2025-11-02@15:19:31 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1245
«yarjejeniya»:
Rahotanni sun bayyana cewa marziyeh Ja’afari ta kafa tarihi inda ta samu kyautar da hukumar kwallon kafa ta asiya ke bayarwa , inda ta zama kociyar da ta kasance zakara a wannan shekara, yayin da Salar Aghapur kuma ya zamo gwarzo a bangare kwallon Fustal na shekara ta 2025 da hukumar AFC ke bayarwa a...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Ismail Baqaei yayi maraba da dakatar da bude wuta da aka yi tsakanin kasashen Pakistan da Afghanistan, kuma yayi kira ga kasashen biyu da su warware sabanin dake tsakanin ta hanyar tattaunawa da kuma diplomasiya. Iran ta dade tana ba da shawarwarin magance matsalolin tsaro a yammacin Asiya da...
Kungiyar Euro-Med ta bukaci bangarori su shiga Gaza domin tattara bayanai kan kisan kiyashin Isra’ila
Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta Euro-med mai hedkwata a Geneva ta yi kira ga kasashen duniya da su tabbatar da shiga Gaza ba tare da ‘yan jarida, masu bincike, da masana harkokin shari’a don tattara bayanan kisan kiyashin da Isra’ila a Gaza da kuma hukunta wadanda suka aikata laifin. A cikin wata sanarwa da...
Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta kama gungun mutane 11 da ake zargi da kasancewa ’yan fashi da makami da ke addabar matafiya a kan hanyar Katsina zuwa Kano. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Abubakar Aliyu, ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba a Katsina cewa waɗanda ake zargin sun kware wajen tare...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a jawabin da ya gabatar a taron tsakiyar shekara ta ministocin harkokin wajen kungiyar yan ba ruwammu wato NAM a birnin Kampala babban birnin kasar Uganda a jiya Laraba, ya jadda bukatar hadin kai da goyon baya a tsakanin kasashen kungiyar, wajen fuskantar rashin mutunta dokokin kasa...
Tsohon ɗan majalisar wakilai, Farouk Lawan, ya ce afuwar shugaban ƙasa ya yi masa, ta ba shi kwarin guiwar yin wata sabuwar tafiyar siyasa. Ya bayyana cewa ya bar tafiyar Kwankwasiyya ne saboda jagorancinta ya yi watsi da shi lokacin da ya fi bukatrsu. ’Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun sace dabbobi a Katsina...
Shugaban Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano (HMB), Dakta Mansur Mudi Nagoda, ya kai ziyarar ba-zata ta duba aiki a Asibitin karbar Haihuwa na Imamu Wali, na Marmara, da kuma Asibitin Sabon Bakin Zuwo. Ya kai ziyarar ce domin tabbar bin umarnin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, na wucin gadi wajen sauya...
Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya
Daga nan sai kakakin ya ce, “Ba zai yiwu bangaren Amurka ya nemi tattaunawa a bangare guda, alhali a daya hannun yana barazanar kaddamar da sabbin takunkumai kan kasar Sin ba. Wannan ba ita ce hanya mai dacewa ta gudanar da cudanya da Sin ba.” (Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin...
A halin yanzu, sama da mata da yarinya miliyan 600 a duniya suna cikin rikici da yaki, sannan mata da ‘yan mata biliyan 2 ba su da tabbacin tsaron zamantakewa. Kamar yadda babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana, cewar har yanzu ci gaban mata a duniya yana fuskantar “kalubale da ba a taba...
Tawagar Super Eagles ta Najeriya sun kara da Cheetahs na Jamhuriyar Benin a wasan neman cancantar shiga gasar cin Kofin Duniya ta 2026. Wasan da suka fafata a filin wasa na Godswil Akpabio da ke Jihar da Uyo ya kasance tamkar mai zafin gaske kuma an nuna bajinta. Tun kafin a fara wasan, an samu...
