Manoman tumatir na tafka asara saboda faɗuwar farashi
Published: 25th, February 2025 GMT
Yayin da aka fara tsinkar tumatari dan rani a Kano da sauran jihohin da ke samar da tumatar a fadin Nijeriya, rahotanni sun bayyana cewa, farashinsa ya fadi sosai fiye da yadda aka yi zato, lamarin da ya jefa manoman cikin damuwa.
Binciken da Jaridar Aminiya ta gudanar ya nuna cewa, a halin yanzu, ana sayar da kwando daya na tumatir a kan Naira 3,500, yayin da ake sayar da babban kwando a kan Naira 10,000.
Wani manomin tumatir, Isah Bello Abba ya bayyana cewa, wannan yanayi ya sa manoma cikin fargaba saboda sun kashe kudade masu yawa wajen noman tumatir na rani, amma yanzu suna fuskantar yiwuwar yin babbar asara.
“Mun zuba jari mai yawa a bana, amma daga dukkan alamu, ba za mu samu riba mai yawa ba. Wannan yanayi yana tsoratarwa, kuma muna fatan abubuwa za sudaidaita nan gaba,” in ji shi.
Shugaban Kungiyar Tomato Out Growers Association of Nigeria (TOGAN) reshen Jihar Kano, Alhaji Sani Danladi Yadakwari, ya bayyana cewa, tabbas wannan yanayi abin damuwa ne, musamman ma tunda yanzu ne farkon kakar, ba lokacin kololuwa ba.
Ya ce, kungiyar ta fahimci matsalar kuma tana aiki tare da Gwamnatin Tarayya don ganin an dauki matakan da za su tallafa wa manoman, inda ya tabbatar cewa, nan ba da dadewa ba za a fito da tsarin magance matsalar.
A cewarsa, ɗaya daga cikin hanyoyin magance matsalar ita ce kafa kananan masana’antu na sarrafa tumatir a fadin kasa, wanda zai rage yawan asarar da ake samu yayin girbi da kuma karancin farashi a kasuwa.
Ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a bangaren kasuwanci da su fara kafa irin wadannan masana’antu domin bunkasa tattalin arziki da rage radadin da manoma ke fuskanta.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: farashi
এছাড়াও পড়ুন:
Nazarin CGTN: Ana Kara Bayyana Rashin Gamsuwa Da Sabuwar Gwamnatin Amurka Daga Ciki Da Wajen Kasar
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp