Sheikh Zakzaky: Gwagwarmayar Musulunci A Lebanon Ta Sake Jaddada Kanta
Published: 23rd, February 2025 GMT
Jagoran harkar musulunci ta Najeriya wanda ya halarci jana’izar shugaban kungiyar Hizbullah Sayyid Shahid Hassan Nasrallah a birnin Beirtu ya bayyana cewa; Yadda miliyoyin mutane su ka halarci jana’izar yana nuni da cewa, gwgawarmayar musuluncin ta sake jaddada kanta.
Sheikh Ibrahim Yakub Ibrahim El_Zakzaky ya kuma ce; Sayyid Hassan Nasrallah yana a matsayin takaitaccen hoton al’ummar musulmi ne, kuma gudanar da jana’izar da na gani yana nuni da cewa; Ruhinsa yana nan a raye cikin fagen daga.
Har ila yau jagoran ja harkar musulunci a Nigeria ya ce, abokan gaba ‘yan sahayoniya sun zaci cewa ta hanyar kisan gilla za su kawo karshen gwgawarmaya,amma abinda yake faruwa a yau, yana nuni da cewa gwgawarmaya ta kara sabunta kanta, kuma da yardar Allah wannan tafarkin zai kai ga samun nasara.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Amincewa Da Kasar Falasɗinu: Birtaniya Ta Gindaya Wa Isra’ila Sharuɗɗa
Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya shimfiɗa wa Isra’ila wasu jerin sharuɗan da ya ce idan ba ta cika ba, Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasdinu.
A ranar Talata ne Mista Starmer ya ce idan har Isra’ila ba ta cika waɗannan sharuɗa ba zuwa watan Satumba Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu.
Sharuɗɗan da firaministan ya gindaya sun haɗa da:
Amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta Bai wa Majalisar Dinkin Duniya damar sake shigar da agaji Gaza Amincewa da yuarjejeniyar zaman lafiya na dogon lokaci wanda zai ”samar da ƙasashe biyu” Tabbatar da cewa ba za a ci gaba da ƙwace Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye ba
Haka kuma Keir Starmer ya kuma sake jaddada buƙatun da Birtaniya ke da su kan Hamas da suka haɗa da:
Amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta Sakin duka sauran Isra’ilawan da take riƙe da su Amincewa ba za ta saka hannu a tafiyar da gwamnatin Gaza ba Miƙa duka makamantaBBC/Hausa