwar Sabuwar Shekara
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Son haihuwar ’ya’ya maza fiye da ‘ya’ya mata abu ne da ake samu tun tale-tale a tsakanin al’ummomi daban-daban. A tsakanin wasu al’ummomin, samun da namiji abin alfahari ne wanda kuma yake nuni da cigaba da dorewar ahali; sai dai ba a cika bai wa haihuwar ‘ya mace irin wannan muhimmancin ba. Ko waɗanne dalilai ne suka sa wasu mutane suka fi son samun ’ya’ya maza a kan ’ya’ya mata? NAJERIYA A YAU: Dabarun Noma Don Samun Kuɗaɗen Shiga DAGA LARABA: Me Ya sa Matasa Ba sa Ɗaukar Koyarwa A Matsayin Sana’a? Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi duba ne a kan dalilan da suka sa mutane suka fi son haihuwar...
    Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ya ce: Batun rusa gwagwarmaya ta zama tatsuniya kuma batun Falasdinawa ya dawo cikin fagen siyasar duniya Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon, Sheikh Na’im Qassem ya jaddada cewa: Harin daukan fans ana “Ambaliyar Al-Aqsa” ta cimma burinta na mayar da al’ummar Falastinu a fagen kasa da kasa, yana mai cewa; Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta zame a matsayin kungiyar ta’addanci ta masu aikata laifuka da kisa kiyashi a idon duniya. Babban sakataren kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Qasem ya bayyana a wani jawabi da ya gabatar a yammacin jiya Litinin game da sabbin abubuwan da ke faruwa a kasar Lebanon da kuma yankin, inda ya ce: “Hare-haren wuce...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, Sharhin bayan labarammu zai yi magana a kan “jajircewar mutanen kudancin kasar Lebanon fuskantar sojojin HKI’ yan mamaya’ wanda ni tahir amin. ///…A Jiya lahadi be wa’adin ficewar HKI daga yankuna da garuruwan da suka mammaye a kudancin kasar Lebanon, amma karfe 4 da safe yana cika mutanen wadannan yankuna suka kwarara zuwa gidajensi, amma ko da suka isa sai suka ga cewa sojojin kasar Lebanon sun sha shinge don hana mutane wucewa zuwa wadannan wurare, don har yanzun akwai sojojin HKI a yankin suna iya kashe su. Banda haka sojojin HKI sun kara wayoyin wasu daga cikin mutanen wadannan yankuna, suna fada masu cewa kada su kuskura su shiga wadannan yankuna. Amma...
    A yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da katin murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, a matsayin martani ga abokai a jihar Iowa ta kasar Amurka, inda ya ce, Sin da Amurka na da manyan muradun bai daya, da damar yin hadin gwiwa, kuma suna iya zama abokan hulda da aminai. Ya yi fatan jama’ar kasashen biyu za su kara cudanya da juna, da kara yin mu’amala da juna, da yin aiki tare wajen rubuta labarin abokantaka a tsakanin jama’ar kasashen biyu, da ba da sabbin gudummawa ga ci gaban dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka. (Mohammed Yahaya)  
    Ana fargabar cewa wani mutum mai shekaru 30, Rabiu Sani, ya mutu a wani kududdufi da ke unguwar Kunture a Ƙaramar Hukumar Ungogo da ke Jihar Kano. Mai magana da yawun rundunar hukumar kwana-kwana, Saminu Yusuf Abdullahi ne ya sanar da hakan a ranar Litinin. ’Yan majalisa sun nemi cin hancin N480m kafin amincewa da kasafin jami’o’i —Bincike NAJERIYA A YAU: Dabarun Bunƙasa Kasuwanci Ta Intanet Ya bayyana cewa ofishin karɓar koken gaggawa ne ya samu kira daga wani Silas Munkhaila dangane da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa jami’ansu sun isa kududdufin inda suka tsamo gawar mutumin wanda ya je ɗebo wa mahaifinsa ruwa. Ya ƙara da cewa sun miƙa gawar mamacin a hannun mai unguwar Kunture, Uba Abdulkadir. Kazalika,...
    Harkar Murnar Sabuwar Shekara Bisa Kalandar Gargajiyar Sinawa Da Tawagar Sin A MDD Ta Shirya Ta Nuna Al’adun Gargajiya
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran jagorori na kasar Sin sun ziyarci ko kuma sun gayyaci wasu su ziyarci tsoffin jami’ai da suka yi ritaya, sun mika gaisuwa gabanin bikin Bazara na al’ummar Sinawa na ranar 29 ga watan Janairun nan. Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kwamitin koli na sojan kasar, da sauran jagororin kasar, sun taya tsoffin jami’an da suka yi ritaya murnar bikin Bazara, tare da musu fatan karin lafiya da kuma tsawon rai. A nasu bangaren kuwa, tsoffin jami’an da suka yi ritaya sun yaba da ayyukan kwamitin koli na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin a shekarar da ta gabata, tare da bayyana goyon bayansu...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi rangadi a rundunar arewaci ta rundunar sojin ’yantar da al’ummar Sinawa wato PLA, gabanin Bikin Bazara. Xi Jinping wanda shi ne sakatare janar na kwamitin kolin JKS kuma shugaban hukumar koli mai kula da ayyukan soji (CMC), a madadin kwamitin kolin da hukumar CMC, ya mika gaisuwar sabuwar shekara ga dukkan jami’an rundunar soji ta PLA, da sojoji ’yan sanda, da fararen hula dake aiki a rundunar soja, da mambobin kungiyoyin sa kai da ma jam’an tsaro da aka kebe domin bukatar gaggawa. A bana, Bikin Bazara na sabuwar shekarar al’ummar Sinawa ya fado ne a ranar 29 ga watan nan na Janairu. (Fa’iza Mustapha)