2025-11-23@09:06:38 GMT
إجمالي نتائج البحث: 233
«yana musayar wasiku»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
’Yan sanda sun kama wani korarren jami’in shige da fice a yayin da yake kokarin sayar da makamai Ga ’yan ta’adda. Kwamishinan ’Yan Sanda na Babban Birnin Tarayya, Olatunji Rilwan Disu, ya bayyana cewa an kama jami’in ne a hanyarsa ta kai wa ’yan ta’addan bindigogi a yankin Zuma da ke Ƙaramar Hukumar Bwari. Da yake jawabi a hedikwatar rundunar, CP Olatunji Rilwan, ya bayyana cewa dubun korarren jami’in tsaron ta cika ne a ranar 27 ga watan Fabrairu, 2025. Ya bayyana cewa jami’an rundunar yaki da masu garkuwa da mutane ƙarƙashin jagorancin OC Mustapha Muhammad ne suka kama shi, bayan samun bayanan sirri. NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Su Ga Ragi A Farashin Man Fetur...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A al’adance, a duk lokacin da watan Ramadana ya ƙarato samari da ’yan mata kan yi musayar kyaututtuka domin kyautata wa juna. Misali, samari kan haɗa kayan buɗe-baki irinsu madara da ƙwai da sauran kayan maƙulashe da ake yi wa lakabi da ‘Ramadan Basket’ a turance su kai wa ’yan matansu. Sai dai a wannan shekarar da alamun abin ya sauya salo, domin kuwa ba kamar yadda aka saba ba, kafafen sada zumunta ba su baza hotuna da bidiyon Ramadan Basket ɗin ba. NAJERIYA A YAU: Yadda za ku yi girke-girken azumi da kuɗi kaɗan DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya A Yau na wannan...
Farashin kayayyakin abinci kamar masara da shinkafa da gero da dawa da wake da gari da waken soya da dai sauransu sun ragu, musamman a manyan jihohin da ake nomawa, kamar yadda wani bincike da Aminiya ta gudanar ya nuna. Wannan na faruwa ne gabanin watan Ramadan, wanda aka fara yau Asabar. Yadda ake ‘Spring rolls’ Ramadan: ’Yan sanda sun tsaurara tsaro saboda azumi a Borno Haka kuma an ce, jihohin da ba sa noma suna jin tasirin rage farashin kayan abinci. Masana sun danganta faduwar farashin da aka samu a kasuwa ga karancin kudi da kuma yadda aka yi bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara, wanda hakan ya haifar da faduwa farashin sosai. Wasu kuma sun ce, yawan shigo da...
Cecekucen dai a tsakanin Donald Trump da kuma Vladmir Zylinesky an yi shi ne saboda banbancin ra’ayin da bangarorin biyu suke da shi akan batun kawo karshen yakin Ukiraniya. Shugaban Amurka Donald Trump dai yana son ganon takwaransa na Ukiraniyan ya amince da kawo karshen yankin da kasarsa take yi da Rasha, yayin da Zylinesky yake Magana akan wasu sharudda kafin hakan ta faru. Shugaban kasar Amurkan ya yi wa shugaban kasar Ukiraniya goron cewa, kasarsa ce take ba su taimakon kudade da makamai, yana mai kara da cewa; Ko dai ya amince da kulla yarjejeniyar kawo karshen yakin ko kuma Amurka ta dakatar da duk wani taimako. Haka nan kuma shugaban na Amurka ya zargi shugaban Ukiraniya da cewa,...
Hukumar Karɓar Koke-Koke da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano (PCACC), ta kama Shugaban Ƙaramar Hukumar Ƙiru, Abdullahi Mohammed, bisa zargin sayar da filin da aka tanada don gina Filin Wasa na Kafin Maiyaki. Ana zargin cewa Mohammed, ya sayar wa wani kamfani mai suna Mahasum filin. An ga watan Ramadan a Najeriya An ga jinjirin watan Ramadan a Saudiyya An gano cewar an tura kuɗin filin Naira miliyan 100 a asusun banki na shugaban. Mai magana da yawun ƙaramar hukumar, Kabir Abba Kabir, ya tabbatar da kama Mohammed. Ya tabbatar da cewa an tura jimillar kuɗi har Naira miliyan 240 tsakanin Nuwamba 2024 zuwa Fabrairu 2025, a asusunsa. Sai dai hukumar ta ce ta karɓo kuɗaɗen haba ɗaya....
Kungiyar Hamas wacce take iko da Zirin Gaza ta bada sanarwan cewa an kawo karshen takaddama da HKI dangane da jinkirin da tayi wajen sakin fursinonin Falasdinawa 620 a ranar Asabar da ta gabata bayan da ta saki fursinoni yahudawa har 6. Tashar talabijin ta Prersstv a nan Tehran ta nakalto kakakin kungiyar Hazem Qassem yana fadar haka a yau Laraba, ya kuma kara da cewa, gwamnatin kasar Masar ce mai shiga tsakani, kuma ta lamuncewa kungiyar kan cewa shirin musayar zai sake komawa kan yadda aka tsara shi, sannan HKI zata sake wadannan fursinoni Falasdinawa. Banda haka labarin ya kara da cewa a gobe Alhamis ma kungiyar Hamas zata mika gawakin yahudawa 4 wadanda take tsare da su a...
Jagoran harkar musulunci ta Najeriya wanda ya halarci jana’izar shugaban kungiyar Hizbullah Sayyid Shahid Hassan Nasrallah a birnin Beirtu ya bayyana cewa; Yadda miliyoyin mutane su ka halarci jana’izar yana nuni da cewa, gwgawarmayar musuluncin ta sake jaddada kanta. Sheikh Ibrahim Yakub Ibrahim El_Zakzaky ya kuma ce; Sayyid Hassan Nasrallah yana a matsayin takaitaccen hoton al’ummar musulmi ne, kuma gudanar da jana’izar da na gani yana nuni da cewa; Ruhinsa yana nan a raye cikin fagen daga. Har ila yau jagoran ja harkar musulunci a Nigeria ya ce, abokan gaba ‘yan sahayoniya sun zaci cewa ta hanyar kisan gilla za su kawo karshen gwgawarmaya,amma abinda yake faruwa a yau, yana nuni da cewa gwgawarmaya ta kara sabunta kanta, kuma da...
Tawagar Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: Ba a hana sayar da jirgin mara matuki ciki na ‘Shahed’ ba Tawagar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta mayar da martani kan baje kolin jirgin saman Iran a babban taron jam’iyyar Republican inda ta ce: Babu wata doka da ta haramta sayar da jirgin sama maras matuki ciki na Shahed. Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya kara da cewa: Jirgin sama mara matuki ciki na Shahed yana daya daga cikin mafi kyawun nau’ikan jiragen sama marasa matuka ciki a duniya, kasancewar yana da kwarewa sosai wajen ganowa, sa ido da kuma aiwatar da aiki inda ya dace, sannan kuma yana da araha da...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yabawa tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) bisa irin gudunmawar da ya bayar ga ci gaban Najeriya. Shugaban kasar a bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da tallafin, tarihin rayuwar Janar Babangida da gwagwarmayarsa yayin aiki, wanda aka gudanar a Abuja. A yayin da yake jawabi a matsayin babban bako na musamman, Tinubu ya bayyana ga irin jagoranci Babangida a yayin mulkinsa, wanda ya ce ya abin koyi ne ga kowa. Ya kuma yaba da rawar da IBB ya taka wajen kafa sabbin bankuna na zamani, wanda ya kawo kyakkyawa sauyi a fannin hada-hadar kudi na Najeriya. Tinubu ya kuma yabawa manufofin Babangida da salon shugabancinsa da suka...
Kungiya mai gwagwarmaya ta Falasdinawa Hamasa ta bayyana cewa tana iya sakin fursinoni yahudawa wadanda suke hannunta gaba daya a lokaci guda a marhala ta biyu ta musayar fursinoni tsakaninta da tare da sharadin ta cika al-kawulan da ta nauyi alhakin aiwatar da shi a wannan karon. Daga cikin har da maida tsagaita wutan na din din din Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Taher Al-Nounou ya cewa idan an yi haka za’a kammala musayar fursononin gaba daya, sannan HKI ta sake duk fursinonin falasdinawa gaba daya da suke hannunta. Yin hakan ya na nuna yanda al-amarin musayar Fursinoni yake da muhimmancin ga falasdinawa. Kafin wannan sanarwan dai ministan yaki na HKI Isarael Katz ya bayyana cewa...
Kasar Sin na maraba da duk kokarin da ake yi cikin lumana don warware rikicin kasar Ukraine, ciki har da tattaunawa tsakanin Amurka da Rasha, kuma Sin na fatan dukkan bangarori da masu ruwa da tsaki za su shiga cikin shawarwarin samar da zaman lafiya in lokaci yayi. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ne ya bayyana hakan a taron manema labarai na yau Talata, yana mai cewa, ko da yaushe kasar Sin tana da yakinin cewa, tattaunawa da yin shawarwari, ita ce hanya daya tilo da za a iya warware rikicin, kuma ta himmatu wajen inganta shawarwari don samar da zaman lafiya. Ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga wata tambaya game da ganawar da jami’an...
Babban kwamandan sojojin kasar Iran ya bayyana cewa: Sun sabunta hanyoyin da sojojin Iran zasu mayar da martani kan duk wani harin wuce gona da iri kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bada umarni Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdur-Rahim Mousawi ya bayyana cewa: Tun tsawon kwanaki da suka gabata jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewa: Idan Amurka ta farma tsaron al’ummar Iran, to lallai Iran za ta kai farmaki kan tsaronta ba tare da wata shakka ba, wannan ya kasance umarni ne bayyananne ga dakarun Iran, kuma kwamandojin sun sabunta shirinsu na aiwatar da wannan umarni, kuma a halin yanzu Iran a shirye take tsaf don gudanar da umarni a aikace. Manjo Janar...
Jaridar Maariv Ta Isra’ila Ta Bayyana Wasu Daga Cikin Hasarorin Da Yakin Gaza Ya Janyo Wa Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya
Jaridar Ma’ariv ta Isra’ila ta bayyana adadin wadanda suka jikkata a cikin sojojin mamayar Isra’ila da kuma miliyoyin yahudawan sahayoniyya da suka samu matsalar tabin hankali a lokacin yakin Gaza Jaridar “Ma’ariv” ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana a jiya litinin, adadin wadanda suka mutu a cikin jerin sojojin mamayar Isra’ila a yayin mummunan ayyukan ta’addancin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan Zirin Gaza, wanda ya shafe tsawon watanni 15 kafin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni a watan Janairun da ya gabata. A cewar jaridar, sojoji 15,000 da ke cikin sojojin mamayar Isra’ila suka jikkata tun farkon yakin ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, yayin da wasu 846 suka sheka lahira. Daga cikin wadanda...
Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da aikin gina titin Kanya Babba (Kwanar Duzau) zuwa Kankare zuwa Ballada zuwa Duzau zuwa Danhill zuwa Kyambo zuwa Mundu zuwa Goron Maje. Aikin wanda aka bayar da shi kan kudi naira biliyan 6 da miliyan 300, wani muhimmin mataki ne a yunkurin gwamnatin jihar na inganta ababen more rayuwa da hanyoyin sada yankuna. Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Namadi ya jaddada muhimmancin hanyoyin, wajen samar da ci gaban tattalin arziki, da inganta hanyoyin samar da ababen more rayuwa, da inganta rayuwar al’ummar yankin. Ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na samar da ingantattun ababen more rayuwa da za a dade ana amfana da su. Ya kuma bayyana cewa, ana sa ran ...
