Hukumar Falasdinawa Ta Mayar Da Martani Kan Mafarkin Gwamnatin Mamayar Isra’ila
Published: 9th, February 2025 GMT
Falasdinawa sun fitar da martanin farko mai gauni kan kalaman fira ministan ‘yan mamayar Isra’ila dangane da furucinsa ga Saudiyya
Kungiyar ‘yantar da Falasdinu ta yi Allah wadai da kalaman da fira ministan mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi game da kafa kasar Falasdinu a cikin kasar Saudiyya.
Sakataren kwamitin zartarwa na kungiyar ‘yantar da Falasdinu Hussein Al-Sheikh ya bayyana cewa: Suna yin Allah wadai da matakin da mahukuntan yahudawan sahayoniyya suka dauka na kai cin mutunci da raina kimar masarautar Saudiyya da ‘yancinta, wanda suka yi kira da a kafa kasar Falasdinu a kasar Saudiyya, kuma wannan furuci na Rashin tunani ya yi cin karo da dokokin kasa da kasa da yarjejeniyar kasa da kasa.
Ya kara da cewa: Suna tabbatar da cewa: Kasar Falasdinu za ta kasance ce a kasar Falasdinu kawai, kuma suna jinjinawa matsayin masarautar Saudiyya da jagorancinta da al’ummarta, wadanda a kullum suke kira jaddada kare jaddada dokokin kasa da kasa da kuma kudurin samar da kasashe biyu na Falasdinawa da na yahudawan sahayoniyya a matsayin tushen samar da tsaro, kwanciyar hankali da zaman lafiya a yankin.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Falasdinu
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Tinubu ya yi wa Arewa adalci a ayyuka da mukamai — Bayo Onanuga
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) ta zargi Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da kin yin adalci wurin ayyuka da raba mukamai tsakanin Arewa da Kudancin Kasar nan.
Wadannan zarge-zarge suka sa fadar Shugaban Kasa ta hannun mai taimaka masa na musamman kan kafofin yada labarai Bayo Onanuga mayar da martani ga kungiyar ta ACF.
Ko wadanne irin martani fadar shugaban kasar ta mayar ga kungiyar?
NAJERIYA A YAU: Yadda Za A Dama Da Matan Arewa A Fannin Kimiyya DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aureWannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan