HausaTv:
2025-07-31@18:06:49 GMT

Sharki: Takaitaccen Rayuwar Sayyid Shahid Hassan Nasarallah (r)

Published: 23rd, February 2025 GMT

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da ‘Sayyid Haassan Nasarallah’ shahidin Al-umma’ wanda aka yi jana’izar sa a ranar lahadin da ta gabata. Wanda ni tahir amin zan karanta.

A ranar lahadi 23  ga watan Fabrayrun shekara ta 2025 ne aka gudanar da Jana’izar babbsan sakataren kungiyar Hibullah, sayyid Hassan nasaralla, da kuma magajinsa na tsawon kwanaki 6 Sayyid Hashim safiyyuda deen, kafin haka shi ne shugaban majalisar zartarwa na kungiyar Hizbullah.

 

An haifi sayyid Hassan nasaralla (r ) a ranar 31 ga watan Augustan shekara ta 1960  a wani kauye a kudancin kasar Lebanon, Sayyid ya tashi a cikin gida mai saukin rayuwa, ya fara karatu kamar yadda ko wani yaro yake tashi a gidajensu a kudancinsu a kudancin kasar Lebanon.  Sannan ya fara karatu addinin a gida, daga bayana ya je birnin Najaf na kasar Iraqi inda yayi karatun a gaban malaminsa nafarko Sayyid Shahid Abbas Al-musawi, amma a gwamnatin Iraki a lokacin wacce ta shiga yaki da kasar Iran ta  kori malaman addina da dama daga kasar ta Iraki daga ciki har da shi Shaida Nasarallah da kuma malaminsa Sayyida Abbas Almusawi.

Bayan sun dawo gida Lebalon Sayyid Hassan Nasarallah ya koma birnin Qom na kasar Iran inda ya ci gaba da karatunsa na addinin. Amma a gwagwarmayan da kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta fara da sojojin HKI wadanda a shekara ta 1982 suka mamaye kasar Lebanon daga ciki har da birnin Beirut na kasar, gwagwarmayan ta gaiga sojojin HKI sun kashe malaminsa kuma shugaban kungiyar wato Abbas Almusawi a shekara ta 1992.

Shahasar Sayyida Abbas Almusawi ya sa kungiyar ta ga cewa ba wanda ya dace da shugabancin kungiyar ta kuma ci gaba da shugabancin sayyid Abbas Musawi sais hi sayyid Hassan nasaralla. Sayyida Hassan Nasarallah ya karbi wannan matsayin a ranar 16, ga watan Fabarairu shekara 1992, kuma tun lokacin ne yake jagorantar wannan kungiyar daga nasara zuwa nasarori.

Da farko kungiyar ta sami nasarar korar sojojin HKI daga kasar Lebanon a shekara ta 2000. Wannan nasarar ta fitar da kungiyar a fili a kasar Lebanon da kuma yankin. Da kuma duniya gaba daya.

Don haka Amurka tare da HKI sun yi shirin shafe kungiyar daga doron kasa, wanda ya kai ga yakin da ake kira “yakin kwanaki 33′ a shekara ta 2006 dakarun Hizbullah karkashin  sayyid Hassan Nasarallah, suka basu mamaki, a yakin, inda ta halaka sojojin HKI da dama, suka lalata tankunan yakin ‘samfurin Mirkava’ kirar kasar Amurka. Don haka a aka tsagaita wuta da HKI, ba tare da sojojin HKI sun shiga kasar Lebanon ba, ballanta na su shafe kungiyar hizbulla daga doron kasa. A dole HKI ta amince da kudurin kwamitin tsaro na MDD mai lamba 1701.

Sannan Sayyid Hassan Nasarallah, ya sami nasar musayar fursinoni na HKI, inda yahudawan suka mika fursinonin 5 masu rai wadanda take tsare da su, daya daga cikinsu Samir Qantar yayi shekaru 30 a cikin gidan yari na HKI, da kuma daruruwan gawakin larabawa musamman Falasdinawa da take rike da su. Sanan kungiyar ta mikawa yahudawan gawakin yahudawa biyu da suke tsare da su.

