Wang Yi: Kasar Sin Na Da Kwarin Gwiwa Kan Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Japan Da Koriya Ta Kudu
Published: 23rd, March 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana a jiya cewa, kasar Sin na dora muhimmanci sosai kan hadin gwiwar dake tsakanin kasarsa da kasashen Japan da Koriya ta Kudu, kuma tana da kwarin gwiwa kan hakan.
Wang ya bayyana hakan ne a lokacin da yake halartar taron firaministan kasar Japan Shigeru Ishiba a birnin Tokyo tare da ministocin harkokin wajen kasashen Japan da Koriya ta Kudu.
Kazalika, dangantakar Sin da Japan da Koriya ta Kudu tana kara bunkasa, za a kara tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Bugu da kari, hadin gwiwarsu na kara zurfafa, kasashen yankin za su kara kaimi wajen tunkarar kalubale daban daban daga waje.
Wang ya kara da cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasar Japan da Koriya ta Kudu, wajen kafa sahihiyar ra’ayi game da tarihin yakin duniya na biyu, da kiyaye tsarin bangarori daban daban, da kiyaye muhimmiyar rawar da MDD ke takawa a tsarin kasa da kasa, da ci gaba da inganta hadin gwiwa, da ba da gudummawa ga samun zaman lafiya da wadata a shiyyar da duniya baki daya. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Japan da Koriya ta Kudu Japan Da Koriya
এছাড়াও পড়ুন:
Xi Ya Jaddada Muhimmancin Tsara Nagartaccen Shirin Raya Tattalin Arziki Da Zamantakewar Al’umma Tsakanin 2026-2030
A cewarsa, wajibi ne shirin ya mayar da hankali kan burin cimma zamanantarwa irin ta gurguzu da nufin gina babbar kasa da samun ci gaba wajen farfado da ita. Shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar, wanda shi ne daftarin dake zaman jigon jagorantar ci gaba na matsakaici da dogon zango a bangaren tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin, yana zayyana baki dayan burikan kasar da manyan ayyuka da manufofin da ake aiwatarwa a dukkan bangarori cikin shekaru 5. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp