Gwamnatin Gombe ta horar da makiyaya kan sabbin hanyoyin kiwo
Published: 19th, February 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Gombe ta horar da makiyaya 684, ciki har da nakasassu, mata, matasa, da tsofaffin ma’aikata, kan sabbin dabarun kiwon awaki da kasuwancinsu.
Wannan horo ya gudana ne ƙarƙashin shirin Livestock Productivity and Resilience Support (L-PRES).
Rigima ta sake kaurewa tsakanin PDP da APC a Zamfara Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a BornoKwamishinan Aikin Gona, Kiwo, da Hada-hadar Ƙungiyoyi na Jihar Gombe, Dokta Barnabas Malle ne, ya jagoranci ƙaddamar da horon a Gombe.
Yayin da yake jawabi, ya jaddada ƙudirin gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, na inganta kiwon dabbobi da tallafa wa al’umma.
Ya ce: “Shirin ya dace da manufofin gwamnati na bai wa kowa damar cin gajiyar shirye-shiryen da ake gudanarwa.”
Shugaban shirin L-PRES na Gombe, Farfesa Usman Bello Abubakar, ya bayyana cewa horon zai taimaka wa makiyaya wajen ƙara ƙwarewa da haɓaka kiwon awaki.
Ya ce: “Mun mayar da hankali kan makiyaya saboda muhimmiyar rawar da suke takawa wajen samar da awaki a tsakanin al’ummarmu.
“Manufarmu ita ce ƙara musu ƙwarin gwiwa da ƙwarewa don su inganta rayuwarsu.”
Farfesa Abubakar, ya ƙara da cewa buƙatar naman awaki a duniya na ƙaruwa, don haka Gombe na da shirin kafa cibiyar kiwon awaki ta zamani da kuma babbar kasuwa ta yanka dabbobi a Najeriya.
A yayin horon, an koyar da mahalarta yadda ake:
Zabar nau’in awaki masu inganci Ciyarwa mai kyau Rigakafin cututtuka Inganta muhalli don kiwoDabarun kasuwanci da sarrafa kayayyakin da ake samu daga awaki
Shugaban Ƙungiyar Masu Nakasassu ta Jihar Gombe, Ja’o Sarkin Aiki, ya yaba wa gwamnatin bisa wannan horo
“Wannan horo zai taimaka mana wajen bunƙasa kiwonmu da kuma dogaro da kanmu don samun ingantacciyar rayuwa.”
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Dalilin karyewar farashin shinkafa a kasuwannin Najeriya
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Rahotanni suna nuna cewa farashin shinkafa, ɗaya daga cikin nau’ukan abincin da ’yan Najeriya suka fi ci, ya karye a wasu sassan ƙasar.
Sauyin farashin ya sa ana tambayoyi — shin me ya haifar da wannan sauyi? Kuma me hakan ke iya haifarwa a rayuwar talaka?
NAJERIYA A YAU: “Dalilin da muke sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki” DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin ArewaA kan wannan sauyi da dalilansa ne shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari.
Domin sauke shirin, latsa nan