A Kalla Falasdinawa 35 Ne Su Ka Yi Shahada A Cikin Sa’o’i 24
Published: 21st, April 2025 GMT
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa; A kalla mutane 35 ne su ka yi shahada, yayin da wasu 62 kuma su ka jikkata a cikin sa’o’i 24.
Ma’aikatar kiwon lafiyar ta Gaza ta kara da cewa; Sojojin Mamaya sun kai wasu hare-hare a gabashin garin Beit-Hanun dake arewacin Gaza.
A cikin hemar ‘yan hijira dake tsakiyar Gaza, Falasdinawa 3 sun yi shahada, bayan da jiragen saman a ‘yan mamaya su ka kai hari.
A kudancin Gaza kuwa sojojin HKI sun tarwatsa wani gini na fararen hula a yankin Misbah dake arewacin birnin Rafah.
Daga ranar 18 ga watan Maris na wannan shekarar zuwa yanzu adadin Falasdinawan da su ka yi shahada sun kai 1864, yayin da wadanda su ka jikkata kuwa sun kai 4890.
Daga 7 ga watan Oktoba 2023 zuwa yanzu jumillar Falasdinawa da su ka yi shahada sun kai 51,240, sai kuma wani adadin da ya kai na mutane 116, 931, da su ka jikkata.
A gefe daya,kafafen watsa labarun HKI sun bayar da labarin cewa, wani yanayi mai tsanani ya faru a Gaza a yau Litinin,da hakan yake nufin cewa an kai wa sojojinsu hari mai tsanani wanda zai iya zama halaka wasu daga cikinsu. Haka nan kuma kafafen watsa labarun na HKI sun ambaci cewa; Uku daga cikin sojojinta sun jikkata saboda fashewar wata nakiya da aka dasa a bakin hanya a Beit-Hanun dake arewacin Gaza.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Riza’i: Babu Hannun Waje A Cikin Hatsarin Da Ya Faru A Tashar Ruwa Ta Shahid Raja’i
Kakakin kwamitin tsaron kasa a majalisar shawarar musulunci ta Iran ya bayyana cewa; ” Ya zuwa yanzu ba za mu iya yin hukunci akan dalilan da su ka haddasa fashewar abubuwa a tashar ruwa ta Shahid Raja’i ba, amma za mu iya cewa babu hannu waje a ciki.
Kakakin kwamitin tsaron kasar ta Iran Ibrahim Rizai wanda ya halarci taron da aka yi a Majalisa akan fashewar da aka samu a tashar ruwan ta shahid Raja’i, ya kuma kara da cewa; Fahimtata da abinda na ji daga abokan aikina dangane da abinda ya faru a tashar ruwa ta Shahid Raja’i, da kuma rahotannin da su ka iso mana, shi ne cewa abinda ya farun ba shi da alaka da waje.”
A ranar Asabar da ta gabata ne dai wasu abubuwa su ka fashe a tashar ruwa ta Shahid Raja’i dake Bandar Abbas a kudancin Iran, wanda ya haddasa asarar rayuka da kuma jikkatar daruruwan mutane.
An bude kwamitin bincike domin gano hakikanin abinda ya faru a tashar da kuma haddas fashewar abubuwan masu karfi.