Dangote Zai Gina Sabuwar Masana’antar Siminti A Jihar Ogun
Published: 22nd, March 2025 GMT
A cewarsa, tun da farko mun kau da kai ga barin sanya hannun jari a shiyyar kasuwanci ta Olokola (OKFTZ), amma saboda manufofinku da kuma yanayin da masu zuba jari ke da shi, ina so in ce mun dawo kuma za mu yi aiki tare da gwamnatin jihar don komawa Olokola, kuma ana shirin gina tashar jiragen ruwa mafi girma a kasar.
Da yake karin haske kan ayyukan da kamfanin ke gudanarwa a Jihar, Dangote ya ce sabbin layukan biyu masu karfin metric tan miliyan 6.0 a kowace shekara na kamfanin siminti an gina su a Itori, yayin da kamfanin siminti na metric ton miliyan 12 a kowace shekara kuma yana nan a Ibeshe.
Bayan kammala aikin, Dangote ya ba da tabbacin cewa, jimillar kamfanonin siminti a jihar za su yi makotaka da metric ton miliyan 18 a duk shekara, wanda zai zama jiha ko yanki mafi girma da ke samar da siminti a Afirka.
“Tare da gudunmawar sauran masu samar da siminti a Jihar, Ogun ta kasance a gaban sauran kasashen Afirka a fannin samar da siminti,” in ji shi.
Dangote ya bayyana cewa kamfanin simintin Dangote ne kan gaba wajen samar da siminti a nahiyar Afirka mai karfin metric ton miliyan 52.0 a duk shekara a fadin nahiyar Afirka.
Ya kara da cewa kashi 70 cikin 100 na simintin ana samar da su ne a Nijeriya, inda kamfanin Obajana da ke Jihar Kogi ke samar da metric ton miliyan 16.25 a duk shekara, wanda shi ne mafi girma a Afirka.
Ya ce zuba jarin da ake yi wajen sarrafa kayayyakin ya sa al’ummar kasar nan ta dogara da kanta wajen samar da siminti, kamar yadda kasar nan ta dogara da kanta wajen samar da taki, inda ake samun rarar kayayyakin da ake samu a kasuwannin ketare, wanda hakan ya sa al’ummar kasar ke samun kudaden musanya da ake bukata.
Yayin da yake lura da cewa burin kamfanin shi ne Nijeriya ta dogara da kanta a duk abin da ake samarwa, Dangote ya bayyana cewa a halin yanzu kamfanin yana biyan bukatun cikin gida na ‘Premium Motor Spirit’ (PMS) daga matatar mai 650,000 a kowace rana a Ibeju-Lekki, da kuma tace man jiragen sama da ‘Likuefied Petroleum Gas’ (LPG).
Ya ce, Nijeriya na kokarin farfado da tattalin arziki; Don haka akwai bukatar kamfanoni masu zaman kansu su kara kaimi ga kokarin gwamnati, yana mai ba da tabbacin cewa kamfaninsa zai ci gaba da nuna imaninsa ga al’ummar kasar da jama’arta ta hanyar zuba jari da nufin kawo sauyi ga tattalin arzikin kasar.
Da yake mayar da martani, Gwamna Abiodun ya jaddada cewa da kafa kamfanin siminti na Itori, zai samar da metric ton miliyan shida na siminti a duk shekara, kuma kamfanin da ake da shi na Ibeshe, yana samar da metric ton miliyan 12, don haka samar da siminti a jihar zai kai metric ton miliyan 18 a duk shekara, wanda zai zama mafi girma a samar da siminti a Nijeriya da kuma yankin Sahara.
Gwamnan ya yaba wa kamfanin bisa yadda bai yi kasa a gwiwa ba wajen aiwatar da ayyukan da suka dace na hadin gwiwa a tsakanin al’umma, kamar yadda a halin yanzu yake aikin gina titin ‘Inter-Change-Papalato-Ilaro’, yana mai tabbatar da cewa gwamnatinsa a shirye take ta hada kai da kamfanin domin ci gaban jihar da kasa baki daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Dimokuradiyya A Shekara 26: Ba Yabo Ba Fallasa
A tsayin wadannan shekarun, Nijeriya ta fuskanci kalubale da dama da suka hada da fafutukar tabbatar da mulkin dimokuradiyya, siyasar yanki, rikita- rikitar addini da kabilanci da kuma gagarumar matsalar tsaro daga Kudu zuwa Arewa.
Mafi yawan al’ummar Nijeriya na bayyana shekaru 26 na mulkin dimokuradiyya a matsayin shekarun gurbataccen mulki, shekarun mulkin danniya da zalunci, cin hanci da rashawa, tabarbarewar tsaro, rugujewar tattalin arziki kana shekaru 26 na satar danyen mai, rashin wutar lantarki, koma baya a sha’anin ilimi, aikin gona da rashin ayyukan yi tare da hauhawar farashin mai da tsadar rayuwa.
Akasin murnar wannan ranar, kungiyoyi a Arewa da Kudu, jam’iyyun siyasa, kungiyoyin farar hula da na matasa da dalibai sun bayyana ‘yan siyasa a matsayin matsalar da ta dabaibaye kasar nan ba wai tsarin aikin gwamnati ba.
A mabambantan bayan su kungiyar dattawan Arewa ta ACF, kungiyar Yarbawa ta Afenifere da Ohanaeze ta Inyamurai sun bayyana amfani, nasarori, illa da matsalolin mulkin dimokuradiyya.
Kungiyar dattawan Arewa ta ce matukar ‘yan siyasa ba su watsar da tsattsauran ra’ayin su na rikau, talakawa ba za su mori romon mulkin dimokuradiyya ba. Ita kuwa kungiyar Yarbawa ta bayyana kima da tasirin mulkin dimokuradiyya ga kasa da ‘yan kasa, sai dai duk da kasawarsa a wasu bangarori ta ce shine tsari mafi inganci ga ‘yan Nijeriya.
Sai dai kungiyar Inyamurai ta bayyana cewar babu wata mafita ta samar da ci-gaba a Nijeriya illa canza fasalin kasa domin a baiwa kowane yanki damar bunkasa tattalin arzikin sa.
Haka ma kungiyoyi da dama sun koka ga gwamnati a kan ta gaggauta shawo kan matsalolin tsadar rayuwa, rage farashin mai da bunkasa tattalin arziki wadanda suka zama silar jefa al’umma a cikin kunci musamman a dalilin cire tallafin man fetur da wasu tsare-tsaren gwamnati masu tsauri.
A cewarsu maimakon shagalin buki, kamata ya yi a yi zaman jajantawa juna kan gurbatacciyar hanyar da shugabannin kasar mabambanta suka hau na rashin ci-gaba akasin ingantacciyar hanyar da shugabannin baya wadanda suka jagoranci samarwa kasar ‘yanci suka dora ta a kai.
Da yawan mutane sun yi tunanin daga shekarar 1999 zuwa yau matsalolin da ake fuskanta za su kau amma sai a ka ga akasin hakan. Abubuwan da ke ciwa jama’a tuwo a kwarya musamman sha’anin samar da hasken wutar lantarki har yanzu ba a shawo kan matsalar ba duk da irin makuddan kudaden da a ka narkar wadanda a ke ganin bai kamata a ce har yanzu babu tsayayyiyar wutar lantarki a Nijeriya.
A ra’ayin wasu gwamnatoci a mataki-mataki sun taka rawar gani. Idan da a ce babu mulkin dimokuradiyya da ba za a samu ‘yancin fadar albarkacin baki ba wanda shi kansa ci-gaba ne.
Haka ma a cewar su idan aka kalli kauyukan kasar nan a kananan hukumomi 774 zuwa yau an samu ci-gaba domin a can baya ba haka suke ba. Sai dai tabbas ci-gaban ba yadda a ka zata ba ne. Watakila gwamnatocin ba su samu kudade yadda ya kamata ba, wasu kuma na kukan matsalar daga hannun shugabanni take.
Mulkin dimokuradiyya a Nijeriya a tsayin wadannan shekaru mulki ne da ke cike da rudu da kwamacalar siyasa daban-daban. A wanann rahoton za mu gabatar da muhimman abubuwan da dama da suka faru a kowace gwamnatin dimokuradiyya daga Obasanjo, ‘Yar’Adua, Jonathan, Buhari zuwa Tinubu da ke jan zaren mulki a yau.
Abubuwan Tunawa A Gwamnatin Obasanjo (1999-2007)
A jiya da yau a kan tuna da Gwamnatin Obasanjo a 1999-2007 ta hanyar kafa Hukumomin Yaki da Almundana da Kudaden Al’umma (EFCC) da (ICPC) tare da karfafawa Hukumar Kula da Da’ar Ma’aikata domin yaki da cin hanci da rashawa. Gurbatattun ‘yan siyasa da mutane da dama sun shiga hannu tare da gurfana a kotu zuwa daurewa a kurkuku a wancan lokacin.
Wasu daga cikin nasarorin da za a iya cewa gwamnatin Obasanjo ta samarwa al’ummarta akwai rattaba hannun shigowa da kamfunan sadarwa wanda ya zama silar samar da wayoyin hannu na GSM wanda daga lokacin zuwa yau kusan babu wani gida a Nijeriya da ba a mallakin wayar tafi-da-gidanka ba.
Gwamnatin Obasanjo wadda aka samu tabarbarewar tsaro da rikita- riikitar kabilanci a mulkinsa haka ma a mulkin sa an shaidi yawaitar faduwar jiragen sama ciki har da jirgin ADC wanda ya dauki rayuwar Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido da muhimman mutane a 2006.
Gwamnatin Obasanjo ta yi matukar kokarin samarwa Nijeriya afuwar bashin zunzurutun kudi har dala Biliyan 18 daga Paris da London wanda ya jima yana ciwa kasar nan tuwo a kwarya.
Bugu da kari a zamanin mulkin Obasanjo ne siyasar ko- a- mutu- ko- a- yi-rai ta samu gindin zama ta yadda aka rika sarawa ko babu gaba ga duk wani ko wadanda suka yi kokarin shiga gona ko huruminsa. Obasanjo a 2007 a kokarin sharewa marigayi ‘Yar’Adua hanyar zama shugaban kasa, ya jagoranci gudanar da kazamin zabe mafi muni a Nijeriya wanda ke cike da aika-aika da murdiyar zabe.
Haka ma Obasanjo ya so yi wa mulkin dimokuradiyya fyade a yayin neman zarcewa saman mulki a wa’adi na uku lamarin da ‘yan Nijeriya suka sa kafa suka shure tare da Allah-wadai kan kokarin yin karan tsaye ga kundin tsarin mulkin kasa, abin da ya kawo karshen bukatarsa wadda hakarsa ta kasa cimma ruwa.
Umaru ‘Yar’Adua (2007-2010)
Umaru Musa ‘Yar’Adua shine shugaban Nijeriya daga Mayu 2007 zuwa 5 ga Mayu 2010 a lokacin da ya yi bankwana da duniya yana a saman mulki.
‘Yar’Adua ne shugaban kasa na farko a tarihi da ya fara bayyana kadarorin da ya mallaka a bayyane tun kafin ya shiga ofis. Haka ma a fili ya fito ya bayyanawa duniya cewar zaben da ya kawo shi saman mulki cike yake da ta’addanci, murdiya da sabawa dokokin zabe.
Haka ma gwamnatin Matawallen na Katsina ta taka rawar gani wajen rage farashin man fetur daga farashin da yake akai zuwa naira 65 a kowace lita. Dukkanin gwamnatocin baya kara farashin mai suke yi, ita kuwa ta ‘Yar’Adua saukar da farashin ta yi. Kazalika takaitacciyar gwamnatin ‘Yar’Adua wadda ba ta yi tsawon rai ba ta cancanci a yaba mata wajen kawo gyara ga dokokin zabe.
Baya ga wannan a mulkinsa ba za a manta da yadda ya sa kafa ya sabawa tsarin mulki wajen rashin hannuntawa mataimakinsa Jonathan ragamar mulki ba a yayin da ya bar kasa zuwa duba lafiyarsa a Saudi Arabiya. Sai dai ‘yan Nijeriya masu kishi da hangen nesa sun tashi tsaye suka jagoranci gyara babbar matsalar tare da tabbatar da zaman Jonathan a matsayin mukaddashin shugaban kasa.
Haka ma gwamnatin ‘Yar’Adua ta samu nasarar kawo karshen ta’addancin tsagerun yankin Neja-Delta da ke talauta kasa ta hanyar yi masu afuwa suka ajiye mukamai tare da tallafa masu a shirin musamman wanda a lokacin ya kawo karshen ta’addanci a yankin mai albarkar man fetur.
Goodluck Jonathan (2010-2015)
A zamanin gwamnatin Jonathan ‘yan ta’addan Boko-Haram sun ci karensu ba babbaka ta yadda al’ummar kasa suka rika bacci da ido daya a gwamnatin Jonathan wanda shine shugaban kasa na farko da ya fito daga yankin Kudu-Maso-Kudu.
Sace ‘yan matan Chibok 100 da mayakan Boko-Haram suka yi awon gaba da su a makarantar mata a Jihar Borno a Afrilu 2014 lamari ne da ya yi matukar jan hankalin al’ummar ciki da wajen kasar nan.
Jonathan ya zama shugaban kasa na farko a tarihi kasar nan da ya sha kasa a zabe yana kan gadon mulki. Fitowa fili da ya yi ya karbi faduwa zabe tare da taya Muhammadu Buhari murna ya daga darajarsa da samar masa kima da dattako tare da tabbatar da karfin mulkin dimokuradiyya.
Muhammadu Buhari (2015- 2023)
Muhammadu Buhari wanda ya zama shugaban kasa a 2015 bayan ya sha kaye a zabukan 2003, 2007 da 2011, ya sake lashe zaben 2019 da gagarumar nasara.
Gwamnatin Buhari wadda ta yi kaurin suna wajen yekuwar yaki da cin hanci da rashawa, ta fadi kasa warwas ta hanyar kasa magance yawaitar cin hanci a fannoni da dama lamarin da jama’a ke ganin batun yaki da cin hanci suna ne kawai a gwamnatin Buhari domin kuwa a yayin da ake gurfanar da magoya bayan PDP a kotu, takwarorinsu na APC suna ci-gaba da cin karensu ba babbbaka a matsayin shafaffu da mai.
Bugu da kari gwamnatin Buhari ta kasance ta farko a dimokuradiyyar kasar nan da ta rika kawar da kai ga mutunta kundin tsarin mulkin kasa ta hanyar katsalandan ga sashen shari’a da rashin mutunta umurnin kotuna.
Misali kotuna daya bayan daya har guda tara sun bayar da belin Sambo Dasuki rsohon mashawarci na musamman kan sha’anin tsaro a gwamnatin Jonathan amma kuma gwamnatin Buhari ta kasa sakinsa a daurin da ta yi masa a kusan shekaru hudu kan badakalar kudin makamai.
A karkashin mulkin dimokuradiyya a zamanin Buhari al’ummar Nijeriya sun fuskanci yawaitar kisan gilla, garkuwa da mutane da ta’addancin Fulani fiye da kowane lokaci gabaninsa wanda bakidaya al’umma musamman a yankin Arewa suke cikin zullumi da fargaba. Haka ma Buhari zai ci-gaba da zama a cikin tarihi a matsayin shugaban kasa da ya kwashe kwanaki 217 wajen duba lafiyarsa a wajen kasar nan.
Bola Tinubu 2023-
A shekaru biyu na mulkin Bola Ahmad Tinubu al’ummar kasa na kuka da kokawa da tsare- tsare da manufofin gwamnatinsa masu tsauri ta yadda da yawa ke kewa da kwadayin mulkin PDP wanda rayuwa ke da sauki a mulkin ta.
Cire tallafin man fetur da Tinubu ya yi a jawabinsa na karbar mulki a 2023 shine babban abin da ya dauki hankalin jama’a tare da girgiza su musamman bisa ga radadi da kuncin da matakin ya jefa kasa da ‘yan kasa a ciki wanda ya haddasa tsada da karancin man fetur a lokaci daya.
Ya zuwa yanzu al’umma na cike da kunci a dalilin hauhawar farashin dukkanin abubuwan da rai ke bukata ta yadda abubuwa da dama musamman abinci ke gagarar talaka.
Duk da cewar farashin abinci yana tashi sama a fadin kasa a tsayin shekaru, amma yanayin a wannan lokacin ya ta’azzara ne sosai a bisa ga illar shiraruwan gwamnati musamman cire tallafin man fetur, faduwar darajar naira da sauransu.
Karuwar Talauci
Al’ummar Nijeriya da ke fama da talauci a zamanin gwamnafin da ta gabata sun kara talaucewa sosai a cikin shekaru biyu na mulkin Tinubu ta yadda a yau suke zumudin zuwan lokacin zabe.
Tsananin talaucin da al’umma ke fama da shi a yanzu, ya sa mafi yawan jama’a kasancewa cikin kuka da kokawa da yadda mulkin Tinubu ya zo masu wanda a baya suke fatar samun saukin al’amurra bayan karewar gwamnatin da ta gabata, amma sai gashi talaucin da ake fama da shi a yanzu ya fi na baya tsanani.
Matsalolin Tsaro
Duk da matakan da gwamnati ke dauka na kokarin samar da ingantaccen tsaro har zuwa yanzu ‘yan ta’adda na ci-gaba da cin karensu ba babbaka ta yadda suke hanawa al’umma bacci da idanu biyu wanda kasawa ce karara ga gwamnati a shekaru 26 na mulkin dimokuradiyya amma a kullum tsaron kasa kara tabarbarewa yake yi.
A yayin jin ra’ayin mabanbantan al’ummar kasa daga Arewa har Kudu kan amfani da alfanun da suka amfana da shi na romon mulkin dimokuradiyya, da yawa daga ciki sun bayyana shekaru 26 na dimokuradiyya a Nijeriya a matsayin shekarun gurbatacciyar dimokuradiyya, mulkin fatara da talauci, mulkin rikice-rikice da tashe-tashen hankula.
Bugu da kari jama’a sun fassara 26 a matsayin shekarun cin hanci da rashawa, shekarun sata da wawashe kudaden al’umma, kazalika shekarun karawa masu karfi karfi da kuma ci- da gumin talaka.
A kan wannan karara a yayin da wasu ke bayyana mulkin dimokuradiyya a Nijeriya a matsayin wata hular baka ce wasu kuwa cewa suke yi Shekaru 26 Na Mulkin Dimokuradiyya A Nijeriya: Da Dadi, Ba Badi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp