A nawa raayin hakan ba zai zama lefi ba indai har tsakani da Allah suke son junansu. Lokacin fira daban lokacin ziyara kuwa shi zuwa yake yi babu wani lokaci a yadda na fahimci topic din. Ni dai zan tsara shi ne ranar Alhamis bayan sallar la’asar zuwa sallar magrib idan ma firar ta dauki lokaci sosai kenan ya isa tunda ana waya ko chart.

A shawarce hakan sai na ga ba lefi bane duba da an zama daya kuma wannan shi ne zai kara sa nutsuwa a zukatanku na tabbacin kowannenku ya san babu wasu da suke kulawa, sannan zai rage karairayin da ake samu wajen sutura ko gidajenmu ko ababen hawanmu dama abokai ko kawayen da muke kulawa. Allah kasa mu dace.

 

Sunana Naja’atu Baffa Jihar Kaduna:

Abin da zan ce da samari masu wannan dai’ar zai iya yu wa mutane ne masu son yin bazata a komai kuma a kowanne lokaci, kuma watakila basu da wani isasshen lokaci idan ba wannan lokacin ba. Ni dai a nawa ganin lokacin daya kamata saurayi ya je zance shi ne da fari ya fara tuntubarta su tattauna ya ji lokacin da ta fi sha’awar su yi hira. A nawa tsarin na fi so saurayi ya zo da dare kamar ranar juma’a ko Alhamis, kuma in ya zo ya kamata ya dan yi satika kafin ya dawo tunda yanzu zamani ne na waya ba wai na zirga-zirga ba.

 

Sunana Umar Babanyaya Sabon-Gida Daga Karamar Hukumar Kafin Hausa A Jihar Jigawa:

Da farko dai batun ware lokaci abu ne mai matukar muhimmanci ga abin da ya shafi soyayya kwarai don haka ya kyautu samari su rinka warewa kansu lokuta na musamman domin hakan zai kara inganta alaka ta soyayya tsakanin masoya. Duk da cewa, ni ban hau gwadaben tsarin soyayya ba, amma na kan tsara lokutan kulawar da zan bawa mata musamman wadda na ga tana sona fatan Allah ya bamu mata nagari. Shawarar da zan bayar ga masoya kuwa ita ce a daina bawa budurwa fifiko kan kannnenku samari, domin mun sani cewa, akwai sabani da wata kila ka iya giftawa tsakaninsu ana da-na-sani Allah ya kyauta.

 

Sunana Zainab Zeey Ilyas Jihar Kaduna:

Yawan zuwan da samari ke yi wa ‘yan matansu ba komai yake nunawa ba face rashin tabbatacciyyar soyayya, rashin aikin yi, da dai sauran su. Tabbas akwai lokacin da ya kamata mutum ya ziyarci mutum dan’uwanshi ba ma iya tsakanin saurayi da budurwa ba, amma tun da yanzu maganar tsakanin saurayi da budurwa ce to, tabbas su ya kamata ma su fi tsara lokutan. Daya daga cikin tsare-tsaren kuwa su ne; kamar tambayar ta lokacin da ta shirya zuwan, shi namijin ya tambayeta kai tsaye lokutan da ta shirya ganinsa. Shawarar da zan ba wa maza masu yin haka ita ce; a maimakon yawan zuwan nan su tsara ranakun da suka fi dacewa don haduwar su.

 

Sunana Abubakar Usman Malam Madori:

Wannan matsala da yawa daga cikin ‘yan mata tana ci musu tuwo a kwarya, abun da ya kamata saurayi ya yi shi ne idan har ya fuskanci budurwar sa ba ta san hakan to ya kauracewa yin hakan, domin gudun wata matsala da za ta afku. Ka tabbatar ka sanarwa da masoyiyarka yayin da za ka zo wajenta idan ta amince sai ka je idan kuma ba ta amince ba sai a hakura duk lokacin da ta bukaci hakan sai a hadu. Ni a nawa ra’ayin ba mace ba, ko namiji ban cika zuwa wajen shi ba, ba tare da na sanar da shi ba, domin gudun samun sabani ko rashin samun shi cikin shiri. Ya kamata samari su zama masu tsari a kowanne lokaci ita ma sai ta fi kaunarka. A gaskiya ba za a ware wani lokaci kai-tsaye a ce wannan lokaci ne da ‘yan mata ko samari suka fi son haduwa ba. Sai dai lokacin da suka ware ko suka cimma matsaya ta haduwa ba tare da cutar da kowanne bangare ba. A matsayi na saurayi lokacin da na fi son hira lokuta biyu ne La’asar ko bayan Isha’i zuwa takwas da rabi 8:30. Shawara ita ce; idan har ka fahimci ba ta son zuwanka ba tare da ka sanar da ita ba, to ka yi kokari ka kiyaye domin hakan zai iya shafar soyayyarku ko kuma rashin fahimta a tsakani.

 

Sunana Amina Abdul’aziz Jihar Bauchi:

Ni dai a nawa ganin lokacin daya kamata saurayi ya je zance shi ne da fari ya fara gane lokacin da ta ke dawowa idan har tana aiki ko zuwa makaranta, sai ya bari in ta dawo ta huta irin da yamma sai ya je, sai kuma weekends, da kuma dare irin bayan mako biyu zuwa wata daya. A ra’ayi na zan duba lokacin da nake ba ni da aiki ko wani nauyi to, awannan lokacin zai iya zuwa. Sannan kuma zamu tattauna don mu fahimci juna, sai musan abin da zai iya fi ma zuwa gidanmu ya ci abincin dare ne da sauransu. Shawarar da zan bawa shi wannan saurayin ya fara tuntubar ita wannan budurwar shin zai iya zuwa a wannan lokacin ko kuwa?, hakan yana nuna abubuwa da yawa kamar ya nuna ka kula da ita, ka girmama ta da dai sauransu

 

Sunana Jamilu Ibrahim Yandaki Jihar Katsina:

Gaskiya a ra’ayina bai dace saurayi ya kaima budurwasa ziyarar bazata ba, saboda hakan ya kan sa a riskesu kwatsam a yanayin da, da an sanar dasu kafin zuwa ba za su yadda a tarar dasu a hakan ba. ‘Yan mata sukan yi kwalliya tare da tanadi na musamman ga samarinsu yayin da suka sanar dasu zuwansu wanda hakan ya kan kara dankon soyayya da kauna a tsakaninsu, addinin musulunci ma ya hana mutum dawowa gidansa da dare ko kwatsam ba tare da sanarwa ba don gudun taras da iyalinsa ciki halin ba zai ji dadi ba, ballantana kuma budurwa. A ra’ayina akwai lokacin da ya kamata samari su rika zuwa wajen ‘yan matansu shi ne bayan La’asar, sabida a dabi’a a wannan lokacin mutane ba su cika kasancewa a cikin wata hidima ba, sannan lokaci ne mai tsawo zuwa magrib. A matsayina na saurayi gaskiya nafi son na ziyarci budurwata duk ranar Jumu’a bayan La’asar idan hali bai samu ba to sai tsakanin magriba da Isha’i. Shawara musamman ga samari su rika tsara lokuta tare da sanarwar zuwa wajen budurwa kafin lokacin zuwa yayi, tare da bada tazara tsakanin lokuttan zuwa din ya zamana ana samu a kalla kwana hudu ko bakwai, saboda karancin zuwan yana sa ‘yan matan mararin zuwan samarin amma idan ya zamana kowane lokaci ya kan zo wajenta da sanarwa ko ba sanarwa to tabbas soyayyarsu za ta iya samun cikas. Su kuma ‘yanmatan dake da samari masu irin wannan halin su bi hanyar da ta dace wajen fadakar dasu mahimmacin sanarwa kafin zuwa.

 

Sunana Abdulrahman Jihar Sokoto, Isa LGA:

A gaskiya ni ban da ra’ayin bi ta layin su budurwa ta saboda kowa na da bukatar lokaci a cikin mu kuma gaskiya bai kamata ka zo kwatsam ba ka riske ta a cikin yanayin da ba za ta ji dadin ka ganta a haka ba, kamar yadda kai ma ba za ka so ta gane ka babu shiri ba. Eh, hakikanin gaskiya ya kamata ace akwai agenda da plan na rana da lokacin duwa wajen budurwa. Za mu zauna mu ware lokaci da rana ko sau biyu a rana ne idan hakan yayi daidai a tsakanin mu shikenan. Bai kamata ba ba tsari bane kuma bai cancanta ba babu dacewa a ciki.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Budurwa Saurayi wannan lokacin wannan lokaci

এছাড়াও পড়ুন:

Birtaniya Ta Yi Barazanar Amincewa Da Kasar Falasdinu A Watan Satumba Idan Yanayin Gaza Bai Canza Ba

Fira ministan Birtaniya ya bayyana cewa: Za su amince da kasar Falasdinu a watan Satumba idan yanayin Gaza bai canza ba

Keir Starmer ya kara da cewa, an dauki wannan matakin ne domin kare tsarin kasashe biyu, kuma kasarsa na da wani nauyi na musamman da ya rataya a wuyanta wajen ganin an samar da zaman lafiya a tsakanin kasashen biyu. Ya ce tallafin da kasarsa ke baiwa Tel Aviv yana nan daram.

Fira ministan na Burtaniya ya jaddada cewa kin amincewar da fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi na samar da kasashe biyu kuskure ne kuma kuskure ne na dabi’a da dabaru.

Ya jaddada cewa dole ne a bude mashigar kasa sannan kuma a bar manyan motocin abinci 500 shiga Gaza a kullum rana.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sojojin Yemen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Saman Lod Da Ke Jaffa Da Makami Mai Linzami July 30, 2025 Faransa Ta Bayyana Wuce Gona Da Irin ‘Yan Sahayoniyya Kan Falasdinawa Da Ayyukan Ta’addanci July 30, 2025 Jagora: Iran Ta Bayyana Karfinta Da Jajircewarta A Yakin Kwanaki 12 Ga Duniya July 29, 2025 Mutum daya Yayi Shahada 4 Sun Ji Rauna Sanadiyar Hare-Haren HKI A Lebanon July 29, 2025 EU Tace Zata Dakatar Da HKI Daga Cibiyar Bincikenta Saboda Gaza July 29, 2025 Ma’aikatar Leken Asirin JMI Ta Ce Ta Gano Shirin Kashe Manyan Mutane 35 a kasar July 29, 2025 Najeriya: Likitoci a Lagas Sun Shiga Yajin Aiki July 29, 2025  Wani Dan Majalisar Iran Ya Yi Kira Ga A Yi Siyasar Kin Gabatar Da Bayanai A Tattaunawa Da Kasashen Turai July 29, 2025 Sojojin HKI Sun Ci Gaba Da Kashe Kawunansu July 29, 2025  Kasar Holland Ta Hana MInistocin HKI Biyu Shiga Cikin Kasarta July 29, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu ya karɓi baƙuncin Abdulmumin Jibrin Kofa
  • Za a kammala shimfiɗa layin dogo daga Kaduna zuwa Kano a 2026 — Gwamnatin Tarayya
  • Malta Zata Amince da Samuwar Falasdinu a Cikin Watan Satumba Mai Zuwa
  • Tattalin arzikin Nijeriya zai ci gaba da bunƙasa har zuwa baɗi — IMF
  • Shugabannin Hukumomin Watsa Labarai Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya ga Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa Aisha Buhari
  • Birtaniya Ta Yi Barazanar Amincewa Da Kasar Falasdinu A Watan Satumba Idan Yanayin Gaza Bai Canza Ba
  • Wakilin Gidan Talabijin Na Al-Alam Ya Bayyana Yadda Shi Da Iyalansa Suka Rayu Kwanaki Biyu Babu Abinci A Gaza
  • Ambaliyar Ruwa: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Ya Ƙaru Zuwa 23 A Jihar Adamawa
  • Pezeshkiya: Iran A Shirye Take Don Mu’amala Amma Bazata Bar Hakkinta Ba
  • Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Bukaci A Kara Inganta Aikin Titin Gabasawa