Kotu ta daure ango wata 6 saboda likin kudi a bikinsa
Published: 8th, April 2025 GMT
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta yanke wa wani shahararren mai sana’ar gyaran fuska, Abdullahi Musa Huseini, wanda aka fi sani da Amuscap, hukuncin daurin watanni shida a gidan yari saboda yin likin da takardun Naira a lokacin bikin aurensa.
Mai Shari’a S.M. Shu’aibu ya yanke wa Huseini Amuscap hukuncin ne bayan ya amsa laifinsa da ake tuhumar sa, wanda ya saba wa sashe na 21(1) na Dokar Babban Bankin Najeriya (CBN) ta shekarar 2007.
Takardar tuhumar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 6 ga Disamba, 2024, a Cibiyar Bikin Ali Jita da ke Kano, inda aka ga angon a wani bidiyo yana yin kari da Naira dubu dari a takardun Naira dubu daya-daya a yayin da yake rawa.
Bayan lauyan Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC), Zarami Mohammed, ya gabatar da hujjojin karar tare da shaidar bidiyo a kotu. da kuma amsar laifin Huseini, Mai Shari’a Shuaibu ya ya yanke masa hukuncin daurin watanni shida a gidan yari ba tare da zabin tara ba.
Gaza: Isra’ila ta kashe Falasdinawa 58 a awa 58 Kisan Janar Alƙali: Kotu ta ɗage shari’a zuwa 28 ga MayuHukumar EFCC ta ci gaba da gargadin jama’a game da bata ko kuma yin amfani da takardun Naira ba daidai ba, musamman a lokacin bukukuwan jama’a, tana mai bayyana irin wadannan ayyukan a matsayin zagon kasa ga tattalin arziki.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Naira
এছাড়াও পড়ুন:
DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu
Hukumar Tsaron Farin Kaya a Nijeriya DSS, ta gurfanar da fitaccen ɗan gwagwarmayar nan, Omoyele Sowore a kotu.
A ƙunshin ƙarar da DSS ta gabatar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta haɗa da shafukan sada zumunta na X da kuma Facebook, inda take zarginsu da ba da ƙofar aibata Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Bida Poly ta sa sojoji kula da jarrabawar ɗalibai Kukan al’umma kan lalacewar hanyar DukkuDarekan shigar da ƙara na Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya, M.B Abubakar da wasu lauyoyi huɗu —M.E. Ernest da U.B. Bulla da C.S. Eze da kuma E.G. Orubor, ne suka shigar da ƙarar a madadin Gwamnatin Tarayya da kuma hukumar ta DSS.
DSS wadda ta kafa hujja da sashe na 24 da ke cikin kundin dokokin yanar gizo, ta ce Sowore ya yi amfani da shafukansa na dandalan sada zumunta na X da Facebook wajen wallafa wani saƙo da ke cin mutuncin Shugaba Tinubu.
Tun dai a farkon watan nan ne DSS ta buƙaci goge wani saƙo da ɗan gwagwarmayar ya wallafa wanda ta riƙa a matsayin bayanan ƙarya, cin zarafi ta yanar gizo da kalaman haddasa ƙiyayya, waɗanda kuma ta ce na iya haddasa rikici su kuma ɓata sunan Najeriya a ƙasashen waje.
Sai dai har zuwa ranar Litinin, 15 ga watan Satumba, babu wani mataki da aka ɗauka na goge saƙon da DSS ɗin ta buƙata.