2025-10-13@20:24:23 GMT
إجمالي نتائج البحث: 10144

«Sarkin Alkaleri»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Masana da shugabanni da suka halarci taron, ciki har da Farfesa Isah Ali Pantami, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da sauran fitattun malamai, sun yaba da wannan ƙudiri na gwamnatin Katsina. Rahotanni sun nuna cewa sama da yara 300,000 ne ba sa zuwa makaranta a Katsina, ciki har da dubban almajirai da ‘yan mata. Wannan ne ya sa gwamnati ta ɗauki wannan mataki domin inganta ilimi da kuma bai wa matasa damar samun kyakkyawar makoma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An ba shi kyautar ne a daren ranar Litinin a Theatre du Chatelet da ke birnin Paris, inda ya doke matashin Barcelona, Lamine Yamal, wanda ya lashe kyautar matashin ɗan wasa mafi ƙwazo. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar Ƙididdiga a Najeriya, NBS ta ce arzikin cikin gida da kasar ke samu ya karu da kashi 4.23 cikin 100 a rubu’i na biyu na shekarar 2025 da muke ciki. Sabbin alkaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa an samu karin kashi 3.48 idan aka kwatanta da irin wannan lokacin a 2024, lamarin da hukumar ta ce alamu ne na ingantar tattalin arzikin kasar. Hukumar ta NBS ta ce fannin aikin gona ne kan gaba wajen samar da karuwar arzikin kasar, wannan ya karu zuwa kashi 2.82 sabanin kashi 2.60 a 2024. Sauran fannonin da hukumar ta ce an samu ci gaba sun hada da fannin masana’antu da, da fan fetur da kuma fannin ma’adinai. NBS ta ce...
    Rahotanni sun bayyana cewa kimanin kaso 8% na mambobin majalisar dinkin diniya ne suka sanar da amincewarsu da kasar falasdinu, a daidai lokacin da Isra’ila take ci gaba da kisan kare dangi a Gaza kuma take kara fadada  mamaye yankuna  a gabar yammacin kogin jodan. Kasaashen faransa, luxambourg , malta da manako ne suka sanar da amincewa da yankin falasdinu a matsayin kasar a wajen taron babban zauren majalisar dinkin duniya,  prime ministan kasar kanada marka caney ya fadi cewa amincewar tana da muhimmanci sosai, kana yayi gargadin cewa an shafe batun yancin cin gashin kai ga yankin falasdinu. Sai dai duk da amincewa da yankin na falasdinu a matsayin kasa, amma ta’addancin da Isra’ila ke yi a yankin gaza...
    Mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng ya gana da tawagar ‘yan majalisar wakilan Amurka karkashin jagorancin Adam Smith a yinin yau Litinin 22 ga wata a birnin Beijing. He Lifeng ya ce, a ranar 19 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaba Donald Trump sun yi wata tattaunawa ta wayar tarho, kuma sun cimma muhimmiyar matsaya, tare da samar da jagoranci bisa manyan tsare-tsare don tabbatar da daidaiton dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka a mataki na gaba. Kasashen Sin da Amurka na da sararin yin hadin gwiwa da kuma samun moriyar juna. Ana sa ran Amurka za ta sa kaimi wajen yin magana da kasar Sin bisa ka’idojin mutunta juna, da zaman lafiya da samun nasara...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a yau 22 ga wannan wata cewa, a yayin da ake raya duniya bisa tsarin bai daya, musayar kwararru a tsakanin kasa da kasa ta sa kaimi ga raya fasahohi da tattalin arzikin kasashen duniya. Kasar Sin tana maraba da kwararru daga bangarori da sana’o’i daban daban na kasa da kasa su zo kasar ta Sin su gudanar da harkokinsu don sa kaimi ga raya zamantakewar al’ummar dan Adam da kuma samun ci gaban sha’aninsu baki daya. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
    Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ayyana gobe Talata, a matsayin ranar ɗaya ga watan Rabi’ul Thani, 1447 bayan hijira, wanda ya kawo ƙarshen watan Rabi’ul Awwal, 1447, daidai da ranar 23 ga Satumba, 2025. Sanarwar ta fito ne a wata takarda da Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaid, wanda shi ne shugaban kwamitin da ke bai wa Majalisar Sarkin Musulmi shawara kan al’amuran addini, ya sanya wa hannu ya kuma raba wa manema labarai. A sanarwar, Sarkin Musulmi bai fayyace wuraren da aka ga sabon watan ba, sai dai ya bayyana cewa ya gamsu da sahihan rahotannin da aka gabatar, lamarin da ya sa ya ayyana ganin watan a hukumance. Ya yi addu’ar Allah Ya kawo zaman lafiya da...
      29. Florian Wirtz (Liverpool)   28. Virgil van Dijk (Liverpool)   27. Declan Rice (Arsenal)   26. Erling Haaland (Man City)   25. Denzel Dumfries (Inter Milan)   24. Fabian Ruiz (PSG)   23. Jude Bellingham (Real Madrid)   22. Alexis Mac Allister (Liverpool)   21. Serhou Guirassy (Borussia Dortmund)   20. Lautaro Martinez (Inter Milan)   19. Joao Neves (PSG)   18. Scott McTominay (Napoli)   17. Robert Lewandowski (Fc Barcelona)   16. Vinicius Jr (Real Madrid)   15. Viktor Gyokeres (Arsenal)   14. Desire Doue (PSG)   13. Harry Kane (Bayern Munchen)   12. Kvicha Kvaratskhelia (PSG)   11. Pedri Gonzalez (Fc Barcelona)   10. Nuno Mendes (PSG)   9. Gigio Donnarumma (Man City)   8. Cole...
    Ɗan wasan gaban PSG da Faransa, Ousmane Dembélé ya lashe kyautar Ballon d’Or ta bana. Balon d’or dai ita ce lambar yabo mafi girma a duniyar ƙwallon kafa wacce ake bai wa gwarzon ɗan wasa na shekara.
        Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Faransa ta bi sahun Birtaniya, Australia da Canada da sauran ƙasashen duniya sama da 140 da suka amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai ’yanci. Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ne ya tabbatar da amincewar gwamnatinsa na kafa ƙasar Falasdinu a hukumance. Tattalin arzikin Najeriya ya ƙara haɓaka — NBS NEF za ta ƙaddamar da taron zuba jari don bunƙasa Arewa Macron ya bayar da tabbacin ne a yayin da yake jawabi a babban taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York. Mista Macron ya ce lokaci ya yi da ya kamata a kawo ƙarshen yaƙin Gaza tare da sakin sauran Isra’ilawa 48 da Hamas ke garkuwa da su. Ya ce lokaci kaɗan ne ya rage wa duniya ta iya wanzar...
    Hukumar Ƙididdigar a Najeriya, NBS ta ce arzikin cikin gida da ƙasar ke samu ya ƙaru da kashi 4.23 cikin 100 a rubu’i na biyu na shekarar 2025 da muke ciki. Sabbin alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa an samu ƙarin kashi 3.48, idan aka kwatanta da daidai wannan lokacin a 2024, lamarin da hukumar ta ce alamu ne na bunƙasar tattalin arzikin ƙasar. An gudanar da bikin ɗaga tutar Falasɗinu a Birtaniya CAC ta soma yi wa kamfanoni rijista da fasahar AI NBS ta ce fannin aikin gona ne kan gaba wajen samar da ƙaruwar arzikin ƙasar, wanda ya ƙaru zuwa kashi 2.82 saɓanin kashi 2.60 a 2024. Sauran fannonin da hukumar ta ce an samu ci...
    Sanarwar ta ƙara da cewa, Gwamna Lawal ya jaddada cewa tsarin dimokuraɗiyyar Kanada, ƙarfafan tattalin arziƙi, hakar ma’adinai ta hanyar da ta dace, da kuma harkokin kasuwanci masu zaman kansu masu kirkire-kirkire sun sanya ta zama abokiyar haɗin guiwar da ta ta dace ga Afrika.   Ya ce, “Idan Afrika za ta cika burinta gaba ɗaya, dole ne mu gane cewa ci gaba ba wai kawai batun manufofin ƙasa bane; yana kuma buƙatar aikace-aikacen matakan jihohi da ƙananan hukumomi.   “Yayin da Gwamnatocin Tarayya ke ba da jagorar manufofi, a matakin Jihohi, larduna, da Ƙananan Hukumomi ake fassara alƙawuran kasuwanci, zuba jari da ci gaba zuwa ainihin gaskiya.   “Matakan jihohi sune inda manoma ke noma abincin da ke ciyar...
    Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta ce a karon farko za ta shirya taron zuba jari da samar da masana’antu na Arewacin Najeriya, wanda aka shirya gudanarwa a ranakun 29 da 30 ga watan Satumba a Abuja. Taron wanda aka shirya tare da hadin gwiwar jihohin arewa 19 da kuma kamfanin raya yankin – NNDC, na da nufin mayar da yankin a matsayin wata cibiya ta samun bunkasar tattalin arziki da habaka masana’antu. An gudanar da bikin ɗaga tutar Falasɗinu a Birtaniya CAC ta soma yi wa kamfanoni rijista da fasahar AI Da yake magana a taron manema labarai da aka gudanar ranar Litinin a Abuja, kakakin kungiyar, Farfesa Abubakar Jika Jiddere, ya bayyana taron a matsayin “kira domin zaburar da...
    Dangane da halin da ake ciki game da rikicin Falasdinu da Isra’ila, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a yau Litinin 22 ga wata cewa, karfin soja ba zai iya samar da zaman lafiya ba, kuma tashin hankali ba zai iya samar da tsaro ba. Kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da kasashen duniya wajen ci gaba da jajircewa a kan tsagaita bude wuta da kawo karshen yakin da ake yi a zirin Gaza, da kuma matukar nuna goyon baya ga tabbatar da adalci ga al’ummar Falasdinawa wajen maido da hakkinsu na kasa, da kuma kara azamar warware matsalar Falasdinu tun da wuri ta hanyar samar da cikakkiyar mafita, mai adalci...
    Tawagar jami’an diflomasiyyan Falasɗinu ta gudanar da bikin ɗaga tutar ƙasar a Litinin ɗin nan a birnin Landan kamar yadda kafar labarai ta DW ta ruwaito. Bikin ɗaga tutar na zuwa ne kwana guda bayan da Birtaniya ta amince da Falasɗinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta. CAC ta soma yi wa kamfanoni rijista da fasahar AI Dalilin da muke goyon bayan Tinubu kan karɓo bashi — Majalisar Wakilai Shugaban tawagar jami’an diflomasiyyan Falasdinawa a Burtaniya Husam Zomlot, ya daga wani allo mai ɗauke da rubutun ‘Ofishin jakadancin Falasɗinu’ sannan kuma ya ce nan ba da jimawa ba za a buɗe ofishin a hukumance bayan kammala wasu sharudda dangane da dokoki da kuma tsarin gudanarwa. Mista Zomlot ya yi...
    A halin yanzu, shugaba Bola Tinubu yana ganawa da gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara a fadar shugaban kasa dake Abuja a yammacin yau Litinin. Ganawar na zuwa ne kwanaki kadan bayan Fubara ya koma ofis a ranar 19 ga watan Satumba bayan da Shugaba Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da aka kafa a jihar Ribas tun farko. Tinubu ya bayyana matakin ne domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali bayan shafe watanni ana rikicin siyasa da ke barazana ga harkokin mulki da tsaro a jihar mai arzikin man fetur. Cikakken bayanai na nan tafe… Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da amincewar da kasashen Birtaniya, Australia, da Canada suka yi wa kasar Falasdinu, tana mai bayyana hakan a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da hakkin al’ummar Palasdinu na kasarsu. A cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Lahadi, kungiyar ta yi kira ga kasashen duniya da MDD da su mayar da Isra’ila saniyar ware tare da dakatar da duk wani nau’i na hadin gwiwa da ita. Hamas ta yaba da wannan amincewa da ita a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da ikirarin da al’ummar Falastinu ke yi na neman kare filayensu da wuraren ibadarsu masu tsarki, tare da fatan samun kasa mai cin gashin kanta wacce take da Quds a...
    Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, ta bayyana cewa “Kisan kare dangi da ake ci gaba da yi a zirin Gaza ya zama babban gwaji ga Majalisar Dinkin Duniya. Idan muna son kungiya mai inganci kuma mai amfani, dole ne mambobinta su dauki matakin gaggawa tare da tsayin daka wajen dakatar da wannan zalunci da hukunta masu laifi.” Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghai ya ce zasu hadu a birnin New York domin halartar taron shekara-shekara na Majalisar Dinkin Duniya. Wannan zaman dai na gudana ne a daidai lokacin da MDD ke bikin cika shekaru 80 da kafuwa, a daidai lokacin da muhimman ka’idojinta da manufofinta ke fuskantar barazanar da ba a taba ganin irinta ba da...
    A Italiya dubun dubatan mutane ne suka fito kan tituna domin yin Allah wadai da yakin kisan kiyashi da Isra’ila ke yi a Gaza. Wannan gangami ya zo ne a ranar da wasu kasashe da dama ke shirin amincewa da Falasdinu a matsayin kasa a Majalisar Dinkin Duniya, bayan Birtaniya, Australia da Canada a ranar Lahadi. Duk da cewa Italiya ba ta da niyyar daukar irin wannan matakin a yanzu, A birnin Rome, fiye da mutane 20,000, ne  suka taru dauke da tutocin Falasdinu domin nuna goyan bayansu. An gudanar da zanga-zangar a wasu garuruwa da dama a fadin kasar, ciki har da Milan inda mutane 50,000 suka shiga zanga zangar in ji masu wadanda suka shirya ta. Saidai Kamfanin...
    Iran ta yi Allah wadai da harin da aka kai kan wani masallaci a Sudan tare da yin kira da a kawo karshen hare-haren da ake kai wa fararen hula cikin gaggawa. Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi Allah-wadai da harin na baya-bayan nan da aka kai da jirage marasa matuka a wani masallaci a birnin Al-Fashir na kasar Sudan, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da jikkata wasu da dama da ba su ji ba ba su gani ba. A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, ma’aikatar harkokin wajen Iran ta kira harin a matsayin ” keta dokokin jin kai na kasa da kasa.” Ta kuma jaddada bukatar gaggauta dakatar da kai hare-hare kan...
    Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a yau Litinin 22 ga wata cewa, nan ba da jimawa ba kasar Sin za ta gudanar da taron mata na duniya a birnin Beijing a daidai lokacin da ake cika shekaru 30 da gudanar da babban taron mata na duniya a shekarar 1995. Ya ce, kasar ta Sin tana son yin aiki kafada da kafada da dukkan kasashen duniya don kara hanzarta aiwatar da sabon tsarin ciyar da mata gaba a dukkan fannoni, da kuma rubuta wani sabon babi na raya al’amuran mata a duniya. Guo ya ce, ta fuskar abin da aka sa gaba a duniya, akwai sauran shekaru biyar kafin a cimma muradun samar...
    Majalisar Wakilai ta bayyana cewa ta amince da duk wasu tsare-tsare da dabarun karɓo rancen kuɗaɗe na Shugaba Bola Tinubu, bisa la’akari da ƙoƙarin da yake yi na farfaɗo da tattalin arziki da kuma rage talauci a ƙasar nan. Shugaban Majalisar, Abbas Tajudeen ne ya bayyana hakan a yayin da yake jawabi ranar Litinin, a taron shekara-shekara karo na takwas kan bitar kasafin kuɗaɗe na majalisun dokokin nahiyyar Afirka (African Network of Parliamentary Budget Offices) da ke gudana a Abuja. Sarkin Ruman Katsina ya rasu Jariri ya mutu a bayan uwarsa yayin tsere wa ’yan bindiga a Neja Abbas ya ƙaryata raɗe-raɗin cewa majalisar ta ƙi amincewa da tsare-tsaren karɓo rance na shugaban ƙasar, inda ya ce zantuka ne marasa...
    Hukumar da ke kula da yi wa Kamfanoni Rajista ta Najeriya (CAC) ta ƙaddamar da sabon shafin intanet mai amfani da fasahar ƙirƙirarriyar basira wato AI domin sauƙaƙa rajistar harkokin kasuwanci da kamfanoni a Najeriya. Shugaban Hukumar, Hussaini Ishaq Magaji (SAN), ne ya bayyana a yayin taron masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya a Kano ranar Litinin. Dalilin da muke goyon bayan tsare-tsaren Tinubu na karɓo bashi — Majalisar Wakilai Sarkin Ruman Katsina ya rasu Ya kuma ce hukumar ta kawo sabbin sauye-sauye da za su inganta ayyukanta da kuma sauƙaƙa wa ’yan kasuwa yin rajista da ita. Magaji ya ce, “Ko ina kake, daga dakinka, ba tare da ka san kowa a CAC ba, kuma ba tare...
    Yayin da “bikin girbi na manoman kasar Sin” na takwas ke karatowa, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, shugaban kasar, kuma shugaban kwamitin kolin soja Xi Jinping, a madadin kwamitin kolin JKS, ya mika gaisuwar bikin, da fatan alheri ga manoma da ma’aikatan dake gudanar da ayyukan da suka shafi harkokin noma, da kauyuka da kuma manoma a fadin kasar. Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a bana, mun shawo kan illar bala’o’i kamar fari, da ambaliyar ruwa, da samun daidaiton noman hatsin rani, da karuwar noman shinkafa mai nuna da wuri, ana kuma sa ran samun karin girbin hatsi. Xi Jinping, ya jaddada cewa, zamanantarwa irin ta kasar Sin ba za a iya...
    Majalisar Wakilai ta bayyana cewa ta amince da duk wasu tsare-tsare da dabarun karɓo rancen kuɗaɗe na Shugaba Bola Tinubu, bisa la’akari da ƙoƙarin da yake na farfaɗo da tattalin arziki da kuma rage talauci a ƙasar nan. Shugaban Majalisar, Abbas Tajudeen ne ya bayyana hakan a yayin da yake jawabi ranar Litinin, a taron shekara-shekara karo na takwas kan bitar kasafin kuɗaɗe na majalisun dokokin nahiyyar Afirka (African Network of Parliamentary Budget Offices) da ke gudana a Abuja. Sarkin Ruman Katsina ya rasu Jariri ya mutu a bayan uwarsa yayin tsere wa ’yan bindiga a Neja Abbas ya ƙaryata raɗe-raɗin cewa majalisar ta ƙi amincewa da tsare-tsaren karɓo rance na shugaban ƙasar, inda ya ce zantuka ne marasa tushe...
    Na hudu, an yi ta samu ci gaban sayayya sakamakon masu yawon bude ido daga ketare. Bisa ga manufar rage haraji lokacin barin kasa da kasar Sin ke gudanarwa, an shirya shirin “Sayayya a Sin” yadda ya kamata, wanda hakan ya canza fa’idar yawan baki daga ketare da suke yawon shakatawa a kasar zuwa habaka kudin da ake kashewa. (Bilkisu Xin) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yau Litinin Allah Ya yi wa Sarkin Ruman Katsina kuma Hakimin Batsari, Alhaji Tukur Ma’azu, rasuwa. Marigayin, wanda ya shafe shekaru 74 a duniya, ya daɗe yana fama da jinya gabanin rasuwarsa. Hisbah ta kama masu safarar mata zuwa Saudiyya a Kano Jariri ya mutu a bayan uwarsa yayin tsere wa ’yan bindiga a Neja Alhaji Tukur wanda ya shafe shekaru 43 yana riƙe da sarautar Hakimin Batsari, ya rasu ya bar mata biyu, ’ya’ya da kuma jikoki. Za a gudanar da jana’izarsa da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin yau a gidansa da ke cikin garin Batsari, kamar yadda sanarwa daga iyalansa ta tabbatar.
    Mutune 70 da aka yi garkuwa da su sun samu ƴanci a Jihar Katsina, bayan yarjejeniyar sulhu da aka ƙulla da fitaccen shugaban ƴan bindiga, Isiya Kwashen Garwa. A wani faifan bidiyo da ya bayyana, Garwa ya saki mutane 40 a ƙaramar hukumar Faskari, kwanaki biyu bayan ya fara sakin wasu 30, wanda hakan ya kai adadin zuwa 70 gaba ɗaya. Rahotanni daga mazauna yankin sun ce sakin na baya-bayan nan ya biyo bayan tattaunawa tsakanin shugabannin al’umma da sansanin Garwa, a wani mataki da ake ganin zai rage tashin hankali da hare-hare a yankin. Duk da haka, Garwa ya nuna rashin jin daɗi kan abin da ya kira sumamen Sojoji a unguwar Ruwan Godiya a lokacin Sallar Juma’a, inda...
    Wani jariri ya rasu a bayan mahaifiyarsa a yayin da take guje wa harin ’yan bindiga a kauyen Allawa da ke Karamar Hukumar Shiroro a Jihar Neja. Sarkin yankin Bassa, Bagudu Amos, ne ya bayyana hakan a lokacin taron tattaunawa da mata kan zaman lafiya da kare su daga cin zarafi, mai taken: “Ƙarfafa kariya daga cin zarafin jima’i da na jinsi a Jihar Neja.” Kungiyar Tunani Initiative, tare da goyon bayan Dorothy Njemanze Foundation da Ford Foundation, ce ta shirya taron domin ƙarfafa mata wajen yaki da cin zarafi da ke ƙara ta’azzara a sakamakon rashin tsaro. Bagudu Amos ya bayyana cewa mahaifiyar ta yi tafiya mai nisa a kafa da jaririn a bayanta domin tserewa daga harin ’yan...
    Wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba sun sace Hakimin Birbyang, Alhaji Zubairu Garba, tare da wasu mata biyu a daren Lahadi a ƙaramar hukumar Kanam ta Jihar Filato. Rahotanni sun ce ƴan bindigar sun shigo ƙauyen ne da tsakar dare, suna harbi a iska kafin daga bisani su yi awon gaba da mutanen. Matar hakimin, wadda aka yi garkuwa da ita a farkon harin, ta samu damar tserewa daga hannun masu garkuwa. Wannan lamari na baya-bayan nan ya biyo bayan sace-shi-da-kashe wa da aka yi wa Dagacin Shuwaka a yankin Kyaram, wanda shi ma ke cikin ƙaramar hukumar Kanam, mako guda kacal da ya gabata. Hakan ya ƙara tayar da hankali a tsakanin al’ummar yankin...
    A kasar Guinea an fara kidaya kuri’un da aka kada na zaben kasa da ake hasashen cewa shugaban mulkin soja zai sami nasara. Kada kur’iar ta raba gardama akan sabon tsarin Mulki zai sama wani gagarumin mataki na fitar da kasar daga mulkin soja zuwa na farar hula. Shugaba Janar Mamadi Doumbouya wanda ya yi juyin Mulki zai iya samun damar ci gaba da zama akan Kargar Mulki. Jam’iyyun hamayyar siyasa a kasar Guinea sun yi kira da a kauracewa kada kuri’ar raba gardamar. Da akwai mutane miliyan 6.7 da su ka cancanci kada kuri’a a fadin kasar. A bisa dokar zaben kasar, idan kaso 50% su ka kada kuri’a, to za a amince da sakamakon abinda su ka zaba....
    Ana ci gaba da takaddama a duniyar kwallon kafa kan wa ya fi cancanta da lashe kyautar Ballon d’Or a matsayin gwarzon dan wasan duniya na  bana. A ranar Litinin din na za a bayar da Kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2025 a birnin Paris na kasar Fasansa, ga wanda alakalai suka zaba a matsayin Gwarzon Dan Wasan Kwallon Kafa na Duniya. Ballon d’Or ce kyauta mafi girma ta shekara-shekara ga ’yan wasan kwalllon kafa saboda bajintar da ya nuna ga ƙungiyarsa da ƙasarsa. Gasar ta bana ta kasance mafi zafi duba da yadda alkaluma ke nuna irin zakakurancin kowanne daga manyan ’yan wasan da ake hasashen za su iya lashe kambin. An rufe sansanin NYSC da kasuwanni saboda rashin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ana ci gaba da takaddama a duniyar kwallon kafa kan wa ya fi cancanta da lashe kyautar Ballon d’Or a matsayin gwarzon dan wasan duniya na  bana. A ranar Litinin din na za a bayar da Kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2025 a birnin Paris na kasar Fasansa, ga wanda alakalai suka zaba a matsayin Gwarzon Dan Wasan Kwallon Kafa na Duniya. Ballon d’Or ce kyauta mafi girma ta shekara-shekara ga ’yan wasan kwalllon kafa saboda bajintar da ya nuna ga ƙungiyarsa da ƙasarsa. Gasar ta bana ta kasance mafi zafi duba da yadda alkaluma ke nuna irin zakakurancin kowanne daga manyan ’yan wasan da ake hasashen za su iya lashe kambin. An rufe sansanin NYSC da kasuwanni saboda rashin...
    Kwamandan sojan Iran Amir Hatami wanda ya gana da kwamandan dakarun kare juyin musulunci Janar Muhammad Pakpour saboda tunawa da makon hadin kai, ya kara da cewa; Bayan cin nasarar juyin musulunci a Iran, Iran da al’ummarta sun fara aiki tukuru domin kare cikakken ‘yancin Iran.” Har ila yau, Amir Hatami ya yi ishara da hadin gwiwa a tsakanin sojojin da dakarun kare juyin juya halin yana a matsayin ginshikin tsaron kasar Iran, kuma wata kofa ta kai wa mataki na koli na tsaro. A gefe daya dakarun kare juyin musulunci ( irgc) sun jaddada matsayarsu ta ci gaba da zama cikin Shirin fuskantar abokan gaba. A cikin wata sanarwa da suka fitar a farkon makon tsaro mai alfarma, na...
     Shugaban kasar Korea Ta Arewa Kim jung Un ne ya sanar da cewa kasarsa ta kera wani sabon makami na sirri, kuma ta samu ci gaba sosai a fagen nazari da binciken kayan tsaro. Shugaban kasar ta Korea Ta Arewa Kim Jun Ung  wanda ya yi Magana da kamfanin dillancin labarun kasar ya kara da cewa; Sabbin makaman da su ka kera za su taimaka matuka wajen karfafa sojojin kasar.” Haka nan kuma ya ce, kasar Korea ta Arewa ta kuma karfafa sojojinta na ruwa ta hanyar kara samar da jiragen ruwa na yaki masu ninkaya a karkashin ruwa.” Kamfanin dillancin labarun Korea Ta Arewa ya sanar da cewa, a ranar Juma’ar da ta gabata ne shugaban kasar Kim Jun...
    A jiya Lahadi ne dai jirgin ruwan agaji da aka bai wa sunan; ” Umar Mukhtar” ya bar ruwan kasar Libya  domin nufar Gaza da zummar karya killace yankin da aka yi na tsawon shekaru 18. Masu kula da jirgin ruwan na “Umar Mukhtar” sun bayyana cewa; Sun yi tanadin kayan aikin liktanci da aka bai wa sunan; Likitan Falasdinawa Husam Abu Saafiyyah. Har ila yau, hukumar agajin kasar Libya ta tanadi jirgin sama mai saukar angulu domin kai daukin gaggawa idan bukatar hakan ta taso. Da akwai mutane 20 a cikin wannan jirgin ruwan da su ka likitoci, masu fafutuka da kuma lauyoyi daga Libya da wasu kasashen turai. Jirgin ruwan na Agaji yana da cikakken goyon bayan al’ummar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Matsalar tsaro san rufe kasuwannin shanu a yankin Kwara ta Kudu da kuma ɗauke sansanin masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) da ke Yikpata, Ƙaramar Hukumar Edu an mayar da ita zuwa Ilorin, hedikwatar jihar. Ƙananan hukumomin biyu na Kwara ta Kudu da arewacin jihar na daga cikin wuraren da matsalolin tsaro suka fi taɓarɓarewa duk da ƙoƙarin gwamnati da hukumomin tsaro. Rufe kasuwannin dabbobi Sanarwar farko ta fito daga Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi bakwai na Kwara ta Kudu, inda suka bayar da umarnin rufe duk kasuwannin Kara a yankin. Shugabannin —Abdulrasheed Yusuf (Ifelodun), Benjamin Jolayemi (Isin), Azeez Yakub (Irepodun), Awelewa Gabriel (Ekiti), James Fadipe (Oke-Ero), Sulyman Olatunji (Offa), da Akanbi Olarewaju (Oyun)— sun ce matakin ya zama dole don...
    Jam’iyyar APC reshen jihar Taraba ta yi yi kakkausar suka ga mulkin Gwamna Agbu Kefas, inda ta ce bayan shekaru biyu a ofis ya gaza cika alkawuran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe. Jam’iyyar ta ce rashin tasirin gwamnatin PDP zai sauƙaƙa wa APC kwace mulki a shekarar 2027 a jihar. Da yake magana a Jalingo, Sakataren APC na jihar, Fidelis Francis, ya zargi Gwamna Kefas da rashin ƙaddamar da muhimman ayyukan raya ƙasa, ciki har da barin hanyar zuwa ƙaramar hukumar gwamnan a lalace bayan gadoji sun karye. Ya bayyana mulkin nasa a matsayin “wanda bai shirya ba kuma ba shi da wani tsari.” Francis ya ƙara da cewa PDP tun daga 1999 ba ta da abin...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci yana taya tawagar kokawa ta Greco-Roma ta Iran murnar lashe gasar cin kofin duniya Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya taya tawagar kokawa ta Greco-Roman ta kasar Iran murnar nasarar da ta samu a gasar cin kofin duniya, yana mai godiya ga ‘yan wasa da masu horar da ‘yan wasa da masu gudanarwa da suka sanya farin ciki a zukatan al’ummar Iran da kuma abin alfahari ga kasar Iran. A cikin sakon nasa, Jagoran ya ce: Ina taya matasan kokawa murna. Ƙudurin ku da himma a cikin kokawa na Greco-Roman sun kawo farin ciki ga zukatan mutane da kuma alfahari ga ƙasar. Ina rokon Allah Ya ba ku daukaka da nasara,...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Kasashen da ba su cika alkawuran da suka dauka ba suke zargin Iran da rashin mutunta yarjejeniyar makamashin nukiliya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Kasashen da ba su cika alkawuran da suka dauka ba, a yanzu suke zargin Iran da kin mutunta yarjejeniyar makamashin nukiliyar. A cikin wata hira da gidan talabijin na CCTV na kasar China, Pezeshkian ya ce, “Suna sa ran za a aiwatar da yarjejeniyar manyan tsare-tsare na shekaru 25 da aka tsara a baya tsakanin Iran da China.” Pezeshkian ya yi ishara da gazawar Amurka da kasashen Turai wajen cika alkawuran da suka dauka karkashin yarjejeniyar makamashin nukiliya, yana mai cewa, a yau kasashen da ba su...
    Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran sun bayyana cewa: Duk wani sabon kuskuren lissafin makiya zai fuskanci mayar da martani mai muni A cikin wata sanarwa da suka fitar a farkon makon tsaro mai alfarma, na ranar tunawa da arangama da gwamnatin Saddam ta yi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a tsakanin shekarun 1980-1988, dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) sun jaddada cewa: Duk wani sabon kuskuren lissafi da makiya za su yi, za su fuskanci mummunan martani da zai zame babban darasi a gare su. A cikin bayanin da suka yi na farkon makon tsaro na dakarun IRGC sun bayyana cewa: A hakikanin gaskiya makon tsaro, biki ne na nasarar gwagwarmayar jama’a, kuma abin...
    Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada cewa: ‘Yan koren Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila na da nufin wargaza hadin kan Larabawa da na Musulmi Jagoran kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen Sayyed Abdulmalik al-Houthi ya jaddada cewa: ‘Yan koren Amurka da na haramtacciyar kasar Isra’ila suna neman tada fitina da sanya kiyayya a tsakanin al’ummomin Larabawa da na Musulmi. Ya yi nuni da cewa wadannan ‘yan kore ba su da wani aiki na gaske da zai yi hidima ga kasashensu na asali, sai dai mayar da hankali kan kokarinsu wajen wargaza zamantakewar al’umma, karkashin kulawar Amurka da tallafin Larabawa da kuma jagorancin yahudawan sahayoniyya. A cikin jawabin da ya gabatar a jiya Lahadi, a daidai lokacin da ake gudanar...
    Ƙaramar Hukumar Sabuwa da ta Ɗandume a Jihar Katsina sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da ’yan bindiga, a wani yunƙuri na kawo ƙarshen hare-hare, kashe-kashe da sace-sacen da suka daɗe suna addabar yankin. An gudanar da taron sulhun ne a ranar Asabar a ƙauyen Kabalawa Dungun Mua’zu, da ke iyaka da ƙananan hukumomin biyu, amma yana ƙarƙashin Sabuwa. Da wannan ci-gaban, adadin ƙananan hukumomi da suka ƙulla yarjejeniyar sulhu da ’yan bindiga a jihar ya kai tara. Sauran sun haɗa da Batsari da Kankara, Kurfi da Musawa da Ɗanmusa da Jibia da kuma Faskari. Yadda aka kashe jami’an tsaro 53 cikin mako biyu NAJERIYA A YAU: Yadda Wata Bakuwar Cuta Take Cin Naman Jikin Mutanen Malabu Shugaban Ƙaramar...
    Sojojin mamayar Isra’ila sun kai hari kan fararen hula, inda suka kashe mutane 5 da suka hada da yara 3 a kudancin kasar Lebanon Ma’aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da mutuwar wasu ‘yan kasar 5 da suka hada da yara uku sakamakon wani hari da jiragen saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a kudancin birnin Bint Jabeil. Kamfanin dillancin labaran kasar Lebanon ya watsa rahoton cewa: Wani jirgin sama mara matuki na makiya yahudawan sahayoniyya ya kai hari kan wani babur da wata mota dauke da makamai masu linzami a garin Bint Jabeil, lamarin da ya yi sanadin mutuwa da jikkata. Wannan harin wuce gona da iri ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin mamayar Isra’ila...
    Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya isa birnin New York, Amurka, domin halartar taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 wanda zai gudana daga ranar Litinin 22 ga Satumba zuwa Lahadi 28, 2025. Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu, zai gabatar da jawabin Nijeriya a gaban zauren, tare da shiga wasu tattaunawa da tarukan a gefe da dama. Ministan Harkokin Ƙasashen Waje, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa Nijeriya za ta ci gaba da mara baya ga tsarin haɗin gwuiwa tsakanin ƙasashe, ciki har da yunƙurin samun kujerar dindindin a Majalisar Tsaron MDD bisa matsayar haɗin kan Afrika, wato Ezulwini Consensus. Ya ce Shettima zai kuma bayyana sabbin manufofin Nijeriya na rage hayaƙin da ke gurbata muhalli bisa...
    Aƙalla jami’an tsaro 53 aka kashe a sassa daban-daban na Nijeriya cikin makonni biyu da suka wuce, bisa ga ƙididdigar da muka tattaro daga rahotannin kafofin yaɗa labarai. Jami’an da abin ya shafa sun haɗa da sojoji da ’yan sanda da jami’an Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula (NSCDC), jami’an shige da fice da na kwastam, da ma jami’an sa-kai da ke taimaka wa jami’an tsaro, ciki har da ’yan sa-kai na JTF da na ƙungiyoyin tsaro na al’umma da gwamnatocin jihohi suka kafa. Yawancin waɗanda aka kashe, ’yan bindiga ne suka halaka su yayin da suke ƙoƙarin kare al’umma a lokacin hari, yayin da wasu kuma aka kashe su ne a wuraren binciken tsaro da sansanoninsu. Wannan adadi ya...
    “A wani ɓangare na wannan dubarar, jam’iyyar a ƙarƙashin kulawar ɗaya daga cikin manyan ma’aikatan gwamnati, ta yi ƙoƙarin shirya zaɓen jagoranci ƙungiyar Musulmai ƴ an asalin Jihar Filato a cibiyar Azi Nyako da ke Dadin-Kowa a garin Jos, wanda daga bayanan da aka samu lamarin ya kasa samun nasara. “PDP na ganin cewa da wannan dubarar na raba kan Musulmin Jihar Filato za ta iya samun nasara a zaɓen 2027, wanda wannan ka iya kawo rashin jituwa da haɗin kan al’umma, musamman a irin wannan lokaci da ake fama da rikice-rikice addini da ƙabilanci da kuma ayyukan ƴ an ta’adda, wanda hakan bai kamata a siyasantar da addini ba. “Yadda PDP ke amfani da addini a matsayin hanyar lashe...
    A kowane wata, hauhawar farashi ta kan kai kashi 0.74, yayin da a watan Agusta, hauhawar farashin abinci ya kasance kashi 1.65. A shekara-shekara, hauhawar farashi yana raguwa da kashi 12.03 idan aka kwatanta da kashi 32.15 da aka samu a watan Agusta 2024. Hukumar ƙididdiga ta bayyana cewa duk da hauhawar farashin na nan, saurin ƙaruwar farashin kayayyaki yana raguwa idan aka kwatanta da watannin da suka gabata. Dangane da iƙirarin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, cewa Ƴan Nijeriya na “mutuwa da yunwa kullum,” Fasua ya ce: “Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, kawai ya sanya siyasa ce cikin lamarin a ƙoƙarinsa na son ya samu shiga ofishin shugaban ƙasa, ni kuma ba na yin tsokaci a harkokin...
    A yau Lahadi 21 ga wannan wata da yamma, firaministan kasar Sin Li Qiang ya gana da tawagar membobin majalisar wakilai ta kasar Amurka da Adam Smith ya jagoranta a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing. A yayin ganawar, Li Qiang ya bayyana cewa, Sin da Amurka manyan kasashe ne dake da muhimmanci sosai a duniya, kiyaye dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka mai dorewa yadda ya kamata ya dace da moriyar kasashen biyu da begen kasa da kasa. Sin tana son yin kokari tare da kasar Amurka wajen girmama juna, da zama tare cikin lumana, da yin hadin gwiwar samun moriyar juna. Kana kasar Sin tana son kasar Amurka ta yi hadin gwiwa tare da ita don sa...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    ’Yan bindiga sun kai hari shingen bincike na ’yan sanda a Jihar Kogi, inda suka kashe jami’ai da wani mutum. Harin farko ya faru da misalin ƙarfe 10:30 na safe a ƙauyen Abugi da ke Ƙaramar Hukumar Lokoja. Mata 400 sun amfana da kayan haihuwa a Gombe Bayan biyan N50m an sako ma’aurata da ’yarsu su da aka sace a Katsina Maharan, sun kai harin ne a kan babur, inda suka buɗe wa ’yan sandan da ke bakin aiki wuce. Wani matashi da ya zo wucewa ta wajen ya rasa ransa. Bayan haka, maharan sun kwashe bindigogin jami’an sannan suka tsere. Daga baya, da misalin ƙarfe 11 na safe, suka sake kai wani hari a shingen da ke kan hanyar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya gargadi cewa, tarihi ba zai gafarta wa shugabannin Arewa ba idan suka kasa daukar matakin gaggawa wajen dakile kashe-kashe, garkuwa da mutane da rikice-rikicen da ke addabar yankin. Ya ce shiru da fifita wasu akan wasu daga cikin shugabanni suna kara ta’azzara matsalar tsaro a jihohin Zamfara, Kaduna, Katsina, Filato da Benuwe.   Ya bayyana cewa akwai damuwa matuka yayin da ‘yan bindiga ke ci gaba da addabar al’umma, wasu daga cikin manyan mutane na fifita shirya shagulgula masu tsada maimakon kiraye-kirayen tarurrukan neman mafita na gaske don kawo karshen wannan rikici.   “Lokacin yin shiru ya wuce, yanzu ne lokacin daukar mataki. Tarihi ba zai gafarta wa halin ko-in-kula ba a lokacin da ake bukatar mataki fiye da...
    Ministan harkokin wajen Falasdinawa Varsen Aghabekian Shahin, ta godewa kasashen  duniya da suka amince da samuwar kasar Falasdinu ya zuwa yanzu kuma kuma wadanda suke shirin yinhaka, sannan tana kodaitar da sauran kasashen duniya da su yi hakan. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shahin tana fadar haka a taron yan jarida da ta kira a yau Lahadi a birnin Ramallah, sannan ta kara da cewa ya zuwa yanzu kasashe da dama  sun bayyana amincewarsu da kasar Falasdinu, Kuma sakone mai kyau ga Falasdinwa, kuma banda haka wannan sakonnin fata ne na samuwar kasar Falasdinu mai zaman kanta. Ta kara da cewa, amincewa da kasar Falasdinu mai zaman kanta yana nufin HKI bata da iko a kanta....
    Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar Abuja zuwa birnin New York na Ƙasar Amurka, domin halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80. Taron zai gudana daga ranar Litinin, 22 ga watan Satumba, zuwa ranar Lahadi, 28 ga watan Satumba, 2025. Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu Jami’ar European-American ta musanta bai wa Rarara digirin girmamawa Shettima zai wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wannan babban taro. Zai gabatar da jawabi, tare da shiga muhawarar shugabannin ƙasashe a zauren taron. A yayin taron, Mataimakin Shugaban zai kuma bayyana sabbin muradun Najeriya a ƙarƙashin yarjejeniyar kare muhalli. Wannan zai gudana ne a wani taro na musamman kan sauyin yanayi da Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya zai shirya a...
    A daren ranar 19 ga wannan wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump sun tattauna ta wayar tarho, inda shugaba Xi ya jaddada cewa, alakar Sin da Amurka na da matukar muhimmanci, Sin da Amurka na iya cimma nasarar bai daya da wadata tare, ta yadda za su amfani kawunansu, da ma sauran sassan duniya baki daya. A nasa bangare kuwa, shugaba Trump cewa ya yi, alakar Amurka da Sin ita ce mafi muhimmancin dangantaka a duniya, yana mai cewa, aiki tare tsakanin kasashen biyu ka iya haifar da manyan abubuwa da za su ingiza zaman lafiya da daidaito a duniya. Ya yi fatan wanzar da babbar dangantaka mai armashi ta dogon lokaci tsakanin...
    Aƙalla mutum ne sun rasu, yayin da wasu 16 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a Ƙaramar Hukumar Karasuwa, a Jihar Yobe. Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Yobe, SP Dungus Abdulkareem ne, ya tabbatar da faruwar hatsarin ya faru a ranar Asabar da misalin ƙarfe 2:50 na rana a ƙauyen Zangon Kanwa. Gwamnan Gombe ya bai wa maharba kyautar motoci da babura don bunƙasa tsaro An sanya tukwicin N10m domin kama makasan limamin coci a Enugu Hatsarin ya rutsa da mota ƙirar Toyota Hiace wadda ke ɗauke da fasinjoji daga Jakusko zuwa kasuwar Jajimaji da kuma mota ƙirar Volvo daga garin Azare. Rahoto ya nuna cewa mota ƙirar bas ce ta ƙwace ta buga wani Keke Napep...
    Kasashen Pakistan da Iran suna shirin fadada dangantakar tattalin arzikin da ke tsakanin daga dalar Amurka biliyon $3 a ko wace shekara zuwa dalar Amurka billion $10. plan to expand bilateral trade from its current level of just over $3 billion to an ambitious $10 billion. Tashar talabijan ta Presstv a nan ta nakalto bangarorin biyu na fadar haka ne a yau Lahadi, a taron kwamitin tattalin arziki na hadin giwa tsakanin kasashen biyu karo na 22nd da aka gudanar a nan Tehran. Labarin ya kara da cewa, kasashen biyu sun amince da cewa, halin da harkokin tattalin arziki tsakanin sub a na gaskiya bane,   tunda a kwai bangarori da dama dabasu taba ba, ko kuma yi magana a kansu...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bukaci kasar Agfanistan ta mayarwa kasar Amurka san sanin sojojin sama na kasar wanda ke Bagram ko kuma zata ga ba dadi. Kafanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka da farko a shafinsa na zumunta na ‘ Truth Social’. Shugaban ya gargadi Taliban kan vewa idan sun ki mayarwa Amurka sansanin sojojin Bagram to wani abu ba dadi zai faru da sun. Trump ya dade yana zargin gwamnatin shugaba Biden da ya gada da yin ba dai-dai ba, daga ciki har da ficewa daga kasar Afganistan bayan mamaya na tsawon shekaru 20 ba tare da shiri ba. Amurka ta mamaye kasar Afganistan tun shekara 2001 har zuwa 2022...
    Firay ministan kasar Burtaniya da tokwarorinsa na kasashen Canada da Australia duk sun bayyana amincewar gwamnatocinsu da samuwar kasar Falasdinu mai zaman kanta. Wanda ya nuna sauyi babba a al-amuran diblomasiyya wadanda suka sha fi HKI da kuma Falasdinawa. Kafin haka dai, idan an masu maganar samar da kasar Falasdinu sai suce sun barwa HKI ta tattunawa da Falasdinawa don warware matsalar tsakaninsu. Sauya matsayinda wadan nan manya-manyan kasashen duniya suka yi ya sake bude batun samar da kasashe biyu, wanda kuma zai kara tura HKI zuwa bongo don amincewa da samar kasar Falasdinu da kuma bukatar ta dai kissan kiyashin da takewa al-ummar Falasdinu a Gaz da kuma yankin yamma da kogin Jordan. Kafin haka Falasdinawa sun bukaci kasashen...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa tattalin arzikin kasar Iran nan gaba zai ginu ne bisa shirin  bayan karewar man fetur ne, inda fasahohi da ilmi da kirkire-kirkire da kuma darussan da za’a dauko daga kasashe kawayen kasar a kungiyoyin BRICS da kuma SCO ne zasu zama  abin dogaru. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto shugaban yana fadar haka  ne a daren jiya Asabar a wani taro wanda yake magana a kan hanyoyin da Iran zata bi don bunkasa fasaha da ilmin kere-keren kasar da samar da ci gaba masu dorewa a kasar. Pezeshkiya yace sauye-suyen da sauri da ake samu a duniya musamman a yankin tekun fariya sun sanya dabarbarun ci gaba na sauyawa...
    Babban mai ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin Wang Yong ya bayyana cewa, kasar Sin tana son karfafa hadin gwiwa da dukkan bangarori a muhimman fannoni kamar na masana’antu. Wang, wanda shi ne mataimakin shugaban babban kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, wacce take babbar hukumar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin, ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen bikin bude taron masana’antun duniya na shekarar 2025 da aka gudanar a lardin Anhui da ke gabashin kasar Sin. Wang ya kara da cewa, a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, kasar Sin tare da dukkan bangarorin da abin ya shafa, sun bi ka’idar samun moriyar juna...
    Abdulahi, wanda ke jigilar kaya daga Agbara a Jihar Ogun zuwa Ibadan, ya ce yana kashe har Naira 25,000 a kowace tafiya da yake yi, inda mafi yawan kuɗin ke shiga hannun ƴ an Agbero a Legas, waɗanda ke gudanar da ayyukansu sa’o’i 24 a rana, kwana 7 a mako. Ya ce daga Berger, gefen Legas, zuwa Agbara, manyan motoci kan gamu da aƙalla tashoshi 15 na ta’annati, inda ake karɓar kuɗi tsakanin Naira 1,000 zuwa Naira 3,000 a kowane wuri. Manajan Daraktan wani kamfani da ke aiki a cibiyar masana’antu ta Agbara a Jihar Ogun, wanda ya nemi a sakaya sunansa ba, ya shaida wa wannan jarida cewa jigilar kwantena na kayayyakin masarufi daga tashar jiragen ruwa ta Apapa...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya bai wa ƙungiyar maharba ta ƙasa (PROHAN) reshen Gombe, kyautar motoci Hilux guda biyu da kuma babura guda biyar domin taimaka musu wajen yaƙi da ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane. An miƙa wa shugaban ƙungiyar, Rabiu Baushe (Baushen Gombe) kyautar, wanda yana cikin shirin gwamnatin na ƙara bunƙasa tsaro da bayar da kyautar kayan aiki don kare rayuka da dukiyoyin jama’a. ’Yan sanda sun kama mutane 5 kan zargin satar abincin yara a Borno Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu Gwamna Inuwa ya ce: “Tsaro shi ne ginshiƙin ci gaban al’umma. Ba za mu samu ci gaba, ba tare da zaman lafiya ba. “Gwamnatina za ta ci gaba da tallafa...
    Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta SERAP tare da Amnesty International sun nemi Shugaba Bola Tinubu ya janye ƙarar da aka shigar a kotu kan ɗan gwagwarmaya Omoyele Sowore, da kuma kamfanonin sada zumunta X da Facebook. Ƙungiyoyin sun bayyana damuwa cewa hukumomin tsaro na ƙara amfani da kotu wajen tsoratar da ƴan Nijeriya da hana su faɗar albarkacin baki. A cikin wata wasiƙar da suka aike wa shugaban ƙasa ranar 20 ga Satumba, 2025, SERAP da Amnesty sun bayyana cewa ƙarar da DSS ta shigar bisa zargin saƙonnin da ake cewa sun na adawa da Tinubu ya zama wani SLAPP (ƙarar da ake amfani da ita don toshe bakin masu suka). Sun ce irin waɗannan suna haifar da tsoro...
    Sabo da irin mawuyacin halin da ake ciki ta fannin tsarin jagorancin duniya musamman a daidai wannan lokaci, ya sa shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar inganta tsarin jagorancin duniya a kwanakin baya, shawarar da ta yi nuni da cewa, ya kamata a tsaya tsayin daka a kan kin yarda da daukar matakai na kashin kai, tare da kiyaye matsayin MDD, don ta taka rawar da ba wanda zai iya maye gurbinta a cikin tsarin jagorancin duniya. Lallai kasar Sin ta gabatar da shawarar, musamman don neman dakile ayyukan nuna fin karfi da ake fama da su a duniya, tare da samar da mafita ga kasa da kasa da suka shiga duhu. A sati mai zuwa, za...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta kama mutum biyar da ake zargi da satar fakiti 7,871 na abincin yara, wanda aka fi sani da Tamuwa, wanda aka tanada don yara masu fama da cutar yunwa. Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 19 ga Satumba, 2025 . Ya bayyana cewa an gano kayan ne a samame guda biyu da aka kai a Maiduguri. Shettima ya bar Abuja don halartar taron majalisar ɗinkin duniya a New York An sanya tukwicin N10m domin kama makasan limamin coci a Enugu Samamen farko ya auku ne a ranar 12 ga Afrilu, lokacin da aka tsayar da wata mota a Njimtilo, kusa da Maiduguri, inda...
    A yayin da ake gudanar da shagulgulan ranar zaman lafiya ta Duniya ta Bana, Kungiyar rajin tabbatar da zaman lafiya da hadin Kai da kuma cigaban Arewacin Nigeria ta yi Kira ga Gwamnati a dukkan matakai da kuma Hukumomin tsaro su karfafa amfani da bayanan tsaro na sirri wajen kare rayukan al’ummar Kasa. Shugaban Kungiyar ta ACI Dakta Abdullahi Idris ya yi wannan Kira a wani taron manema labarai da Kungiyar ta Kira a Kaduna. Ya yi bayanin, Kungiyar ta lura da matakan da Gwamnati da Hukumomin tsaro suka dauka domin maido da zaman lafiya a wasu sassan Arewcin Kasar nan. Dakta Abdullahi Idris ya ce, matakan da aka dauka abin a yaba ne, Amma kuma sun yi kadan matuka...
    Wanda zan iya tunawa za su kai goma haka. Ko akwai wani fim wanda bayan fitar sa ka samu ƙalubale daga dangi ko wajen masu kallo? Gaskiya a fim dai har yanzu ban samu wani ƙalubale ba, saboda duk abin da nake fitowa a rol na malunta ne. Kawai dai akwai wata waƙa da na yi bidiyonta a kanta ne gaskiya na fuskanci ƙalubale sosai, dan akwai wanda ya taɓa kira na yana hawaye ya ce min me ya ja min wannan harka haka har na fito ina rawa da jaruma?. To, sai na ji ban ji daɗi ba a lokacin, dan akwai gidajen TƁ da suka karɓa suke haskawa, nayi sauri na hana a haska ɗin. Sai kuma wani...
    Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar Abuja zuwa birnin New York na Ƙasar Amurka, domin halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80. Taron zai gudana daga ranar Litinin, 22 ga watan Satumba, zuwa ranar Lahadi, 28 ga watan Satumba, 2025. Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu Jami’ar European-American ta musanta bai wa Rarara digirin girmamawa Shettima zai wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wannan babban taro. Zai gabatar da jawabi, tare da shiga muhawarar shugabannin ƙasashe a zauren taron. A yayin taron, Mataimakin Shugaban zai kuma bayyana sabbin muradun Najeriya a ƙarƙashin yarjejeniyar kare muhalli. Wannan zai gudana ne a wani taro na musamman kan sauyin yanayi da Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya zai shirya a...
    Duk tawagar da ta ƙare a mataki na ɗaya daga kowane rukuni guda tara na nahiyar Afirka, ita ce za ta samu gurbi kai-tsaye. Daga baya sai a zaɓo huɗu mafiya ƙoƙari da suka ƙare a mataki na 2, inda za a fitar da ɗaya daga cikinsu sannan ta kara da takwararta ta wata nahiyar. Rabon da Nijeriya ta samu gurbin Kofin Duniya tun a 2018 da aka yi a Rasha, inda ta gaza zuwa na 2022 a Ƙatar wanda tawagar ƴ anwasan ƙasar Argentina ta lashe ƙarƙashin jagorancin Lionel Messi. Jimilla Nijeriya ta je gasar Kofin Duniya sau shida a tarihi – 1994, 1998, 2002, 2010, 2014, 2018. A wasannin neman gurbin na gasar 2026, wasanni biyu kacal Nijeriya...
    “A yayin binciken motar, an samu waɗannan abubuwa daga hannun wanda ake zargin: bindiga ta gida guda ɗaya, harsashi guda huɗu, harsashi biyu da aka harba a baya, katin shaida na ƴ an sanda na bogi, da kuma ƙarin lambar rijistar mota ta (Kano FGE 68).” “Wanda ake zargin yana tsare a hannun jami’an tsaro yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike don gano ainihin dalilan mallakar bindiga, katin shaida na bogi, da sauran abubuwan da aka kama daga gare shi.” “Ƙungiyar jami’an tsaro, bisa ƙarin lura da dabarun tsaron zamani, ta dakatar da wani motar Toyota Corolla, launin toka, mai lambar rijista Lagos GGE 473 BH, wanda wanda ake zargi ya ke tukawa. Bayan an yi masa...
    Ƙasar Birtaniya a wannan Lahadin za ta amince a hukumance da kafa ƙasar Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta. Birtaniya wadda ta daɗe tana goyon bayan Isra’ila za ta juya mata baya, sakamakon hare-haren da Isra’ilar take kai wa Zirin Gaza, wanda ya samo asali bayan da ƙungiyar Hamas ta kai wani mummunan hari a ranar 7 ga watan Oktoban 2023. Jami’ar European-American ta musanta bai wa Rarara digirin girmamawa An sanya tukwicin N10m domin kama makasan limamin coci a Enugu Tun a watan Yulin wannan shekarar Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya ce zai goyi kafa ƙasar Falasɗinu yana mai gindaya wa Isra’ilar sharaɗin yanke wannan shawarar. Starmer ya ce zai amince da ƙasar Falasɗinu muddin Isra’ilar ba...
    Ministan harkokin wajen Iran ya kore abinda wasu kafafen watsa labaru su ka watsa na zantawa a tsakaninsa da manzon Amurka a gabas ta tsakiya Steven Witkoff. Ministan harkokin wajen na Iran, Abbas Arakci ya fada wa kamfanin dillancin labarun “Tasnim” na Iran cewa; Babu gaskiya a cikin labarun da wasu kafafen watsa labaru su ka watsa.” Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma ce; Da akwai tuntubar juna a tsakanin Tehran da Washington kodai ta kai tsaye ta hanyar wasiku, ko kuma ta hanyar  masu shiga Tsakani idan bukatar hakan ta taso.” Wasu kafafen watsa labarun kasashen turai ne dai su ka watsa labarin dake cewa;  Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya gana da manzon musamman na Amurka...
    Kungiyar Hizbullah ta fitar da wata sanarwa ta gayyata domin halartar taron tunawa da zagayowar ranar shahadar Sayyid Hassan Nasrallah wanda za yi a ranar 27 ga watan nan na Satumba. Tunawa da Shahid Sayyid Hassan Nasrallah da sauran wadanda su ka yi shahada a lokacin, kamar su Shahid Sayyid Hashim Safiyuddin, zai kasance a wani gagarumin taro a birnin Beirut da kuma sauran garuruwan Lebanon  a ranar 27 ga watan Satumba da misalin karfe: 4;30. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka  Hamas...
    Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta bayyana cewa, laifukan da HKI take tafkawa akan jami’an kiwon lafiya suna da bukatar duniya ta yunkura cikin gaggawa. A wata sanarwa da kungiyar ta Hamas ta fitar a jiya Asabar wacce ta kunshi wannan bayanin ta kuma ce; Sojojin mamaya suna ci gaba da rusa sauran cibiyoyin kiwon lafiya da su ka saura a yankin Gaza,haka nan kuma kai wa likitoci da ma’aikatan kiwon lafiya hari. Kungiyar ta Hamas ta bayyana abinda HKI take yi a karkashin ci gaba da rusa duk wani abu mai amfani a yankin Gaza. Wani sashe na sanarwar kungiyar ta Hamas ya kuma ambaci cewa; Ya zuwa yanzu adadin likitoci da ma’aiaktan kiwon lafiya da HKI ta kashe...
    A wata sanarwa da dakarun kare juyin juya halin musulunci ta Iran ta fitar a jiya Asabar ya ce; Abinda ya faru a lokacin yakin tsaron kasa mai tsarki na farko da na biyu, mayar da martanin Iran ya haifar da sakamako mai karfi wanda aiki ne na tsawon lokaci. Haka nan kuma sanarwar ta ce, duk wani sabon kuskure da abokan gaba za su yi na kawo wa Iran hari, to jamhuriyar musulunci ta Iran za ta sami fifiko akansu a fagen daga, domin martaninta zai zama mai tsanani. Dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran sun kuma bayyana makon tsaron kasa mai tsarki na tunawa da yake-yaken da aka kallafawa Iran, a matsayin daya daga cikin lokuta...
    Sanarwar ta ƙara da cewa, an bayar da ƙarin kayayyakin da za a raba a matsayin tallafin ne daga Hukumar Kula da Ilimi ta Duniya (UBEC) da UNICEF.   A jawabinsa a wajen taron, Gwamna Lawal ya sake nanata cewa gwamnatinsa ta zo ne da aikin ceto da sake gina jihar.   Ya ce: “Tun da farko mun gane cewa hanya mafi inganci wajen dawo da Zamfara kan turba ita ce saka hannun jari a zukatan al’ummarmu.   “A yau, a cikin wannan alƙawari, na yi farin cikin sanar da raba kayayyakin koyo da koyarwa 408,137 da gwamnatin jihar Zamfara ta sayo kai-tsaye.   “Wannan shi ne ɗaya daga cikin mafi girma na zuba jari a cikin albarkatun koyarwa da...
    A ɓangare ɗaya kuma Turkiyya na ƙara nuna damuwa bayan harin da Isra’ila ta kai a birnin Doha. Mai magana da yawun ma’aikatar tsaro ta Turkiyya, Rear Admiral Zeki Akturk ya yi gargaɗin cewa “Isra’ila za ta iya faɗaɗa hare-harenta baya ga Ƙatar. Za ta iya ingiza yankin baki ɗaya cikin bala’i.” Mece ce shawarar da Masar ta bayar? Shawarar da Masar ta bayar ya ƙunshi samar da tsarin haɗe ayyukan sojin ƙasa da na sama da cibiyoyin tsaro, tare da haɗe cibiyoyin horaswa da ayyukan soji. Haka nan kuma ƙasashen ne za su yanke hukunci kafin amfani da dakarun bayan tattaunawa a tsakaninsu. Kafar yaɗa labarai ta Al Akhbar da ke Lebanon ta ce a ƙarƙashin tsarin, Masar ta...
    “Sanarwar jan hankaki – Taron bogi ‘convocation’ a Nijeriya – Jami’ar ba ta ba Dauda Kahutu Rarara digirin girmamawa ba”.   A yau (Lahadi) ne aka sanar da Jami’ar EAU labarin wani biki da kafafen yada labarai na Nijeriya suka rahoto ƙaryar cewa, Jami’ar ta gudanar da wani taro a ranar Asabar a Hotel din ‘NICON Luxury’ Abuja, Nijeriya.   Jami’ar ba ta ba da izinin gudanar da wani taro a wannan wuri a ranar ba, kuma an shirya wannan taron ne ta hanyar damfara ba tare da sanin ko izinin Jami’ar ba. Waɗanda suka shirya wannan taron sun yaudari wasu da yardar cewa suna wakiltar Jami’ar EAU, amma wannan gaba ɗaya ƙarya ce kuma ba su da ikon yin...
    Gwamnatin yahudwan sahuniya ta kaddamar da hari da makami mai linzami kan wata motar hawa a layin Nabatiya- marjiyun dake khardali a kudancin labanon a ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da buda wuta da aka cimma tun 27 ga watan nuwamba na shekara ta 2024. Wannan hari wani bangare ne na kata yarjejeniyar da bangarorin biyu suka cimma, da hakan ya jawo mutuwar daruruwan mutane kuma ke kara jawo zaman dar-dar yankunan dake iyakar kasar da kuma HKI. Rahotanni da kafafen yada labarai na kasar labanon  suka fitar ya nuna cewa wadannan hare haren wani nau’I ne na keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma , da kuma ci gaba da wuce gona da iri a yankin...
    Shugaban kasar Iran Masud pezishkiyan ya bayyana cewa Iran ba za ta mika wuya ga bukatun da suka wuce kima ba, kuma za ta iya shawo kan duk wani takunkumi da aka kakaba mata, Shugaban ya fadi haka ne a wajen bukin karrama yan kasar da suka samu lambobin yabo a gasar Olympic ta kimiyya ta duniya , bayan da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya kada kuriar amincewa da kudurin dawo da takunkumi dake da alaka da shirinta na nukiliya. Haka zalika shugaban kasar yace makiya suna iya kai hari kan sakamakon binciken fasaha da aka yi, amma kwararru da masana ilimin kimiya wadanda suka samar da wadannan naurorin su ne hakikanin gaskiyar dukiya ga kasarmu, don haka...
    Rahotanni daga Islamabad sun nuna cewa gwamnatin kasar tana kwatanta yarjejeniyar tsaro da ta kulla da kasar Saudiya ,da irin wadda ke tsakanin dakarun tsaron kasashen turai da kuma kungiyar tsaro ta nato. Kasashen saudiya da Pakistan sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro tsakaninsu a wata ganawa da aka yi tsakanin prime minisata shehabaz sharif na Pakistan da takwaransa na kasar Saudiya Mohammad bn Salman a birnin Riyadh a ranar laraba da ta gabata inda suka kirata da yarjejeniya kan dabarun kasa, Musadik ya fadi cewa yarjejeniyar bata barazana ga kowa, kuma bata gayyaci wani ya kai wa kowa hari ba, amma kamar idan wata kasa dake cikin kungiyar kwance ta nato akai kai mata hari to kamar an kai...
    Shugaba kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Matatar Man Fetur na Kamfanin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewa tun bayan fara samar da man fetur a shekara guda da ta gabata, matsalar dogon layin man fetur da ta shafe shekara 50 ana fama da ita ta zama tarihi. A lokacin wani taron bita da aka gudanar don murnar cika shekara ɗaya tun bayan ƙaddamar da samar da man fetur daga masana’antar dake samar da ganga 650,000 a kowace rana, Dangote ya jaddada cewa Ƴan Nijeriya sun sha fama da dogon layin mai tun daga 1975, amma wannan matsala ta fara zuwa karshe tun lokacin da masana’antar ta fara aiki a ranar 3 ga Satumba, 2024. Dangote ya yi nuni da kalubale...
    Jami’ar European American University ta musanta bai wa fitaccen mawaƙin siyasar nan, Dauda Kahutu Rarara, digirin girmamawa na dokta. A jiya Asabar ce dai wani bidiyo da ya karaɗe dandalan sada zumunta ya nuna yadda ake karrama Rarara da digirin girmamawa a wani bikin yaye ɗalibai da aka gudanar a otel ɗin NICON Luxury da ke Abuja. Mutum 9 sun rasu a hatsarin jirgin ruwa a Sakkwato NAF ta hallaka Boko Haram 32 a Borno Sai dai cikin wani saƙo da ta fitar a shafinta a ranar Asabar, jami’ar ta ce sam ba ta da hannu a lamarin kuma ba da izininta ba. Jami’ar ta bayyana cewa, ba ta taɓa ba da izinin gudanar da taron karramawa ko taron yaye...
    Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin sahyuniya ta gaddamar da shirin mamaye wasu sabbin yankuna a kusa da birnin Qudus inda ta mamaye yankuna guda 3 kuma ta bukaci falasdinawa neman izini kafin su shiga gidajensu. Wannan mataki ya canza ka’idar mallakar kasa, bayan da Isra’ila ke kokarin kwace iko da muhimman wurare a gabar yammacin kogin jodan, wanda zai yi illa sosai ga yiyuwar samun kasar falasdinu mai cin gashin kai . Ana su bangaren hukumomin falasdinawa sun yi tir da wannan mataki, kuma sun bayyana shi a matsayin mataki mai muhimmacin wajen hade birnin Qudus da sauran yankunan falasdinawa ,kuma take hakokin falasdinawa ne. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies...
    A ranar Alhamis 18 ga watan nan, aka kaddamar da fara nuna fim din nan mai taken “Evil Unbound” a dukkanin sassan duniya, fim din da ya ba da labarin yadda a yayin yakin kin mamayar dakarun Japan, wata rundunar dakarun sojin kasar Japan ta aiwatar da wani shirin sirri, na gwaje-gwajen kimiyya ta makamai dake iya illata lafiyar bil’adama, a wani boyayyen wuri dake lardin Heilongjiang na arewa maso gabashin kasar Sin. Duk da cewa akwai shaidu na hakika, da suka tabbatar da aukuwar muggan laifukan da rundunar ta 731 ta tafka, bukatar kasar Sin ta shigar da wannan lamari cikin kundin killace abubuwan tarihi na UNESCO ya gamu da tsaiko, har na tsawon sama da shekaru shida. Kazalika,...
    Al’ummar Jihar Sakkwato na cike da fargaba da alhini bayan da wasu mazauna kauyuka da dama suka rasu a hatsarin kwale-kwale a Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato. Lamarin ya faru ne lokacin da jama’a ke tserewa daga wani sabon harin da ‘yan ta’addan Lakurawa suka kai, inda kwale-kwalen da ke dauke da mutane fiye da kima ya kife. Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na Rundunar ‘Yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Abubakar Rufa’i, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga wakilin Rediyon Najeriya a jihar. ASP Abubakar ya ce har yanzu ba a tantance adadin mutanen da suka shiga kwale-kwalen ba, yana mai jaddada cewa ana ci bincike da aikin ceto. Wani shaidan gani da ido, wanda bai...
    A gun liyafar murnar cika shekaru 76, da kafa Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin da ofishin jakadancin Sin dake Birtaniya ya shirya a jiya Jumma’a 19 ga wata, an gabatar da wani fim mai taken Shen Zhou 13, fim din kasar Sin na farko da aka dauka kai-tsaye a sararin samaniya kuma bisa fasahar 8K, wadda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar wato CMG ya tsara. Wannan ne karo na farko da aka gabatar da fim din a kasashen waje. Al’ummun kasar Birtaniya daga bangarori daban daban, da jami’an diflomasiyyar kasa da kasa dake Birtaniya, gami da Sinawa dake zaune a kasar sama da 400, sun halarci liyafar. Wasu ’yan saman jannati uku na kumbon Shenzhou-13, wato Zhai Zhigang,...
    Rundunar Sojin Saman Najeriya, ta kashe ’yan ta’addan Boko Haram 32, a wani farmaki da ta kai garin Banki da ke Ƙaramar Hukumar Bama, a Jihar Borno. Rahoton ya bayyana cewa farmakin ya auku ne a ranar 18 ga watan Satumba da misalin ƙarfe 10:15 na safe. Bayan biyan N50m an sako ma’aurata da ’yarsu su da aka sace a Katsina Mutum 9 sun rasu a hatsarin jirgin ruwa a Sakkwato Wannan na zuwa ne bayan ’yan ta’addan sun kai hari hedikwatar ’yan sanda da ke Banki. A lokacin kai farmaki , sojoji biyu sun rasa rayukansu, haka kuma wani ƙaramin yaro mai shekara tara, Ismail Abubakar, ya rasu. Har ila yau, maharan sun ƙone motocin soja uku. Bayan kai...
    Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta ce matsayin Sin dangane da batun kamfanin TikTok a bayyane yake, kuma tana jaddada aniyar gwamnatin kasar na martaba hakkokin kamfanoni yadda ya makata. Ma’aikatar ta ce Sin na maraba da matakin gudanar da shawarwari da kamfanoni bisa doron dokokin kasuwa, ta yadda za a iya kaiwa ga shawo kan matsaloli daidai da dokokin kasar Sin, da ka’idoji, da daidaita moriyar dukkanin sassa masu takaddama. Ma’aikatar ta ce Sin na fatan Amurka za ta dauki makamancin wannan tafarki, ta cika alkawuran da ta dauka, da samar da wata kafa ta adalci, marar nuna wariya, kuma ta bunkasa muhallin kasuwanci ga kamfanonin kasar Sin, ciki har da kamfanin TikTok, ta yadda zai ci gaba da...
      Kamfanin dillancin labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, lamarin wanda ya faru ne a lokacin da ake gudanar da aikin a ƙarshen mako a masana’antar, ya yi sanadin mutuwar ma’aikata biyu ciki har da wani jami’in soji da ke aiki tare da jikkata wasu huɗu.   “Na ji wani babban ƙara har sai da ya girgiza gine-ginen da ke kewayen DICON. Mutane na ta gudu daga wurin, amma muna tunanin fashewar bam ne, amma daga baya mun gano cewa daga masana’anta ne,” inji wani mazaunin da ya nemi a sakaya sunansa.   Shaidun gani da ido sun ce fashewar na da nasaba da samar da hoda mai matukar muhimmanci wajen ƙera hodar harsashi ga sojojin Nijeriya. Daga...
    A kwanan nan ne aka rufe taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO a takaice, a birnin Tianjin dake arewacin kasar Sin, inda shugaban kasar, Xi Jinping ya gabatar da shawarar tsarin inganta jagorancin duniya. Wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, ta zanta da shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, wanda ya halarci taron, inda ya ce, ana amfani da ma’aunai biyu a halin yanzu a duk duniya. A cikin shawarar tsarin inganta jagorancin duniya da shugaba Xi Jinping ya gabatar, akwai wani muhimmin bangare na gudanar da harkokin duniya bisa dokokin kasa da kasa, wato ya kamata a mutunta ka’idoji. Masoud Pezeshkian, ya ce bai kamata a aiwatar da ma’aunai biyu a...
    Iran ta yi gargadin cewa za ta kawo karshen duk wata yarjejeniyarta da hukuar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, muddin ake sake dawo mata takunkuman MDD. Kwamitin koli na tsaron kasar Iran ya ce Tehran za ta dakatar da hadin gwiwar da take yi da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) bayan da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’ar dage takunkumin da aka kakabawa Tehran na dindindin. A cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Asabar, babban jami’in tsaron kasar Iran ya yi Allah wadai da matakin “marasa hankali” da Birtaniya, Faransa, da Jamus –wanda aka fi sani da E3– game da shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran cikin lumana Mataimakin ministan shari’a da...
    Venezuela ta yi Allah-wadai da Amurka kan abinda ta danganta da yakin da ba ta shelanta ba a yankin Caribbean, ta kuma bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta binciki sabon harin da Amurka ta kai kan wani jirgin ruwa, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane uku.. Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin cewa sojojin Amurka sun kai hari na uku kan wani jirgin ruwa da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi. Ya fitar da wani sabon faifan bidiyo da ke nuna abin da ya yi ikirarin harin da Amurka ta kai da ya kashe ‘yan ta’adda uku.. Wadannan hare-haren da jiragen yakin Amurka F-35 suka kai, rahotanni sun ce sun kashe akalla mutane 17 a cikin ‘yan makonnin nan....