HausaTv:
2025-09-18@01:00:31 GMT

Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan (a) 105

Published: 5th, April 2025 GMT

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’ani  mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da Littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin Rumi, ko kuma cikin wasu littafan.

Da fatana masu sauraro zasu kasance tare da mu.

///.. Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Alhassan lamami na biyu daga limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All…(s) kuma da na farko ga Fatimah (s) diyar manzon All..(s).

A cikin shirimmu da ya gabata,  mun yi magana kan yadda aka zabi Khalifa na uku Uthman bin Afffan a matsayin khalifa, a dai dais aura kadan lokacinda Khalifa na biyu ya ware-masu na su zabi daya daga cikinsu a sare wuyoyin su.

Abdurrahman dan Auf wanda shi ne shugaban kwamitin ya rasa abinda zai yi, yayi ta neman shawara daga mutane daban daban. Kowa da abinda yake fada masa. Ammar dan Yasir ya ce masa idan yana son hadin kan musulmi to ya zabi Aliyu dan Abitalib(a) . wasu kuma sun ce masa idan yana son hadin kan kuraishawa to ya zabi Uthman dan Affan. Wannan haka ya ci gaba da faruwa, har zuwa lokacinda Sa’ad dan Abi wakkas ya zo kusa ya fada masa cewa ya yi saura a yanke wannan jayayyar ya zabi daya daga cikin wadannan mutane biyu.

A nan ne sai ya zo kusa da Aliyu dan Abitalib (a) yace masa, zan yi maka bai’a tare da sharadin zaka yi hukunci da littafin Allah da sunnar manzon All..da kuma ayyukan Abubakar da Umar. Sai Ali(a) ya bashi amsa da cewa, sai da littafin All..da sunnan Manzon All..da kuma ijtihadi na da ra’ayi na.

Sai abdurrahman yayi kokarin gamsar da shi ya amince da hakan, amma ya ki amincewa. Sai kawai ya koma wajen Uthmanu, ya bijiromasa sharuddan da ya bijirowa Aliyu (a). sai ya  ce ka kawota da dukkan sharuddanta na amince. Sai Abdurrahman yayi masa bai’a a matsayin khalif ana hudu.

Aliyu dan Abitalib (a) bai ji dadi ba, sai ya zo ya fadawa Abdurrahman kan cewa yayi wa Uthman bai’a ne don ya mayar masa da ita wata rana, sai yayi addu’a , yana cewa All..kada ya daidaita a tsakaninsu.  

Daga nan sai Aliyu (a) ya juya ta fita daga cikin masallaci ko wurin taron. Wannan duk yana faruwa a gaban Imam Hassan (a). Ya ga a wannan karomma yadda aka hana babanshi hakkinsa, wanda All..ya bashi. Daga nan Magana ta kare, Uthman ya zama khalif ana ukku. Amma wani irin shugabancin ne Uthman yayi?

Malaman tarihi da dama sun bayyana cewa uthman ya karbi Khalifanci ne kawai amma ya barwa Marwan dan Hakan dan amminsa kuma surukinsa yana tafiyar da al-amura al-ummar musulmi.

Shugabancinsa na ciki da matsalolin. Banda haka sanadiyyar yadda ya tafiyar da shugabancinsa al-ummar musulmi ta fada cikin matsaloli, kafin a kashe shi da kuma bayan kisansa har zuwa yau shekaru kimani 1400 da suka gabata, musulmi suna dandana, musibar abinda shugabancin Khalifa Uthman ya jawo, kuma har tashin kiyamah.

Matsala ta farko wacce Khalifa Uthman ya fara fuskanta ita ce. Ubaidullah dan Umar dan Khalifa Umar ya dauki makami ya je ya kashe Hurmozan, da Jufainatu da kuma diyar Abu Lulu’a don daukar fansar kissan mahaifinsa Khalifa na biyu. Wadan nan da ya kashe ba sune suka kashe babansa ba, wanda ya kashe babansa shi ne Abu lulu’a shi kuma ya gudu ya bar gari.

Wasu kuma sun ce wasu sahabban manzon All..(s) sun kashe shi, amma babbar matsala ita ce kissan da Ubaidulahi dan Umar yayiwa, Hurmozan, da Jufainah da kuma diyar Abu Lulul’i. don basu da hannu wajen kashe Khalifa Umar.

Har’ila yau wannan kissar ta faru ne kafin a zabi Khalifa na ukku bayan da Abu lulu’I ya soki Khalifa da wuka a masallaci yana bada sallah, kafin a zabi khalif ana uku.

Don haka matsala ta farko wacce ya fuskanta ita ce batun hukuncin Ubaidullah dan Umar, wasu sahabban manzon All..(s) sun dage kan cewa sai an yi kisasi kan Ubaidullah, saboda kissan da gangan ce. Daga cikin wadanda suke da wannan ra’ayin akwai amirulmuminina Aliyu dan abitalib (a).

Don haka Khalifa Uthman ya nemi shawarar sahabban manzon All..(s) da dama, wasu suce ya yi kisasi wasu kuma su ce ya biya diyya, wasu sun ce masa ta yaya zai kashe dan Khalifa Umar a yau bayan an kashe babansu a jiya. Wasu kuma sun ce masa a wajen yin kisasi shi ya dace, don kada wani dan babban gida ya sake irin wannan, ya zama idan mutum ya fita daga gidan babban mutum sai a ki yi masa hadda, amma in dan talaka ne sai a zartar da haddi a kansa, da sauransu.

Amma Amru dan Asi ya bashi shawara kan cewa.:

A lokacinda ubaidulla kashe wadannan mutane, kai ba khalifa bane, don haka kada ka sa kanka cikin matsala, kayi duk abinda zaka yi da shi in banda kisa.

A nan khalifa ya karbi shawarar dan Ass, ya ce zai biya diyyar kissan Hurmuzan, daga cikin kudinsa ba na Baitul mali ba, sannan ya bada umurnin a saki Ubaidullah dan Umar wandakafin haka ana tsare da shi a gidan yari.

Amma wasu sahabban sun ci gaba da yi masa barzana kan cewa duk sanda aka sami dama sai an zartar da haddin kisasa a kansa.

Daga cikinsu akwai Ziyad dan Lubaid, wanda Ubaidullah ya kai kararsa gaban Khalifa, uthman wanda ya kira shi ya kuma ce masa kada ya sake.

Daga karshe dai Khalifa ya ce masa ya bar madina ya koma Kufa da zama, ya bashi gida a can har lokacinda al-amura zasu lafa. Da haka aka wuce maganar Ubaidullah dan Umar.

Malaman addinin musulunci a tsawon tarihi sun yi ta sabani a tsakaninsu dangane da yadda Khalifa na uku ya warware maganar kissan Hurmuzan da Juhainatu da kuma diyar Abu lulu’a a farkon khalifancinsa.

Wasu suna ganin alkawalin da Khalifa Uthman ya dauka daga Abdurrahman dan Auf na cewa za iyi hukunci da littafin All..da sunnar manzon All…(s), ya sabawa masu a hukunci na farko da yayi a farkon Khalifancinsa.

Suna kafa hujja da hadisin manzon All..(s) wanda yake Magana a kan zartar da haddin All..a kan talaka da masu arziki, kuma ya nuna masu a aikace kan wani ko wata da tayi sata kuma wanda ya fito daga babban gida. Don haka ya zartar da hukunci All..a kanta. Sannan yace.. da Fatimah(s) diyar Muhammadu (s) zata yi sata da ya yanke hannunta.

Amma Taha Hussain sanennen marubuci dan kasar Masar ya na ganin a wannan halin, matakin da khalifa Uthman ya dauka shi ne dai dai, don a musulunci manzon All..(s) ya bada umurnin a yi watsi da haddi ko da da Shubha ne, yace ana iya daukar shubaha a nan kasancewar ubaidullahi dan Umar yana cikin fushi a lokacinda ya kashe wadannan rayuka guda uku.

Amma idan mun dawo kan Imam Hassan (a) a zamanin Khalifa Uthman, zamu ga cewa a lokacin shi matashi ne dan shakara kimani 20 a duniya. Wasu malaman tarihi sun bayyana cewa, Imam Hassan (a) ya je yaki  karkashin rundunar Ukbatu dan Nafiu, da Abdullahi dan Nafiu, zuwa afrika kuma sun sami nasara yada fadada daular musulunci a lokacin har zuwa mafi yawan arewacin Afrika.

Sannan daga baya Abdullahi dan Abisarkh ya nemi izinin Uthman ya kara fafada daular musulunci a arewacin Afirka, sai ya bashi izini, ya kuma kara masa sojoji. Abdullahi dan Abisarkh ya fadada daulara a wasu yankuna.

Wasu malaman sun bayyana cewa a cikin rundunar Akwai, Amr dan Ass, Abdullahi dan Jaafar, da Alhassan da Alhussain (a). kuma sun sami nasara a yankin.

Hakama sun fito yaki zuwa Tabriztan a cikin kasar farisa a lokacin ina shima suka sami nasara.

Sai dai akwai wasu malamai suna musanta cewa Imam Alhassan da Imam Alhussain sun je yaki fadada daular musuluni a zamanin khalifa Uthman kamar yadda muka ambata.

Hakama marubucin littafin futuhatul Islamiyya, bai kawo labarin cewa Alhassan da Alhussain (a) sun je yake-yaken futuhat a zamanin khalif ana ukku a arewacin afrika ba. Amma ya kawo cewa sun halacci yakin Tabristan na kasar Farisa a lokacin.

Ynazun kuma sai siyasar dukiya a zamanin khalifa na uku, wanda yake da bambanci so sai idan an kwatanta da wadanda suka gaba ceshi. Khalifa na farko ya ci gaba da raba kudi kamar yadda manzon All..(s) yake yi a mafi yawan lokuta. Amma khalifa na biyu shi ne ya samar da matakai-matakai a tsakanin musulmi, kamar yadda muka fada a baya.

Asalin rabon kudi a musulunci, kamar yadda Amirulmuminina (a) ya fadawa Abdullahi dan Zam’ah a lokacinda ya zo masa a lokacin khalifancinsa.yace masa (wannan dukiyar nan aka b aba nawa bane, wannan dukiyar na musulmi ne, wanda takubbansu suka samar da su, idan ka yi tarayya da su a yakin da suka yi, kaima kana da rabo kamar yadda suke da shi a cikinsa, in ba haka ba, abinda suka samar ba zai zama rabon waninsu ba.).

Banda haka ya rubutawa walinsa a Makka Kathum ibn Abbas, y ace masa: ka duba cikin abinda ka tar ana dukiya, ka raba shi cikin wadanda suke da iyali mai yawa, da kuma wadanda suke fama da yunwa. Ka tabbatar da cewa ka bawa wadanda suke fama da talauci …sannan abinda ya rage ka aiko mana don mu rabawa wadanda suke wajemmu..

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wata fitowa idan all..ya kaimu wassalamu alaikum warhamatullahi wa barakatuhu.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Ubaidullah dan Umar Khalifa Uthman ya khalifa Uthman ya wadanda suke wasu kuma su masu sauraro kamar yadda

এছাড়াও পড়ুন:

An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar

Antoni Janar na Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke birnin Yamai a Nijar, ya bayyana cewa an kama tsohon Ministan Harkokin Waje, Ibrahim Yacoubou, bisa zargin hannunsa a cikin wata aika-aika ta kisan kai domin yin tsafi.

A cewar Maazou Oumarou, lamarin ya samo asali ne daga wani binciken ’yan sanda da aka fara gudanarwa tun a ranar 29 ga Yuli, 2025.

KEDCO ya ƙaryata asibitin AKTH kan mutuwar majinyata saboda ɗauke wuta Dole sai mun tantance wa’azi kafin a yi —Gwamnan Neja

Ya bayyana cewa, an soma gudanar da binciken ne dangane da yunƙurin kisa a wani yanki da ke wajen birnin Yamai, lamarin da ya kai ga cafke ababen zargin a garin Dosso.

Wani mutum mai suna Mahamadou Noura ne ya bayyana cewa shi ne ya yi yunƙurin kisan, tare da wasu kashe-kashe guda shida da ya aiwatar a baya, bisa umarnin wasu mutane, ciki har da tsohon ministan Ibrahim Yacoubou.

Mutumin ya shaida wa mahukunta cewa ya aikata hakan ne domin yin tsafi da gawarwakin, a madadin wasu mutane da suka haɗa da: Issa Ali Maiga da Ismael Morou Karama da Elhadji Bilya da kuma Issa Seybou Hama.

TRT ya ruwaito cewa tuni dai an cafke duk ababen zargin, yayin da Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta umurci ’yan sanda da su ci gaba da bincike tare da ɗaukar ƙarin matakan da za su tabbatar da gaskiya.

Sanarwar ta ce: “Manufar wannan mataki na shari’a ita ce a tattara cikakken rahoto da ke ƙunshe da dukkan abubuwan da suka faru, sannan a miƙa shi ga ɓangaren gurfanarwa.”

Mai shigar da ƙara a ɓangaren gwamnati ya ce, la’akari da girman wannan lamari, wajibi ne a gudanar da bincike cikin gaggawa.

Haka kuma ya buƙaci al’umma da su mutunta ’yancin kotu tare da bayar da cikakken goyon baya domin fayyace gaskiya.

Ana iya tuna cewa, Ibrahim Yacoubou na daga cikin manyan jami’an da aka kama bayan juyin mulkin Nijar na ranar 26 ga Yuli, 2023, sai dai daga bisani an ba shi beli na wucin gadi a cikin watannin baya.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
  • An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • Chadi:  Majalisa ta amince a baiwa shugaban kasa  damar ci gaba da Mulki har karshen rayuwa
  • Sowore Ya Maka DSS, Meta da X A Kotu Kan Take Masa Haƙƙi
  • NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano
  • ’Yan ‘Mafiya’ na ƙoƙarin kashe matatar man fetur da na gina —Ɗangote
  • ’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhu
  • NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas
  • An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar