An kama korarren jami’in tsaro da ke sayar wa ’yan ta’adda makamai
Published: 6th, March 2025 GMT
’Yan sanda sun kama wani korarren jami’in shige da fice a yayin da yake kokarin sayar da makamai Ga ’yan ta’adda.
Kwamishinan ’Yan Sanda na Babban Birnin Tarayya, Olatunji Rilwan Disu, ya bayyana cewa an kama jami’in ne a hanyarsa ta kai wa ’yan ta’addan bindigogi a yankin Zuma da ke Ƙaramar Hukumar Bwari.
Da yake jawabi a hedikwatar rundunar, CP Olatunji Rilwan, ya bayyana cewa dubun korarren jami’in tsaron ta cika ne a ranar 27 ga watan Fabrairu, 2025.
Ya bayyana cewa jami’an rundunar yaki da masu garkuwa da mutane ƙarƙashin jagorancin OC Mustapha Muhammad ne suka kama shi, bayan samun bayanan sirri.
NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Su Ga Ragi A Farashin Man Fetur Ba? Abubuwa 11 da ba a sakaci da su a Ramadan — Sheikh DaurawaDisu wanda ke bayani kan ayyukan rundunar daga watan Janairu zuwa Maris na 2025, ya ce an ƙwato wasu sabbin manyan bindigogi biyu ƙirar CZ Scorpion EVO 3 A1 a hannun wanda ake zargin.
Ya bayyana cewa rundunar tana tsare da wanda ake zargin yana amsa tambayoyi
Ya kara da cewa rundunar yaƙi da masu garkuwa da mutanen ta kuma halaka wasu ’yan bindiga bakwai a wani samamen da ta kai maɓoyar ɓata-garin a ƙauyen Gidan-Dogo da Daji Kweri da ke kan iyakar Abuja da Jihar Neja.
Ya ce an kama ’yan bindiga ɗauke da bindigogi ƙirar AK47da sauran wasu makamai a yankunan.
AA cewarsa, jimillar ’yan fashi da makami 59 da masu garkuwa da mutane tara da masu kai musu bayanai 10 ne dubu su ta cika a tsawon lokacin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Tsaro Ya bayyana cewa
এছাড়াও পড়ুন:
Ɗangote zai gina ɗakunan kwanan ɗalibai 250 a Jami’ar Ilorin
Babban attajirin Afirka kuma Shugaban Rukunin Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ɗauki nauyin gina ɗakunan kwanan ɗalibai masu gadaje 250 da Babban Masallacin Juma’a na Ilorin ya tsara a Jami’ar Ilorin da ke Jihar Kwara.
An kiyasta aikin zai ci kusan naira biliyan 1.1, kuma an ƙaddamar da shi ne domin samar da hanyar samun kuɗin kula da masallacin.
Ana sa ran kuɗaɗen haya da za a samu daga ɗaliban da za su zauna a wurin zai rika shiga asusun kula da masallacin.
Sakataren kwamitin amintattu na masallacin, Alhaji Shehu AbdulGafar, ya shaida wa manema labarai a Ilorin cewa Ɗangote ya riga ya sanar da su cewa zai ɗauki nauyin aikin gaba ɗaya.
Cire tallafin man fetur shi ne abin da ya dace —Sarki Sanusi II NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar RuwaYa ce an riga an rattaba hannu kan yarjejeniya da Jami’ar Ilorin wadda ta ba wa masallacin damar mallaka da gudanar da ɗakin kwanan ɗaliban na tsawon shekaru 21 kafin a miƙa shi ga jami’ar.
Baya ga aikin ginin, Ɗangote ya kuma yi alƙawarin bayar da tallafin Naira miliyan 5 a kowane wata domin kula da masallacin har sai an kammala aikin.
AbdulGafar ya ce wannan taimako zai rage nauyin kuɗin aikin, tare da tabbatar da ɗorewar ayyukan masallacin.
Ya ƙara da cewa ɗakin kwanan zai taimaka wajen rage matsalar ƙarancin wurin kwana ga ɗaliban jami’ar.
Shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki sun yaba wa Ɗangote, sun bayyana wannan mataki a matsayin abin koyi na yadda za a iya haɗa kai tsakanin cibiyoyin addini da ’yan kasuwa wajen ci-gaban al’umma.