2025-10-15@12:21:25 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3342
«makaranta sun»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya ce idan bukatar hakan ta taso, zai iya janye burinsa na takarar shugaban kasa a 2027 don mara wa matashi baya. Atiku, wanda jigo ne a haɗakar jam’iyyun adawa ta ADC, ya bayyana hakan ne a wata hirarsa da BBC Hausa a ranar Laraba. NAPTIP ta kama mahaifin da ke ƙoƙarin safarar ’yarsa zuwa Iraƙi ci-rani Tinubu ya buƙaci ’yan Najeriya su daina yi wa ƙasar mummunan fata Da aka tambaye shi ko zai tsaya takarar shugaban kasa a 2027, sai ya ce lokacin tattauna hakan bai yi ba. Ya ce, “Lokacin hakan bai yi ba tukuna. Idan lokaci ya yi, zan yanke shawara. Abin da muke yi yana da amfani ga kasa....
Ya ce bambancin Nijeriya na ƙabilu, addinai da al’adu bai kamata a ɗauka a matsayin matsala ba, illa ma ya zama ƙarfin ƙasar. “Idan aka tafiyar da bambancin nan da kyakkyawan shugabanci, Nijeriya za ta samu girmamawa a duniya,” in ji shi. Obasanjo ya jaddada cewa ilimi shi ne tushen ci gaba, ba tare da la’akari da ƙabilanci, addini ko al’ada ba. Ya yaba wa Gwamnan Jihar Sakkwato Ahmed Aliyu, Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, da kuma Bishop Matthew Kukah saboda jajircewa wajen haɗa kan jama’a da zuba jari a ilimi. Bishop Kukah ya bayyana cewa cibiyar da mai bayar da tallafi Afe Babalola ya gina za ta bayar da horo kyauta ga kowa a fannin amfani da kwamfuta, ƙirƙirar manhajoji,...
Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce soke faretin zagayowar ranar ’yancin kai karo na 65 da sojoji ke yi ya ba shi damar yin lafiyayyen barci da kuma yin kyakkyawan kari a ranar Laraba. Aminiya ta rawaito cewa Gwamnatin Tarayya ta soke bikin da aka shirya domin murnar cikar Najeriya shekara 65 da samun ‘yancin kai a ranar Laraba, daya ga watan Oktoba. Tinubu ya buƙaci ’yan Najeriya su daina yi wa ƙasar mummunan fata Rashin Tsaro: An rufe makarantu sama da 180 a Arewacin Najeriya Sanarwar ta fito ne daga Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya a ranar Litinin. “Gwamnatin Tarayya na sanar da soke bikin zagayowar ranar ‘yancin kai da aka shirya domin murnar cikar ƙasar shekara 65 a ranar...

Kwara ta bukaci a sanya ido sosai, yayin da jami’an tsaro ke kara kai hare-hare a maboyar masu garkuwa da mutane
Gwamnatin jihar Kwara ta shawarci al’ummar da ke kewayen kananan hukumomin Ekiti, Ifelodun, Isin, Oke Ero, da Irepodun, da su yi taka-tsan-tsan tare da takaita harkokin a wuraren da sojoji ke aikin musamman. A wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar, Bolanle Olukoju ya fitar t cea shawarar ta biyo bayan tsaurara matakan tsaro da hadin gwiwar jami’an tsaro suka yi a garuruwan Kogi da Kwara, inda ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da su. “Muna kira ga jama’a da su yi taka-tsan-tsan tare da takaita zirga-zirgar ababen da suka dace kawai, wato don gudun kada a kama su ba tare da saninsu ba, yayin da masu garkuwa da mutane ke tserewa maboyarsu, ba...
Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana damuwarta kan yadda likitoci ke kin zuwa aiki musamman a lokutan da suke kai ziyara wuraren kiwon lafiya da ba a shirya ba. A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya ta jihar, Suleiman Isah ya fitar, ya ce kwamishinan lafiya Dr. Nafisa Muhammad Maradun ta yi gargadi ga likitoci a babban asibitin garin Gusau, bayan da suka gano rashin zuwan su a wata ziyarar ba-zata. Dakta Maradun, wadda ta kai ziyarar bazata asibitin, ta ce ta firgita da ganin cewa babu wani likita da ke bakin aiki, inda ta bayyana hakan a matsayin wani abu da ke faruwa a baya. Ta yi Allah wadai da lamarin a matsayin...
Tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Gombe, Julius Ishaya Lepes, ya rasu. Ishaya, ya riƙe mukamin Kwamishina a farkon gwamnatin Inuwa Yahaya na tsawon shekaru huɗu, amma ya yi murabus domin yin takara. Tinubu ya buƙaci ’yan Najeriya su daina yi wa ƙasar mummunan fata Rashin Tsaro: An rufe makarantu sama da 180 a Arewacin Najeriya Ya rasu bayan a ranar Laraba, bayan fama da ciwon ƙoda. Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana baƙin cikinsa kan rasuwar marigayin. A cikin saƙon ta’aziyyarsa, gwamnan ya ce Julius Ishaya, mutum ne nagari mai basira da jajircewa. Hakazalika, ya ce ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban jam’iyyar APC a jihar, musamman kafin kafa gwamnatinsa. Ya ce a lokacin da Ishaya yake Kwamishinan...
Mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatemah Mohajerani ta fayyace cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta maraba da yaki, amma tana ci gaba da shirye-shiryen tsaro mafi girma don kare kanta. Ta kara da cewa Tehran ta bayar da shawarar tattaunawa da Amurka kai tsaye a wata ganawa tare da ministocin Turai, amma wakilin Amurka Steve Witkoff ya ki isa a lokacin da aka tsara. Mai magana da yawun gwamnatin ta Iran ta kuma bayyana cewa, kasarta na ci gaba da musayar sakwanni kai tsaye da kuma a fakaice, kuma tana ci gaba da kokarinta, sai dai kuma gwamnatocin yammacin duniya su ne ke warware alkawuran da suke dauka. A nasa bangaren, sakataren majalisar kula da harkokin tsaron kasar,...
Aƙalla makarantu 188 na gwamnati aka rufe a Arewacin Najeriya sakamakon ta’azzarar matsalar tsaro. ’Yan bindiga sun kai wa wasu makarantun hari, yayin da wasu kuma yanzu ana amfani da su a matsayin mafakar ’yan gudun hijira ko sansanonin sojoji. Antoine Griezmann ya ci ƙwallo 200 a Atletico Kwamitin Shura ya dakatar da Malam Lawan Triumph daga yin wa’azi a Kano Rahotanni sun nuna cewa an rufe makarantu 39 a Zamfara, 30 a Jihar Neja, shida a Sakkwato da Kaduna, 52 a Katsina, sannan 55 a Benuwe. Adadin na iya haura haka saboda akwai yankunan da ba za a iya shiga ba don gudanar da bincike ba. Binciken bai haɗa da jihohin Borno, Yobe da Adamawa ba waɗanda Boko Haram...

A yau sharhin namu zai yi muku Magana ne game amincewa da falasdinu a matsayin kasa da wasu kasashen turai suka yi a baya bayan nan ciki har da birtaniya da kasar Faransa, sai dai amincewa da kasar falasdinu ci gaba ne babba mai cike da tarihi amma haka
A yan kwanaki kin nan kasashen duniya sun fuskanci wani lamari mai jan hankali sosai, wanda ya jaddada hakkin falasdinu na kafa kasarsa mai cin gashin kai, hakika wannan lamari ya kai kololuwasa inda ya kai ga ranar litinin da ta gabata aka kira wani taro a gegen taron majalisar dinkin duniya karo na 80 domin bayyana nuna amincewa da warware rikicin falasdinu na kafa kasashen biyu masu cin gashin kansu, Akwai abubuwa guda buyi masu gayar muhimmancin da suka sanya aka gudanar da taron kafa daula biyu, na farko hakika yazo a yan kwanaki kadan sanar da shimfida taswirar hanya na kafa kasar falasdinu mai cin gashin kai bisa iyakoyin da aka cimma a wata yuni shekara ta 67...
Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar yan jarida da bata da iyaka a karon na biyar ta shigar da kara a babban kotun duniya mai hukumta laifukan yaki ICC kan kisan da HKI take yi wa yan jaridu a bakin aikinsu a yankin gaza. A ranar talata ce aka sanar da sake shigar da karar,tun bayan harin 7 ga watan oktoba da isra’ila ta kaddamar a yankin gaza, inda ta kai hari kan yan jarida 30 daga watan mayu na 204 zuwa Augustan shekara ta 2025 ta kashe 25 daga ciki ta jikkata wasu gida biyar kuma. Darakatan sadarwa na kungiyar ta RSF Antoine bernard ya bayyana cewa isra’ila a koda yaushe tana kokari ne wajen rufe bakin yan jarida, Yace...
Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar Pakistan sun bayyana cewa sun yi gwajin makami mai linzami na fatah 4 da aka kara inganta shi, wanda zai iya kai hari mai nisan kilomita 750 ba tare da wani kuskure ba, wanda ya kara inganta karfin makamai masu linzami na kasar. Babbar nasarar da aka samu wajen gwajin makamai mai linzami da aka kara inganta shi acikin gida na fatah 4,wanda aka karfafa shi da wani tsari na zamani, makamin zai iya kaucewa harin makami mai linzami na makiya ta hanyar tsarin rungumar kasa yayin da yake kai hari, Wannan wani bangare ne na karfin sojin kasar kuma da sannu za su kara inganta karfin makami mai linzami na fatah 4,...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A cewar Wike, ana sa ran kamfanin CCECC zai kammala aikin gabanin kaddamar da fara amfani da titin nan da watan Yunin shekarar 2026. Tsarin aikin ya kunshi komai da komai, ba kawai shimfida titin ba har ma da gada mai ginshikai guda hudu. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Ina kira ga kowane ɗan Nijeriya da ya rungumi zaman lafiya, kwanciyar hankali, da haɗin kai a gidajenmu, al’ummominmu, da fadin ƙasarmu. Tare, cikin haɗin kai da ƙauna, za mu iya gina Nijeriya ta mafarkinmu. Barka da ranar ‘Yancin Kai!” in ni Shettima. Akan hakan, Shettima ya jinjinawa ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wanda ya samar da abubuwan ci gaban ƙasa, inda ya ƙara da cewa, idan aka ƙara haƙuri abubuwa za su yi kyau a Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Jihar Gombe ta sanar da fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare da kuma takaita zirga-zirgar makiyaya tsakanin kananan hukumomi daga ranar Laraba, daya ga watan Oktoban 2025. Shugaban kwamitin sasanta rikicin manoma da makiyaya na jihar, wanda kuma shi ne kwamishinan Ma’aikatar Noma da Kiwo ta jihar, Dakta Barnabas Malle, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar. Gwamna Abba ya bukaci Tinubu ya cire Kwamishinan ’Yan Sandan Kano Bayan wuya sai daɗi: Sakon Tinubu ga ’yan Najeriya Sanarwar ta ce matakin na cikin tsare-tsaren tabbatar da zaman lafiya a lokacin kakar bana, wanda manoma ke girbe amfanin gonarsu. Daga cikin ƙa’idojin da aka kafa akwai hana kiwo daga ƙarfe 6 na yamma zuwa ƙarfe...
‘Yan ƙasashen ƙetare da suka karya dokar shige da fice ta Nijeriya za su fuskanci hukunci, wanda zai iya haɗawa da tara, kora, ko kuma yiwuwar hana sake shigowa Nijeriya nan gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Argchi ya bayyana a jiya Talata kan cewa yana dab da fara tattaunawa ta karshe dangane da shirin Snapback wanda ya maida takunkuman tattalin arziki na MDD kan kasar bayan daukewa na shekaru 10. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Aragchi yana fadar haka a birnin NewYork na kasar Amurka, a jiya Talata. Ya kuma kara da cewa tattaunawarsa da babban sakataren MDD kan shirin na Snapback na karshe. Ya ce a tattaunawar zai gabatarwa Antonio Guttres matsayin kasar Iran kan wannan matakin da kasashen E3 suka dauka a kan kasar Iran. Yace wannan ya nuna irin ketan da wadan nan kasashe sukewa JMI da kuma kiyayyar da suke nuna mata....
Dakarun sojin Najeriya sun kama wasu mutum biyu da ke sanye da kayan ’yan sanda dauke da motoci biyu kirar Hilux da ke makare da tabar wiwi a jihar Taraba. Dakarun rundunar sojojin ta shida tare da hadin gwiwar jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ne suka sami nasarar cafke mutanen bayan samun sahihin bayanan sirri. Bayan wuya sai daɗi: Sakon Tinubu ga ’yan Najeriya An haifi jariri da ‘fuska biyu’ a Bauchi An cafke su ne a tashar Takum da ke karamar hukumar Wukari, suna sanye da kayan jami’an ’yan sandan kwantar da tarzoma. An gano cewa motocin biyu kirar Toyota Hilux da ake tuhuma cike suke da kayan da ake zargin tabar wiwi ce. ‘Yan...
Tsohon shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa,Muhammmad El-Baradei ya ce, Shirin na Trump akan Gaza ba komai ba ne sai kokarin tilasta larabawa su mika wuya, su kuma rusuna. Muhammad El-Baradei ya wallafa a shafinsa na X cewa; na saurari taron manema labaru a fadar White House akan Gaza, amma na fada cikin damuwa mai tsanani akan halin da Gaza take ciki da kuma makomarta, haka nan kasashen larabawa baki daya.” Tsohon shugaban hukumar makamashin Nukiliyar ta kasa da kasa ya kuma ce; Wannan Shirin ba komai ba ne, sai na neman a mika wuya a kuma rusuna, ba shiri ne na neman zaman lafiya ba.” Har ila yau, ya kuma yi suka akan yadda shugaban na kasar...
Sauran matakan sun haɗa da haramta sayar da amfanin gona kafin makota su kammala girbi da hana girbi da fitar da amfanin gona da dare, kana ya da umarci manoma da makiyaya da su guji ɗaukar doka a hannunsu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun daga ranar 1 ga Oktoba, 1960, Najeriya ta samu ’yancin kai daga Turawan mulkin mallaka. Amma tun daga wannan lokaci, al’ummar Najeriya sun kasance cike da bambance-bambancen addini da kabila da harshe da al’adu da kuma ra’ayin siyasa. Wadannan bambance-bambancen sun kasance ginshiki guda biyu: a wani lokaci suna zama jigo wajen gina ƙasa mai cike da nishaɗi da ɗimbin albarkatu, wani lokaci kuma suna haifar da tangarda wajen tafiyar da ci gaban ƙasa. Bayan shekaru 65 da samun ’yancin kai, ana iya cewa bambance-bambancen da ke tsakanin ’yan Najeriya sun taka muhimmiyar rawa wajen gina ƙasar, amma kuma sun bar gibi a fannin haɗin kai da kwanciyar hankali da samar...
Ɓangarorin biyu sun tashi baran-baran a wata tattaunawar da suka yi ƙarƙashin jagorancin Ministan ƙwadago na Nijeriya, Mohammed Dingyadi a ranar Litinin. Wannan yajin aiki na PENGASSAN ya shafi rufe ɓangarori da dama na harkar mai a Nijeriya, ciki kuwa har da babban kamfanin mai na ƙasa, NNPCL, tare da dakatar da ba matatar Ɗangote ɗanyen mai. Kungiyar ta PENGASSAN ta ja daga, inda ta bayyana cewa, “Muna kan bakar mu har yanzu, saboda mutanen mu da aka kora daga aiki, muna so dole a mayar da su.” Wannan na zuwa ne a yayin da wata kotun Abuja ta bayar da umarnin hana yajin aikin ƙungiyar ta PENGASSAN da ɗaukar matakin hana kai wa matatar Ɗangote ɗanyen...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga daukacin jama’ar kasar Sin da su yi aiki tukuru, tare da ingiza wanzar da zamanantarwa irin ta Sin. Xi, wanda kuma shi ne sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin Sin, ya yi kiran ne yayin taron bikin cika shekaru 76 da kafuwar janhuriyar jama’ar kasar Sin, wanda ya gudana yau Talata a babban dakin taruwar jama’a dake birnin Beijing. Shugaba Xi, ya jaddada cewa a gabar da yanayin harkokin duniya ke saurin sauyawa cikin sama da karni guda, dole ne a yi aiki tukuru wajen yayata akidun bai daya na dukkanin bil’adama, da aiwatar da tsarin cudanyar mabanbantan sassa, da ingiza aiwatar da shawarwarin bunkasa ci gaban...
Gwamnatin Jihar Gombe ta ƙaddamar da wani shiri na rajistar yara kyauta domin rage adadin waɗanda ke zaune gida ba tare da zuwa makaranta ba. Bincike ya nuna cewa fiye da yara 787,000 ne ba sa zuwa makaranta a faɗin jihar, wanda hakan ya sanya gwamnatin ta tashi tsaye wajen kawo sauyi a ɓangaren ilimi. Mata masu zaman kansu za su fara biyan haraji a Nijeriya An yi garkuwa da tsohon Shugaban SUBEB na Jihar Neja Uwargidan Gwamnan Gombe, Hajiya Asma’u Inuwa Yahaya, ce ta ƙaddamar da shirin a hukumance, inda ta ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na ganin kowane yaro ya samu damar karatu. A cewarta, shirin zai taimaka...
Ambaliyar ruwa a Sudan na barazana ga rayuwar dubban mutane tare da kara munana matsalolin jin kai Kogin Nilu ya mamaye yankuna da dama a Sudan, lamarin da ke barazana ga rayuwar dubban mutane. Ambaliyar ruwa ta lalata gonaki da kadarori a jihar Al-Jazirah da kewaye, lamarin da ya shafi dubban iyalai tare da barin su cikin bukatar tallafin gaggawa da matsuguni da abinci da magunguna. Haka zalika ruwan sama kamar da bakin kwarya ya dakatar da zirga-zirgar wasu jama’a a wasu yankuna, yayin hukumomin cikin gida suke kokarin rage barnar da ake amma lamarin ya foi karfinsu sakamakon karancin kayan aiki. Ambaliyar ruwan ta kara ta’azzara matsalar jin kai a birnin El Fasher da sauran garuruwa, inda mazauna garin...
“Wannan muhimmin al’amari ya sake tabbatar da himmar Gwamnatin Tarayya a fili don kiyaye walwala da haƙƙin ’yan fansho dake ƙarƙashin shirin (DBS) bisa ga manufar sabunta fata,” in ji Daraktan PTAD. Mahukunta PTAD sun nuna jin daɗinsu ga shugaba Tinubu kan amincewa da tallafin gaggawar, wanda a cewarsu hakan zai inganta jin daɗi da walwalar masu karɓar fanshon. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin soma karɓar haraji daga hannun mata masu zaman kansu waɗanda suka mayar da karuwanci sana’a. Shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan manufofin kuɗi da gyaran dokokin haraji, Taiwo Oyedele, ya ce kuɗaɗen da masu sana’ar karuwanci ke samu za a riƙe cire musu haraji a ƙarƙashin sabuwar dokar haraji ta ƙasar. Oyedele ya yi wannan bayani ne a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafin X a jiya Litinin, inda ya kawo misalan hanyoyin samun kuɗin da ake sanya wa haraji. Masanin harajin ya bayyana cewa sabbin dokokin ba su bambanta tsakanin hanyar halal ko ta haram wajen samun kuɗi ba — abin da suke dubawa kawai shi ne ko kuɗin ya fito daga...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya buƙaci jihohin Arewa 19 da su tsaya ƙyam su jajirce su yi magana da murya ɗaya kan harkokin tsaro da tattalin arziki. Gwamnan ya jagoranci taron ranar farko ta bangaren Zuba Jari da Bunƙasa Masana’antu ta Arewacin Nijeriya a ranar Litinin a otel ɗin Abuja Continental. Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa Ƙungiyar Dattawan Arewa ƙarƙashin jagorancin Farfesa Ango Abdullahi ce ta shirya taron zuba jarin. Sanarwar ta ƙara da cewa, taken taron shi ne “Buɗe Dabarun Damarmaki”, kuma ya tattaro duk masu ruwa da tsaki a sassan Arewacin Nijeriya. A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya yaba wa Ƙungiyar Dattawan Arewa bisa jajircewar da...
Mahukuntan Taliban a Afghanistan sun sanar da rufe dukkanin hanyoyin sadarwa a fadin kasar, makonni bayan da suka fara katse intanet, domin hana abin da suka bayyana a matsayin tabarbarewar tarbiyya. Wata kungiya mai sa ido kan harkokin yanar gizo ta ce yanzu baki ɗaya ana fama da rashin intanet a kasar. Wani jami’in Taliban ya ce rufewar za ta ci gaba har sai an bayar da wata sanarwa a nan gaba. Shugaban Taliban, Hibatullah Akhund-zada, ya bayar da umarnin fara cire wayoyin sadawar dake ƙarkashin kasa na intanet tun a farkon wannan wata. BBC ta rawaitu cewar kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce ya rasa ji ta hanyoyin sadarwa daga ofishinsa na Kabul, ciki har da ta wayar...
Gwamnatin tarayya ta soke bikin faretin da aka shirya gudanarwa domin murnar cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai a ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba. Wannan sanarwar ta fito ne a ranar Litinin daga Ofishin sakataren gwamnatin tarayya. “Soke faretin bikin ƴancin kai da gwamnati ta shirya gudanarwa a ranar Laraba, 1 ga Oktoba ba zai rage darajar wannan muhimmiyar rana ta tarihi ba,” in ji sanarwar. Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnati na ba da haƙuri kan wannan sauyi, amma sauran ayyukan da aka tsara domin zagayowar ranar za su ci gaba kamar yadda aka tsara. Wannan ya haɗa da jawabin shugaban ƙasa, bukukuwan al’adu, da wasu abubuwa da aka shirya.
Ƙungiyar manyan ma’aikatan kamfanonin iskar gas da fetur PENGASSAN ta ce tana nan kan bakarta na ci gaba da yajin aiki bayan kasa samun maslaha tsakaninta da matatar Dangote. Bangarorin biyu sun tashi baran-baran a tattaunawar da suka yi karkashin jagorancin ministan kwadago na Najeriya Mohammed Dingyadi a ranar Litinin. A ranar Litinin ne ƙungiyar PENGASSAN ta shiga yajin aiki na sai baba ta gani saboda matakin matatar Dangote na korar wasu ma’aikatanta kimanin 800. Babu dai wata sanarwa daga ɓangaren Matatar Dangote bayan tattaunawa da kungiyar PENGASSAN, amma a sanarwar da ta fitar ranar Lahadi ta ce ta sallamar ma’aikatan ne a wani mataki na ƙoƙarin daidaita tsarin aikin matatar. Matatar Dangote ta kuma bayyana matakin yajin aikin PENGASSAN...
Kwamitin ladabtarwa na Hukumar Ƙwallon Ƙafa FIFA ya sanar da matakin da ta ɗauka a kan tawagar ƙwallon Afirka ta Kudu, inda ta rage mata maki, sannan ta ci ta tarar kuɗi. Kwamitin ya bayyana cewa ƙasar ta karya doka ne ta hanyar amfani da ɗan wasa da bai cancanci buga wasan ba, a fafatawar da suka yi da Lesotho, inda Teboho Mokoena ya taka leda a ranar 21 ga Maris, 2025. FIFA ta ce amfani da ɗanwasan ya saɓa da sashe na 19 da kundin laifuka na hukumar, sannan ya kuma saɓa da sashe na 14 na kundin shirye-shiryen farko-farko na gasar cin kofin duniya na shekarar 2026. FIFA ta ce bayan nazarin binciken da aka gudanar, ta ƙwace...
Gwamnatin Tarayya ta wajabta wa ɗaliban da suka kammala karatu mika kundin bincikensu na ƙarshe a matsayin sharaɗi kafin a tura su aikin yi wa kasa hidima NYSC. Dokar za ta fara aiki ne daga ranar 6 ga Oktoba, 2025, kamar yadda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya sanar. Ya bayyana cewa dokar ta shafi duk ɗaliban ajin ƙarshe da suka cancanci zuwa NYSC ko da kuwa a ƙasashen waje suka kammala karatu. Bisa haka, daga yanzu babu ɗalibin da za sahalewa zuwa NYSC ba tare da ya miƙa takardar shaidar kammala binciken karshe na kammala digirinsa ba. Gwamnatin Tarayya ta ce hakan zai taimaka wajen yakar matsalar amfani da takardun kammala karatu na bogi da kuma adana ilimi...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Malaman Kwalejin Kimiyya da Ƙere-ker ta Nuhu Bamalli da ke Zariya a Jihar Kaduna sun tsunduma yajin aiki. Ƙungiyar Malaman Kwalejin Kimiyya da Ƙere-kere (ASUP) reshen makarantar ta fara yajin aikin ne daga yau Talata, 39 ga Satumba, 2025. Ƙungiyar ta fara yajin aikin ne bayan zaman da ta yi da wakilan gwamnatin jihar, inda Babban Sakataren Gwamnatin Jihar, ya buƙaci su ƙara haƙuri, yana mai alamta cewa Gwamna Uba Sani ya ba da izinin biyan buƙatunsu. Sanarwar da Kwamared Usman Shehu Suleiman ya sanya wa hannu ta ce, “Daga Talata , 30 ga Satumba 2025 mu fara yajin aiki har sai abin da hali ya yi.” An shiga taron gaggawa kan takun saƙar PENGASSAN da Matatar Dangote ASUU ta...
An sanar da wannan matakin ne a yau 29 ga watan Satumba, 2025 a karkashin dokokin FIFA, amma kuma har yanzu SAFA suna da kwanaki goma domin daukaka kara a gaban kwamitin daukaka kara na FIFA. Tawagar Afirka Ta Kudu wadda Hugo Broos ke jagoranta a halin yanzu suna kan gaba a rukuninsu na C na neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya, bayan da suka samu maki 17 daga wasanni takwas, amma kuma yanzu makin ya rikito zuwa 14 sakamakon zabtare maki 3 da hukumar FIFA ta yi musu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin...
Shugaban kasar Iran mas’ud pezishkiyan ya bayyana a wajen taron ranar yan kwana-kwana ta kasa da aka gudanar a ranar litinin a birnin Tehran cewa yayi tir da takunkumin da kasashen turai suka sake kakabawa iran, yace duk wani kokarin durkusar da kasar iran ba wani abu bane face mafarkin tsaye. Shugaban ya kara da cewa an yi amfani da sanya takunkumin ne don kara matsin lambar siyasa kan kasar iran da kuma wulakanta ta,amma tuni gwamnati ta bullo da dabaru acikin gida na nuna cirjiya kan takunkumin. Matakin na kasashen turai kan kasar iran yazo ne adaidai lokacin da ake cikin mawuyacin yanayi a yanki, da kuma nuna harshen damo game da rikicin dake faruwa a yankin Gaza ,...
Gwamnatin Nijeriya ta ayyana ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba, 2025 a matsayin ranar hutu albarkacin cikar ƙasar shekaru 65 da samun ’yancin kai. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya fitar a madadin Gwamnatin Tarayya. Ɗalibar jami’ar IBB ta faɗi ta rasu FERMA ta ƙaddamar da aikin gyara tsohuwar hanyar Kano Tunji-Ojo ya taya ’yan Najeriya da ke zaune a nan cikin gida da ƙetare murnar zagayowar wannan rana mai tarihi, kamar yadda babbar sakatariyar ma’aikatar harkokin cikin gida, Dakta Magdalene Ajani ta bayyana a ranar Litinin. Ministan ya roƙi ’yan Nijeriya da su ci gaba da rungumar kishin ƙasa, haɗin kai da kuma juriya, domin a cewarsa, su ne ababen...
Kwamitin harkokin waje da tsaron kasar Iran ya kammala dukkan shirye shirye na ficewar kasar daga yarjeniyar NPT ta hana yaduwar makaman nukliya ko na kissan kare dangi. Isma’il Riza’e shugaban kwamitin ya fadawa ya fadawa tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran kan cewa, kwamitinsa ya kammala shiri na dukkan takardu da tsare-tsaren da ake bukata don ganin kasar Iran ta fice daga yarjeniyar NPT ta hana yaduwar makaman Nukliya saboda kasashen Turai sun maida dukkan takunkuman tattalin arzikin da MDD ta dorawa kasar. Iran a Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0...
