Cikin kasa da wata guda, an yi asarar hannayen jari da darajarsu ta kai dala triliyan 4, inda damuwar da duniya ke da shi kan manufofin haraji na Amurka ke haifar da fargaba a kasuwar hannayen jari ta kasar.

Wani nazari da kafar CGTN ta gudanar tsakanin jama’ar duniya masu amfani da intanet ya nuna cewa, mutane na bayyana shakku kan manufofin haraji na sabuwar gwamnatin Amurka, kuma sun damu ainun da mummunan tasirinta kan kasuwar hannayen jari ta kasar dake tafiyar hawainiya.

Wani mai bayar da amsa cikin nazarin ya kuma bayyana cewa, sanya haraji kan dukkan kayayyakin kasashen wajen, bai taba haifar da da mai ido ba.

A baya bayan nan, shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa, “ba zai yuwu mu mayar da hankali sosai kan yanayin kasuwar hannayen jari ba.” A martaninsu, kaso 86.7 na wadanda suka bayar da amsa cikin nazarin, sun yi imanin cewa, wannan wani yunkuri na rage mummunan tasirin da manufofinsa na haraji suka haifar kan kasuwar hannayen jari ta kasar. Har ila yau ba da jimawa ba, shugaba Trump ya sanar da karin haraji kan kayayyakin karafa da gorar ruwa da kasar Canada ke kai wa Amurka, inda ya kara harajin zuwa kaso 50 bisa dari, lamarin da ya kara hargitsa kasuwar hannayen jarin. Don gane da hakan, kaso 86.8 na masu bayar da amsa sun yi ammana cewa, faduwar darajar hannayen jari da aka samu a baya bayan nan a Amurka, ta nuna rashin kwarin gwiwa mai tsanani dake akwai a kasuwar zuba jari a tattalin arzikin Amurka, inda ake kara damuwa cewa, durkushewar kasuwar hannayen jarin ka iya tasiri kan kasuwanni duniya da rage kwarin gwiwa a duniya baki daya.

Nazarin ya gudana ne a dandamalin kafar CGTN na harsunan Ingilishi da Faransanci da Larabci da Rashanci, inda mutane 7,875 suka kada kuri’a tare da bayyana ra’ayoyinsu cikin sa’o’i 24. (Fa’iza Mustapha)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: kasuwar hannayen jari ta kasar

এছাড়াও পড়ুন:

Iran, Lebanon, Iraki, Yemen sun fara atisayen hadin gwiwa na goyan bayan Gaza

Kasashen Iran, Lebanon, Iraki, da kuma Yemen sun kaddamar da wani atisayen hadin gwiwa na sojojin ruwa domin nuna goyan baya ga  Falasdinawa a zirin Gaza, wadanda ke ci gaba da fuskantar zalinci  na gwamnatin Isra’ila.

An fara faretin hadin gwiwa a tekun Fasha, da yankin gabar tekun Makran, da kuma tekun Caspian da ke arewaci da kuma kudancin yankin ruwan Iran yau Alhamis gabanin ranar Qudus ta duniya.

Kwamandan rundunar sojojin ruwa na IRGC Rear Admiral Alireza Tangsiri ya ce jiragen ruwa masu nauyi da marasa nauyi 3,000 ne ke halartar faretin.

Ya kara da cewa, faretin na da nufin nuna karfin ruwa na bangaren ‘yan gwagwarmaya da kuma isar da sako ga miyagu da azzalumar gwamnatin Isra’ila.

A yayin faretin, an nuna tutar Falasdinu, sannan aka kona tutar Isra’ila a mashigin tekun Farisa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jagora Ya Yi Kira Ga Iraniyawa Su Fito Don Gudanar Da Gagarumar Zanga-Zargar Ranar Kudus Ta Duniya
  • Iran Ta Bada Amsa Ga Wasikar Shugaban Kasar Amurka Ta Gayyatar Kasar Zuwa Tattaunawa Kan Shirinta Na Makamashin Nukliya
  • Kasar Sin Na Adawa Da Kara Yawan Kamfanoninta Cikin Jerin Wadanda Amurka Ta Takaita Fitar Da Kayayyakinsu
  • Karin Harajin Amurka Zai Illata Tattalin Arzikin Duniya
  • Iran, Lebanon, Iraki, Yemen sun fara atisayen hadin gwiwa na goyan bayan Gaza
  • Sin Za Ta Dauki Matakai Don Kiyaye Hakki Da Muradun Kamfanoninta
  • Kasuwar Kayayyakin Masarufi Ta Sin Za Ta Ci Gaba Da Nuna Yanayin Bunkasa Bisa Daidaito A Bana
  • Alamar Deepseek” Ta Bude Kofar Gyara Na Kara Kunno Kai A Harkokin Duniya
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Ce Zargin Kasar Amurkan Dangane Da Kamfanonin Man Fetur Na Kasar Ba Gaskiya Bane
  • Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Lebanon Ya Ce Basa Da Wani Shiri Na Samar Da Haldar Jakadanci Da HKI