“Wannan sauye-sauyen an yi su ne, bisa manufar bin ka’idar shigar cikin Tashar, musamman domin a dakile satar hanyar shiga cikin Tashar ga manyan motocin da ba su gabatar da takardun shedar ka’idar shiga cikin Tashar ba.” Acewar Sanarwar.

Kazalika, Hukumar ta NPA, ta bayar da umranin da a gaggauta wanzr da sauyin, biyo bayan sauya wadannan sabbin matakan da Hukumar ta yi, wanda za su fara aiki a cikin watan Fabirairun 2025.

“Bisa wannan sauyin, daga yanzu daukacin  manyan motocin da suka tunkaro  domin shiga cikin Tashar, dole su kasance suna sanye da lambar manyan motocin, domin bin ka’idojin da Hukumar ta gindaya.” Inji Sanawar.

“Dole ne manyan motocin su manna kwafin takardun shedar bayar bayar da kariya  wato MSS, a jikin Gilsan manyan motocin su da ke nuna alamar cewa, an yarje masu shiga cikin Tashar.” A cewar Sanarwar.

“Daga yanzu gabatar zallar shedar lambar motocin a kofar shiga Tashar, Hukumar ba za ta sake lamuntar hakan ba.” Inji Sanawar.

“Sauyin bin ka’idar za ta fara aiki ne, daga ranar 3 ga watan Fabirairun 2025, kuma Hukumar ta umarci masu hada-hadar zirga-zirgar manyan motoci a Tashar da sauran masu ruwa da tsaki, da su tabbatar da sun kiyaye wannan ka’idojin, ko kuma Hukumar, ta kakaba masu takunkumi.” Inji Sanawar.

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: shiga cikin Tashar manyan motocin

এছাড়াও পড়ুন:

Sabbin Bayanai Kan Fashe-Fashe Wasu Abubuwa A Tashar Jiragen Ruwan Kasar Iran

Gwamnan lardin Hormozgan (mai hedikwata a Bandar Abbas), Mohammad Ashouri, ya ce wani bangare na lamarin tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’i ya faru ne sakamakon keta sanarwar adana kayayyaki ne, wani bangaren kuma na da alaka da sakaci da rashin kulawa (a wajen ajiya).

AShouri, wanda ya bayyana ta hanyar faifan bidiyo a wata hira da aka watsa ta talabijin a yammacin jiya Litinin, ya bayyana sabbin alkaluman wadanda suka bata: Akwai mutanekusan 22 da suka bace, kamar yadda wasu gawarwakin mutane 22 ba a iya tantace su ba ko su waye ba.

Ya ce: “Wasu daga cikin wadanda suka jikkata an hanzarta jigilar su ta jirgin saman soja zuwa asibitin birnin Shiraz.”

Gwamnan lardin Hormozgan na Iran ya ce: An cimma wasu bincike na farko dangane da yiyuwar yin sakaci a wannan fanni, kuma ana gudanar da bincike sosai kan dukkan al’amuran da suka faru. Kuma babu wata daga kafa da za a yi ga duk wanda aka samu da yin sakaci a kan haka za a tuhume shi kamar yadda shari’a ta tanada.

 Ya ci gaba da cewa, “Ta hanyar nazarin faifan bidiyo daban-daban na aukuwar lamarin tashar jirgin ruwa ta Shahid Raja’i, an lura da cewa, an yi jigilar kaya a lokacin da lamarin ya faru, inda hayaki ke tashi, sai kuma fashewar wani abu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnan Sokoto Ya Amince Da Sauya Wa Manyan Sakatarori 25 Ma’aikatu A Jihar 
  • Ma’aikatar Sharia A Nan Iran Zata Bayyana Abinda ya farsu A Tashar Jiragen Ruwa Na Shahid Rajae
  • NEMA Ta Karɓi ‘Yan Nijeriya 203 Da Suka Maƙale A Libya
  • Dalilin da manyan ’yan siyasa ke barin NNPP — APC
  •  Manyan Malaman Roman Katolika Sun Fara Taron Zabar Paparoma
  • Riza’i: Babu Hannun  Waje A Cikin Hatsarin Da Ya Faru A Tashar Ruwa Ta Shahid Raja’i
  • Sabbin Bayanai Kan Fashe-Fashe Wasu Abubuwa A Tashar Jiragen Ruwan Kasar Iran
  • Boko Haram ta kashe masu zaman makoki 7 a Chibok
  • Sama Da Masu Sayayya Daga Ketare 220,000 Ne Suka Halarci Bikin Baje Kolin Canton Karo Na 137
  • Jagora Ya Bada Umurnin A Gudanar Bincike Mai Zurfi A Fashewar Tashar Jiragen Ruwa Na Shaheed Rajae