Wannan ma ya kara fitarb da kungiyar ga duniya gaba daya da kuma gano irin kwakwalwan da shugaban wannan kungiyar yake da shi.

Sannan yakin da kungiyar ta shiga don tallafawa Falasdinawa a Gaza, a ranar 8 ga watan Octoban shekara ta 2023, ya kara fitar da irin karfin da kuma ci gaban da kungiyar Ta tayi, inda a cikin watanni kusan 12 na farkon na yakin ta sami nasara korar yahudawa daga arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye, ta lalata na’urorin leken asiri HKI da dama a yankin, sannan ta sami nasar amfani da jiragen yakin leken asirinta mai suna Hud-hud wajen saukar hotunan wurare masu muhimmanci a cikin HKI. Da kuma daga karshe bayan da jiragen yahudan suka sauke ton 85 na makaman a kan gine gine guda 6 wadanda suka tabbatar yana cikinsu, sun kashe Sayyid Hassan nasaralla a ranar 27-ga watan Satumba -2024.

Amma kungiyar ta nuna karfta na makamai masu linzami da kuma makamai wasu wargaza tankunan yaki na mirkava, da kuma halaka sojojin HKI, na tsawon kwanaki 60. Wanda ya tilastawa HKI bukatar a tsagaita wuta., amma ba’a sami damar ya masa da kuma Sayyid shafiyyud deen jana’iza ba sai ranar Lahadi 23-02-2025.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Sayyid Hassan nasaralla sayyid Hassan nasaralla Hassan Nasarallah a kasar Lebanon a shekara ta kungiyar ta da kungiyar

এছাড়াও পড়ুন:

Fiye Da Kamfanoni 30,000 Masu Zuba Jari Daga Waje Aka Kafa A Sin A Rabin Farkon Bana

Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta bayyana cewa, a cikin watanni shidan farko na bana, an kafa sabbin kamfanoni 30,014 na masu zuba jari daga kasashen waje a babban yankin kasar Sin, wanda ya nuna karuwar hakan da kashi 11.7 cikin dari a mizanin duk shekara.

Kazalika, bayanai sun nuna cewa, saka hannun jari daga kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya ya karu da kaso 8.8 cikin dari a tsakanin lokacin.

Har ila yau, jarin da aka zuba daga kasar Switzerland ya karu da kaso 68.6, na Japan ya karu da kashi 59.1, na Birtaniya ya karu da kaso 37.6, sai kuma na Jamus da ya karu da kashi 6.3, kana wanda aka zuba daga Jamhuriyar Koriya kuma ya karu da kashi 2.7 bisa dari. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kananan Yan Wasan Dabben Gargajiya Na Iran Sun Zama Zakara A Gasar Wannan Shekara
  • Sin Na Ci Gaba Da Kyautata Rayuwar Al’umma Ta Amfani Da Hidimomin Dijital Da Na Kirkirarriyar Basira
  •  Shugaban Kasar Lebanon Aun Ya Ce Mun Aike Wa  Amurka Sakwanni Akan Dakatar Da Hare-haren HKI
  • Amurka Ta Ce HKI Ba Zata Fice Daga Kasar Lebanon Ba Sai An Kwance Damarar Hizbullah
  • Fiye Da Kamfanoni 30,000 Masu Zuba Jari Daga Waje Aka Kafa A Sin A Rabin Farkon Bana
  • Jagora: Iran Ta Bayyana Karfinta Da Jajircewarta A Yakin Kwanaki 12 Ga Duniya
  • Rasha Ta Mayar Da Martani Ga Shugaban Amurka Kan Gindaya Wa’adin Kawo Karshen Yakin Ukraine
  • Hamas: HKI Da Amurka Sun Janye Daga Tattaunawa Ne Don Sake Damarar Yaki
  • Iran Ta Ce Amurka Ce Bayan Hare-haren Da Aka Kai Zahidan
  • Shugaban Kasar Masar Ya Roki Trump Ya Kawo Karshen Yaki A Gaza