2025-07-04@07:15:35 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1568
«Kwantaragi»:
Gwamnatin kasar Saudiya ta yi amfani da fasahar kirkirarren tunani ko (AI) don sauwakawa kanta da kuma mahajjata a hajjin wannan shekara ta 2025, kama daga kula da cinkoson mutane, kiyaye lafiyar mahajjata da haka kuma ta kyautata ayyukan mahajjata a cikin nutsuwa da rashin damuwa. Jaridar ArabNews ta kasar Saudiya ta bayyana cewa tare...
Shugabannin nahiyar Afirka sun tattauna hanyoyin samar da maganin kwalara a cikin nahiyar. An tattauna wannan batun ne dai a yayin taron da aka yi ta hanyar bidiyo daga nesa akan hanyoyin magance cutuka mabanbanta da su ka hada da riga-kafi. Wadanda su ka halarci tattaunawar ta bidiyo sun hada shugabannin kasashen Angola, Namibia, Malawi...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yau mutane na kallon bukukuwan Sallah da ido daban—yayin da wasu ke ganin ta zama lokaci na shakatawa nishadi kawai, wasu kuwa na cewa an bar al’adun da ke nuna kimar wannan babban lokaci na Musuluncin. Wadanda suka manyanta na ganin akwai abubuwa da dama da a...
Gidauniyar ta kuma kai ziyara fadar Hakimin Mokwa, Alhaji Muhammed Aliyu Shaaba, inda wakilan fadar suka yi maraba da tawagar wakilan gidauniyar tare da jinjina taimako da goyon bayan da aka nuna musu a wannan hali da suke ciki na ibtila’i. Kamar yadda Babban daraktan yankin, Musa Aliyu ya bayyana, gidauniyar Dr. Abubakar Bukola Saraki...
Mai bawa jagoran Juyin juya halin musulunci shawara kan al-amuran siyasa Ali Shamkhani ya sake tabbatar da cewa kasar Iran ba zata dakatar da aikin tace makamacin Uranium kamar yadda gwamnatin Amurka take so ba. Sannan ya kara da cewa kasar tana kokarin sake gabatar da wata shawara daban ga kasar Amurka. Ali shamkhani ya...
Farfesa Jibril Amin Likita kuma tsohon malamin Jami’a, ya rasu a jiya Laraba yana dan shekara 85 a duniya. Jaridar Daily Trusta ta Najeriya ta nakalto majiyar iyalar mamacin na tabbatar da haka. Ta kuma bayyana cewa kwamishin gidaje a jihar Adama Hon Abdullahi Prambe ya tabbatar da labarin. Sannan ya kara da cewa an...
Lamarin ya ƙara tsananta ne bayan fitowar wani littafi mai taken Original Sin da ya zargi wani na kusa da Biden da ɓoye yadda jikinsa ya gaza yayin yaƙin neman zaɓen 2024, wanda daga ƙarshe ya janye. Wannan ya ƙara sanya tambayoyi kan ko an san da cutar sankarar da ya kamu da ita tun...
Mahajjata aikin hajjin bana suna ci gaba da tururuwa zuwa tsayiwar Arafat a yau Alhamis Mahajjata na ci gaba da tururuwa zuwa Arafat domin gudanar da muhimmin rukunnan aikin Hajji. Mahajjata suna gudanar da ranarsu tun daga ketowar alfijir har zuwa bayan sallar isha’i a filin Arafat, bayan sun gudanar da ibadar ranar Tarwiyah, wadda...
Sojojin Yemen sun kai hare-hare kan filin jirgin saman Lod da ke Jaffa da aka mamaya da jiragen sama biyu marasa matuka ciki Sojojin Yemen sun sanar da kai wani farmakin soji kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye, domin jaddada goyon baya ga al’ummar Falastinu da ake zalunta da...
Abubakar ya tabbatar da cewa rundunar na da cikakken niyyar kare sararin samaniyar Nijeriya da rayuka da dukiyoyi a faɗin ƙasar nan. Ya kuma gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda irin goyon bayan da yake bai wa sojoji, musamman ta fannin kayan aiki da walwalar ma’aikata. A makon da ya gabata, rundunar ta kashe...
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya ce jam’iyyar PDP ce har yanzu jam’iyyar adawa mafi ƙarfi a Najeriya. Ya ce PDP tana da ƙarfi kuma za ta iya ƙalubalantar jam’iyya mai mulki a zaɓen 2027. Barazanar Yajin Aiki: Abuja da wasu jihohi 3 za su faɗa cikin duhu A shekara 25, na kashe tiriliyan...
Ma’aikatan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC), sun yi barazanar shiga yajin aiki, wanda hakan zai iya jefa Abuja, Kogi, Nasarawa da Jihar Neja cikin duhu. Ma’aikatan, ƙarƙashin ƙungiyoyin NUEE da SSAEAC, sun ce kamfanin ya gaza cika alƙawuran da ya ɗauka bayan sun dakatar da wani yajin aiki a watan Nuwamban 2024. A...
Attajirin nan na duniya dan asalin kasar Amurka, Bill Gates, ya ce a shekara 25 da gidauniyarsa ta yi da kafuwa, ya kashe Dalar Amurka biliyan 100, kwatankwacin Naira tiriliyan 161 wajen inganta kiwon lafiya a nahiyar Afirka. Attajirin ya bayyana hakan ne a Legas yayin wani taro da gidauniyarsa ta Gates Foundation ta shirya...
Gwamnatin kasar Amurka wacce ta bude cibiyoyin rarraba kayakin Agaji a Gaza, ta ce zata rufe cibiyoyin zuwa ranar Alhamis mai zuwa don sake tsara ayyukan Rabomn. Majiyar gwamnatin Amurka ta bayyana cewa ta dauki wannan matakin ne saboda sojojin yahudawan suna kashe falasdinawa wadanda suke fama da yunwa a lokacinda suka iso cibiyoyin raba...
Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Nain Qasim da kuma ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi sun gana a birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon inda bangarorin biyu suka tattauna al-amuran siyasa da yankin kudancin Asiya tare da kasar Lebanon. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto aragchi yana cewa dangantaka...
Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta jaddada haramcin gudanar da hawan Durbar na shagulgulan Babbar Sallah. Wannan sanarwar na cikin wata takarda da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya sanya wa hannu, kuma aka rabawa manema labarai a Kano. Sanarwar ta bayyana cewa an sanya wannan doka ne bisa...
ROOSC Ta Kaddamar Da Rabon Kayan Koyon Karatu a Karamar Hukumar Kaduna Sout Shirin Dawo da Yara Makaranta na Gwamnatin Jihar Kaduna Mai suna ROOSC ya kaddamar da rabon kayan koyon karatu ga dalibai a Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, Jihar Kaduna. An gudanar da bikin kaddamarwar ne a Makarantar Firamare ta LEA da ke...

Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Cewa: Amurka Da Isra’ila Suna Da Mugun Nufi Kan Iran Da Kasashen Musulmi
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila suna da mugun nufi kan Iran da kasashen musulmi Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila na da mugun nufi kan Iran da kasashen musulmi. A yayin wani jawabi da ta gabatar a wajen juyayin tunawa da rasuwar...
Sojojin Yemen sun kai hari kan filin jirgin saman Ben Gurium a wani aiki na musamman na tallafawa al’ummar Gaza Sojojin Yemen sun sanar da kai wani gagaruminj hari kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye ta hanyar amfani da makami mai linzami kirar Falasdinu 2. Hari ya gudana daidai...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yayin da sallah ya gabato, mutane da dama kan yi fadi tashi don biyan wasu bukatun su na bukukuwan sallah, kuma kamar yadda aka saba, a irin wannan lokaci ne iyalai da dama kan maida hankulan su don ganin sun biya wasu daga cikin bukatun su musamman wadanda...
Sanarwar tafiyar tasa ta biyo bayan ganawar da Inzaghi ya yi da jami’an Inter a ranar Talata, sanarwar da Inter Milan ta fitar ta ce Kulob din da Simone Inzaghi sun yanke shawarar rabuwa, “Wannan shi ne shawarar da aka dauka bisa yarjejeniyar juna”, shugaban Inter Giuseppe Marotta ya kara da cewa “Ina so in...

Guardian: Isra’ila Tana Kai Wa Makarantun Dake Dauke Da ‘Yan Gudun Hijira a gaza Hari, Tana Sane Da Hakan
Jaridar Guardian ta ta kasar Birtaniya ta bada labarin cewa, Hare-haren da sojojin HKI su ka kai kan wata makaranta, inda yan gudun hijira Falasdinawa suke samun mafaka da gangan suka yi shi, suna sane, kuma a halin yanzu suna Shirin kai wa wasu makarantun guda 4 hare-hare nan gaba. Jaridar ta kara da cewa:...
A cikin sanarwar da dukkan bangarorin da suka halarci taron suka sanya wa hannu, an amince da cewa, kungiyar za ta ba da wata guda domin tattauna bukatun JUSUN. Wani bangare na yarjejeniyar ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta saki kudaden da suka wajaba ga bangaren ma’aikatan shari’a a cikin wannan watan. Sanarwar ta...
Yau Talata, kungiyar masu jigilar kayayyaki da sayayya ta kasar Sin ta gabatar da alkaluman watanni 4 na farko na bana, wadanda suka nuna cewa, a watan Afrilu, sha’anin jigilar kayayyaki ya bayyana inganci da boyayyen karfi, kuma duk da kalubaloli da matsin lamba daga ketare da aka fuskanta, ya tafi yadda ya kamata tare...
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, yace nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu cikin shekaru biyu kadai shaida ce ta shugabanci mai hangen nesa da jaruntaka. Ya bayyana haka ne a yayin taron farko na National Dialogue on Citizen Engagement and National Security da aka gudanar a Abuja, mai...

Iran Ta Yi Watsi Da Da’awar Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa Na Da’awar Mallakar Wasu Yankunan Iran
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Tsibiran guda uku na Tunb Babba da Tunb Karami da Abu Musa yankuna ne Iran Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi watsi da ikirari da kungiyar hadin kan kasashen Larabawan yankin tekun Fasha (PGCC) ta yi dangane da tsibiran Iran guda uku, yana...
Ya ce yanzu lokaci ne da Arewa za ta nuna adalci ta hanyar barin shugaba daga Kudu ya kammala wa’adin mulkinsa. Ya ƙara da cewa, “Idan za a fitar da wani ɗan takarar shugaban ƙasa daga ‘yan adawa a nan gaba, to ya dace ya fito daga Kudu maso Yamma. Wannan ne dai-daito da adalci.”...
Farashin kayan miya, musamman kayan gwari ya yi tashin gwauron zabo a yayin da Babbar Sallah ta bana ta kawo jiki. Kuɗin kayan lambu ya ninka sau uku a cikin mako biyu, a yayin da Babbar Sallar ta zo wa iyalai da dama a Najeriya a hagunce, a sakamakon fama da matsananciyar matsalar tsadar rayuwa....
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya amince da biyan ma’aikatan gwamnati da ‘yan fansho da ke fadin jihar kyautar Sallah (Eid-el-Kabir) a matsayin alawus-alawus da ake yi a fadin jihar domin nuna tausayi da jajircewa wajen kyautata rayuwar ma’aikata. Kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar, Mahmud Muhammad Dantawasa ne ya bayyana haka...
Masu sayar da rago a jihar Zamfara sun nuna damuwarsu kan rashin samun ciniki gabanin bikin Eid-el-Kabir, duk da cewa ana samun dabbobi a kasuwanni. Shugaban kungiyar masu sayar da dabbobi ta jihar Zamfara, Malam Saidu Ibrahim Gusau ya bayyana haka a wata tattaunawa da gidan rediyon Najeriya a Gusau. Malam Gusau ya...
Dillalan rago a jihar Kano sun nuna damuwarsu kan rashin zuwan masaya da suke fuskanta duk da ‘yan kwanaki da suka rage ayi bukukuwan Sallah. Ziyarar da aka kai kasuwar dabbobi ta Gandun Albasa ta nuna cewa, da yawa daga cikin masu sayar da kayayyaki sun shafe tsawon yini ba tare da yin cinikin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya ƙara da cewa FRSC ta fara bincike kan dalilan da ke jawo hatsarin, kuma za ta gabatar da sakamakon binciken ga hedikwatarta da kuma Gwamnatin Jihar Kano domin ɗaukar matakan da suka dace don hana irin faruwar irin wannan iftila’i a gaba. Hukumar ta kuma sake jaddada ƙudirinta na wayar da kan al’umma kan...
Kasar Sin ta yi hasashen cewa an yi balaguro miliyan 657 a tsakanin yankunan kasarta lokacin hutun bikin Duanwu, wato Dragon Boat, daga ranar 31 ga watan Mayu zuwa ranar 2 ga watan Yuni, inda matsakaicin adadin tafiye-tafiyen da aka samu lokacin hutun bikin a kowace rana ya kai miliyan 219. Ma’aikatar sufuri ta kasar...
Ya ce an kai farmakin ne a kudancin yankin Mai-Galma a karamar hukumar Maru, domin dakile wani gagarumin farmaki da ‘yan bindiga suka shirya kai wa wasu al’ummomi. Bayan harin ta sama, sai aka tura sojojin kasa domin bin sahun ‘yan ta’addan da aka tarwatsa. “Sun tabbatar da lalata babura tare da kashe...
Ministan harkokin wajen Jamhuriyar musuluinci ta Iran wanda ya kai Ziyarar aiki kasar Masar ya bayyana cewa, cinikayya a tsakanin kasashen biyu za ta karu. Ministan harkokin wajen na Iran wanda ya gabatar da taron manema labaru na hadin gwiwa da takwaransa na kasar Masar ya ce: “A bisa yarjejeniyar da bangarorin biyu su ka...
Gwamnatin Kano ta ba makarantu hutun kwanaki goma domin bikin Babbar Sallah da za a yi ranar Juma’ar wannan makon. Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, a cikin wata sanarwa ta bayyana cewa makarantun za su fara hutun ne daga ranar Laraba, 4 ga watan nan na Yuni da muke ciki, zuwa ranar Lahadi, 15 ga...
Ranar Laraba, ruwan sama da hazo za su afkawa jihohin Zamfara, Adamawa, Kaduna, Sokoto, Kebbi da Taraba. Daga baya kuma, za a samu ruwan sama a jihohin Katsina, Bauchi da Sakkwato. Arewa ta rsakiya za ta fuskanci ruwan sama a Abuja, Nasarawa, Neja da Binuwe da safe, yayin da yamma za ta shafi Nasarawa, Filato,...
Wani shafin yanar gizo na sojojin Amurka ya tabbatar da cewa dakarun kasar Yemen ne suka kaiwa jirgin Truman mai dakon jiragen sama hari Wani shafin yanar gizo na sojojin Amurka ya amince da cewa: Dakarun kasar Yemen ne suka lalata jirgin Truman. Shafukan yanar gizo na rundunar sojin Amurka Stars and Stripes sun watsa...
Sojojin Yemen sun kai jerin hare-hare har sau 4 kan filin jirgin saman Ben Gurion tare da wasu wurare masu muhimmanci a cikin Isra’ila Sojojin Yemen sun sanar da aiwatar da hare-haren soji masu tsanani guda hudu a kan filin jirgin sama na Lod, wanda aka fi sani da “Ben Gurion” a haramtacciyar kasar Isra’ila,...
Wasu ’yan daba sun yi wa Mataimakin Firinsifal na wata makarantar sakandare dukan tsiya a wani mummunan harin da suka kai masa saboda ya hana wani ɗalibi satar jarabawa. A yayin da ake ci gaba da jarabawar kammala sakandare ta WASSCE da ake yi a halin yanzu ne, Mista Rotifa, mataimakin shugaban wata makaranta mai...
Aƙalla mutane 20 ne suka mutu bayan wani hari da jiragen sama na sojojin Najeriya (NAF) ya kai domin fatattakar ’yan bindiga a a Jihar Zamfara. Jiragen sojin sun kashe wasu ’yan sa-kai bisa kuskure, a yayin da ’yan sa-kan suke ƙoƙarin fatattakar ’yan bindiga da suka kai hari a yankin Mani a Ƙaramar Hukumar...
Aƙalla mutane 20 ne suka mutu bayan wani hari da jiragen sama na sojojin Najeriya (NAF) ya kai domin fatattakar ’yan bindiga a a Jihar Zamfara. Jiragen sojin sun kashe wasu ’yan sa-kai bisa kuskure, a yayin da ’yan sa-kan suke ƙoƙarin fatattakar ’yan bindiga da suka kai hari a yankin Mani a Ƙaramar Hukumar...
A wani yunkuri na rage adadin yara da suka daina zuwa makaranta, Gwamnatin Jihar Kaduna ta kaddamar da shiri mayarda yara 200,000 zuwa makaranta a cikin shekaru hudu masu zuwa, karkashin shirin Reaching Out-of-School Children (ROOSC). An bayyana wannan shiri ne a wani taron bita na kwanaki biyu da aka shirya tare da...
A wani lokaci yau Litini ne ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi zai fara ziyarar kwanaki biyu a kasashen Masar da Lebanon. Yayin ziyarar Araghchi zai gana da manyan jami’an Masar da na Lebanon domin tattauna dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu dama rikicin yankin. Ziyarar Araghchi a Masar za ta gudana ne bisa gayyatar...
Kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya sun bayyana rashin jin dadinsu ga Isra’ila, kan hana su ziyartar yankunan Falasdinawa Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa sun bayyana rashin jin dadinsu ga gwamnatin Isra’ila, game da rashin amincewa da tawagar kungiyar kasashen ta ziyarci yankin da aka mamaye a Gabar Yamma da kogin Jordan don tattaunawa da shugaban...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Shin wanne ya fi zafi – takaicin rasa matsuguni ko alhinin rashin sanin halin da ɗan uwa na jini yake ciki? Wannan ne halin da wasu al’ummomi a Ƙaramar Hukumar Mokwa ta Jihar Neja suke ciki, bayan da suka tsinci kansu tsamo-tsamo a tsakiyar wata mummunar ambaliyar ruwa....
Mahukuntan kasar Saudiyya sun sanar da cewa a ranar hawan arfa na bana, za a fassara hudubar da za a yi da harsuna 34 daga cikinsu da akwai Hausa da filatanci. Wasu harsunan Afirka da za a fassara hudubar ta Arfa da su, sun hada yarabanci, Sawahili, Somali da kuma Amharic na kasar Habasha. A...
barka.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp