2025-05-01@08:24:57 GMT
إجمالي نتائج البحث: 803

«ababen hawa da»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Majalisar dokokin jihar Jigawa ta jaddada aniyar ta na hada kai da ofishin kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF domin samun nasarar aiwatar da tsare-tsare da za su inganta rayuwar yara da marasa galihu a jihar.   Mataimakin kakakin majalisar, Alhaji Sani Isyaku Abubakar, ya bada wannan tabbacin lokacin da ya karbi bakuncin tawagar ofishin UNICEF na Kano karkashin jagorancin Hajiya Fatima Adamu.   Ya lura cewa irin wannan haɗin gwiwa tsakanin majalisa, Action Against Hunger da Save the Children International sun haifar da sakamako mai kyau ta hanyar tallafawa matakan majalisa ta hanyar fasaha da ba da shawara don tsara manufofin da sauran tsare-tsaren a Jigawa.   Alhaji Sani Isyaku Abubakar ya bada tabbacin ci gaba...
    Falasdinawa sun gudanar da wata gagarumar liyafar tarbar fursunonin Falasdinawa 114 a Ramallah da aka sako daga gidan yarin ‘Yan sahayoniyya Daruruwan jama’a a birnin Ramallah da ke gabar yammacin kogin Jordan sun gudanar bikin tarbar fursunoni 114 da aka sako daga gidan yarin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a wani bangare na biyu na yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya, yayin da wasu fursunoni 16 daga cikinsu suka isa birnin Zirin Gaza. Jama’ar garin Ramallah sun dauki fursunonin da aka sako a kafadarsu a matsayin alamar nasara. Fursunonin sun bayyana godiyarsu ga ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa kan jajurcewar da suka yi a Gaza, kuma har ta kai ga kulla yarjejeniyar musayar. A yayin bikin,...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya zayyana wani ra’ayi mai manufar tsarkake zirin Gaza. Trump na mai cewa yana son aikewa da Falasdinawa daga yankin zuwa kasashen Masar da Jordan “na dan lokaci” ko kuma “a cikin dogon lokaci”. don samun zaman lafiya. Ana dai ganin tamakar Trump na kwatanta yankin Falasdinu da “wurin rushewa nan gaba” bayan watanni 15 na yakin da Isra’ila ta kadamar kan Gaza.