Shugabannin kasashen Amurka, Masar,Katar da Turkiya da su ka halarci taron na “ Herm-Sheikh” a kasar Masar sun sanya hannu akan yarjejeniyar tsagaita wutar yaki a Gaza. A jiya Litinin ne dai aka bude taron na Kasar Masar, wanda kuma ya sami halartar Fira ministan kasar Pakistan da kuma shugaban kasar Faransa. Da yake gabaatar...
Mai bai wa shugaban kasar Iran shawarar akan harkokin mata da iyali Malama Zahra Beruz Azar ta gabatar da shawarar a kulla wata yarjejeniya ta tausayawa a tsakanin matan duniya domin samar da damar gina rayuwa ta jin kai da ‘yan’adamtaka mai dorewa. Malama Zahra Behruz Azar ta gabatar da wannan shawarar ne dai a...
“Idan mutum ya shiga jarrabawa kuma Allah Ya kawo dama ta afuwa, dole ne ya yi farin ciki. Ni da iyalina da masoyana mun yi murna ƙwarai,” in ji Lawan. “Na gode wa Allah da kuma Shugaba Tinubu saboda ya yi abin da ya kamata a yaba masa.” Ya bayyana cewa rayuwa a gidan yari...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Shekara da shekaru kungiyar malaman jami’oi ASUU ta kwashe ta na gudanar da yajin aiki ba tare da samun biyan bukata ba. Irin wannan yajin aiki da kungiyar malaman ke shiga ya jefa dalibai da malaman da ma harkar ilimi cikin halin ni ‘yasu a Najeriya. NAJERIYA...
Jam’iyyun adawa a ƙasar Jamhuriyar Kamaru sun ayyana Issa Bakary Tchiroma a matsayin wanda lashe zaɓen shugaban ƙasar da gagarumin rinjaye. Gamayyar jam’iyyun adawa da ƙungiyoyin fararen hula na Union for Change ta ce sakamakon da suka tattara daga fadin ƙasar da ƙasashen waje ya nuna Bakary ya samu kashi 60 zuwa 80 cikin ɗari na...
Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar wa al’ummar jihar a shirye ta ke ta ci gaba da kare mutuncin daidaikun mutane da kungiyoyin da suka sadaukar da kansu domin samar musu da sahihin bayanan sirri da za su kara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Nijar. ‘Yan sanda a jihar Neja da ma...
Kungiyar ‘Yan Dako ta kasa reshen jihar Jigawa ta kaddamar da Malam Muhammad Tajudeen Maigatari a matsayin sakataren kungiyar na jihar. Da yake jawabin a lokacin bikin kaddamawar a garin Maigatari, Shugaban kungiyar na jihar Malam Nasiru Idris Sara, ya bayyana shugabanci a matsayin rikon amana a maimakon hanyar tara dukiya da alfahari, a don...
A cewar NEMA, mutane 135,764 ne suka rasa matsugunansu, yayin da 115 aka bayyana bacewarsu, yayin da wasu 826 suka samu raunuka sakamakon ambaliyar. Bugu da kari, gidaje 47,708 sun lalace, yayin da gonaki 62,653 suka lalace a fadin jihohin da abin ya shafa. Hukumar ta kara da cewa, daga cikin wadanda abin ya...
Cibiyar kula da lafiya ta Nasser Medical Complex da ke Gaza ya bayyana cewa: Yara 5,500 ne ke bukatar agajin gaggawa a kasashen waje Daraktan cibiyar kula da lafiya ta Al-Shifa da ke Gaza ya ce: Babu wani agajin jinya da ya shiga zirin Gaza duk da cewa an shafe sa’o’i 72 tsagaita bude wuta....
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan yadda shugaba Bola Tinubu ya yi wa wasu mutane afuwa, ciki har da waɗanda suka aikata manyan laifuka. A cikin saƙon da Atiku ya wallafa a shafinsa na X, ya ce ana yin afuwa ne ga waɗanda aka yi wa rashin adalci ko waɗanda suka...
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya ASUU a ranar Lahadi ta sanar da shiga yajin aiki na makonni biyu, wanda zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, a duka jami’o’in gwamnati na ƙasar. Shugaban ƙungiyar Farfesa Chris Piwuna ne ya sanar da hakan a lokacin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja, a ranar...
Kasashe hudu da suka fi kokari a cikin wadanda suka kare a mataki na hudu za su fafata wasannin raba-gardama, sai wadanda suka samu nasara su sake raba-gardama da wasu kasashen na waje. A yanzu daI manyan kasashen nahiyar ta Afirka irin su Kamaru da Nijeriya suke fuskantar barazanar rasa gurbi, duk da haka...
Nasarorin da kasar Sin ta samu a cikin gida, sun kafa ginshikin jagorancin duniya, wajen samar da ci gaban harkokin mata, musamman ta hanyar fitar da darussa, ta hanyar kyautata mu’amala tsakamnin bangarorin biyu. Babban misali shi ne yadda ake samun bunkasar dangantakar mata tsakanin kasashen Kenya da Sin, wadda aka inganta yayin ziyarar...
Rundunar sojin Najeriya, ta bayyana cewa dakarunta sun kashe ’yan ta’adda biyar a wani samame da suka kai yankin Magumeri da Gajiram, a Jihar Borno. Kakakin rundunar Operation Haɗin Kai, Kanar Sani Uba, ya ce dakarun sun yi arangama da wasu ’yan ta’adda 24 da ke tafe a ƙafa a ranar Juma’a. Mutane 2 sun...
Rundunar ‘yansanda ta tabbatar da cewa ana gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin musabbabin mutuwarta. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tsaro Sojoji Sun Ƙaryata Rahoton Cewa Ƴan Bindiga Sun Mamaye Sansaninsu A Kwara October 5, 2025 Tsaro Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 450, Sun Ceto Mutane 180 A Satumba — DHQ October 4,...
Shugabannin Faransa, Jamus, da Biritaniya: Sun kuduri aniyar farfado da tattaunawa da Iran Kasashen Faransa da Jamus da Birtaniya sun bayyana aniyarsu ta farfado da shawarwari da Iran da Amurka dangane da shirin makamashin nukiliyar Iran da nufin cimma cikakkiyar yarjejeniya mai dorewa. A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa, kasashen uku sun yi la’akari...
Aƙalla mutum takwas ’yan Ƙungiyar tsaro ta Civilian JTF ko ’yan ƙato da gora aka sanar an kashe a ƙauyen Dan Loto da ke Ƙaramar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara. Harin dai na zuwa ne makonni biyu kacal bayan da wasu ’yan bindiga suka kai hari a wani masallaci tare da kashe wasu masallata biyar...
Bugu da kari, an rufe shafukan hakar ma’adanai haramtacce 98 a fadin kasar. “An kiyasta cewa Nijeriya na asarar kusan Dala biliyan 9 a kowace shekara sakamakon haramtacciyar hakar ma’adanai. Wannan sata ta albarkatunmu da ya kamata ta bunkasa kasarmu ta wuce kima, kuma lokaci ya yi da za a kawo karshensa,” in ji...
Hukumar Kwastam shiyyar bodar Najeriya ta Seme da ke jihar Legas ta ce ta cafke motoci biyar da ke maƙare da buhuna 10,000 na lalatacciyar fulawa da darajarsu ta kai Naira biliyan 1.2. Rundunar ta kuma ce ta tara jimillar kuɗin shigar da ya kai Naira biliyan daya da rabi a watan Satumba, wanda hakan...
Hukumar Bunkasa Ma’aikata ta Jihar Jigawa ta shirya taron karawa juna sani na kwana daya ga jami’an kula da dakunan karatu a wani bangare na aikinta na daga darajar ma’aikata da ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu. A jawabinsa na bude taron, Darakta Janar na MDI, Umar Farouk Wada, ya ce makasudin shirya taron...
A cewar kungiyar, wadannan kalubalen sun hada da takurawar dokoki daga hukumomin gwamnati, karancin isar da danyen mai daga Kamfanin Man Kasa na Nijeriya (NNPC), matsalolin da suka shafi farashin kayayyaki, da kuma tsoma bakin kungiyoyin ma’aikata da na dillalan man fetur. ACF ta fi mayar da hankali ne kan rawar da Kungiyar ’Yan...
Cibiyar Kula da Harkokin kasuwanci ta kasa ta bayyana kafa Cibiyar Gudanar da taron Kasuwanci na Najeriya a wani bangare na ganin ba a samarda cibiyoyi da ke da aiki iri ɗaya ba. Babban magatakardar Cibiyar Mista Victor Olannye, ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da takardar a yayin taron jin...
Gwamnatin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da tsare tsare da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar a hukumance, kamar yadda ofishin Firayim Ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sanar a yau Juma’a. Wannan dai na zuwa ne bayan ci gaba da tsaikon da aka samu na tsawon kwana daya biyo bayan...
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci dukkanin bangarorin da su yi aiki da kuma mutunta yarjejeniyar da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da kuma yin amfani da wannan damar. Da yake jawabi a wurin taron Majalisar Dinkin Duniya, Guterres ya bayyana cewa, “Ina kira ga dukkan bangarorin da su mutunta...
Gwamnatin tarayya ta yi asarar jimillar gangar danyen mai miliyan 13.5 wanda kudinsa ya kai dala biliyan 3.3 sakamakon sata da fasa bututun mai tsakanin shekarar 2023 zuwa 2024, in ji wata kungiya mai fafutukar kare masana’antu ta Nijeriya (NEITI). Sakataren zartarwa na NEITI, Dokta Ogbonanya Orji, ne ya bayyana hakan a Legas a taron...
Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko October 8, 2025 Daga Birnin Sin Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan October 8, 2025 Daga Birnin Sin Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai...
Jami’an Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) a Jihar Jigawa, sun kama wani matashi da ake zargi da sato motar asibiti daga Jamhuriyar Nijar, yayin da yake ƙoƙarin shigowa da ita Najeriya. Kwanturolan hukumar a jihar, Tahir Abdullahi Musa ne, ya tabbatar wa manema labarai hakan a Dutse. Falasdinawa na murna da tsagaita wutar...
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kaddamar da sabuwar cibiyar taro ta Ahmadu Bello da aka gina a Bauchi, inda ya bayyana ta a matsayin alamar ci gaba a gwamnatin Gwamna Bala Mohammed. Da yake jawabi a wajen taron, Obasanjo ya jaddada muhimmancin dunkulewar duniya, inda ya ce babu wata al’umma da za ta...
Ƙungiyar Ma’aikatan Manyan Makarantun Najeriya (SSANU) da Ƙungiyar Ma’aikatan Ilimi (NASU), sun shirya gudanar da zanga-zangar gargaɗi ta rana ɗaya a yau Alhamis saboda Gwamnatin Tarayya ta gaza cika musu alƙawuran da ta ɗauka. Ƙungiyoyin, ƙarƙashin jagoranci Joint Action Committee (JAC), sun gudanar da taron gaggawa a ranar Laraba don shirya zanga-zangar. 2027: Atiku, Jonathan...
Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne, sun tare hanyar Gusau zuwa Gummi a Jihar Zamfara, inda suka sace mutane da dama. Wata majiya ta bayyana cewa, maharan sun tare motoci sannan suka yi awon gava da fasinjojin da ke ciki. Yadda Obasanjo ya ƙaddamar da cibiyar taron ƙasa da ƙasa a Bauchi Ban yi...
Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ƙaddamar da sabon ginin Cibiyar Taron Ƙasa da Ƙasa, wadda aka sanya wa sunan Sir Ahmadu Bello a Jihar Bauchi. An ƙaddamar da cibiyar ne kafin babban taron zuba jari da nufin bunkasa kasuwanci da masana’antu a jihar. Ban yi murabus don ina da laifi ba — Nnaji Kamfanonin...
