Sahel: CILSS ta yi gargadi game da sake bullar ‘’kwarin dango’’ a yankin sahel
Published: 22nd, April 2025 GMT
Kwamitin kasa da kasa kan yaki da fari a yankin Sahel (CILSS) ya yi wani gargadi na musamman kan sake bullar ‘’kwarin dango’’ a yankin Sahel, wanda ke da hadarin yin illa nan gaba.
Shafin yanar gizo na CILSS ya bayar da rahoton cewa, “Kwananan kwararru kan yaki da fari sun fitar da sanarwar sake bullar farar kwarin dango a kasashen Sahel da dama.
CILSS ta yi gargadin cewa “, wannan na iya haddasa matsala sosai a lokacin noma a yankin da ya riga ya kasance mai rauni’’.
Yayin da ake fuskantar wannan barazana, CILSS na ganin cewa, ya zama wajibi a ba da goyon baya mai dorewa ga kasashendake sahun gaba wajen fuskantar irin wannan matsala na yankin Sahel, wajen aiwatar da shirye-shiryensu na gaggawa, domin dakile duk wata matsalar fari da ka iya yin illa ga kakar noma mai zuwa a yankin Sahel.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: a yankin Sahel
এছাড়াও পড়ুন:
Ƙungiyar Rays Heaven ta Ƙarfafa Wayar da Kai kan Lafiyar Kwakwalwa a Kaduna
Daga Abdullahi Shettima.
Ƙungiyar taimako mai zaman kanta mai suna Rays Heaven for Special Needs Children and Adults ta gudanar da taron wayar da kai a Kaduna domin ƙarfafa fahimtar muhimmancin kula da lafiyar kwakwalwa da kuma magance matsalolin tattalin arziki da ke shafar rukunin jama’a masu rauni.
Shugaban shirye-shiryen ƙungiyar, Sadiq Abdilatif, ya bayyana cewa wannan shiri mai taken Youth Resilience Project ana aiwatar da shi ne da tallafin Ƙungiyar Tarayyar Turai (European Union) tare da Global Youth Mobilization Fund.
Ya ce manufar shirin ita ce wayar da kai ga makarantun sakandare, al’ummomi, da sansanonin ’yan gudun hijira kan mahimmancin lafiyar kwakwalwa, tare da ƙarfafa matasa su koyi magana idan suna fuskantar damuwa ko matsaloli, da kuma koyar da malamai da shugabannin al’umma hanyoyin taimaka musu.
Mr. Abdilatif ya bayyana cewa matasa da mutane masu buƙata ta musamman, ciki har da ’yan gudun hijira, na fama da ƙalubalen tunani da na tattalin arziki da ke rage musu ƙarfi wajen gudanar da rayuwa. Ya ce wannan shiri yana nufin gina ƙarfin gwiwa da samar da wakilai a cikin al’umma waɗanda za su ci gaba da yada wannan saƙo a yankunansu.
Ya ƙara da cewa ƙungiyar na da shirin haɗa shugabannin gargajiya da na addini domin tabbatar da ci gaba da wayar da kai a matakin ƙasa, yana mai cewa batun lafiyar kwakwalwa abin ne da ya shafi kowa.
Ɗaya daga cikin mahalarta shirin, Salma Hussaini, wadda ba ta da gani, ta yaba da yadda ƙungiyar ta haɗa masu buƙata ta musamman a cikin shirin. Ta ce ta amfana sosai wajen fahimtar yadda ƙarfin tunani da dogaro da kai ke taimakawa mutum ya shawo kan ƙalubalen da yake fuskanta duk da rashin lafiyar jiki.