HOTUNA: Gobara ta laƙume shaguna 100 a Kasuwar Sakkwato
Published: 1st, March 2025 GMT
Ana fargabar cewa wata gobara ta laƙume aƙalla shaguna 100 a Kasuwar Kara da ke Jihar Sakkwato.
Gobarar wadda ta tashi tun da Asubahin wannan Asabar ɗin ta shafe sa’o’i 9 tana ta’adi.
An raba wa ma’aikatan gona babura 200 a Yobe Yadda farashin kayan abinci ya sauka a kasuwannin ArewaWani ɗan kasuwar da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce tun da misalin ƙarfe 6:30 amma sai wurin ƙarfe 3:30 na rana aka samu nasarar kashe ta.
A cewarsa, gobarar ta yi ta’adi a ɓangaren shagunan masu sayar da abinci da suka haɗa da gero, dawa da masara da shinkafa.
Haka kuma, majiyar ta ce wutar ta yi ɓarna a ɓangaren masu ƙyamare da layin maƙera da masu maganin gargajiya.
“A ƙiyasi an yi asarar kuɗi za su kai Naira miliyan 500 domin dukkan shagunan da gobarar ta taɓa sun ƙone ƙurmus, masallaci ne kawai abun bai shafa ba.”
Ya buƙaci gwamnati da ta jingine batun siyasa a gefe wajen kafa kwamitocin da take ɗora wa alhakin bibiyar wannan ibtila’i domin ɗaukar matakan da suka dace bisa adalci.
Ya bayyana cewa wannan shi ne karo na uku cikin ƙasa da shekara ɗaya da ake samun tashin gobara a kasuwar.
Ya nanata kiran cewa bayan jajanta wa ’yan kasuwa akwai kuma buƙatar gwamnati ta ɗauki matakin kare dukiyar mutane daga irin wannan hasara.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gobara Jihar Sakkwato Kasuwar Kara
এছাড়াও পড়ুন:
Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura Isa
Tsohuwar jarumar Kannywood, Mansurah Isa, ta ƙaryata labarin da wata jaridar intanet ta yaɗa cewa wai tana son ta auri shahararren dan TikTok, Ashiru Mai Wushirya, wanda ya yi tashe a kafafen sada zumunta a ’yan kwanakin nan.
A wani saƙo da ta wallafa, Mansurah ta ce labarin ƙarya ne kuma ya jefa ta da iyalinta cikin ruɗani da damuwa.
Ta ce, “Na shiga firgici bayan na ga wannan labarin. Ba ni da wata alaka da Mai Wushirya. Wannan sharri ne tsagwaron karya.”
Rahoton da aka yada a jaridar AMC Hausa ya yi iƙirarin cewa wai Mansurah ta ce ta shirya auren Mai Wushirya idan har yana son ta da gaske.
Kofin kofi mafi tsada a duniya ya shiga kasuwa a kan Naira miliyan 1.5m An yi garkuwa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin KebbiAmma jarumar ta yi watsi da wannan iƙirarin, tana mai cewa jaridar ta ɓata mata suna kuma ta karya ƙa’idojin aikin jarida.
Ta ce, “Na kira su, na ba su awa 24 su sauke labarin, amma har yanzu ba su yi hakan ba. Sun kira ni sun ba ni hakuri a waya, amma labarin har yanzu yana nan. Wannan abu ya zubar min da mutunci kuma ya saka iyalina cikin tashin hankali,” ina ji ta.
Mansurah ta bayyana cewa yanzu tana cikin shirin ‘WalkAwayCancer’, wani gagarumin shiri na wayar da kan jama’a kan mcutar daji, amma wannan labarin karya ya yi ƙoƙarin karkatar da hankalin mutane daga ainihin aikinta.
“Kun hana ni barci da kwanciyar hankali saboda labarin da babu gaskiya a cikinsa. Amma in sha Allahu, za ku ji daga gare mu,” in ji ta cikin fushi.
Har zuwa lokacin da muka kammala wannan labarin dai, kamfanin AMC Hausa bai fitar da wata sanarwa ba dangane da ƙarar da Mansurah ke shirin kai musu bisa zargin yaɗa labarin ƙarya.