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bai wa wata ma’aikaciyar lafiya ’yar ƙabilar Igbo kuma ‘yar asalin jihar Anambra, Marbel Ijeoma Duaka, kyautar gida mai dakuna biyu. Gwamnan ya kuma ba ɗan ma’aikaciyar aikin yi na dinidindin saboda jajircewarta da sadaukarwa wajen hidimtawa jihar na sama da shekara 20. Matar aure mai ’ya’ya huɗu...
Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran ya jaddada cewa: Iran ba zata daina samar da magungunan da take yi ta hanyar fasahar makamashin nukiliya ba Kakakin Kwamitin Tsaro da Harkokin Waje na Majalisar Shawarar Musulunci (wato Majalisar Dokoki) Ibrahim Reza’ei, ya tabbatar da cewa ana ci gaba da samar da magungunan ta hanyar fasahar makamashin...
Haka kuma ya buƙaci a aiwatar da gyare-gyare don farfaɗo da tattalin arziƙi, inganta ilimi da kiwon lafiya, tare da samar da damammaki ga matasa.Ya ƙara da cewa majalisar za ta sake duba Kundin Tsarin Mulki na 1999 domin bunƙasa dimokuraɗiyya da inganta mulki a Nijeriya.ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan LabaraiDa Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC...
Mambobin kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ reshen jihar Nasarawa sun zabi sabbin jami’anta da za su gudanar da harkokin kungiyar na tsawon shekaru uku masu zuwa. Shugaban kwamitin zaben, Mista Samson Osuo, ya sanar da Abubakar Abdullahi na jaridar Daily Trust a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 21 da Danjuma Joseph...
Sisi: Samun zaman lafiya na gaskiya a Gabas ta Tsakiya ya dogara da kafa ‘yantacciyar kasar Falasdinu
Shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sisi ya ce, “Za a samu zaman lafiya na gaskiya a yankin Gabas ta Tsakiya ne kawai idan an kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta bisa ka’idojin kasa da kasa da kuma hanyar da za ta maido da hakkokin masu hakki.” A jawabin da ya yi na bikin cika...
Ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya tana aiki don ƙirƙirar yanayi mai sauƙin zuba jari, da zaman lafiya don masana’antu, da haɓaka tattalin arziki mai dorewa. A ƙarshe, ya kira masu ruwa da tsaki da su fifita tattaunawa a wajen neman mafita maimakon rikici, yana cewa, “Nijeriya ƙasa ce mai girma da ke neman...
Talaucin Da Ya Ninku Fiye Da Sau Biyu A Gwamnatin Tinubu, An Ƙuduri Aniyar Kawar Da Shi Nan Da Shekaru 5
A cewar Bankin Duniya, talauci a tsakanin mazauna karkarar Nijeriya ya kai kashi 75.5 cikin dari, wanda ke nuna ƙaruwar rashin daidaito da kuma tsananin matsin tattalin arziki a fadin kasar. Ministan ya ce, gwamnati ta kuma kuduri aniyar inganta hasashen tattalin arziki da inganta sauye-sauyen da zai sanya Nijeriya ta samu ci gaba...
Sanarwar ta ce, hare-haren kakkaɓe maɓoyar ‘yan bindigar na zuwa ne a karkashin shirin ‘Operation Lafiya Nakowa’, da nufin fatattakar ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a jihar Taraba. Ya kara da cewa, harin ya biyo bayan sahihan bayanan sirri kan ayyukan ‘yan ta’addan a kusa da Tarhembe, Tornyi, TY Farm, da...
A karon farko a tarihin kwallon raga ta mata ta Iran ta zami lashe kofin zakarun Asiya, bayan samun galaba akan kawarta ta kasar Uzbakestan. An fara wasan fidda gwani a tsakanin kungiyoyin kwallon raga na mata na Asiya a ranar 2 ga watan nan na Oktoba, a birnin Tashqand wanda ya zo karshe a...