Duniya Na Ci Gaba Da Mayar Wa Da Donald Trump Martani Akan Gaza
Published: 6th, February 2025 GMT
Kasashen larabawa masu kawance da Amurka sun kasance a sahun gaba wajen mayarwa da shugaban kasar Amurkan martani, bayan da ya bayyana cewa kasarsa za ta shimfida ikonta a Gaza, bayan fitar da Falasdinawa da Gaza.
Gabanin wannan sanarwar ta Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa ya tuntubi kasashen Jordan da Masar masu makwabtaka da Falasdinu da su karbi bakuncin mutanen Gaza na wani lokaci har zuwa sa’adda za a gyara wajen.
Masar da Jordan sun yi watsi da wannan shirin da suke dauka a matsayin wata dabara ce ta fitar da Falasdinawa daga cikin kasarsu, da maye gurbinsu da yahudawa ‘yan share wuri zauna.
A wani bayani da kungiyar hadin kan Larabawa ta fitar ta bayyana cewa; Abinda Trump din ya fada yana da tayar da hankali, kuma yin kira ne ga hargitsa yankin.
Kungiyar mai kasashe mambobi 22 ta kuma kara da cewa, wannan shawara da Trump ya fito da ita, tana cin karo da dokokin kasa da kasa.
Ita ma kungiyar kasashen musulmi ta ( OIC) da take wakiltar musulmin duniya miliyan 1.5, ta ce za ta ki amincewa da wannan shawarar wacce take son sauya tsarin zamantakewa na wannan yankin.
Wasu daga cikin kasashen wannan yankin abokan Amurka da su ka yi watsi da shirin na Trump na korar Falasdinawa daga Gaza sun hada Saudiyya, Jordan, Masar, Katar da Hadaddiyar Daular Larabawa, sai kuma Turkiya.
Ita ma MDD ta bayyana cewa hanyar kawo karshen batun Falasdinu shi ne abinda ta kira; Kafa kasashe biyu.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: bayyana cewa
এছাড়াও পড়ুন:
Za mu halasta kafa ƙasar Falasɗinu muddin Isra’ila ba ta cika wasu sharuɗa ba — Birtaniya
Birtaniya ta sanar da cewa muddin Isra’ila ba ta biyayya wa wasu sharuɗa ba, to kuwa a watan Satumba mai zuwa za ta amince da Falasɗinu a matsayin halastacciyar ƙasa a yayin taron Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA).
Firaiministan Birtaniya Keir Starmer ne ya bayyana haka a wani jawabi da ya gudanar a yau Talata.
Starmer ya ce za su amince da ‘yancin Falasɗinu idan har Isra’ila ba ta ɗauki hanyar kawo ƙarshen halin da ake ciki a Gaza ba, ciki har da tsagaita wuta da kuma tsarin samar da zaman lafiya na din-din-din.
Nijar da Rasha sun ƙulla yarjejeniyar makamashin nukiliya Remi Tinubu ta bai wa waɗanda harin Benuwe ya shafa tallafin Naira biliyan ɗayaA cewarsa, hakan zai tabbata “har sai idan Isra’ila ta ɗauki matakai na kawo karshen abin da ke faruwa a Gaza, ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, ta kuma tabbatar da cewa ba za a ƙwace Gaɓar Yamma ba, har ma da cimma yarjejeniyar zaman lafiya ta tsawon lokaci da za ta haifar da mafitar ƙasashe biyu.”
Firaministan ya ƙara nanata cewa babu wani bambanci tsakanin Isra’ila da Hamas kuma buƙatar da Birtaniya take da su kan Hamas suna nan — cewa dole su saki dukkan waɗanda suke garkuwa da su, su saka hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta, su kuma amince cewa ba za su saka baki a gwamnatin Gaza ba sannan su ajiye makamai.
Starmer ya ce za su ci gaba da duba lamarin da ke faruwa a Gaza gabanin taron babban zauren MDD da za a yi don ganin yadda ɓangarorin biyu suka ɗauki matakai na samar da zaman lafiya kafin ta ɗauki mataki na karshe.
Matakin da Birtaniyar ke shirin dauka na zuwa ne biyo bayan matsin lamba da Starmer ke sha a cikin ƙasar, inda ‘yan majalisu sama da 200 a makon da ya wuce, suka buƙaci ya aminta da ‘yancin Falasɗinu.
Baya ga haka kuma, ɗaruruwan mutane sun gudanar da zanga-zanga a titunan birnin Landan, suna mai kira ga Starmer ya amince da buƙatarsu na a samar da ƙasar Falasɗinu.
Ƙasashe da dama, kusan 139 sun amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa a hukumance, kuma a makon da ya wuce Faransa ta ce za ta yi shelar hakan yayin taron na Majalisar Ɗinkin Duniya da ke gudana yanzu haka.
Rikicin Gabas ta Tsakiya na ƙara ƙamari, inda al’ummar Gaza ke mutuwa a kullum , yayin da suke fuskantar matsananciyar yunwa, abinda wasu ke ganin samar da ƙasar Falasɗinu ne na mafita domin kawo ƙarshen yaƙin baki ɗaya.
A halin yanzu ƙasashen duniya sama da 100 ne ke tattauna makomar Falasdinu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa matsalar yunwa mafi muni a duniya na shirin faruwa a Gaza, saboda yadda mutane ke mutuwa wasu ke galabaita a dalilin rashin abinci.