Salma Muhammad Salisu matashiya ce da ba ta taba mafarkin yin sana’ar kayan makulashe ba, bayan da ta kammala digirinta na farko a fannin Kididdiga (Statistics). Shekara biyar da kammala jami’a, matashiyar ta tsinci kanta cikin matsalar rashin aikin ofis, duk kuwa da karancin kwararru mata a fannin da ta karanta. Hakan ya sa ta fara tunanin yadda za ta fara sana’a domin dogara da kanta kafin Allah Ya kawo mata aiki. Daga nan ne tunanin fara kasuwancin harkar girke-girke da hada lemo ya zo mata, har ta fara ‘M&S Mannah Wassalwa Kitchen’. Labarin Salma na kama da matasan Nijeriya da dama da suka kammala manyan makarantu, amma ba su samu aikin ofis ba. Hakan ne ya sanya a baya-bayan...
Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta sanar da cewa, za a ci gaba da musayar fursunoni kamar yadda aka tsara a karkashin yarjejeniyar da aka cimmawa. A yau Alhamis ne dai kungiyar ta Hamas ta sanar da cewa za ta saki fursunoni kamar yadda yake a jadawalin da aka tsara. Tashar talabijin din Aljazira ta ambato majiyar kungiyar ta Hamas tana cewa, tawagarta tana tattaunawa d a Masar da Katar a matsayinsu na masu shiga tsakani musamman akan yadda za a kai wa mutanen Gaza, hadaddun matsugunan da za su rayu a ciki da kuma magunguna da sauran bukatu na kiwon lafiya na gaggawa. Haka nan kuma an warware matsalar kai kayan agaji da za a bari su rika shiga...
Wata Babbar Kotu a Abuja, ta ɗage yanke hukunci kan buƙatar bayar da belin Tsohon Shugaban Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, wanda ke fuskantar zargin cin hanci da rashawa. A ranar Laraba ne, Mai shari’a Chinyere Nwecheonwu, ta bayar da umarnin ci gaba da tsare Yusuf a gidan gyaran hali na Kuje har zuwa ranar 27 ga watan Fabrairu. Sojoji sun doki ’yan sanda kan kama ‘mai laifi’ Fitaccen ɗan siyasa Ahmadu Haruna Zago ya rasu A lokacin ne kotun za ta yanke hukunci kan buƙatar bayar da belinsa. Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), na zargin Yusuf da karkatar da kuɗaɗen gwamnati lokacin da yake jagorancin NHIS a shekarar 2016. Ana...
Falasdinawa sun fitar da martanin farko mai gauni kan kalaman fira ministan ‘yan mamayar Isra’ila dangane da furucinsa ga Saudiyya Kungiyar ‘yantar da Falasdinu ta yi Allah wadai da kalaman da fira ministan mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi game da kafa kasar Falasdinu a cikin kasar Saudiyya. Sakataren kwamitin zartarwa na kungiyar ‘yantar da Falasdinu Hussein Al-Sheikh ya bayyana cewa: Suna yin Allah wadai da matakin da mahukuntan yahudawan sahayoniyya suka dauka na kai cin mutunci da raina kimar masarautar Saudiyya da ‘yancinta, wanda suka yi kira da a kafa kasar Falasdinu a kasar Saudiyya, kuma wannan furuci na Rashin tunani ya yi cin karo da dokokin kasa da kasa da yarjejeniyar kasa da kasa. Ya kara da cewa:...
Sojojin mamayar Isra’ila sun fara janyewa daga yankin Netzarim da ke tsakiyar Zirin Gaza Kafofin yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun tabbatar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila za su fara ficewa daga yankin Netzarim da ke tsakiyar Zirin Gaza a daren jiya. Jaridar Yedioth Ahronoth ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta watsa rahoton cewa: Rundunar sojin mamayar Isra’ila ta ba da umarnin ficewa daga yankin Netzarim da ke tsakiyar Gaza a wani bangare na aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin kungiyar Hamas da gwamnatin mamayar Isra’ila a yankin. Jaridar ta bayyana cewa: Runduna ta 162 ta sojojin mamayar ta sake matsawa zuwa kusa da kan iyaka da kuma janyewa daga yankin Netzarim na nufin cewa, babu sojojin mamayar Isra’ila a arewacin...
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Idan Amurka ta yi barazana ga tsaron kasar Iran, to lallai Iran ta kalubalance ta Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Tattaunawa da Amurka ba wayo ba ce, kuma ba hikima ba ce, kuma gogewa ta tabbatar da hakan. Yayin ganawarsa da tawagar kwamandojin sojojin sama da na sararin samaniya na sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada cewa: Idan Amurkawa suka yi barazana wa Iran, to lallai za su fuskanci mayar da martani, idan kuma suka aiwatar da wannan barazanar, to za su fuskanci mayar da martani Iran mai gauni, kamar yadda idan suka kawo hari kan kasar Iran, za...
“Kowannen masu hada-hadar musayar kudade da aka san da zamansu da suka biya kudinsu na sake sabunta lasisinsu na 2025, an shawarce su da su rubuta zuwa ga Daraktan sashen kudi da tsare da sanya ido na Bankin, domin su karbi kudansu, da aka dakatar da biyan kudi, zuwa cikin asusunsu.” Inji Takardar Takardar ta bayar da tabbacin cewa, Bankin na CBN, har yanzu a tsaye yake akan kafarsawajen ganin ya samar da daidaito da bin ka’ida, musamman wajen gann ana gudanar da hada-hadar musayar kudade na waje a kasuwar musayar kudi.
“Wannan sauye-sauyen an yi su ne, bisa manufar bin ka’idar shigar cikin Tashar, musamman domin a dakile satar hanyar shiga cikin Tashar ga manyan motocin da ba su gabatar da takardun shedar ka’idar shiga cikin Tashar ba.” Acewar Sanarwar. Kazalika, Hukumar ta NPA, ta bayar da umranin da a gaggauta wanzr da sauyin, biyo bayan sauya wadannan sabbin matakan da Hukumar ta yi, wanda za su fara aiki a cikin watan Fabirairun 2025. “Bisa wannan sauyin, daga yanzu daukacin manyan motocin da suka tunkaro domin shiga cikin Tashar, dole su kasance suna sanye da lambar manyan motocin, domin bin ka’idojin da Hukumar ta gindaya.” Inji Sanawar. “Dole ne manyan motocin su manna kwafin takardun shedar bayar bayar da kariya wato...
Kasashen larabawa masu kawance da Amurka sun kasance a sahun gaba wajen mayarwa da shugaban kasar Amurkan martani, bayan da ya bayyana cewa kasarsa za ta shimfida ikonta a Gaza, bayan fitar da Falasdinawa da Gaza. Gabanin wannan sanarwar ta Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa ya tuntubi kasashen Jordan da Masar masu makwabtaka da Falasdinu da su karbi bakuncin mutanen Gaza na wani lokaci har zuwa sa’adda za a gyara wajen. Masar da Jordan sun yi watsi da wannan shirin da suke dauka a matsayin wata dabara ce ta fitar da Falasdinawa daga cikin kasarsu, da maye gurbinsu da yahudawa ‘yan share wuri zauna. A wani bayani da kungiyar hadin kan Larabawa ta fitar ta bayyana cewa; Abinda Trump...
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya nada Sheikh Na’im Qassim a matsayin wakilinsa a kasar Lebanon Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya nada babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah Sheikh Na’im Qassim a matsayin wakilinsa a kasar Lebanon. Marigayi Sayyid Hassan Nasrullahi tsohon babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah da ya yi shahada, a yakin baya-bayan nan kan kasar Lebanon, shi ne tsohon wakilin mai martaba Imam Khamenei a kasar Lebanon kafin shahadarsa.
Kungiyoyin kare bil’adama ta Falasdinawa guda biyu sun bada rahoton cewa gwamnatin HKI tana azabta falasdinawa da suke tsare da su. Sun kuma kara da cewa sojojin HKI tana wulakanta Fursinonin Falasdinwa suna kuma azbtar da su, musamman bayan sakin 183 daga cikinsu, a musaya ta huda. Inda Falasdinawa suka mika masu fursinoni 4 da ke hannunsu. Hukuma mai kula da fursinoni Falasdinawa ko (PPS) ta bayyana cewa a marhala ta 4 Falasdinawar 183 yahudawan suka sallama, ammam 111 daga cikinsu wadanda sojojin yahudawan suka tsare a lokacinda ake yaki na watanni 15 da su ne. Har’ila yau daga cikin wadanda aka sallama a jiya Asabar 18 daga cikinsu ta yanke masu hukuncin daurin rai da rai ne, har mutuwa....
‘Yan gwagwarmayar Siriya sun sanar da fara kaddamar da hare-haren daukan fansa kan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila Sojojin mamayar Isra’ila sun yifuruci da cewa; Sun fuskanci bude wuta daga yankin kudancin Siriya, wanda kungiyar gwagwarmayar al’ummar Siriya ta yi ikirarin kai harin wanda shi ne irinsa na farko tun bayan da sojojin mamaya suka kutsa kai cikin yankunan Siriya bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad. Sojojin mamayar Isra’ila sun tabbatar da kai wani farmaki kan rundunar sojinsu a kudancin Siriya a jiya Juma’a. A jiya ne sojojin mamayar Isra’ila suka kai farmaki kauyen Taranja da ke yankin Quneitra a kudu maso yammacin kasar Siriya, inda suka kame mutane biyu. Wakilin gidan rediyon sojojin mamayar Isra’ila ya...
Har ila yau, sun bayar da wannan shawara ce, duba da irin rawar da wadannan kalubale biyar ke takawa a lokacin kakar noma ta 2023 da kuma ta 2024. 1- Kalubalen Rashin Tsaro: Wannan matsalar na jawo wa manoma da sauran masu son zuba hannun jari a fannin koma baya, musamman duba da yadda ‘yan bindigar daji ke halaka manoma da kuma yin garkuwa da su da dama a 2024. Hakan ya haifar da hauhawar farashin kayan abinci da ya kai kimanin kashi 39.84, musamman a watan Disambar 2024. Kwararrun sun bayar da shawarar cewa, idan har ana bukatar samar da wadataccen abinci a 2025, ya zama wajbi a dauki matakan da suka dace, don kare rayukan manoma da kuma...
“Kamafanin na LNG na kasa, na bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunkasa tattalin azrikin Nijeriya da kuma kara bayar da goyon baya wajen ganin ana fitar da kaya zuwa ketare, kuma zamu tabbatar da cewa, an kara karfafa hadaka a tsakanin Hukumar da Kamfanin.” Inji Dantsoho. “Rarar da Nijeriya ta samu na hada-hada ta kai ta Naira tiriliyan 5.81 wacce ta yi daidai da dala biliyan 3.7, a zango na uku hudu a 2024.” Kamar yadda rukunonin taron bunkasa tattalin arziki na Nijeriya NESGya ruwaito. Rahoton ya sanar da cewa, an samu wannan nasarar ce, biyo bayan amfanin da Tashoshin Hukumar Jiragen Ruwa ta Kasa NPA.
Firai ministan HKI Banyamin Natanyahu Ya bada umurnin a dakatar da musayar fursinoni da kungiyoyi masu gwagwarmaya a Gaza. Bayan da Falasdinawa sun Saki mutane 8 ya zuwa yanzu, yahudawa 3 da kuma wasu yan kasar Thailand 5. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labaran yahudawan suna fadar haka. Sun kara da cewa firai ministan ya ce a dakatar da sakin fursinoni Falasdinawa 110 wadanda yakamata HKI ta sallamesu a yau. Kafin haka dai Falasdinawan sun salami wadannan fursinonin yahudawan 8 ne a zagaye uku na musayar fursinoni da kuma janyewar sojojin yahudawan daga yankunan gaza. Majiyar ofishin firay ministan ya bayyana cewa an dakatar da musayar fursinonin ne har sai abinda hali yayi. Da...
Ministan harkokin wajen Iran ya ce Tehran ba ta samu wani sako daga sabuwar gwamnatin Amurka dangane da tattaunawar janye takunkumin ba. Abbas Araghchi ya fada a ranar Laraba cewa duk wani matakin shiga irin wannan tattaunawa ya ta’alaka kan kwarin gwiwar da gwamnatin Donald Trump take da shi. Ministan ya ce Iran ta riga ta shiga tattaunawa da bangarorin Turai da ke cikin yarjejeniyar nukiliyar ta 2015, kuma tana jiran Washington ta fayyace manufofinta. “Ba a aika ko karbo wani sako na musamman ba tsakanin kasashen biyu ba; saidai abubuwan da muke ji a kafafen yada labarai kawai.” An yi ta rade-radin cewa gwamnatin Trump ta yi musayar sakonnin sirri da Iran. “A baya mun cimma yarjejeniya; Iran ta...
Sojojin mamayar Isra’ila sun tarwatsa wasu gidaje da rumbun ajiya a sansanin Tulkaram a Gabar yamma da Kogin Jordan Sojojin mamayar Isra’ila sun tarwatsa gidaje da rumbun adana kayayyaki a sansanin ‘yan gudun hijira na Tulkarm da ke Gabar yammacin Kogin Jordan a cikin daren jiya, inda haka ya yi sanadiyyar tashin gobara. Shafin watsa labaran Falasdinawa na yanar gizo ya bayyana cewa: Wasu shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun tarwatsa wani rumbun ajiyar kaya da ke kasan benen wani ginin da ke unguwar Al-Wakala a tsakiyar sansanin, lamarin da ya yi sanadin tashin gobara mai tsanani ta ya shafi wani shagon sayar da silinda gas da ke yankin da wasu gidaje da yawa...
Wani jirgin kamfanin Max Air ya tsallake rijiya da baya yayin sauka a filin jirgin Malam Aminu Kano (MAKIA) a ranar Talata da daddare. Jirgin wanda yake ɗauke da fasinjoji 53 da ma’aikata shida yana dawowa daga Jihar Legas ne lokacin da haɗarin ya faru. Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS? Mun kama mutum 46 da miyagun ƙwayoyi a Yobe — NDLEA Wani fasinja ya bayyana cewa jirgin ya rasa tayar gabansa yayin sauka a filin jirgin. Fasinjan ya yi karin bayani da cewa cewa tayar jigin ta fashe sannan ta kama da wuta a daidai lokacin da ya sauka cikin filin da misalin karfe 10:19 na dare. “Daidai lokacin da tayar ta...
Dan Majalisar Dattijan Amurka Ya Mayar Da Martani Kan Kalaman Trump Na Tilastawa Falasdinawa Gudun Hijira
Dan Majalisar Dattawan Amurka ya bayyana kiran da shugaban Amurka ya yi tilastawa Falasdinawa gudun hijira Falasdinawa da cewa kokari ne na shafe wata al’umma daga kan doron kasa Dan Majalisar Dattawan kasar Amurka Sanata Bernie Sanders a jiya Litinin ya fara mayar da martani ga shugaban Amurka Donald Trump inda ya bayyana kiran da Trump ya yi na korar Falasdinawa daga Zirin Gaza zuwa kasashen da ke makwabtaka da su a matsayin kokarin “Shafe wata al’umma ce daga kan doron kasa kuma laifin yaki ne” inda ya bukaci dukkan Amurkawa da su yi Allah wadai da wannan furuci. A ranar Asabar da ta gabata ce shugaban Amurka Donald Trump ya ba da shawarar mayar da Falasdinawa daga zirin Gaza...