Gwamnatin Tarayya wajabta wa ɗaliban da suka kammala karatu mika kundin bincikensu na ƙarshe a matsayin sharaɗi kafin a tura su aikin yi wa kasa hidima (NYSC). Dokar za ta fara aiki ne daga ranar 6 ga Oktoba, 2025, kamar yadda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya sanar. Ya bayyana cewa dokar ta shafi duk ɗaliban ajin ƙarshe da suka cancanci zuwa NYSC ko da kuwa a ƙasashen waje suka kammala karatu. Wannan yana daga cikin sauye-sauyen da Gwamnatin Tarayya ta yi wanda ya alaƙanta aikin Yi wa Ƙasa Hidima (NYSC) da Tsarin Tattara Bayan Ilimi ma Kasa (NERD). Ranar Laraba jirgin ƙasan Abuja-Kaduna zai dawo aiki Shekara 1 bayan rushewa, har yanzu ba gyara titin Kano–Maiduguri ba Bisa...
Gwamnatin Tarayya wajabta wa ɗaliban da suka kammala karatu mika kundin bincikensu na ƙarshe a matsayin sharaɗi kafin a tura su aikin yi wa kasa hidima (NYSC). Dokar za ta fara aiki ne daga ranar 6 ga Oktoba, 2025, kamar yadda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya sanar. Ya bayyana cewa dokar ta shafi duk ɗaliban ajin ƙarshe da suka cancanci zuwa NYSC ko da kuwa a ƙasashen waje suka yi karatu. Wannan yana daga cikin sauye-sauyen da Gwamnatin Tarayya ta yi wanda ya alaƙanta aikin Yi wa Ƙasa Hidima (NYSC) da Tsarin Tattara Bayan Ilimi ma Kasa (NERD). Bisa haka, daga yanzu babu ɗalibin da za sahalewa zuwa NYSC ba tare da ya miƙa takardar shaidar kammala binciken...
A ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba, 2025, jirgin ƙasan da ke jigilar fasinja tsakanin Abuja zuwa Kaduna zai dawo aiki. Hukumar Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta ce jirgin farko a ranar zai baro tashar Idu da ke Abuja da ƙarfe 8.45 na safe, ya iso Kubwa 9.05 sannan ya sauka a tashar Rigasa da ke Kaduna da misalin 12.42 na rana. Daga Kaduna kuma jirgi zai baro Rigasa da misalin ƙarfe 2.30 na rana ya isa Kubwa da ƙarfe 8.40 na yamma. Sanarwar ta ƙara da cewa daga bisani za a ware kowace ranar Laraba domin aikin kula da lafiyar jiragen da ke aiki a layin na Abuja zuwa Kaduna. Shekara 1 bayan rushewa, har yanzu ba...
Shekara guda matafiya da direbobi a ƙauyukan Malori-Guskuri da Sabon Gari da ke Ƙaramar Hukumar Katagum a Jihar Bauchi na ci gaba da fama da wahala bayan da ruwan sama ya karya babban titin Kano–Maiduguri. A ranar 7 ga Agusta, 2024 ne ruwa ya cinye babbar hanyar a Malori-Guskuri, ya kuma yanke babban ɓangare na hanya. Mako guda bayan nan kuma wani ɓangaren ya rushe a Sabon Gari. Shekara guda da wata ɗaya bayan faruwar lamarin, wanda ya mayar wuraren da suka rushe sun koma tarkon mutuwa da ke haddasa haɗurra da suka kashe mutane da raunata wasu da dama. Wakilinmu da ya kai ziyara ya samu wani kamfanin gine-gine ya dawo Malori da kayan aikinsa. Mazauna sun tabbatar da...
Sabuwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC daga jihar Kano ta samu nasararta ta farko a gasar Firimiyar ta Nijeriya (NPFL) bayan doke Kun Khalifa daga jihar Imo a wasan mako na 5 da aka buga a birnin Aba. Wannan shi ne karon farko da ƙungiyar ta samu nasara tun bayan haurowarta gasar. A minti na 14 da fara wasan ne Kun Khalifa suka fara zura ƙwallo a ragar Barau FC. Sai dai minti biyu kacal bayan haka, Yahaya Ibrahim ya farke wa Barau FC kwallo, wanda ya buɗe musu ƙofar dawowa cikin wasan. Mataimakin Shugaban BUK Ya Buƙaci ‘Yan Siyasa Da Su Yi Koyi Da Tallafin Karatu Na Barau Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibril Ya Yi Alhinin Rasuwar...

Xi Ya Yi Kira Ga Makarantun Horar Da ‘Yan Jam’iyya Da Su Kara Azamar Kyankyashe Hazikai Da Gabatar Da Shawarwari Ga JKS
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga makarantun horar da ‘yan jam’iyya da su taka rawar gani wajen kyankyashe hazikai, tare da gabatar da shawarwari ga JKS. Xi, wanda shi ne sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin kasar Sin, ya yi kiran ne cikin wani umarni da ya gabatar ga makarantun koyar da jagoranci na ‘ya’yan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jigon jam’iyyar APC a Jihar Kano, Seyi Olorunsola, ya ce jam’iyyar za ta iya samun nasara a jihar a zaɓen 2027 ba tare da taimakon Rabiu Musa Kwankwaso ba. A baya-bayan nan an yi ta raɗe-raɗin cewa Kwankwaso zai fice daga NNPP tare da komawa jam’iyyar APC. Sojoji sun kama mai yi wa Boko Haram safarar man fetur a Borno Jami’ar Bayero ta sallami ɗalibai 57 kan maguɗin jarrabawa A taron manema labarai da ya yi a Kano ranar Lahadi, Olorunsola, ya ce Shugaba Tinubu da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, sun bai wa Kwankwaso kulawa fiye da ƙima. Ya ce APC na da manyan ’yan siyasa a Kano da za su iya tabbatar da nasarar jam’iyyar....
Dakarun Operation Haɗin Kai su kama wani mutum da ake zargi yana kai wa Boko Haram man fetur a Jihar Borno. Wanda aka kama, mai suna Thomas James, mai shekaru 54, an cafke shi ne ranar 23 ga watan Satumba a kusa da sansanin Forward Operating Base da ke Ngwom. PENGASSAN ta tsunduma yajin aiki kan korar ma’aikata a kamfanin Dangote Jami’ar Bayero ta sallami ɗalibai 57 kan maguɗin jarrabawa An same shi da kwalabe 23 na man fetur da ya ɓoye cikin jaka a lokacin da yake tafiya daga Maiduguri zuwa Gamboru Ngala. Bincike ya gano cewa yana yi wa Boko Haram safarar man fetur, sai dai wannan karon an yi nasarar kama shi. Wanda dai ba shi ne...
An kori Lage daga Benfica duk da wasa daya ya yi rashin nasara a dukkan karawa a kakar nan, kuma Mourinho ya gaji kungiyar da take ta shida a teburin Primeira Liga da tazarar maki biyar tsakani da Porto mai jan ragama. Ya fara da wasa ranar Asabar, inda suka ziyarci ABS, wadda take ta 17 a kasan teburin a babbar gasar kasar Portugal. Mourinho, dan kasar Portugal wanda ya bai wa kansa sunan ”the special one’ a 2004 zai ziyarci tsohuwar kungiyarsa wadda ya koyar sau biyu a tarihi wato Chelsea a Champions League da Benfica za ta buga ranar 30 ga watan Satumba. Jerin kungiyoyin da Mourinho ya koyar Porto (2002-04) Primeira Liga biyu, Champions League, Uefa Cup...
Yayin da yake bayani kan muhimmancin wannan shiri, Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki, ya ce: “Wannan Cibiyar wata gagarumar alama ce ta kudurin Gwamnatin Jihar Kaduna na bunkasa koyon sana’o’i, karfafa matasa, da haɓaka tattalin arziki. Yace An zaɓi fannonin sana’o’i 14 ne cikin hikima domin su magance manyan bukatun ƙwararrun ma’aikata a bangarorin gine-gine, makamashi, fasahar zamani (ICT), kula da baƙi, da harkokin ƙirƙira. Muna da yakinin cewa waɗanda suka kammala karatu a wannan Cibiyar ba kawai za su samu ayyukan yi ba ne, har ma za su zama masu dogaro da kai kuma su samar da dama ga wasu.” Shima Shugaban Cibiyar, Malam Husaini Haruna Muhammad, ya jaddada muhimmancin da horon ke...
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya sake kakabawa Iran takunkumman da aka dage wa kasar a karkashin yarjejeniyar nukiliyar ta shekarar 2015, matakin da ya biyo bayan zargin da kasashen Turai ke yi kan shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya. Kwamitin sulhun ya maido da takunkumin ne a cikin daren jiya, wanda ya hada da toshe kadarorin Iran da ke ketare, da dakatar da kwangilar sayen makamai da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, da kuma makamai masu linzami na kasar. Wannan shawarar dai na zuwa ne kwanaki biyu kacal bayan da Amurka da kawayenta suka yi watsi da daftarin kudurin da kasashen Sin da Rasha suka gabatar, na neman jinkirta matakin dawo da takunkuman. Share 0 0 votes Article Rating...
A Italiya mutane da dama sun jikkata yayin arangama tsakanin ‘yan sanda da masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu. Rahotanni sun ce kimanin mutane 10 ne suka jikkata yayin zanga-zangar ta nuna goyon bayan Falasdinu bayan da ‘yan sanda suka yi kokarin hana masu zanga-zangar da ruwan zafi da hayaki mai sa hawaye a ranar Asabar. Zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinu, wacce ta fara ranar Juma’a a Rome, Milan, Naples, da Bologna, ta bazu a ranar Asabar zuwa Florence, Pisa, Ancona, Trieste, Bari, da Alessandria. Zanga-zangar ta nuna goyon baya ga Gaza da al’ummar Palasdinu na karuwa a tashoshin jiragen ruwa, jami’o’i, makarantu, da wuraren taruwar jama’a a Italiya gabanin zanga-zangar kasa da aka shirya yi a ranar 4 ga Oktoba...
Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandare a Nijeriya (NECO) ta jaddada cewa Jihar Kano ce ta fi kowace jiha samun nasara a sakamakon jarrabawar bana, tana mai ƙaryata rahoton da jaridar Premium Times ta fitar, wanda ya ce Jihar Abia ce ke kan gaba. A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa rahoton da jaridar Premium Times ta wallafa ba shi da tushe balle makama, inda ta bayyana shi a matsayin mai cike da ruɗu da rashin inganci. Makon gobe za a dawo jigilar jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna — NRC Tun daga shekarar 1899 Faransa take haddasa mana rikici — Nijar “Rahoton ya ce bayan bincike da kuma nazarin bayanan sakamakon jarrabawar bana, Premium Times ta tabbatar...
Kasashen Afirka ta Kudu da Sin sun kaddamar da wani sabon yunkuri na zurfafa dangantakar tattalin arziki, inda Beijing ta yi alkawarin zuba jari a fannin hakar ma’adinai, makamashi, da ababen more rayuwa. Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Pretoria ke fuskantar matsanancin matsin lamba daga sabbin harajin da Amurka ta sanya mata wanda ke yin barazana ga damar da ta ke da ita a karkashin dokar bunkasar Afirka da damammaki (AGOA). Taron bunkasa harkokin kasuwanci na kasashen Afirka ta Kudu da Sin karo na 9, wanda aka gudanar a ranar Talata, ya jaddada aniyar kasashen biyu na karfafa hadin gwiwar tattalin arziki. A wajen taron, shugaban kungiyar tattalin arziki da cinikayya ta kasar Sin da Afirka ta...
Gwamnatin Jamhuriyyar Nijar ta zargi Faransa da ɗaukar shekaru tana haifar da rikice-rikice da rashin tsaro a ƙasar da maƙotanta na yankin Sahel, tun daga shekarar 1899. Firaministan Nijar, Ali Lamine Zeine, ne ya yi wannan furuci ranar Asabar yayin gabatar da jawabi a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 (UNGA 80) da ke gudana a birnin New York na ƙasar Amurka. Ɗalibi ya kashe malaminsa har lahira a Kuros Riba Ma’aikatan jinya sun tsunduma yajin aiki a Zamfara Lamine Zeine ya zargi Faransa da yin amfani da ƙungiyoyin “ta’addanci” domin tayar da rikici da haddasa rashin tsaro a ƙasarsa da maƙotanta na yankin Sahel, inda ya buƙaci mahukunta a Paris su “tuna tare da ɗukar alhakin laifukan...
Ko za ka fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinka? An haife ni a unguwar Tudun Nufawa dake Kano Municipal, na yi karatun firamare a jakara ‘Special Pramary School’, na yi sakandare a Gwammmaja 2. Sannan babban Sakandare a ‘GSS Dala’. Na yi karatun ‘Diploma’ a fannin ‘computer’, sannan na yi ‘National Diploma’ akan lafiyar hakori ‘Dental Surgery Technician’. Ya batun iyali, shin akwai ko babu? Ina da Aure, mata ta daya da ‘ya’ya biyar biyu maza uku mata. Wane rawa ka ke takawa a cikin masana’antar Kannywood? Na farko zan iya cewa ni ‘film maker’ ne, amma nafi karfi a ‘directing’. Sannan ina ‘Camera’ ina rubutu, Ina ‘acting’, Ina ‘Editing’. Me ya ja hankalinka har ka tsunduma...
Gwamnatin Jamhuriyyar Nijar ta yi zargin cewa tun daga shekarar 1899 Faransa take fafutikar tayar da rikici da haddasa rashin tsaro a ƙasar da maƙotanta na yankin Sahel. Firimanistan Jamhuriyyar Nijar, Ali Lamine Zeine, ya yi wannan caccakar ce kan Faransa a ranar Asabar yayin da yake gabatar da jawabi a Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA 80) da ke gudana a birnin New York na Amuka. Ɗalibi ya kashe malaminsa har lahira a Kuros Riba Ma’aikatan jinya sun tsunduma yajin aiki a Zamfara Lamine Zeine ya zargi Faransa da yin amfani da ƙungiyoyin “ta’addanci” domin tayar da rikici da haddasa rashin tsaro a ƙasarsa da maƙotanta na yankin Sahel, inda ya buƙaci mahukunta a Paris su “tuna tare da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yawan ribar da manyan kamfanoni na kasar Sin suke samu ta karu da kashi 0.9 cikin 100 a mizanin shekara-shekara a cikin watanni takwas na farkon shekarar 2025, lamarin da ya farfado da raguwar da aka samu da kashi 1.7 cikin 100 a tsakanin watannin Janairu zuwa Yuli, kamar yadda alkaluman hukuma suka nuna a yau Asabar. Jimillar ribar da kamfanonin da ke samun makudan kudin shiga na kasuwanci a shekara na akalla yuan miliyan 20 (kimanin dalar Amurka miliyan 2.81) ta kai kusan yuan tiriliyan 4.7 a cikin watannin takwas, a cewar hukumar kididdiga ta kasar Sin. A cikin watan Agusta, ribar da manyan kamfanonin suka samu ta farfado sosai, inda ta karu da kashi 20.4 cikin 100 a...
Ƙungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta Najeriya, reshen Jihar Zamfara, ta ce sun shiga yajin aiki na kwanaki shida a matsayin gargaɗi. Shugaban ƙungiyar, Sani Shehu, ya ce sun ɗauki wannan mataki ne domin tunatar da gwamnati batun sabon tsarin albashi na ma’aikatan lafiya. AGILE ta raba kayan karatu da sana’o’i a cibiyoyi 54 a Gombe HOTUNA: An kai gawar Arase Benin domin yi mata jana’iza Ya ce duk da cewa gwamnati ta amince da tsarin CONHESS na ma’aikatan lafiya, amma har yanzu ta kasa aiwatar da tsarin CONMESS na likitoci. A baya, ƙungiyar ta fara yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai a ranar 11 ga watan Satumba, amma ta dakatar bayan kwana ɗaya saboda alƙawarin da gwamnati ta yi...
Ƙungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta Najeriya, reshen Jihar Zamfara, ta ce sun shiga yajin aiki na kwanaki shida a matsayin gargaɗi. Shugaban ƙungiyar, Sani Shehu, ya ce sun ɗauki wannan mataki ne domin tunatar da gwamnati batun sabon tsarin albashi na ma’aikatan lafiya. AGILE ta raba kayan karatu da sana’o’i a cibiyoyi 54 a Gombe HOTUNA: An kai gawar Arase Benin domin yi mata jana’iza Ya ce duk da cewa gwamnati ta amince da tsarin CONHESS na ma’aikatan lafiya, amma har yanzu ta kasa aiwatar da tsarin CONMESS na likitoci. A baya, ƙungiyar ta fara yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai a ranar 11 ga watan Satumba, amma ta dakatar bayan kwana ɗaya saboda alƙawarin da gwamnati ta yi...
Da yake bayani a wajen taron na tunawa da shahadar sayyid Hassan Nasrullah da kuma sayyid hashim safiyyudden , babban sakatare janar din kungiyar Hizbullah, shaikh Naim qasem,yace tsayin daka da marigayi sayyid hassan nasrullah yayi ya zarce bangaranci, kuma ya zaburar da musulmi da kirsitoci da duk masu kishin addini , Yace tunani da ruhun nasarallah sunan acikin lamirin yan gwagwarmaya, kuma tafarkinsa a kungiyance yana ci gaba da tafiya akan wannan tsarin har zuwa cin nasara. Har ila yau ya kara da cewa shahadar sayyid nasarullah da zafi sosai acikin zukata, sai dai kasancewarsa acikin zukatan yan gwagwarmaya yana nan a fili. Yace tunani da ruhin sayyid Nasarullah da jininsa suna bayyana hakikanin gwagarmayar da za ta yi...
Yunkurin kasashen rasha da china na jirkinta dawowa da iran takunkumi har na tsawon wata 6 bai yi nasara ba a kwamitin tsaro na MDD saboda kasashe 4 ne suka nuna goyon bayansu da suka hada da kasashen China Rasha Pakistan da kuma Aljeriya, yayin da kasashe 9 kuma suka nuna rashin amincewa da shirin ciki harda mambobin kwamitin tsaro na mdd wato kasashen Birtaniya, Faransa da kuma Amurka. Kasar Rasha taki amincewa da wannan lamarin na dawo da takunkumin madd kan kasar iran , kamar yadda ita ma kasar china ta nuna rashin amincewarta afili da wannan mataki. Ana sa bangaren shugaban kasar iran Masud pezeshkiyaan ya bayyana cewa da sannuu Tehran za ta yi galaba akan wannan batun...
Shirin AGILE, ya raba kayan koyarwa da na sana’o’i ga cibiyoyin karatun boko na wucin gadi guda 54 a faɗin Jihar Gombe. Kwamishiniyar Ilimi ta jihar, Dakta Aishatu Umar Maigari, ce ta ƙaddamar da rabon kayan a cibiyar Community Education Resource Centre da ke Gombe. HOTUNA: An kai gawar Arase Benin domin yi mata jana’iza Mutum 7 sun rasu yayin da tirela ta murƙushe motoci a Madalla Ta ce manufar shirin shi ne bai wa ɗalibai damar koyon karatu, lissafi da kuma sana’o’i domin su samu rayuwa mai inganci. “Ba wai kawai karatu muke son su samu ba, har da ƙwarewar sana’a da za ta taimaka musu da iyalansu,” in ji ta. Shugabar shirin AGILE ta jihar, Dakta Amina Haruna...
A jawabinsa na maraba da mahalarta taron, Shugaba kuma Wakilin ofishin hukuma da ke Abuja wanda har ila yau wakilin UNESCO, na Nijeriya, Mista Mendy Albert, wanda Misa Manish Joshi ya wakilta, ya ce tsarin da akwai kwas na mako 10- ta kafar sadarwa ta zamani wanda aka kammala a watan Yuli, an shirya shi ne domin a karawa masu halartar taron yadda za su bunkasa da zamantar da ilimin koyon sana’a da fasaha. Yace TBET wata babbar madafa ce da zata iya taimakawa matasa wajen koya masu dabarun da suka dace, wadanda ta haka ne za su damar tsayawa da kafafunsu dpomin samun bunkasar zamantakewa da tattalin arziki. A nata jawabin,darekta ta fasaha da kimiyya ma’aikatar ilimi ta tarayya,...
Wane irin farin ciki za ku ji a matsayinku na iyaye, a cewa ’ya’yanku biyu sun kammala jami’a da Digiri Mai Daraja ta Ɗaya (First Class) a lokaci guda kuma daga wani kwas mai farin jini a wannan zamani na kimiyyar zamani? Wani labari mai sha’awa shi ne yadda wasu ’yan uwa biyu suka kammala karatun jami’ansu da maki iri ɗaya a matakin Digiri Mai Daraja ta Ɗaya a wannan shekarar daga jami’o’i daban-daban. Maryam Salisu da yayanta Suleiman Salisu kowannensu ya kammala karatun digirinsa na farko ne da maki 4.51 daga fannin Kimiyyar Kwamfuta, a wannan shekara ta 2025 a Jihar Katsina. A halin yanzu Suleiman ya fara aikin Yi wa Ƙasa Hidima (NYSC) a yayin da ƙanwar tasa...
Kamfanin Matatar Man Ɗangote ya sanar da dakatar da sayar da manta ga kwastomomi a kan farashin Naira. Kamfanin ya ce daga ranar Lahadi 28 ga watan nan na Satumba da muke ciki, zai koma sayar da tataccen mansa a kan farashin Dala. Wata samarwa da ya aike wa kwastomominsa ta ce, yin hakan ya zama dole saboda yarjejeniyar da suka ƙulla na sayar masa da ɗanyen man Najeriya a kan farashin Naira ya kawo ƙarshe. Kasancewar za a fara sayar masa da ɗanyen man a farashin Dala, kamfanin ya ce zai dakatar da sayar da tataccen mansa a farashin Naira. In an email sent to customers at 6:42 pm on Friday, the refinery announced that the suspension will...
Gwamnatin Jihar Gombe ta haramta amfani da littattafan karatu da ba sa iya amfani sau biyu da kuma bukukuwan ‘sign-out’ da dalibai ke gudanarwa a bayan jarrabawar kammala karatu. Daraktan Kula da Ingancin Ilimi na Ma’aikatar Ilimi ta jihar, Sa’idu Dauda Gadam, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a. Ya ce yin littattafai masu guraben amsoshi ko sarari na rubutu da ba sa sake amfani yana jefa iyaye cikin halin ƙuncin tattalin arziki, tare da haifar da asarar kuɗaɗe. Don haka, daga ranar 15 ga Satumba, 2026, dukkan makarantu za su daina amfani da irin wadannan littattafai. Yadda A ‘Daidaita Sahu’ ya ƙwace kasuwar bas da tasi Ƙasashen duniya sun ƙaurace wa Isra’ila a...
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta kirayi jakadun kasarta a kasashen Biritaniya, faransa da kuma jamus domin tuntuba, a daidai lokacin da takun tsaka tsakaninta da kasashen ke kara kamari sanadin yunkuinsu na ganin an sake dawo ma Iran da takunkuman MDD. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar yau Asabar ta ce “Bayan matakin rashin da’a da wasu kasashen Turan uku suka dauka na cin zarafin yarjeejniyar nukiliyar 2025 na JCPOA na maido da kudurorin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da aka soke, an gayyaci jakadun Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Jamus, Faransa da Birtaniya zuwa Tehran.” A ranar Juma’a, Amurka, Birtaniya, Faransa, Denmark, Girka, Panama, Saliyo, Slovenia, da Somaliya sun yi watsi da daftarin matakin da Rasha...
Ya kara da cewa wadanda ake zargin suna nan a gidan yari kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da su a gaban kotu domin hukunci. Kwamishinan ’Yansandan Jihar, CP Bello M. Sani, ya yaba wa kwazon da DPO da ’yan banga suka yi da gaggawa, inda ya jaddada muhimmancin hadin kan ‘yansanda da al’umma wajen magance miyagun laifuka. Ya kuma tabbatar wa mazauna Jihar Kebbi cewa, rundunar ‘yansandan ta jajirce wajen kawar da masu aikata laifuka da samar da yanayi mai tsaro. Daga nan sai ya bukaci jama’a da su sanya ido tare da bayar da sahihan bayanai ga jami’an tsaro domin daukar matakin gaggawa. Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, rundunar ‘yansandan Jihar Kebbi ta kama wasu...
Hukumar jin daɗin Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta sanar da farashin aikin Hajjin 2026, inda aka samu ragin kaso 9.7% cikin ɗari idan aka kwatanta da farashin Hajjin bara 2025. A cewar sanarwar da shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya fitar ranar Juma’a da daddare, alhazai daga gundumar Maiduguri–Yola (Borno, Yobe, Adamawa da Taraba) za su biya N8,118,333.67, yayin da sauran jihohin Arewa za su biya N8,244,813.67. A gefe guda kuma, alhazai daga jihohin Kudu za su biya N8,561,013.67. Wannan na nufin cewa kowanne mai niyyar tafiya Hajji a bana zai samu ragin kimanin N200,000 ƙasa da farashin 2025. EFCC Ta Kama Daraktocin NAHCON 2 Kan Zargin Karkatar Da Kuɗin Hajjin 2025 Hajji: NAHCON Ta Kammala Jigilar Kashi 77...
MDD ta kara yawan sunayen kamfanonin da su ka yi aiki tare da HKI wajen keta hakkokin al’ummar Falasdinu, ta hanyar ayyukan da suke aiwatarwa a cikin sansanonin yahudawa ‘yan share wuri zauna. A cikin rumbun bayanan MDD dai an fara zayyana sunayen kamfanoni 11, da a halin yanzu sun karu zuwa 158. Tun a shekarun baya ne dai MDD ta fara fitar da sunayen kamfanonin da suke aiki tare da HKI a wajen keta dokokin kasa da kasa da keta hakkokin al’ummar Falasdinu. Daga cikin kamfanonin bayan nan da aka kara sunayensu da akwai Heidelberg na kasar Jamus da kuma Ineco na kasar Spain. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies...
Haka kuma, ya fadi zaben shugaban kasa na 2015 ga dan takarar jam’iyyar APC, Marigayi Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a watan Yuli na wannan shekara. Akwai zazzafar muhawara kan dokar da ta bai wa Jonathan damar sake tsayawa takarar shugaban kasa a 2027, tsohon gwamnan Jihar Jigawa kuma daya daga cikin shahararrun jiga-jigan jam’iyyar PDP, Sule Lamido, a kwanan nan ya bayyana Jonathan a matsayin mafi kyawun dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2027. Lamido ya kuma yi kira da shugabancin jam’iyyar na kasa su yi kokarin tabbatar da an tsayar da shi takarar shugaban kasa a 2027. Jonathan ya ce, “Dimokuradiyya a Nahiyar Afirka na fuskantar babbar barazana, sannan ta kusa da rushewa sai dai masu...
Wanda duk zai gaya maka gaskiya musamman wanda yake zaune ko ya ke zuwa wuraren da aka samu matsalar tsaro a wasu kananan hukumomi na jihar Katsina zai fada maka cewar an samu zaman lafiya fiye da lokutan baya. An sha ruwaito wadanda wannan bala’i ya shafa suna maida martani ga masu suka sulhu da cewa duk wanda baya goyon bayan wannan sulhu dan ba a wannan yanki yake da zama ba. Sai dai kuma yin sulhu da barayin daji ba yana nufin an samu zaman lafiya dari-bisa-dari ba. Ana dai samun saukin kai hare-haren ‘yan bindigar amma ba wai an daina ba ne baki daya. To, ta ya ya al’umma za su amfana da wannan yarjejeniyar zaman sulhu da...
Gwamnatin Jihar Kano ta miƙa ƙorafe-ƙorafen da aka yi a kan Malam Shu’aibu Abubakar, wanda aka fi sani da Triumph, ga Kwamitin Shura na Jihar don ɗaukar matakin da ya dace. Sakataren Gwamnatin Jihar ne, ya tura ƙorafe-ƙorafen a ranar Juma’a, inda kwamitin ya fara zama domin sauraronsu. ’Yan Najeriya da tauraronsu ya haska a Ballon d’Or Yadda ’yan haya za su samu ragin N500,000 a shekara A cewar kwamitin, za a gayyaci masu ƙorafi da Malam Triump domin su gabatar da hujjoji. Masu ƙorafi za su fayyace abubuwan da suke tuhumar malamin, yayin da shi kuma za a ba shi damar kare kansa. Bayan haka kwamitin zai tattauna bisa ƙa’idojin shari’ar Musulunci. Sakataren kwamitin, Shehu Wada Sagagi, ya shaida...
Jami’an ’yan sanda a Jihar Ondo sun kuɓutar da wata yarinya ’yar shekara huɗu da ta ɓace tare da gano wasu masu fataucin yara da ke gudanar da ayyukan su a yankunan Jihohin Ondo, Delta da Anambra. An fara shari’ar ne a ranar 3 ga Fabrairu, 2025, lokacin da Sunday Kingsley da ke yankin Alagbaka Extension a garin Akure, ya ruwaito cewa ’yarsa Jesinta, ta ɓace ne a lokacin da take tare da mahaifiyarta Sunday Happiness. Gwamnatin Kebbi ta sake jaddada goyon bayanta ga hukumomin tsaro Naɗin Olubadan: Tinubu da manyan jami’ai sun ziyarci Ibadan Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, Olusola Ayanlade ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar kuma aka sanarwa manema labarai a Akure ranar...
Gwamnatin Tarayya ta amince da sabuwar dokar haraji wadda za ta bai wa ’yan haya damar samun ragin har Naira dubu ɗari biyar. Dokar ta amince da yi wa ’yan haya ragin kashi 20% daga harajin kudin shiga a kan kuɗin hayar da suke biya a shekara. Sojoji sun kashe ’yan ta’adda tare da ƙwato makamai a Neja Babu wata jam’iyya dana ke shirin komawa — Kwankwaso Sai dai kuma, wannnan ragin ba zai haura haura Naira 500,000 ba. Kafa sabuwar dokar A watan Agustan shekarar 2023 Shugaba Bola Tinubu ya kafa kwamitin sake fasalin haraji karkashin jagorancin Taiwo Oyedele. Bayan shekaru biyu, Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da sabbin dokoki guda hudu, wadanda shugaban kasar ya rattaba hannu...
Reform ya kuma ce yana shirin hana wani wanda ba dan Biritaniya ba damar samun walwala. Jam’iyyar ta yi ikirarin cewa shirin nasu zai yi tanadin fam biliyan 234 cikin shekaru da dama. Chancella Rachel Reebes ta ce tanadin da aka ba da shawarar “ba shi da tushe a zahiri” kuma tuni gwamnati ta fara duban hana walwalar bakin haure. Jagoran kawo sauyi a Burtaniya, Nigel Farage, ya ce bai kamata Birtaniya ta zama “bankin abinci na duniya ba”. Da yake kaddamar da sabbin manufofin, Farage ya ce: “Ba a gare mu ba ne mu bane a ce mutane na shigowa daga ko’ina cikin duniya.” A karkashin tsarin na yanzu, bakin haure na iya neman izinin zama na dindindin bayan...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Aƙalla mutum biyar ne suka rasu lokacin da ’yan bindiga suka kai hari wani Masallaci, yayin da ake tsaka da sallar Asuba a garin Yandoto da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara. Harin ya faru ne da safiyar ranar Juma’a, lamarin da ya girgiza al’ummar yankin. ‘Da albashin aikin masinja na fara kasuwancin Sahad Store’ Ganduje ya gindaya wa Kwankwaso sharadin shiga APC Shaidu sun ce maharan sun kutsa cikin Masallacin inda suka fara harbi ba tare da ƙaƙƙautawa ba, inda suka kashe mutum biyar nan take tare da jikkata wasu da dama. Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce maharan sun kuma yi awon gaba da wasu Masallata. Ya bayyana lamarin a matsayin “rashin...
Duk wani bangaren wayewa da kimiyya da fasaha za ka ga asali malaman Musulunci ne suka zo da shi, babu lokaci isasshe da mun kawo misalai masu yawa. yana daga cikin wayewar nan: tashi a sama zuwa duniyar wata, da duk “technology” din nan na zamani, harkar zane-zane, kade-kade, bushe-bushe. Amma duk aka kwashe wadannan aka bar mu sai dai halal da haram kawai! Su ma din an hana ma halal din gurbin ta, ba mu da wata magana sai dai haram! Da a ce malamai biyar za su taru, to za ka ga ba za su kago komai ba sai haram. Amma sauran malaman kasar Turai kuwa da zarar sun hadu sai ka ga sun kago wata sabuwar kira,...
Sahad Store sanannen suna ne a fadin Nijeriya, wanda yawancin wanda ya ji sunan, abin da ke fara zuwa ransa shi ne manyan shagunan sayar da kaya. Amma ba kowa ne ya san tarihin yadda ya faro ba, balle mallakinsa. Alhaji Ibrahim Mijinyawa, dan kasuwa, haifaffen unguwar Mandawari da ke birnin Kano. A cikin wata hirarsa da gidan Talabijin na Kaftan TV, a shirin Sirrin Nasarar Kasuwanci, attajirin ya bayyana yadda ya fara kasuwancinsa da yadda ya samar da sunan Sahad. Alhaji Mijinyawa wanda mahaifinsa dan unguwar Tamarmara ne da ke kusa da Mandawari, ya ce rayuwarsa cike take da dinbin abubuwan mamaki, wadanda lokaci ba zai bayar da damar ya iya zayyana su a dan takaitaccen lokaci ba. Ya...
Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ba su da matsala da yunkurin da aka ce tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso na yi na komawa jam’iyyar. Sai dai Ganduje ya ce suna da sharadin da dole sai Kwankwason ya amince da shi kafin ya shiga jam’iyyar. Aminiya ta rawaito yadda majijoyi masu tushe suka tabbatar da cewa tuni Kwankwaso ya fara tattaunawa da shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda, a kan batun komawar. Kwankwaso ya fara tattaunawa da Nentawe kan maganar komawa APC Sauya Sheƙa: Kwankwaso ya gindaya sharuɗa kafin sake komawa APC Amma a cikin wata tattaunawarsa da Sashen Hausa na BBC, ranar Juma’a Ganduje ya ce jam’iyyar tana da dokoki da sharudda,...
Sojojin Yemen sun kaddamar da mummunan farmaki kan yankin Jaffa da makami mai linzami Sojojin Yemen sun sanar a yammacin jiya Alhamis cewa; Sun kai hari da makami mai linzami kan yankin Jaffa da aka mamaye. A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Yemen ta fitar ta tabbatar da cewa: Rundunar sojinta ta kai wani harin soji mai inganci ta hanyar amfani da makami mai linzami kirar Falasdinu 2 mai dauke da kawuna da dama, inda harin ya yi mummunan barna a yankin Jaffa da aka mamaye. Sanarwar ta kara da cewa, wannan farmakin ya samu nasarar cimma manufofinsa, kuma ya sa miliyoyin garken yahudawan sahayoniyya sun tsere zuwa matsugunin karkashin kasa tare da dakatar da zirga-zirga a filin jirgin...

Yadda Sauye-Sauyen Da Aka Yi A Fannin Mai Da Iskar Gas Suka Samar Da Gagarumin Ci Gaba A Wannan Shekarar
Shugaban a kasidar da ya gabatar a wajen taron mai taken: “Ingantattun Sauye-Sauyen da Nijeriya ta kirkiro da su domin cin gajiyar albarkatun da ke a Man Fetur da Iskar Gas”, ya jaddada mahimmancin da ke a fannin Makamashi, musamman wajen kara bunkasa tattalin arzikin kasa da kuma yadda Afirka, za ta amfana. Ya ci gaba da cewa, sabon sauyen da aka samar a kasar nan a karkashin dokar Masana’antar Man Fetur ta 2021 ta samar da sabon sauyi, a bangaren gudanar da shugabanci na gari. Shugaban ya kara da cewa, Hukumar musamman a karkashin shugabancin shugaba Tinubu, ta kara zagayewa wajen sanya ido sosai a fannin na sarrafa Mai da Iskar Gas. Ya ce, Hukumar kusana a cikin shekaru...
A yau Juma’a Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo zai mika sandar sarauta ga sabon Olubadan na Ibadan na 44, Oba Rashid Adewolu Ladoja. Ana sa ran Shugaba Bola Ahmed Tinubu da tsohon mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar za su halarci wannan gagarumin biki da aka shirya yi a Ibadan babban birnin Jihar Oyo. Bikin da ba a taba yin irinsa a Ibadan ba Shugaban Hadaddiyar Kungiyar Dattawa ’Yan asalin Ibadan (CCII), Cif Ajeniyi Ajewole ya ce, dukkan attajirai ’yan asalin Ibadan an dora masu haraji daga Naira miliyan 10 zuwa sama a matsayin gudunmawarsu ga wannan biki da aka fara da addu’ar rokon Allah a ranar Litinin da ta gabata. Ya ce, “mun kammala shirin yin bukukuwan nada...
Tashar ta jihar Legas na da natukar mahimmanci a tsarin jigilar shofar da kaya a kasar nan wadda kuma ta kasance a kan gaba wajen kara bunkasa fannin tattalin arzikin kasar nan. A hirar da da manema labarai Manajin Darakta na TTP Jama Onwubuariri ya bayyana cewa, wasu daga cikin nasarorin da aka samu a bangaren na TTP tun lokacin da aka faro sun hada da, sanya ido kan sama da manyan motocin miliyan uku da ke shiga cikin Tashoshin musamman bisa nufin rage cunkoson da kuma sake fitarsu, daga cikin Tashoshin a kan lokaci Ya sanar da cewa, kirkiro da tsarin biyan kudade kan lokaci na shigar motocin cikin Tashoshin hakan ya taimaka matuka, wanda kuma bisa hadakar da...
Daga karshe,mahalarta taron sun meni a samar da wata kungiya da za ta jagoranci isar da sakon akidojin Bala Usman ga al’umma domin bai kamata a bar irin wannan kyawawan fata na Bala Usman su tafi a banza ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Alkaluma sun nuna cewa, a yankin Arewa Maso Gabas, kalubalen rashin tsaro ya dakatar da akalla yara miliyan 20, daga zuwa Makarantar Boko tare tare da kuma yadda hare-haren, suka lalata Makarantun Boko da dama da ke a yankin, wanda hakan ya janyo gagarumar tazara a tsakain yankin da kuma Kudancin kasar, tare da kuma wasu lamuran da suka shafi al’ada a fadin kasar, wanda ya kai kaso 15. Misali, yankin Arewa Maso Gabas, kacal irin wadannan hare-haren babu kakkautawa da mahara ke kai wa ya dakatar da yara miliyan biyu daga zuwa Makaranta inda hare-haren suka lalata gine-genen Makarantu da dama hakan kuma ya kara haifar da karancin Malaman. Malamai 915,913 kacal ne a matakin karatun Firamare ke koyar...
Dakarun Yaman sun sanar da cewa, sun kai wani harin soji mai inganci ta hanyar amfani da makami mai linzami na “Falasdinawa 2” mai dauke da kawuna da dama, kan wasu hare-hare da Isra’ila ta kai a yankin Jaffa da ta mamaye. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta Birgediya Janar Yahya Saree ya karanta, rundunar sojin kasar ta Yemen ta tabbatar da cewa farmakin ya cimma manufofinta tare da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin sama na Lod (Filin jirgin sama na Ben Gurion). A gefe guda kuma, Dakarun Yaman sun jaddada cewa, dakarun tsaron sama sun kame wasu jerin hare-haren Isra’ila da makamai masu linzami na sama zuwa sama, lamarin da ya dakile wani...
Kwararan bayanai na nuni da cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya fara tattaunawa da Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, kan shirin komawa jam’iyyar. Majiyoyi daga cikin APC a Kano sun bayyana cewa Kwankwaso ya rubuta wasiƙa zuwa sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa a Abuja, yana sanar da aniyarsa ta komawa jam’iyyar. An rufe wurin haƙar zinare a Kebbi Sauya Sheƙa: Kwankwaso ya gindaya sharuɗa kafin sake komawa APC Sai dai Aminiya ba ta iya tabbatar da hakan ba ya zuwa lokacin hada wannan rahoton. Wata majiya daga sakatariyar APC ta ƙasa kuma ta tabbatar da cewa ana ci gaba da tattaunawa tsakanin Kwankwaso da Farfesa Nentawe kan sauya shekar, kuma maganar ta yi nisa...
Dangin wata yarinya ’yar shekara 14 a unguwar Gangare da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, sun nemi a bi musu haƙƙi bisa zargin fyaɗen da wani mazaunin unguwar ya yi mata. Bayanai sun ce tun farko an cafke mutumin da ake zargi, Ibrahim Rawi, wanda da fi sani da Baban Siyama, amma daga bisani aka sake shi bayan wasu dattawan unguwar sun sa baki. Matashi ya kashe kakanninsa saboda abinci a Kano An kashe ’ya’yan magoya bayan Gwamna Zulum Budurwar da abin ya faru da ita da ke koyon sana’a a wajen mutumin da ake zargi, ta ce lamarin ya faru ne tsakanin ƙarfe 7 zuwa 8 na daren ranar Lahadi yayin da ake ruwan sama. A cewarta:...
Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta kama wani matashi ɗan shekara 30 mai suna Mutawakilu Ibrahim da laifin daɓa wa kakanninsa wuwa har lahira bayan wata taƙaddama kan abinci a Ƙofar Dawanau Ƙuarters da ke cikin birnin Kano. A cewar wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ta ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 25 ga watan Satumba, 2025 da misalin ƙarfe 9:30 na safe. An kashe ’ya’yan magoya bayan Gwamna Zulum Zan kare muradun Yarbawa idan aka zaɓe ni a 2027 — Atiku Rahotannin ’yan sanda sun nuna cewa, wanda ake zargin ya yi zazzafar taƙaddama da kakansa, Muhammad Dansokoto mai shekara 75 da kuma kakarsa, Hadiza Tasidi...

An Yi Bikin Nune-Nunen Hotuna Da Bidiyo Na MDD Da Bikin Kade-Kaden Fina-Finai Masu Alaka Da Zaman Lafiya A Birnin New York
Bugu da kari, mahalarta bikin sun bayyana cewa, bikin ya nuna maimaituwar tarihin MDD na shekaru 80 da suka gabata, tare da yin kira da a karfafa hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban, domin karfafa aniyar al’ummomin kasashen duniya ta kare zaman lafiya, da inganta fahimtar juna. Haka kuma, Babban rukunin gidan rediyo da talibijin na kasar Sin CMG, ya shirya wani bikin kade-kaden fina-finai masu alaka da zaman lafiya, mai taken “Hadin kai a duniya, Muryar zaman lafiya”, a cibiyar fasaha ta Lincoln da ke birnin New York na kasar Amurka a daren ranar Talata. Mataimakin sakantaren MDD mai kula da harkokin watsa labarai, Melissa Fleming, ta taya murnar bude bikin ta kafar bidiyo. Haka kuma, shugaban...
Ba madatsar ruwa ta Dashimen kadai ce ta ba da damar noma amfanin gona a cikin yankin hamada ba. A cikin shekaru goma da suka gabata, yawan madatsan ruwa da aka gina ko gyara a yankin kwarin Tarim ya kai fiye da 120, wadanda suka hada rassan kogin Tarim 144, kuma hakan ya samar da babban tsarin ban ruwa a wurin, har ya mai da sassan hamada su zama gonaki. A cikin hamadar da ke gundumar Qiemo, ana ta kara samun dausayi, inda masarar da malam Li Wenbin ya shuka ta kusan nuna. A cikin shekaru goma da suka gabata, karuwar gonaki a jihar Xinjiang ta kai fiye da muraba’in kilomita 8000, wanda ya sa jihar zamanto yankin da ya...
An gurfanar da wasu malamai biyu na wata makaranta ta Zariya Children School da ke yankin GRA Zariya, a gaban kotun majistare da ke Tudun Wada bisa zargin lalata wata ɗalibar makarantar mai shekaru 11. Jami’in da ke gabatar da ƙara a gaban kotun, ASC Mustapha Abdulkadir, ya ce malamai biyu tare da wasu uku da suka tsere, na fuskantar tuhuma kan laifin aikata lalata, wanda ya saba wa sashi na 259 na kundin laifukan Jihar Kaduna na shekarar 2017. An ceto mutum 5 bayan gini ya rufta da su a Legas Gwamnatin Katsina ta kori ma’aikata da malaman makaranta na bogi 3,488 Ya bayyana cewa, a ranar 11 ga watan Satumba wani mai suna Yahaya Aliyu, mazaunin Tudun Jukun...
Shugaban Hukumar Alhazzan Jihar Yobe, Alhaji Mai Aliyu Usman Biriri ya bayyana cewar sun gudanar da aikin Hajjin 2025 cikin nasara da kwanciyar hankali. Mai Aliyu ya bayyana hakan ne ranar Laraba a tattaunawarsa da manema labarai a babban ɗakin taron Hukumar da ke garin Damaturu dangane da yadda suka gudanar da aikin hajjin bara. An ceto mutum 5 bayan gini ya rufta da su a Legas Muhimman abubuwa 7 da Najeriya ta fada yayin jawabinta a taron MDD Shugaban ya ƙara da cewa, duk da cewar sakamakon yanayin yadda lamurran rayuwa suke ga al’umma wadda ya kai da ba su samu damar cika yawan kujerun da aka bai wa Jihar ba, amma duk da haka kusan mahajjata 1098 ne suka...
Gwamnatin Jihar Katsina ta kori ma’aikata 3,488 daga ƙananan hukumomi 34 da hukumomin ilimi na ƙananan hukumomi (LEA) bayan wani binciken tantance su ya bankado badakala. Gwamnan jihar, Dikko Radda, wanda ya karɓi rahoton kwamitin a ranar Laraba, ya ce an tantance ma’aikata 50,172, inda aka tabbatar da sahihancin 46,380, yayin da sauran suka bayyana da takardun bogi, takardun daukar aiki na ƙarya, wasu kuma suka ki bayyana a gaban kwamitin. Muhimman abubuwa 7 da Najeriya ta fada yayin jawabinta a taron MDD FBI ta sanya la’adar N15m kan dan Najeriyar da take nema ruwa a jallo An gabatar da rahoton a zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar, inda manyan jami’an gwamnati da mambobin kwamitin tantancewa suka halarta. A cewar rahoton,...
Wannan domar dai an dogara da kundin tsarin aikin gwamnatin Tarayya bisa ga sashe na 10(1) na dokar Ilimi ta (National Minimum Standards and Establishment of Institutions) ta shekarar 1985. A baya-bayan nan, an gano cewa sama da mutum 22,500 sun yi amfani da takardun bogi daga jami’o’i marasa izini a Benin da Togo daga shekarar 2019 zuwa 2023. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp