Jirgin Max Air ɗauke da fasinjoji 59 ya tsallake rijiya da baya a Kano
Published: 29th, January 2025 GMT
Wani jirgin kamfanin Max Air ya tsallake rijiya da baya yayin sauka a filin jirgin Malam Aminu Kano (MAKIA) a ranar Talata da daddare.
Jirgin wanda yake ɗauke da fasinjoji 53 da ma’aikata shida yana dawowa daga Jihar Legas ne lokacin da haɗarin ya faru.
Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS? Mun kama mutum 46 da miyagun ƙwayoyi a Yobe — NDLEAWani fasinja ya bayyana cewa jirgin ya rasa tayar gabansa yayin sauka a filin jirgin.
Fasinjan ya yi karin bayani da cewa cewa tayar jigin ta fashe sannan ta kama da wuta a daidai lokacin da ya sauka cikin filin da misalin karfe 10:19 na dare.
“Daidai lokacin da tayar ta taɓa ƙasa sai ta kama da wuta, hayaki ya turnuke a cikin jirgin wanda ya sa dole muka fita ta ƙofar fitar gaggawa.
“Yayin da muke fitowa daga jirgin, wasu ’yan kashe gobara sun riga sun fara watsa wa jirgin ruwa domin kashe wutar.”
Da yake zantawa da manema labarai, Manajan Max Air reshen Jihar Kano, Malam Bello Ramalan, ya ce ba a samu asarar rai ko jin rauni ba.
“Ina ba da haƙuri bisa matsalar da ta faru, kuma muna godiya ga Allah bisa tseratar da fasinjojin da Ya yi. Ni lafiyar fasinjoji ce a gabana.
“Dangane da bin dokokin saukar jiki, kamfaninmu ya bi ka’idojin da suka dace na yin saukar gaggawa, wanda Allah Ya sa abin ya zo da sauƙi.
“Ka’idojin sun hada da fitar da fasinjoji cikin gaggawa, killace matuƙa jirgin da kuma haɗa kai da hukumomin bincike.”
Kamfanin Max Air ya ce yana aiki tare da hukumar binciken haɗuran jiragen sama AIB da AED domin bincike kan dalilin aukuwar lamarin.
Malam Ramalan ya ce “bincike na farko ya nuna cewa matsalar tayar jirgin ce ta haddasa haɗarin.”
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Yawan Kadarorin Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Sin Ya Wuce Yuan Triliyan 90 a Lokacin Shirin Raya Kasa Na 14 Na Shekaru 5
Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya taron manema labarai a yau 17 ga wata, inda aka bayyana cewa, tun daga fara aiwatar da shiri na 14 na shekaru 5 na raya kasa, wato daga shekarar 2021 zuwa ta 2025, karfin kamfanoni mallakar gwamnati ya kara karuwa, kuma jimillar kadarorinsu ta wuce yuan tiriliyan 90, kwatankwacin sama da dalar Amurka tiriliyan 12.6.
Darektan kwamitin sa ido kan kadarori mallakar gwamnati na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, Zhang Yuzhuo ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2021 har zuwa yanzu, jimillar kadarorin kamfanoni mallakar gwamnati ta karu daga kasa da yuan tiriliyan 70, kwatankwacin dalar Amurka kimanin tiriliyan 10, zuwa sama da yuan tiriliyan 90, kwatankwacin sama da dalar Amurka tiriliyan 12.6, yayin da jimillar ribar da suka samu ta karu daga yuan tiriliyan 1.9, kwatankwacin sama da dalar Amurka biliyan 267, zuwa yuan tiriliyan 2.6, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 365. Matsakaicin karuwar jimlolin biyu a kowace shekara kuwa ya kai kashi 7.3 cikin dari da kashi 8.3 cikin dari bi da bi.
Bugu da kari, tun daga aka fara aiwatar da shirin, kamfanoni mallakar gwamnati sun biya kudin harajin da yawansu ya zarce yuan tiriliyan 10, kwatankwacin fiye da dalar Amurka triliyan 1.4, kuma darajar yawan hannun jarin da suka mikawa asusun inshorar zaman al’umma ta kai yuan tiriliyan 1.2, kwatankwacin fiye da dalar Amurka biliyan 168.(Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp