Ficewar Kasar Nijar Daga Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kasa Da Kasa Barazana Ce Ga Tsaro -Hedikwatar Tsaro
Published: 12th, April 2025 GMT
Haka zalika, Kangye ya kuma tabbatar wa da al’umma cewa; jami’an tsaro na ci gaba da mayar da hankali wajen cafke fitaccen shugaban ‘yan ta’addan nan, Bello Turji.
Sannan, ya yi watsi da ikrarin da sojoji suka yi na cewa; sun dakile hare-haren makiyaya da ‘yan ta’adda da kuma barayin shanu da sauran makamantansu.
Da yake yin jawabi game da kyautata wa sojojin da suka jikkata, Kangye ya musanta zargin yin watsi da sojojin da suka samu raunuka.
Ya ce, “To, a iya sanina dangane da abin da hukumar sojoji ke yi, sojojinmu na samun isasshiyar kulawa, kuma kai dan jarida ne, da ka lura da lokacin hutun Sallah, za ka ga yadda babban hafsan soji da hafsan hafsoshin sojin sama da wasu manyan hafsoshi daga hedikwatar hukumar suka ziyarci sojojin, domin taya su murnar Sallah.
“Sannan kuma, zan iya fada muku cewa; hedikwatar rundunar sojojin Nijeriya, na kula da marasa lafiya da wadanda suka samu raunuka da wasu da ke bukatar a fitar da su zuwa kasashen waje, ana fitar da su, domin nema musu lafiya; wasu sun tafi Masar, wasu Turkiyya, wasu kuma Kasar Indiya. Kamar yadda muke magana yanzu, wasu har yanzu suna can suna samun kulawar likitoci a can.”
Ya kuma bayyana cewa, a ‘yan watannin da suka gabata, an raba wa sojojin da suka samu jikkata a fagen-daga gidaje.
Kangye ya kuma yi nuni da cewa, an raba wa sojojin da suka jikkatan gidajen kyauta ne, domin kuwa wasu daga cikinsu; ba za su iya dawowa fagen aiki ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Nijar
এছাড়াও পড়ুন:
Bankin Duniya Ya Daga Hasashen Ci Gaban Tattalin Arzikin Sin Na 2025 Da Maki Kaso 0.4
Bankin duniya ya fitar da sabon hasashensa kan tattalin arzikin Sin a bana a jiya Alhamis, inda ya daga na kasar Sin da maki kaso 0.4.
Bankin ya ce manufofin kudi masu inganci sun sun taimaka wa harkokin sayayya da na zuba jari. Haka kuma, bukatu daga kasashe masu tasowa sun ingiza fitar da kayayyaki daga kasar.
Daraktar sashen kula da harkokin Sin da Mongolia da Korea na bankin duniya, Mara Warwick, ta ce ci gaban kasar Sin a shekaru masu zuwa zai kara dogara kan sayayya a cikin gida. Kuma baya ga dabarun kashe kudi na gajeren lokaci, inganta gyare-gyaren tsarin kyautatawa al’umma da samar da kyakkyawan muhallin kasuwanci, ka iya taimakawa kara kwarin gwiwa da shimfida tubalin juriya da ci gaba mai dorewa. (FMM)
ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA