Hukumar fansho ta jihar Jigawa da kananan hukumomin jihar ta fara biyan sama da naira miliyan 733 ga  ma’aikata sama da 280 da suka yi ritaya da kuma ‘yan uwan ​​ma’aikatan da suka rasu.

Shugaban hukumar Dakta Bilyaminu Shitu Aminu ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga wadanda abin ya shafa a ofishin fansho da ke Dutse babban birnin jihar.

Ya bayyana cewa kudaden sun hada da na barin aiki,  da na ma’aikatan da suka mutu.

A cewarsa, ma’aikatan 281 sun hada da na jiha, da kananan hukumomi da na hukumar ilimi, wadanda suka yi ritaya na son rai ko kuma sun kai shekarun ritaya ko kuma wadanda suka mutu suna aiki.

Dakta Bilyaminu Shitu ya ci gaba da bayanin cewa  za a biya ma’aikata 208 da suka yi ritaya daga aiki sama da naira 542, yayin da za a biya sama da Naira miliyan 144 ga ‘yan uwan ​​wadanda suka mutu a bakin aiki su 47.

A cewarsa, rukunin karshe su ne ma’aikata 26 da suka yi ritaya daga aiki kuma suka fara karbar fansho duk wata amma sun mutu kafin su kai wa’adin mafi karancin shekaru biyar bayan sun yi ritaya.

Shugaban hukumar ya bayyana cewa jihar Jigawa  na daya daga cikin jihohin da ke da kyakkyawan tsarin fensho mafi inganci a kasar nan, duba da yadda ta ke kokarin biyan wadanda suka yi ritaya ba tare da wata matsala ba kuma akan lokaci.

Ya ce wannan gagarumin ci gaba ya nuna irin yadda gwamnatin jihar ta himmatu wajen kyautata rayuwar ‘yan fanshonta da kuma muhimmancin tabbatar da biyan hakkokin wadanda suka yi wa jihar hidima.

Shugaban ‘yan fanshon ya ce, hukumar ta jajirce wajen tabbatar da biyan kudaden fansho cikin lokaci da inganci kuma tana sa ran za ta ci gaba da yin sabbin abubuwa da nufin inganta jin dadin ‘yan fanshonta.

Biyan kudaden da aka gudanar a hedikwatar hukumar fansho ta jihar Jigawa dake Dutse, wani bangare ne na kokarin karrama kwazon ma’aikatan gwamnati da suka sadaukar da kai wajen yi wa jihar hidima.

Shugaban hukumar ya kuma yabawa Gwamna Malam Umar Namadi bisa irin goyon bayan da yake bai wa hukumar.

Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, wadanda aka biya hakkokin nasu, sun nuna jin dadinsu da yadda aka biya su akan lokaci.

Sun yi nuni da cewa, biyansu kudaden  zai ba su damar sauke nauyin da ya rataya a wuyansu da kuma inganta rayuwarsu a lokacin ritaya.

 

Usman Muhammad Zaria

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa da suka yi ritaya wadanda suka

এছাড়াও পড়ুন:

Aikin Hajji: Za A Fara Jigilar Alhazan Jihar Kwara A Ranar 12 Ga Watan Mayu

A cewarsa, tuni aka shirya wuraren kwana da abinci ga maniyyatan a kasar Saudiyya.

 

Abdulkadir ya tabbatar da cewa, ana shirye-shirye, inda za a yi alluran rigakafi a ranar 28 ga Afrilu, za a raba tufafi a 30 ga Afrilu, sannan kuma za a raba jakunkuna a ranar 1 ga Mayu.

 

Ya kara da cewa maniyyatan da suka biya sama da Naira miliyan 8.4 na kudin aikin Hajji, za a biya su bayan sun dawo daga Saudiyya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu gobe Alhamis
  • Tsoffin ma’aikatan NECO na neman a biya su bashin haƙƙoƙinsu
  • Za A Yi Allurar Rigakafi Ga Dabbobi Sama Da Miliyan Daya A Babura
  • Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Shirya Fara Tantance ‘Yan Fansho
  • Gwamna Namadi Ya Nada Aisha Mujaddadi Sabuwar Shugabar Hukumar InvestJigawa
  • Boko Haram ta kashe masu zaman makoki 7 a Chibok
  • Hajjin 2025: An Fara Yi Wa Maniyyata Allurar Rigakafi A Jigawa
  • Hajjin 2025: Gwamna Namadi Ya Nada Sarkin Kazaure Amirul Hajj
  • Aikin Hajji: Za A Fara Jigilar Alhazan Jihar Kwara A Ranar 12 Ga Watan Mayu
  • Iran Da Rasha Sun Jaddada Yin Aiki Tare A Fagen Kiwon Lafiya